Wannan bincike yana magana ne a kan yadda ake amfani
da siddabaru wajen gudanar damfara wanda ya shafi kowane ɓangare na al’umma.
Binciken ya fito da hanyoyin da ake amfani da su na damfara na gargajiya, wanda
ya ƙunshi amfani da siddabaru wajen gudanar tafiyar da
hankalin mutane, kuma wannan damfara ya taƙaita ƙwarai
da gaske a kan waɗanda ake damfara da kuma abin da ake samu wajen damfarar.
Sannan binciken ya fito da dabarun damfara na zamani wanda suka haɗa da amfani da
Intanent da kuma wayar hannu da sauran hanyoyi wajen gudanar da damfara. Sannan
kuma an fito da dabaru na zamani wajen gudanar da damfara. Wanda ya ƙusnhi
hanyoyi daban-daban da kuma amfani da na’urori na zamani wajen aiwatar da
damfara. Duk da cewa wasu mutane jahilci ne ya haifar da aka damfare, wasu kuma
kwaɗayi
ya haifar da haka. Kuma wannan damfarar ruwan dare ne game duniya, domin babu
lungun da ba a yin wannan damfarar kuma babu wasu rukuni na jama’a da suka kuɓuta daga faɗawa daga cikin
wannan damfarar. Domin kai na wayewa su kuma `yan damfara suna ƙara
fito da hanyoyi na gudanar da damfara. Binciken ya fito da dalilan da suke
haifar da damfara da kuma illolin damfara ga tattalin arzikin ƙasa
da kuma ɗaiɗaikun jama’a.
Siddabaru
Adon Damfara: Nazarin Damfara Jiya Da Yau
Hassan
Salihu
1.0
Gabatarwa
Siddabaru
da damfara ɗanjumma ne da ɗanjummai
domin kuwa damfara ba ta yi yuwa a wasu lokuta sai an haɗa
da siddabaru, domin ta hanyar siddabaru
ne ake tafiyar da hankali da tunanin wanda za a damfara ya amince da abin da za
a gabatar masa, domin a karɓi kuɗi
ko wata ƙaddara daga hannunsa. Damfara a cikin
al’ummar Hausawa daɗaɗɗiyar
sana’a ce wadda wasu mutane suka riƙa
domin samun kuɗaɗen
biyan buƙatunsu na yau da kullum. A da, akwai
dabaru da `yan damfara na wancan lokaci ke amfani da su waɗanda
suka yi daidai da zamaninsu. Yanzu kuwa damfara ta ɗauki
sabon salo, saboda sabbin hanyoyi da aka ɓullo
da su na zamani ta hanyar amfani da abubuwan da zamani ya samar domin gudanar
da wannan sana’ar ta damfara. Don haka wannan takarda za ta yi tsokaci ne a kan
damfara jiya da yau. Ma’ana takardar za ta dubi hanyoyi ko dabarun damfara na
gargajiya da kuma na zamani waɗanda ake amfani da su
wajen karɓar kuɗaɗe
a hannun mutane. Domin yana da matuƙar
wahala mutum ya yi farat ɗaya ya gane dabarun
damfara na zamani, saboda amfani da fasahar zamani yin damfara, kamar amfani da
wayar salula da kuma hanyar Intanet. Wannan damfara tana faruwa ne saboda ƙwaɗayi
da son tara abin duniya cikin sauri ko kuma rashin sani. Don haka wannan
bincike zai bi hanyoyin da suka dace domin tattaro bayanai kan abubuwan da `yan
damfara suke amfani da su wajen yawo da hankalin mutane, don su faɗa
tarkon su. Dabarun da `yan damfara suke amfani da su a wannan zamani masu sarƙaƙiya
ne, waɗanda
tilas sai an kwantar da hankali za a iya fahimtar su. Domin sukan laɓe
ga bagaruwa su harbi karsana, wato sukan yi amfani da wani tsari ko shiri wanda
hukuma ta ɓullo da shi domin aiwatar da wasu
dokoki misali, BƁN da sauransu, su damfari
jama’a ta hanyar saka tsoro a cikin zukatansu. Musamman a kan abin da ya shafi
harkar kuɗi a bankuna. Mutane da dama sun faɗa
wannan tarko a lokacin da aka fito da wannan shiri na BƁN
inda za a yi amfani da wannan damar a kwashe kuɗin
ajiyar da ke cikin asusun bankin mutum ba tare da saninsa ba.
1.1 Dabarun Bincike
Duk
wani abin da ɗan Adam zai gudanar a rayuwarsa, to
yana buƙatar a ɗora
shi bisa wani mizani da zai dace da tafarki madaidaici domin cimma nasara.
Nasarar kowani irin bincike ta dogara ne ga irin hanyoyin da aka bi wajen
tattara bayanan da za su samar da abin da ake buƙata.
Don haka an ɗora wannan bincike a kan waɗannan
hanyoyi:
1.
Hanya ta farko da za a fara bi wajen
gudanar da wannan bincike ita ce, nazartar wasu littattafai da aka wallafa waɗanda
suka danganci dabarun damfara jiya da yau. Waɗannan
littattafai ba lallai ne su yi magana kan dabarun damfara kai tsaye ba, salon
da suka yi amfani da shi a wurin fito da waɗannan
hanyoyi da za a iya cin karo da su, za su taimaka wa binciken.
2.
Binciken ya yi amfani da kundaye na digiri
na farko da na biyu da kuma na uku, domin tsamani cin karo da waɗanda
suka tsakuro wani abu daga cikin irin dabarun da `yan danfara ke amfani da su
don wajen damfara na gargajiya da na zamani. Haka kuma, binciken ya waiwayi
mujallu daban-daban har da waɗanda aka saka a yanar
gizo. Hakan ya taimaka wa wannan bincike don cimma nasara.
3.
Binciken ba zai yi tuya ya manta da albasa
ba, ya zama wajibi a tuntuɓi masu ruwa da tsaki
masana da suke da masaniya a kan irin waɗannan
hanyoyi na damfara na gargajiya da na zamani da kuma waɗanda
suka faɗa
tarkon mayaudara musamman na zamani.
1.2 Ra’in Bincike
Kasancewar
ɗabi’ar
son banza da cima zaune sun yi katutu a zukatan wasu Hausawa, wannan ya yi
sanadiyyar samar da sana’ar damfara a cikin al’umma. Don haka an a za wannan
bincike ne a kan ra’in Kwaɗayi
mabuɗin wahala
da wannan ra’in za a gudanar da wannan bincike, domin fito da wannan ra’i a fili
a cikin wannan bincike. Saboda in babu kwaɗayi
babu yadda za a yi a yi damfara.
1.3 Farfajiyar Wannnan Bincike
Wannan
bincike an iyakance shi ne a kan, “Nazarin damfara jiya da yau”. Mai bincike ya
tsayar da akalan wannan bincike a kan jiya da yau wato na gargajiya da na
zamani saboda rashin wadatar kuɗi da kuma isasshen
lokaci. Wannan ya yi wa mai bincike takunkumin fita daga muhallin binciken
saboda rashin wadataccen kuɗi da ake buƙata wajen yin zirga-zirgan farautar
neman sahihan bayanai. Domin abu ne mawuyaci ɗan
damfara ya bayyana hanyoyi da yake amfani da su wajen gudanar da wannan
sana’ar. Sannan kuma wanda aka damfara ba ya son bayanawa saboda gudun kada a
raina masa wayo da hankali a cikin jama’a.
Kafin
a zunduma cikin bayani za a fayyace abin
da ake nufi da siddabaru da damfara sannan kuma a nuna alaƙar da ke tsakaninsu domin a cire wa
idon kwantsa.
