39) Bai bari na sani in yana da kuɗi ko ba shi da shi. Ban ma san
bankunansa ba bare asusunsa.
Kundin Ma’aurata 42:
Tambayoyin Neman Ƙarin Haske
Baban Manar Alƙasom
Zauren Markazus Sunnah
Ina da tambayoyin neman ƙarin haske guda 2
da nake son duk mace da wasu mazan su taimaka min, za a zabi daya ne ("a-
koyaushe" ko "b- galibi" ko "c- wani lokaci" ko
"d- ba koyaushe ba"):-
1) Maigidana bai ba ni damar fadin ra'ayina a komai.
2) Bai damu da ni ba, bai saurarata, bai buƙatatar sanin komai game da ni.
3) Bai ƙin yi min bin da nake so komai
wahalarsa.
4) Bai kula damuwata.
5) Yakan tilasta ni amsar ra'ayinsa duk yadda yake.
6) Yana mu'amalla da ni kamar 'yar aiki ko nani.
7) Yana barina na yi abin da na ga dama.
8) Bai yarda ina da wani 'yanci ba sam.
.
9) Yana mummunar ladafta ni komai kasawar kuskure.
10) Yana son na gaya masa komai nake ciki, shi kuma ba abin da na sani
nasa.
11) Bai yafe wani kuskure da na yi bisa tsautsayi.
12) Bai ganin cewa iyalin rabo biyu ne, yana da daya ina da daya.
13) Duk wani nawa kai tsaye yake shiga ya yi kane-kane.
14) Abin da ya kamata na yi magana in yana wurin shi yake da alhakin yanke
hukunci.
15) Bai taimakona a wani aiki na gida, yana ganin hakan ƙasƙanci ne.
16) Duk wani abin da zan taba sai na nemi izininsa tukun.
.
17) Yakan shagaltu da ayyukansa, in ya dawo gida kuma 'ya'yansa.
18) Bai bari na ja kan wata magana, a koda yaushe maganarsa ce daidai.
19) Yana mu'amalla da ni a matsayin mai binsa ba abokiyar rayuwarsa ba.
20) Yakan ba ni haƙuri koda kuwa ni ce na yi kuskure.
21) Ina fadin fahimtata sai ya zama wani laifi da zai yi ta mita a kai.
22) Da na matso kusa da shi zai tashi ya ba ni wuri, ko ya dauki waya.
23) Yana iya ba ni komai don ya gamsar da ni.
.
24) Zai iya marina in na baƙanta masa rai.
25) Duk wani abu na gida shi kadai yake da hakkin yin magana.
26) Zai ba ni kudi bai damu da yadda nake kashewa ba.
27) In na bar gida harkarsa kawai yake yi da 'yammata.
28) In na ba shi shawara dariya kawai yake yi kamar abar banza.
29) In ba ni da lafiya sai dai 'yan uwana su kula da ni.
30) Bai bari na san yana cikin wani hali don kar hankalina ya tashi.
31) Duk abin da zan yi sai ya kishiyanta shi.
32) Sai abin da 'yan uwansa suka yi a gidan, banda damar yin magana.
33) Haka zai bar ni ya je ya yi kwanciyarsa, sai dai na kwanta ni kadai ko
tare da 'ya'yana.
34) Bai ba ni damar na tarbiyantar da 'ya'yana.
.
35) A ganinsa duk umurnin da zai yi dole a zartar nan take.
36) Bai cika murmushi a gida ba, bai ma zama a gidan.
37) Bai yaba wa duk wani ƙoƙari da na yi.
38) Bai yarda da duk abin da na yi wanda ban shawarce shi a kai ba.
39) Bai bari na sani in yana da kuɗi ko ba shi da shi. Ban ma san
bankunansa ba bare asusunsa.
40) Kansa kawai ya sani koda kuwa a shimfida ne, yana gamawa shi kenan.
41) Zai iya wulaƙanta ni ko a gaban jama'a ne.
42) Kullum kuskurena yake kallo.
43) Duk in na yi kuskure sai ya yi min kashedi da cewa zai sake ni ko zai
yo min kishiya.
44) Bai iya hararo abubuwa masu kyau da nake masa.
.
45) Bai daura min abin da ya san ba zan iya ba, ko ya ga cewa zan sha
wahala.
46) Kullum sai ya rarumo wata matsalar da zai yi ta masifa a cikin gida.
47) In ya ga dama sai ya kore ni ma daga gida.
48) Bai daukata in zai tafi wani sha'ani ko tafiyar da zai dade kuma yana
da halin yin hakan.
49) Bai jin nauyin ya sa ni wani abu koda banda lafiya.
50) Yana yi min godiya in na yi masa abu mai kyau.
51) Yakan kula da haƙƙina a
shimfida.
52) Yakan wahala in ya ga banda lafiya.
53) Bai iya cin abinci in ya ga ban ci ba.
54) Hankalisa bai kwanciya sai ya ga haƙorana.
55) Duk bayan wasu 'yan kwanaki sai ya ziyarci uwayena kamar yadda nake ziyartar
nasa.
56) In bai yi min abu ba zai yi ta ba ni haƙuri.
.
57) Yana ganin ni ce ma maigidan ko yananan ko ba yanan.
58) Ya yi alƙawarin in muka yi aure zan ci gaba
da karatu kuma ya cika.
59) Yakan dan taimaka min a zumuntata in yana da hali.
60) Ba ya bari wani ya raina ni.
61) Yana jin dadi in ya ga na yi masa kwalliya.
62) Yakan yi min kyaututtuka ba tare da wani dalili ba.
63) Shi yake sayo min kayan kwalliya.
64) Ba ya buƙatar na gode masa in ya yi min abin
alkhairi.
65) Duk hukuncin da na yanke a gidan ya yanku.
.
Waɗannan su ne 'yan tambayoyin ƙarin haske da za mu so a dan cike mana, babu laifi in
maza sun sa hannu duk da cewa kamar mata aka nema su cika, misali mutum ya
rubuta 23) b, mu kuma za mu gane abin da yake nufi, in hali ya yi za mu ji
ra'ayoyin maza game da yadda matansu suke kaikomo a cikin gida, ƙila suna yin abin da ya dace, wata ƙila kuma samsam ba su ma damu da abin da mazan suke ciki
ba, amma tabbas a wannan matattarar akwai kwamacalar da dole sai an gyara ta,
in ba haka ba kuwa to za a yi ta tabka kuskure, matsalolin aure ba tsari ko
saki barkatai, uwaye in ba su damu da kula da diyoyinsu maza a lokutan da suke
yin aure ba tare da ikon kula da matan ba, ya dace a ce uwayen matan sun sanya
idon kula da lissahi ga duk wanda ya matso kusa da diyarsu, har sai sun
tabbatar zai kula da ita, ya ba ta haƙƙoƙinta da shiri'a ta tsaga mata, aure dai ibada ne ba ado
ba ne ko yayi da mutum zai yi lokacin da ya ga dama.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.