Kundin Ma’aurata 44: Ci Gaba....


56) Kar ki yarda yaranki su san sun fi ƙarfinki, ko da a zahiri din sun fi. Kar ki riƙa gaya musu cewa za ki gaya wa ubansu kaza... Ke nan ke ba abin da za ki iya yi musu...


Kundin Ma’aurata 44: Ci Gaba....

Baban Manar Alƙasom
Zauren Markazus Sunnah

45) Dole ki nuna damuwarki a lokacin da maigidanki bayanan, yana dawowa ki nuna sakewarki, kar ki fara zayyano masa matsalolin da kuka shiga tun bai huta ba.

46) Kar ki cika nuna damuwarki a dadewar da ya yi, gwara ki ce "Na san ka damu sosai saboda nesa da mu da ka yi".

47) Ki kyauta gyaran gidaki don naki ne, daga maigidan har 'ya'yansa mataimaka ne.

48) A lokacin da abubuwa ba su kai yadda ake so ba, ki fara da waɗanda suka fi zama wajibi tukun.

49) In kina da hali ki dan riƙa canja abubuwa, kamar labulen ƙofa, ko kwanon cin abinci, ko kofin shayi da sauransu, sai ki nuna masa cewa na canja maka kaza, kar ki damu don bai yi magana ba, wallahi ya ji dadi a zimuciyarsa.
.
50) Kar ki yarda ya tsame hannunsa a kan tarbiyar 'ya'yansa, ki dage shi ma ya riƙa shiga, amma cikin hikima ba daga murya ba.

51) Wani lokaci uba in ya yi fushi yakan yi wani hukunci wanda a zahiri kuskure ne, kamar koran yaro daga gida saboda babban laifin da ya yi, ko wata iriyar ladabtarwa wace hankali ba zai dauka ba, kar ki shiga tsakani ki bari sai ya sauko.

52) Ki lura da maigidanki, in ya yi tsanani ke ki yi sauƙi, sai ki riƙa sanin sirrorin yaranki da irin matakan da za su dauka, ki jawo su a jiki, in ya susuce kamar ba namiji ba kuma kin nuna masa bai iya daukar mataki ba to nemi 'yar uwarki ta shigo ciki, ta jawo yaran kusa da ita ta riƙa mu'amalla da su, ke kuma ki tsaya sosai ki zama namijin don kyautatuwar tarbiyar diyoyinku a nan gaba.
.
53) 'Ya'ya mata ba mai iya ba su tarbiyar da ta dace kamar uwarsu, to ki mai da su ƙawayenki, amma kowa ya san matsayinsa.

54) Kar ki yarda burbushin matantaka ta yi nesa da su, mace 'yar yauƙi ce, ki koya mata sanin komai na riƙon gida tun tana ƙarama, kamar tsafta, ado da kwalliya, gwanancewa kan abinci.

55) Kar ki riƙa kawo kukan yara da zarar ubansu ya shigo, ko ya tashi daga barci, ko lokacin da zai ci abinci, ki bar shi ya huta, don hakan zai iya wargaza lamarinsa ya kasa sake miki yadda kike buƙata saboda ransa riga ya baci a wani dalili.
.
56) Kar ki yarda yaranki su san sun fi ƙarfinki, ko da a zahiri din sun fi. Kar ki riƙa gaya musu cewa za ki gaya wa ubansu kaza... Ke nan ke ba abin da za ki iya yi musu.

57) Ki kiyaye irin muryar da za ki riƙa magana da ita, ta zama murya ce mai laushi mai dadin ji, kar ki yarda ya kasance duk lokacin da kika yi masa ƙaramar murya ya san za ki nemi wani abu.

58) Ki riƙa ƙoƙarin zama da shi a inda yake, kamar lokacin cin abinci, ko kallon talabijin da sauransu.
.
59) Kar ki kuskura ki riƙa kwatanta shi da abokansa ko 'yan uwansa, in kina haka a ƙarshe ba za ki gode abin da yake miki ba.

60) In kika ga yana nuna alamar buƙatarki ki nuna masa kin fi shi buƙata, in kina cikin al'ada kar ki ce masa ba zai yuwu ya kusance ki ba, ki nuna masa tausayi na ƙarshe ki ba shi haƙuri, sannan ki nisance shi, kar ki yi abin da zai sa ya wuce gona da iri.

61) Akwai lokutan da maza kan so shimfida lura da su: In gari ya natsu kamar ruwan sama, dare, lokutan dawowa daga tafiya, bukukuwa, cin nasara a wasu abubuwa, sai lokutan shagala.
.
62) Haƙƙinsa ne ya san wasu abubuwa da suke zagaye da shi, don haka in kina da matsala da 'yan uwanki za ki iya gaya masa, sai dai akwai wasu bayanai na sirri waɗanda ba dole ne ya sani ba, ki gaya masa abubuwan da kowa zai iya ji kawai.

63) Ki girmama 'yan uwansa iya girmamawa, kar ki yarda su fahimci cewa kin fi son naki a samansu, su ma kenan bare uwayensa.

64) Ki sami lokacin zuwa wurin uwayensa da taimaka musu aiki, da ba wa maigidan shawarar ya taimake su a abubuwan da suke da buƙata ko waɗanda kika san zai iya.

65) Ki ajiye uwayensa a matsayin naki, ki yi musu duk abin da za ki iya yi wa uwayenki.
.
66) In ke ma'aikaciyar gwamnati ce kina samun kudi ko kina da sana'arki ki riƙa taimaka masa lokacin da kika sami hali, wani namijin ba zai iya roƙonki ba.

67) Wani sa'in 'yan uwan miji, ko surukanki za su riƙa cutar dake, ki fahimci cewa rayuwarki suke shiga ki yi mu'amalla da su kawai, amma gida Allah SW ya riga ya baki, kar ki yi adawa da su.

68) Ki dena nuna kina ƙyamar 'yan uwansa in za su ziyarce ku, koda kuwa kina ganin suna cutar da shi ne, ba za ki iya hana naki zuwa ba don su ba za su yi masa komai ba, mutane ba za su fahimci haka ba.

69) Ki gane cewa aure ibada ne, kuma za ki yi wa mijinki komai ne don Allah SW, saboda haka in ya saba miki ba za ki dena taimakonsa ko yi masa biyayya ba don tun asali ba don shi kike yi ba.

70) To yanzu dai ki nemi aljannarki a gidan aurenki.
.
Aure ya wuce sanya ruwa a buta, ko yi na yi bari na bari, ko dafa abinci, ko miƙa wuya a shimfida, abubuwa ne masu damar gaske kamar yadda kika gani, ba zai taba yuwuwa a ce sai da yarinya ta isa aure sannan za a zo da ita a yi mata wannan tilawar a ce duk ta haddace ba, abubuwa ne da suke buƙatar daukar dogon lokaci ana bibiyarsu kafin a kiyaye su gaba daya, in yarinya ta balaga bai nufin ta isa aure sai ta san waɗannan gaba daya, na gama da ke, kai kuma amsa min tambayoyinnan.

Post a Comment

0 Comments