2.0 Ma’anar Siddabaru
A
hasashen Bunza, (1989) Siddabaru ba hastin bara ba ce, watao kalma ce ta Hausa
tsintsa don haka ne ma masanin ya bayyana ta da waɗannan
abubuwa:
i.
Cukurkuɗa
abubuwa ko kuma rikita su tare da ɓatar
da bakin zare. Idan mutum ya cika sassarƙe
bayani, ana cewa ya cika siddabaru a zancensa.
ii.
Wayo da dabara wajen kare kai, ko kuɓutar
da kai daga wani abu. Da za a koro ɓarawo
ya shiga nan ya fita can, har ya dubultar da masu nemansa, a ce, ya yi masu
siddabaru.
iii.
Hikima da basira ta fuskar ƙagen wasu abubuwa. Domin kuwa yau
saboda ci gaban wannan ƙarni,
da an ga jirgin sama ko rediyo ko salula (wayar hannu) ko mota a kan ce siddabarun
Bature ne.
A
ra’ayin Adamu, (2014:38-39) siddabaru shi ne, sanin yadda za a yi wasa da
hankalin mutum har ya yi mamakin yadda abubuwa ko ayyuka suka faru.
A
taƙaice dai ssiddabaru yana nufin
zunzurutun wayo da ɓatar da hankalin mutane a
kan wani abu ko a shagaltar da mutane a aiwatar da wani abu wanda bai san yadda
aka yi shi ba.
2.1.1 Ma’anar Damfara
Damfara
kalma ce Bahaushiya ba hatsin bara ce, ma’ana kalma ce ta Hausawa ba aron ta
suka yi daga wasu baƙin
al’ummu ba. Masana da manazarta al’ada sun tofa albarkacin bakin su a kan
ma’anar damfara, daga cikin akwai:
Maiyama,
(2001:27) ya bayyana damfara da cewa:
“Hanya ce da wani ƙwararre ke bi ya
mallaki abin mutum ta hanyar amfani da daɗi lafazi da nuna kwaɗayi zuwa ga wanda za a zalunta don ya yarda ya saki
jiki har ya amince don ƙwaɗayin abin da aka yi masa nuni da shi”.
Shi
kuwa Bunza, (1994:2) cewa ya yi:
“Amfani da dabara ta fuskar nuna wayo da yaudara a
kaikaice domin a karɓi dukiyar mutum. Damfara ta keɓanta ga kuɗi tsabarsu ko wasu
ƙaddarorin da ake iya kaɗarwa nan take a sami tsabar kuɗi. Da yawa takan
samo asali ne daga kawo kuɗi in yi maka kuɗi ko alƙawarin samun kuɗin cikin sauƙaƙƙar
hanya”.
Shi
kuwa Doma, (2018) ya bayyana damfara da cewa:
“Damfara hanya ce ta cuta wanda ake amfani
da ita wajen karɓar kuɗin mai son banza, ta hanyar kwaɗaitar da mutum a
kan abin da ya ke so”.
Shi
kuwa Ƙamusun Hausa (2006:92) ya bayyana
damfara da yaudara ko zamba da ake yi wa wani mutum da yake zaton zai sami wata
ƙaruwa. A yayin da Adamu, (2014:118-119)
ya kalli damfara a matsayin wata hanya da mutum zai shirya ta wayo da ƙarya domin ya karɓi
abin hannun jama’a.
A
fahimtar wannan bincike, damfara hanya ce ta karɓar
kuɗi
a hannun mutane ta amfani da siddabaru da ƙwaɗaitar
da mutum bisa samun abin duniya cikin sauƙi.
Waɗannan
hanyoyi sun haɗa da dabarun gargajiya da na zamani.
2.1.2 Dangatakar Siddabaru Da Damfara
Dangantakar
da ke tsakanin siddabaru da damfara ta jini da tsoka ce. Domin kuwa damfara ba
ta gudana sai an haɗa da siddabaru, don ta
hanyar siddabaru ne ake jawo hankali mutane har a damfare su. Wannan ya yi
daidai da bayanin da Bunza, (1989) ya kawo a kan yadda ake amfani da siddabaru
wajen yin damfara. Misali siddabarun rubutu cikin ruwa, wanda malaman tsibbu ke
yi wajen damfarar masu neman maganin zana da baduhu. Yadda suke yi shi ne za su
sami wata farar takarda su saka a cikin wani kasko da wani kasko kamar sa sai
su dinga rubuta wasu ayoyi a kaskon da aka rufe da farar takarda a ciki, a
cikin ruwa. Idan an buɗe sai ka ga takardar da
ke cikin ruwa da rubutun da aka yi a kan kasko ya fito a cikinta, cikin ruwa ɓaro-ɓaro,
kuma har ka ɗauko takardar ka karanta.
Wannan
siddabarun shi zai taimaka a yi damfara domin in ba a gwada wa mutum abin da
hankalinsa ya kasa ganewa ba, ba zai aminta ya ba da kuɗi
ba. Saboda haka, duk inda za a yi damfara to sai an fara yin siddabaru don ita
ce adon damfara. Wannan ya tabbatar da maganar Adamu, (2014) inda yak e cewa
hanyoyi nuna wayo da dabaru waɗanda sukan kauce hanulan
mutane su ne suke ɗaukar siffa ta siddabaru
a sha’ani na damfara a ƙasar
Hausa.
2.1.3 `Yan Damfara
`Yan
damfara kamar yadda Bunza, (1989:269) ya bayyana cewa su ne mutane masu yawo
wuri-wuri ba su sayar da wani magani illa yawon damfara a birane da ƙauyuka. Sukan yi wa mutum kuɗin
yabu ko su yi dabon kuɗi nan take, ko su ce za
su yi wa mutum dukiya. Wasu kan shirya mota ta kara su sihirce ta su sayar wa
mutum, sai ya shiga sai ya ga kara. Wasu kan tafi da mutum Makka da dai
sauransu.
Wannan
bayani ya yi daidai da wasu daga cikin siffofin `yan damfara domin har kamfanin
ƙarya suke shiryawa su nuna wa mutum
takarda na rigistar kamfani daga bisa su umurce shi da ya saka hannun jari,
sannan su nuna masa irin riba mai tsoka da zai sami cikin ƙanƙanen
lokaci.[1] Da
zarar hakan ta faru, shi ke nan sun washe mutum domin bayan kwana biyu idan
mutum ya dawo zai tarar da babu wannan kamfani kuma takardun ƙarya suka ba shi. Haka kuma a wannan
zamani akwai `yan damfara masu zaunawa su yi amfani da Inatent da wayar hannu
wajen aika saƙo ga mutane wanda
ya shafi harkokinsu na kuɗi a banki ko shafukan
sada zumunta ko Imel da sauransau
To, a duk lokaci da za a yi damfara tilas ne
sai an samu `yan kore domin su ne kanwa uwar gami. To wane ne ɗan
kore? Mene ne matsayinsa a wajen gudanar
da damfara.
2.1.3 Ɗan
Kore A Wajen Damfara
Ɗan kore shi ne kanwa uwar gami a
wajen aiwatar da damfara. Domin duk wani abu da ya gudana ɗan
kore ya shirya shi ya kuma aiwatar ta yadda hankalin mutane ba zai gano abin da
ake nufi ba. Don haka Bunza, (1989) ya bayyana ɗan
kore da cewa shi ne mai koro wa ɗan
damfara mutane ana karɓar dukiyarsu. A
hasashensa an samo wannan suna ne daga mai kiro jama’a. Wato ɗan
kore yakan kasance namiji ko mace, babba ko yaro, ɗan
gida ko baƙo wanda zai dinga
taimaka wa ɗan damfara a kaikaice ba da sanin
mutane ne ba. Kusan duk abin da ke bayan fage da sanin ɗan
kore kuma duk wata damfara da za a yi a bayan fage ko abu ya faɗo
daga sama ko a ji ƙarar
shi da dai sauran su duk da hannun ɗan
kore. Ɗan kore dole ya zama mai wayo, mai natsuwa
da gaggawa ga aikata duk wani aikinsa ba da ɓata
lokaci ba. Kuma an fi son ɗan kore ya zama ba
sananne ba ne a idon mutanen gari. Idan so samu ne a wani lokaci an fi son baƙo, a wani lokaci ko ɗan
gari sai a ƙulla da shi indai
ba sananne ba ne a idon jama’a. Ɗan
kore yakan yi shiga daban-daban, wani lokaci yakan yi shigar ƙauyawa, yakan kuma saka kayan Fulani,
a wani lokaci yakan yi shigar yara gayu ko ya yi shiga ta siffar malamai da dai
sauransu. Idan ɗan kore ya ƙware sosai babu yadda za a yi jama’a
su gane cewa haɗin baki aka yi da shi a
cuce su. Idan ɗan kore ya iya taka rawarsa sosai ɗan
damfara zai tara kuɗi mai yawa. Bunza,
(1989).
2.1.4 Matsayin Ɗan Kore A Damfara
Ɗan kore yana da muhimmancin ƙwarai da gaske wajen gudanar da
damfara. Shi ne suke fara nuna wa mutane cewa abin da aka nuna masu gaskiya
musamman ta hanyar siddabarun dandali.
Idan ɗan damfara ya nuna wa mutane kuɗi
a bayyane yana cewa, “Ina mai naira ɗari
ko ɗari
biyar”, alhali a hannunsa akwai naira dubu ko dubu biyar. Cikin ɗan
lokaci idan naira ɗari ce sai ka ga wani ya
zo ya ce, ‘na saya naira dubu’. Bayan ya riƙe
hannusa sai ya ce, “Malam ban sayar ba”. Bayan ya saki hannunsa sai ka ga naira
dubu ta koma dubu biyar na take.
A
ko da yaushe, irin wannan damfara mai suna, “Marmashe” duk wanda ka ga ya faye
cin ta ɗan
kore ne. kuma in mutum ba ɗan kore ba ne ko ya ci
ana son a jawo hankalinsa ne a yaye shi sosai, shigo-shigo ba zurfi ne kawai.
Kuma duk wanda ka ga ya riƙe
hannunsa sai yawan kuɗin ya karu shi ma ɗan
kore ne, shi ya miƙa
kuɗin
a yayin da yake haɗa jiki cikin ɗan
lokaci (Bunza, 1989:277-278).
Bayan wannan a wannan zamani ɗan
kore yana taka rawa wajen gudanar da damfara, misali lokacin da aka shigo da
shirin MMN Pozy Sheme a Nijeriya sai da suka yi amfani da `yank ore ta hanyar
ba su ninika masu kuɗin da suka fara zubawa.
Don haka su ne suka riƙa
shiga cikin jama’a suna nuna masu irin ribar da suka samu da kuma ƙwaɗaitar
da su, su shiga. Har ila yau, akan yi amfani da dabarar ‘hacking’, wato ɗan
damfara aka shiga cikins wani ‘group’ ma’ana ƙungiya
na wasu ma’aikata sannan ya talla hajarsa a matsayin ɗan
wannan ƙungiya. Wannan kore ke nan ta amfani
da na’urar zamani da sauransu.
2.2 Dalilin Yin Damfara
Hausawa sukan ce, “Banza ba ta kai
zomo kasuwa”. Haka kuma, Ruwa ba sa tsami banza. Haka kuma ra’in wannan bincike
shi ne, kwaɗayi mabuɗin wahala. Dangane da wannan akwai dalilai da dama da
suka haifar da wanzuwar damfara a ƙasar
Hausa. Dalilan kuwa su ne:
a.
Kwaɗayi:
Hausawa sukan yi karin magana suna cewa, ‘kwaɗayi
mabuɗin
wahala’. Wannan haka yake domin dogon guri ga rayuwa kan haifar da rashin
dangana da wadatar zuci wanda kan yi sanaɗiyar
faɗawa
tarkon damfara. Tsammanin son wani abu wanda mutum bai mallaka ba ko son karɓar
abu cikin a wajen wani mutum shi ke jefa mutane cikin damfara tsundum (Adamu,
2008, Maiyama, 2001). Wannan bayani ya yi daidai da abin mawaƙi Muhammadu Ɗanƙurji
yake cewa:
:Lantana
jikanyar Buhari Aljannan makaɗa.
…………………………………………….
:Ɗan
Malam Bawa mai mahaukaciyar biɗa,
:Ga ka da fam goma
ka ga ƙwanjan sule guda,
:Har ka tsaya mai
sule guda yana maka sababi
(Muhammadu Ɗanƙurji:
Waƙar `yan caca).
b.
Son
banza: Duk ɗan damfara yana son banza, haka shi
ma wanda aka damfara son banza ya kai shi. Domin hangen abin da ke hannun wani
da raina na shi shi ya kai har ka damfare shi.
c.
Neman arziki dare ɗaya:
Sau da yawa mutane kan tsunduma cikin harkokin damfara saboda neman arziki
cikin sauƙi babu wahala.
Haka wanda aka damfara, tun da sun ga kuɗi
ruwa-ruwa ana facaka, su ma sukan shiga ko sa samu nasu (Adamu, 2008).
d.
Ƙuncin
rayuwa: Ƙuncin rayuwa na ha’ula’i wanda mutum
kan shiga ya rasa abin da zai ci kan haifar da tunanin shiga harkar damfara.
Domin yunwa ba a ba ta sunan Allah. Don haka dole ne mutum ya yi tunanin
mafita, wanda wasu kan faɗa damfarar mutane.
e.
Nuna bajinta: Nuna ta maza ko kuma aikata
wani abin da duk ba kowa zai iya ba yinsa ba da son ayaba shi ke haddasa mutum
ya shiga harkar damfara ta hanyar amfani da siddabaru da kuma amfani da na’urar
zamani.
f.
Bushewar Zuciya: Wannan shi ne Yahya,
(1994 da 1996) ya kira da rashin imani wato rashin tausayi. Rashin imani ke
haifar da bushewar zuciya. Idan zuciyar mutumta bushe, wannan na iya sa mutum
ya aikata duk wani abin assha da tir. Bayan kasancewar ɗan
damfara mai cutarwa da rashin sanin ya kamata mutane suna masa kallon maras
tausayi da guma baƙin
ciki.
g.
Rashin Aikin Yi Ga Mutane: Rashin abin yi
ga mutane kan haifar da zaman kashe wando. Zaman kashe wando zama ne na jiran
tsammani na jiran Allah Ya ba ku mu samu. Akwai tabbacin cewa irin wannan zama
na iya kai wa ga lalaci da yin damfara. Domin duk lokacin da zaman banza ya
yawaita, mutuwar zuci kuwa za ta rufa baya a ƙarshe
abin da zai faru shi ne rashin ɗiyauci. Matuƙa mutum bai da aikin yi, bai kuma ƙirƙiro
wa kansa ba aikin da zai amfane shi ba to shi ƙarshensa
damfara. Wannan ya zama tilas domin babu rayuwar da za ta iya tabbata cikin
talauci da rashi, gashi kuwa tana ganin jama’a na kai kawo da harkokin kuɗi
ba ta san ranta (Maiyama, 2001).
2.0
Ire-Iren Damfara
Masana da manazarta al’adun Hausawa sun
raba damfara zuwa gida biyu manya, wato akwai damfarar gargajiya da kuma
damfarar zamani.
2.1
Damfarar Gargajiya
Wannan
ita ce nau’in damfara wadda Hausawa suke gudanar da ita ta hanyar amfani da
dabarun gargajiya. Kuma wannan damfara na gudana ne a wuraren daban-daban, sannan
kuma sukan yi ƙaryar ba da
magani, kamar yadda Bunza, (1989) ya ce, “Ba sayar da wani magani suke yi ba
illa yawon damfara, a birane da ƙauyuka”.
Wannan nau’i na damfara ta kasu kashi-kashi kamar haka:
2.1.1 `Yan Wala-Wala
`Yan
wala-wala mutane ne da ke amfani da wuri ko da takarda ko kati mai launin
alamu, su juya su ta hanyar dabara don su yaudari idon mai kallo da taimakon
`yan kore. Wala-wala caca ce wadda ake sa mai kwaɗayi
ya zaɓi
kati, in ya yi kuskure dole ya biya kuɗi
(Alhassan da wasu, 1982:88).
`Yan
wala-wala su ne `yan damfara da suka fara fitowa a ƙasar Hausa bayan bayanar Turawa a
wannan ƙasa.[2]
Wala-wala da kati ake yin ta, irin katin da ake caca da ita. Sukan shiga kasuwa
su a je dandalinsu musamman a wuraren da ake yin ciniki sosai na awaki ko shanu
ko dai wani abu mai kama da haka. Sukan nuna wa mutum kati a fili suna cewa:
“Wannan mai ci, wannan babu,
Idan
ka ɗauki
wannan ka ɗauki mai ci,
Idan
ka ɗauki
wannan ka ɗauki banza”.
A
kan samu `yan kore masu ƙoƙarin nuna wa wanda bai sani ba, mai
ci. `Yan koren nan sun san duk katin sosai da sosai. Da yawa sun sha haukata ƙauyawa musamman Fulani da ke zuwa da
dukiya mai yawa kasuwa. Ana ce da su `yan wala-wala saboda yawan yawon da suke
da hannuwansu wajen yin amfani da katin da lalewa da bazawa a ƙasa. Sukan ce, “Wala-wala ya ci ka”
idan sun ci mutum, shi ya sa ake kiransu `yan wala-wala. (Maiyama, 2011:28)
A
wasu lokuta `yan wala-wala sukan aro kuɗi
hannun mutum sai su yi a ci, don ka gani wai kasa da kanka. Sun riga sun kiyaye
duk katin, ko ka ga sun a je shi a gabanka ko ka ɗauka
sai ka tarar ba mai ci ba ne.
2.1.2 `Yan Kalambe
Kalambe
kwali ne ake yi wa zane-zane da hoton abubuwa da dama kamar kada da tsari da
damo da mota da keke da shamuwa da maciji da sauransu. Za a huje tsakiyaarsa a
saka icce da waya a yi mata ƙugiya
a jiye a yi rami a yi mata turke. Mai buga kalamben zai zauna a kan turmi ƙafafunsa na ƙasa, yana mazaya abubuwan kalamben na
gewaye kamar tayar keke da gudu. (Maiyama, 2011:28 a cikin Bunza, 1989).
Ɗan damfara kan fara sa kuɗinsa
`yan korensa su sa nasu, sai ƙauyawa
da masu son kuɗin banza su yi tasa nasu. Duk hoton
da ƙugiyar ta nuna mai hoton ne ya ci. A
irin wannan damfarar mai buga kalamben da ke zaune da ya ga hoton da ɗan
kore ya zaɓa sai ya ɗaga
guiwarsa ya tsayar da wayar a hankali ba da sauri ba, yadda ɗan
kallo ba zai fahimta ba. Yanzu irin wannan damfarar a ƙauyuka ne kawai ta ke ci ko a cikin
yaran da ba su san ciwon kansu ba. (Doma, 2018:23).
2.1.3 `Yan Marmashe
`Yar
marmashe dai ita ce damfarar da ake yi a fili ƙuru-ƙuru a idon jama’a. Mai damfarar zai ɗauko
yagaggun takardu ne ya ce, ina mai saya naira goma, ga kuma naira ɗari
a cikin hannusa ana gani. A wasu lokuta kuɗin
na ƙaruwa kamar dai a ce magani ne alhali
dabaru ne kawai. Bisa gaskiya idan mutum ba ɗan
korensu ba ne ba zai ci nasara samu kamar sa. Yadda suke wannan damfara shi ne
idan mai damfar ya ce wa zai saya? Sai
wani ɗan kore zai zo ya ce, “na saya
biyar”. Bayan ya riƙe
hannunsa sai ya ce: Malam ban sayar ba. Bayan ya sake hannunsa sai ka ga kuɗin
ya koma naira arba’in ko naira ɗari nan take. A koyaushe
a irin wannan damfara mai suna, ‘Marmashe’ duk wanda ka ga ya faye ci to, ɗan
kore ne. idan kuma mutum ba ɗan kore ba ne, ko ka ga
ya ci ana so a jawo hankalinsa ne a yaye shi sosai. Shiga-shigo ba zurfi ne
kawai. Kuma duk wanda ka ga ya riƙa
hannunsa sai yawan kuɗin ya ƙaru shi ma ɗan
kore ne, shi ya miƙa
kuɗin
a lokacin da suka haɗa jiki cikin ɗan
lokaci ƙanƙane
kuma ana yin aikin cikin hanzari da wayo sosai (Bunza, 1994).
2.1.4 Damfarar Dabo
Masu
wannan damfara sukan yi kuɗi ne, ko su tono su daga
cikin ƙasa, ko su karɓo
su daga sama. Suna kuma iya cika wani abu da su, a gani kamar da gaske. Wato
sukan yanka fararen takardu su zama kuɗi.
Amma a zahiri ba haka yake ba kau da ido ne, domin yawancin lokuta da sun ba
mutum kuɗi
za su ɓace
ko kuma su koma takarda ko ganye. Suna nuna wa mutane gawar jikinsu a cikin
ruwan masaki ko kwartanniya, sannan su shawarce su a kan yadda za su yi su kuɓuta
daga halaka. A kan kira masa maƙiyinsa
a nuna masa a gabansa. Wasu kuma sukan saka ƙwai
a cikin kwalba ya kuma yi magana. Bayan haka ana harhaɗa
wasu abubuwa a tada wuta ko a fitar da ruwa, ko a fitar da wani wuri ko wani
abu, kamar a fitar da zinari ko azurfa daga wani wuri ko daga jikin kowane abu,
ko a yi ruwan kuɗi ko a nuna dabbobi ko
wani abin hawa kamar jirgin ruwa da mota.
Haka
nan kuma suna iya juyar da murya wadda ba a sanin mai ita, ko su nuna wa mutum
abubuwan fake, kamar kiran sarkin Aljannu, a yi magana da shi baki da baki, ko
mayar da ƙarhu ko jela ko
wata igiya ta zama maciji, ko a mayar da sansami ko ganye ko wani abu kuɗi
wanda ake amfani da su a wannan lokaci. Ana iya canza kamannin mutum, kamar
gajere ya zama dogo, ko ramamme ya zama mai ƙiba
ko marar lafiya ya ji ya warke, da sauran siddabaru da suke yi don su damfare
mutane da su.
Duk
wannan damfara ba yiwuwa sai da saddabaru saboda abubuwan da suke yi tsagwaron
wayo ne kawai ba tsafi ba ne. `Yan
siddabaru sukan yi amfani da ƙahon
rago ƙarami su sami takalman soso, su soka
allurai kamar ɗari a soson, sai su saka shi a cikin ƙaho. Bayan wannan, sai su rufe ƙahon da wani marfi daban, a yi wa
marfin huda gwargwadon yawan allurai da ke cikin ƙahon.
Kuma za a yi saiti daidai yadda da an ɗauko
ƙahon, aka jirkita kaɗan,
sai a ga allurai sun turo kansu da yawa amma ba za su fito ba, domin suna ɗaure
a can cikin ƙahon.
Bayan
an shirya wannan ƙaho
sai mai siddabaru ya shiga damfara yana karɓar
kuɗin
mutane. Idan ya tara kuɗin mutane da sunan ba su
wani abu, sai ya ce ya fasa, can sai wani mutum ya fito ya ce, “Wallahi bai
amince ba, sai an biya shi kuɗinsa, nan take sai ɗan
siddabaru ya ce, “Zan harbe ka da allura”. Ya zaro ƙaho ya fito da alluran, ya yi ihu sai
a ga mutumin ya faɗi yana kuka, ga allurai a
rigarsa da hularsa da wandonsa a sassaƙe,
ga su ko’ina a suturarsa daɓa-daɓa.
Hausawa sun ce, gani ga wane ya isa wane tsoron Allah. Da zarar mutane sun ga
wannan sai su riƙa
cewa, “Mun yafe” a dinga suɗaɗewa
ana tserewa da ɗaiɗai
da ɗaiɗai.
Amma a zahirin gaskiya mutumin da ya zo ya ce bai yarda ba ɗan
kore ne. kuma dama kafin ya shigo fage ya sossoka allurai a suturarsa a ko’ina
yadda idan mutum ya gani sai abin ya ba shi tsoro da mamaki ya kuma zaci cewa
lallai mai magani ne ya harbe shi da allurai. Yana fito wa sai ɗan
siddabarun ya yi hito ya ciro wani ƙahi
da allurai suke ciki ya ce ya harbe shi, shi ko ɗan
koren ya faɗi (Bunza, 1989).
2.1.5 Damfarar Bokaye
Tun
kafin zuwan Musulunci bokaye su ne likitocin gargajiya na kowace irin cuta ko
annobar da ta ɓulla a ƙasar
Hausa. Sun riƙa ba da magani
kuma wurinsu ne ake zuwa a karɓi magani. Don haka kafin
bayyanar asibitocin zamani, bokaye ke cin Karen su babu babbaka domin ba su da
abokan hamayya. (Bunza, 1989, Wushishi, 2011:51).
Idan
mutum ya je wurin boka domin neman wani taimako sukan umurce shi da yin waɗansu
abubuwa kamar shiga da ƙafar
hagu ko shiga da baya, ko kar a yi sallama, ko su ce a yi a hankali kada a taka
masu `ya`yan aljannu. Wasu sukan bayyana abin da ke tafe da mutum ta hanyar faɗi
sunan mutum da iyalansa da sana’arsa da buƙatar
da ke tafe ta shi. Duk wannan yana faruwa ne ta hanyar ɗan
kore. Domin shi ne zai ba mai buƙata
shawara da ya tafi wurin boka wane aikinsa yana ci. Dama gidan boka ƙofa biyu ne, ɗaya
na boka da mutanensa aljannu da `yan kore, ƙofa
ɗaya
kuma na shigowar mutane. Bayan haka sai su ce Aljanni ya ce buƙarka za ta biya amma sai ka kawo baƙin bunsuru ko baƙar kaza ko ƙahon wani dabba, kamar jaki ko raƙumi, ko nonon kaza, ko bahagon ɓera
da dai sauransu. Idan mutum ya ce bai iya samowa sai su ce ya kawo kuɗi
a ba aljannu su samo masa waɗannan abubuwa. Saboda
tsabar iya siddabaru da wayo idan mutum ya kawo kuɗin
su ce ya ajiye a ƙasa
ba su amsa da hannunsu sai aljannu za su ɗauka
da kansu. (Ibrahim, 2012:25)
2.1.5 Damfara A Ciki Tsibbu
Tsibbu
ba Bahaushiyar kalma ba ce, daga Larabci Hausawa suka aro ta. Amma an Hausance
kalmar, tsibbu na nufin magani da ya keɓanta
ga malamai. (Wushishi, 2011). Malamin
tsibbu yana amfani da ayoyin Alƙur’ani
wajen gudanar da ayyukansa. Waɗannan malamai ba su yi
karatu da yawa ba sai dai sun iya karatu baki gwargwado. Sharuɗɗan
tsibbu shi tilas ne malamin ya mallakin kundi[3]
wanda ciki ne ya ajiye kayan aikinsa. Bayan haka malaman tsibbu sukan yi duba
ta hanyar bugun ƙasa
da istihara[4]
da fassarar mafarki da duban carbi da
sauransu. (Yahaya da wasu, 2001:32-34).
Ta
wannan fuskar Malaman tsibbu suna da hanyoyi da suke gudanar da damfara a cikin
al’ummar Hausawa ta hanyar amfani da maganin da suke kira, ‘sirri’[5] da
‘naƙali’[6]
sukan yi amfani da waɗannan abubuwa wajen yin
damfara ta hanyar sa dokoki masu tsanani da wuyar kiyayewa don haka sai mai biɗar
magani ya nemi sauƙi
ta yadda za su tsadance da shi. Malam sukan yi amfani da siddabaru wajen karɓar
kuɗi
a hannu mutane, wanda wannan zunzurutun wayo ne da dabara da kaifin hankali har
mutum ya ɗauka cewa Rauhani ko Aljani ko Ibilis
ne ke yin wannan aiki domin ya saɓa
wa hankali. Daga cikin wannan siddabaru akwai bugun alƙalami da fito da hatimi a takarda a
cikin ruwa da dabon hatimi a gaban idon mutum da sa ƙwai a ciki kwalba a ɗaure
su da sa ƙwai ya tashi sama
da sa kwalba ta kama takalmi ko kara da sauransu. (Bunza, 1989).
2.1.6 Damfarar Zamba Cikin Aminci
Alhasan,
da wasu (1982) sun bayyyana wannan damfara da cewa, ita ce ake yi wa mutum idan
mutum ya kawo kuɗinsa ajiya, domin zai haɗu
da wani mutum mai albarka. A kan yi wa mutum dabara a nuna masa sani da sabo,
inda a kan kira sunansa da na iyayensa, da garinsu, da sana’arsa da kuma buƙatar da ya sa wa gaba a ransa. A kan
kuma yi wa namiji ƙifƙiftau da mace, a dibirce shi, ko a yi
da mace ko da wani mai kuɗi ko sarauta ko ilimi, ta
hanyar zamba cikin aminci. Wannan duk yana faruwa ne ta hanyar ɗan
kore wanda zai ba da bayanin mutumin da buƙatarsa
tun kafin ya zo wurin. Sannan kuma shi ne zai turo wannan mutumin zuwa wannan
wurin domin biyan buƙatarsa.
Misali wannan damfara shi ne kamar yadda Maiyama, (2008) ya kawo misali a cikin
Littafin Ruwan Bagaja inda Alhaji
Imam ya yi Malam Zulƙe
wayo ya damfare shi a lokacin da suke cikin tafiya tare, sai ya kwashe labarin
yadda ya samu kuɗinsa kaf ya shaida wa
Alhaji Imam saboda aminci. A lokacin da Malam Zulƙe
zai tsaya ratsi sai ya ba Alhaji Imam kuɗi
ya riƙe mashi, amma da ya dawo ya buƙaci kuɗinsa
sai Alhaji ya hana shi, ya ce, ‘kuɗinsa
ne’. Haka kuma wani misali na fito da damfarar zambo-cikin-aminci a lokacin da ɓarawo
ya zo yi wa Alhaji Imam sata sai Alhaji ya yi amfani da wannan dabara ta zambo
ciki aminci, ga yadda abin ya kasance:
“Maraba, maraba. Ga tabarma ka zauna. Ashe za
ka zo ka ƙi gaya mini tun da rana da muka gamu a kasuwa. Alhaji
ya ci gaba da cewa, “Na yi ta yi masa magana kamar na san shi.
Da ɓarawo ya fahimci nuna sani ya yi yawa, sai ya ce, “Ina
ka san ni?’.
Shi kuma Alhaji ya ce, ‘ai tuni na san ka, bari ta kai
ma duk danginka na san su, duk kuwa sun san ni’.
Da ɓarawo ya ga da gaske Alhaji yake yi sai ya ce wa
Alhaji, “Kai in ka san ina sunana?’. Sai Alhaji ya ce, “Na yi ihu da ƙwarai
na ce, ‘ai sunanka, ‘Ɓarawo”.
Muna
iya cewa Alhaji ya yaudari wannan ɓarawo
ta hanyar nuna sani wataƙila
ba don ya yi amfani da wannan hanyar damfara ba da ɓarawo
ya cuta masa. Don haka ana ganin Alhaji ya yi amfani da wannan hanya ce don ya
kori ɓarawo.
To,
haka masu yin wannan damfara ke yin amfani da nuna sani a fili domin su damfari
mutum. Don haka a lura duk lokacin aka ga mutum yana ƙoƙarin
nuna wa wani sani ƙarfi
da yaji ya dace a tuhumi wannan mutum sannan kuma kada a yi saurin amincewa da
shi domin gudun faɗawa tarkon damfar zambo
cikin aminci.
2.1.7 Damfarar Ɗauki-Ka-Ba-Ni
Wannan
damfara ce da ake yi wa `yan damfara, ba kowane irin mutum ake yi wa ba. Galibi
bayan `yan damfara sun yi damfara sun tara abin duniya, sai mai ɗauki-ka-ba-ni
ya zo dare ɗaya, ko ma rana ɗaya,
ya yi masu wayo da dabara ya damfare su ya kwashe duk abin da suka tara kaf, ya
tafi abinsa. Watau dai son abin duniya da ƙwaɗayi
da rashin aikin yi su ke sa mutum ya tasirantu da damfara har ya yarda a
damfare shi (Alhasan da wasu, 1986:89).
2.1.8 Damfarar Gada-Gada
Wannan
nau’in damfara kamar yadda Maiyama, (2008) ya riwaito Bunza, (1994) cewa ita ce
damfarar da ake yawo da hankalin mutum da dibirta shi wanda akasari aka fi yi
wa baƙi waɗanda
ba su san gari ba. Kuma masu yin wannan damfarar wasu lokuta sukan shiga rigar
hukuma. Misali idan mutum baƙo
ya zo yana neman wani wuri musamman mutumin karkara wasu `yan birni kan yi
amfani da wannan damar wajen damfarsa. Misalin wannan shi ne lokaci da Malam
Haruna da Maikuɗi suka tafi birni duba ɗan
uwansu da hukuma ta kama. Ga yadda abin ya kasance:
“Malam Haruna da Maikuɗi suka yarda
saurayin ya wuce gaba suka bi shi. Ya shiga wannan lungu da su ya fita wancan
har dai suka gaji da tafiya. Har Malam Haruna ya ce, “Shin samari har yanzu ba
mu zo wurin ba ne?”
Ga
abin da ɗan
banzan ya ce:
“Kada ka gaji baba, ai wurin ne da `yar tazara, amma
mun kusa zuwa. To, ba don kun same ni na ɗauki ɗawainiyar kawo ku ba, da ya za ku zo nan da kanku”.
Bayan `yan tafiya kaɗan suka iso wani ɗan fili sai gogan ya ce, to, sai ku tsaya nan in je in
sanar da masu gadin ga ku kun zo, in yi muku iso.
Jin kaɗan saurayi ya dawo ya koma ya ce, to, na shaida masu.
Amma da ƙyar da lalama daban baki suka yarda. Kun yi sa’a da
cewa suka yi wai tikitin rasil ɗin shiga ya ƙare sai jibi. To,
amma tunda sun yarda sai ku kawo kuɗin tikitin rasil na Naira huɗu ku biyu ke nan.
Malam Haruna ya sa hannu ya ɗauko jakarsa ya
kwance ƙullin ya zazzaro Naira huɗu ya miƙa
masa. Bayan ya ga ya damfari ƙauyawa sai saurayin ya koma bakin ƙofar
kurku ya ɗan jima kaɗan sai ya dawo ya miƙa wa Malam Haruna
da Maikuɗi waɗansu `yan guntayen jajayen takardu guda biyu ya ce,
‘To ga tikitinku na rasil. Ku je ku shiga kawai. Sai Malam Haruna suka karɓi wannan rasil
suka kuma gode nasa. Ba su san cewa ɗan saurayi damfararsu ya yi ba.
2.1.9
Damfarar Gardawa
Gardawa suna nuna siddabaru da waibuwa
iri-iri domin su damfari mutane. Suna gwada abubuwa kamar cin kasuwar sama, ko ƙone yaro da yanke shi, a warkar da
shi, ko a ƙona tufa daga baya
a fito da ita. Kuma ana iya shiga cikin wata dabba a fita wani wuri ko su shuka
duma ko kabewa ya tsiro ya yi yaɗo
da `ya`ya nan da nan. Ana iya kuma saka wuƙa
cikin baki a fitar da ita ta hanci ko a karɓo
wani abu daga sama Bunza, (1986).
2.2
Damfarar Zamani
“Zamani
abokin tafiya, idan zamani ta ɗinka riga tilas ne a sa”.
Damfara ta shiga cikin tafiyar zamani, domin lokacin da ake ganin an samu ilimi
da wayewa ta ƙara yawa, a
lokacin ne mutane suke ƙara
fito da sabbin hanyoyin damfara. Sannan samuwar na’urori da ci gaba zamani su
ne suka haifar da damfara zamani. Damfara ta shiga hanyoyin zamani kuma babu
wanda yake tsallake wannan nau’i na damfara. Ma’ana da jahilai da masu kuɗi
da masu ulimi duk suna faɗawa cikin wannan tarko.
3.2 Hanyoyin Damfara Na Zamani
Akwai
hanyoyi da dama da ake amfani da su wajen gudanar da damfara ta zamani waɗannan
hanyoyi su ne:
3.2.1 Ta Hanyar Satar Bayanan Sirri Na
Asusun Ajiyar Kuɗi A Banki
Mutane
da dama sun samu kansu cikin rigima da bankunansu ta hanyar bayar da bayyanin
siiri a kan asusun ajiyar kuɗinsu na banki. Dabarar da
`yan damfara ke amfani da ita, ita ce ta hanyar kiran mutum a waya, su ce daga
banki ne, ana buƙatar
ya ba da lambar sirri wato PIN[7] ko
lambobi huɗu na ƙarshe
a katin ATM. Da zarar sun sami abin da suke buƙata
sai su washe asusun nan take.
A
wasu lokuta sukan tura saƙo
a wayar mutum cewa daga bankin da yake hulɗa
da su ne, akwai matsala a asusun ajiyarsa don haka ya kira wannan lambar domin
warware wannan matsalar. Idan mutum ya kira su za su buƙaci muhimman abubuwa da suka shafi
asusun ajiyarsu, idan aka yi rashin sa’a suka samu nan take sukan kwashe kuɗin
ajiya daga asusun. Haka kuma akasari sun fi yin wannan damfarar ranar da banki
ba su aiki. Don haka kafin ranar da za a kai ƙorafi
a banki sun riga sun kammala nasu aikin na damfara.
Akwai
wasu mutane da kan zo su tsaya a injin na cire kuɗi
wato ATM[8]
suna ƙoƙarin
satar lamar sirri na mai hulɗa da banki. Idan kuma sun
yi sa’a wanda ya zo cire kuɗi bai iya amfani da
na’urar ba kuma ya nemi taimakonsu, sannan ya nuna masu lambar sirrinsa. Daga
nan shi ke nan sun dinga ɗiban kuɗinsa
sai in ya je banki ya kai ƙorafi
an toshe wannan asusu. Mutane da dama sun faɗa
cikin wannan tarkon.[9]
3.2.2 Damfara Ta Hanyar Mutuwa Da
Taimako
Wannan
ita ma wata hanya ce ta damfara, a kan turo saƙon
Email ko kuma a kira mutum kai tsaye daga wata ƙasa
ana shaida maka cewa wani bawan Allah ya mutu kuma ba shi da mai gadonsa amma
kai ake so a miƙa
wa wannan dukiya ta hanyar amfani da bayanan da wannan mutumin ya bari na
wasiyya cewa, akai dukiyarsa ƙasashen
Afrika. Sukan yi amfani da muryar mace ko wani namiji da sunan ma’aikacin baki
ko kuma manajan wannan mutumin da ya mutu. Daga ƙarshe
za su buƙaci mutum ya tura wasu kuɗaɗe
waɗanda
za a gyara hanyoyin da kuɗaɗen
za su isu wajensa. Wannan wata sabuwar hanyar damfara ce.
3.2.3 Damfara Ta Hanyar Aljannu Masu
Taimako
Wannan
wata hanya ce da `yan damfara ke amfani da ita da sunan taimako don cutar da
jama’a. Yadda suke yin abin shi ne wani ne zai kiraka a waya ya ce, yana buƙatar ka yi wa Annabi Muhammadu (S.A.W)
salati, ka karanta wasu ayoyi sai ya umurce ka da ka matsa gefe guda. Idan mutum ya faɗa
wannan tarko sai ya ce, “Shi Aljani ne”. Daga nan sai ya yabeka ya nuna ka taɓa
taimakonsa ko mahifinsa ko wani abu mai Kaman haka shi ne yake so ya saka maka
da dukiya mai yawa. Saboda haka zai fara faɗa
maka ka yi kaza, ka yi kaza. A ƙarshe
ya ce wasu irin kuɗi kake buƙata a taimaka maka da su, misali idan
mutum ya ce dalar Amurka yake so, sai ya ce, ka je ka same su ka zuba cikin abu
irin kaza a kai wuri kaza, a daidai loaci kaza za su mayar maka da su miliyoyi.
Wani lokaci za ka ji sun ce su Aljanu ne daga Makka ka fara sayen kati ka tura
masu.
To
ko dai mene ne Aljanu ba su magana da mutane ta waya, kuma ba sa buƙatar layin sadarwa domin su yi
magana. Hasali ma ba a ganin Aljani kuma ba yin magana da su sai ta bori ko ta
Rukiyya, in ba haka ba duk wanda ya ce shi Aljani ne yana magana da mutane kai
tsaye to ɗan damfara ne, a kiyaye.
3.2.4 Damfara Ta Hanyar Kwangilar Kwastam
(Custom)
Wannan
ya fi yaɗuwa
a shafin sada zumunta na Facebook. Wani kan fito ya ce shi ne jam’in hana fasa ƙwabri mai kula da kayyakin da suka
kwace waɗanda
aka shigo da su ta ɓarauniyar hanya. Saboda
haka gwamnati tana yin gwanjonsu sai ya lissafo kayayyakin da kuɗinsa
sannan ya saka adireshin Intanet da za bi a biya kuɗin.
Irin wanann damfara an daɗe ana cutar mutane da
ita, kuma hukumar Kwastan ta sha fitowa tana cewa ba ta da alaƙa da irin waɗanann
mutane don haka a yi hattara.
3.2.5 Damfara Ta Hanyar Buɗe
Shafin Sada Zumunta da Sunan Mace
Wannan
shi ma a shafin sada zumunta na Facebook da Whatsapp ake yin sa. Sukan buɗe
shafin sada zumunta da Facebook ko Whatsapp da sunan mace sanann kuma su saka
hoton mace kyakkyawa domin ɗaukan hankali. Daga nan
sai su aiko da saƙo
neman abokata dazarar ka amince har kuka fara hulɗa
sai a aiko maka da hotuna na jan ra’ayi daga nan sai a fara neman wasu kuɗaɗe
da zumar toshi.
Yawanci
irin waɗannan
shafuka na maza ne suke amfani da ita wajen damfara. Idan mutum ya matsa cewa
sai ya yi magana da ita sai su nemi wata mace su ba ta ku yi magana. Da haka
har su damfari mutum kuɗi mai yawa sai daga ƙarshe idan dangantaka ta ginu sai
goge wannan shafin.
3.2.6 Satar Shafin Sada Zumunta Da
Wani
`Yan
damfarar zamani sukan yi ƙoƙari su saci shafin sada zumunta na
mutum su yi amfani da shi wajen yaudarar mutane musamman abokansa da kuma
makusantansa. A kan yi magana da abokan mutum a matsayin shi yake yi, sai su yi
amfani da wanann damar su nemi taimako na kuɗi
na wucin gadi da cewa idan sun haɗu
za ya biya. Wani lokaci sukan buƙaci
a aika masu da katin waya. Sukan nuna cewa suna wani wuri kuma sun samu matsala
don haka suna buƙatar
kati. To wanan ma wata hanya ce ta damfara.
3.2.7 Saƙon Albishir Daga Kamfanin Waya
Wata
hanya ta damfara a wannan zamani ita ce ta aiko da saƙon albashir daga gidan waya na cewa
mutum ya yi nasarar cin wata kyauta ko kuma lambar aka zaɓa
a wajen gudanar da wannan gasa kuma ya ci naira miliyan ɗaya
da sauransu. Don haka ana buƙatar
ka ba da kuɗi kaza kafin a aiko maka da waɗannan
kuɗaɗe.
To wannan ma wata hanyar damfara ce.
3.2.8 Damfarar Kawo Kuɗi
Na Ninka Maka
Wannan
hanyar damfara ta shahara a Intanet da zahiri. Wanann wankiya ce tsagwaronta da
ake amfani da dabarar buɗe wani kamfani. Za a faɗa
cewa wanann kamfani yana harkar sayar da ɗanyan
mai da gwal. Don haka idan ka saka hannun jari na naira dubu ɗaya
wani mako mai zuwa za su ninika maka ya koma dubu biyu ko fiye da haka.
Haka
kuam a Intanet a an ɓullo da wani tsari na
kasuwanci wanda ake kira Foreɗ Trading wanda a zahiri
akwai su. Amma `yan damfara suna amfani da wanann wajen cutar mutane ta hanyar ƙwaɗaitar
da su cewa duk abin da mutum ya sa za a nininka ma shi. Kuma kuɗinka
zai riƙa ƙaruwa
dangane da yawan mutanen da ka kawo. Sukan yaudari mutane da fara ba mutanen
farko domin su yi shigo-shigo ba zurfi. To duk waɗanda
suka biyo bayan wannan mutum duk yaudararsu za su yi.
3.2.9 Damfarar Ta Satan Bayanan Sirri
Wannan
hanya ce da ae damfara ta amfani da na’urar kwanfuta. Wanann satar bayanai
sirri shi ne ake cewa, “Techincal Hacking”. Domin kowace kwanfuta tana da abin ɗaukar
hoto wanda ƙwararru suke
amfani da ita wajen gano bayanan sirri na mutum. Domin babu wani abu da mutum
zai yi face suna ganinsa. Sukan yi amfani da wannan damar wajen samun bayanai
na siiri da kuma amfani da su wajen damfara. Misali: Mutum yana zaune wata ƙasa yana shiga yanar gizo domin neman
bayanan sirri ta hanyar Imail da sauransu. A irin wannan damfarar a kan samu
bayanan sirri na banki a shiga cikin asusun masu ajiya a ɗebi
kuɗi
ba da saninsu.[10]
3.2.10 Damfara Ta Amfani Da Na’urar
Kamfuta
Masana
ilimin kwanfuta na amfani da ita wajen gudanar da damfara. Ana amfani da wannan
na’ura a matsayin `yan koren zamani. Bokaye na sanya na’urar kamfuta a wani ɗaki
da suke fara ajiye mutane kafin su gane da su. A lokacin da mutum yake wannan
wuri duk abin da yake aikatawa suna ganinsa. Don haka da ya zo sai su fara ba
shi labarin abin da ya aika a bayan idonsu. Wanann kan ba mutum mamaki ya ɗauka
cewa wata baiwa ce ta daban. Don haka du abin da aka faɗa
masa sai ya amince nan take.
Haka
kuma sukan yi amfani da wannan na’ura wajen faɗa
wa mutum wasu matsaloli da yake fuskanta. Wannan yana faruwa ne ta hanyar `yank
ore. `Yan kore kan zauna su riƙa
amfani da tsarin sadarwa na Whatsapp suna ba da bayanin abin da mutum yake
aikatawa alhali bai sani ba. Don haka sai `yan damfara su kira mutum su riƙa faɗa
masa abin da yake aikawa a halin yanzu. Daga sai su umurce da ya kai wasu kuɗaɗe
a wani wuri ko kuma ya aikata wani abu buƙatarsa
za ta biya.
3.2.11 Damfarar Neman Aiki
Wannan
wani nau’in damfara ce da ake aiwatar musamman ga masu neman aikin gwamnati. A
irin wannan damfara akan yi wa mai neman aiki alƙarin
sama masa gurbin aiki a wata ma’aikata ko kuma wata hukuma amma sai a umurce
shi da sai ya biya wasu kuɗaɗe
na toshiya baki kafin a ba shi takardar ɗaukan
aiki. Mafi yawa `yan boko ne masu son
samun aiki a ma’aikata mai tsoka wato NNPC ko kuma wani kamfani don haka a kan
umuurce su da biyan kuɗaɗe
masu tsoka kuma daga ƙarshe
ba su ga tsuntsu ba su ga tarko.[11]
3.2.12 Damfara Ta Hanyar Wayar Hannu
Ana
mafani da wayar hannu wajen gudanar da damfara. Masu yin wannan damfarar sukan
kira mutum ne su ce daga bakinsa sannan su bayyana masa sunansa da shekarun
haihuwarsa da ranar da ya buɗa asusun ajiya. Daga nan sai su buƙaci ya ba su lambar katin ATM. Wasu
kuma sukan nemi lambar sirri na ajiyar kuɗi.
Haka kuma wata hanya ita ce wadda ake cewa an kawo wani tsari na taimakonn
jama’a. wanda mutum zai ba da kuɗi
a ninika masa.misali: MNN Ponzy Scheme wanda aka yi amfani da shi aka damfari
mutane da yawa. A halin yanzu an ɓullo
da wata hanyar yaudara ta waya wanda za a aiko wa mutum a umurce shi da ya
shiya wani tsari wanda daga bisa za a buƙaci
ya cike ta hanyar bayar da sunansa da lambar asusun ajiyarsa na banki da
sauransu. Da zarar mutum ya bi umurnisu to, shi ke nan za a kwashe duk ajiyarsa
a banki.
Akwai
kuma hanyar aiko da saƙo
da hanyar Imel wanda ake yi wa mutum albishir cewa yana daga cikin wanda
gwamnati ta zaɓa da za a ba muƙamai don haka ya turo bayanansa wato
CƁ
da zarar ya yi sai kuma su aiko masa cewa akwai buƙatar ya aiko da wasu kuɗaɗe
domin za a kama masu wurin da za a ba su horo na sanin makaman aiki. Daga ƙarshe sai akai mutane a ajiye a wani
hotal wanda bai kai yawan kuɗin da suka aika ba. Kuma
irin wannan damfara an fi yi masu ilimi kuma da gogaggun yan boko.
3.3 Illolin Damfara
Babu
tantama, damfara ba ce mai tattare da illoli masu yawa ga al’umma. Bisa ga
bayanai da aka samu ƙalatowa
yayin gudanar da wannan bincike sun haɗa
da:
a.
Haifar da tsiya da talauci: Mutane da yawa
sun tsiyace saboda an raba su da abin da suka malla don haka suka faɗa
cikin talauci. Kamar yadda Ibrahim, (1982) ya bayana cewa damfara ta haifar da
talauci da jefa mutane cikin rayuwar ƙa-ƙanikayi. Wasu ma takan yi sanadiyyar
rasa hankulan su ko ma rayuwa baki ɗaya.
b.
Sauya Bagirn Arziki: Idan aka damfari
mutum duk abin da ya mallaka yakan sauya hannu daga wannan zuwa wancan. Don
haka ɗan
damfara da arziki sun riski juna ne don ba shi ya nemo shi shi ya sa ake samun
lalacewa arzikin da ka samu ta hanyar damfara.
c.
Karya tattalin Arzikin Ƙasa: A duk lokacin da aka samu
arzikin ƙasa na bin hanyar da bai dace ba,
ma’ana haramtacciyar hanya wadda gwamnati ba ta amince da ita ba, to yakan
haifar da matsalar tattalin arziki a wannan ƙasa.
Domin gwamnati za ta rasa hanyar samun kuɗaɗen
shiga. Haka kuma idan ɓarnar damfara ta yawaita
tana iya durƙusar da ƙasa nan take musamman `yan damfara na
zamani ta hanyar Intanet da ke kai kuɗi
ƙasashen ƙetare suna ɓoyewa.
4.0 Sakamakon Bincike
A
ƙarshe an fahimci cewa damfara, ruwan
dare babu jinsin da ba su yi. Kuma babu wanda ya ƙetare
karkonsu sai wanda ya cire wa kansa kwaɗayi
da son abin duniya. Binciken ya fito da dabarun bincike na gargajiya da na
zamani waɗanda ake amfani da su wajen karɓar
kuɗi
a hannun mutane. A zamanin da, `yan damfara suna amfani da hanyoyin siddabaru
na gargajiya wajen aiwatar da damfara, sannan damfar da su ta danganta ne ga
wanda bai san irin siddabarun da suke amfani da shi kuma taƙaita ne a wurin da suke gudanar da
ita kawai. Wanda yanzu a wannan zamani damfarar ta ɗauki
sabon salo, domin ana amfani da abubuwan da zamani ya shigo da su wajen
yaudarar mutane. Nau’o’in damfarar zamani sun haɗa
dukan rukunin jama’a da ke cikin al’umma. A damfarar zamani wasu takan rutsa da
wasu mutane saboda rashin sani, wasu kuma tsananin kwaɗayi
ne ke haifar da shi. Masu damfara sukan yi amfani da sabon tsarin da bankuna
suka fito da su, wajen damfarar mutane. Wasu mutane ne kuma suna amfani da
wayar hannu domin damfara, yayin da wasu kuma sukan shiga shafukan sadarwa na
zumunta na zamani domin damfarar mutane. Sannan damfara mafi muni shi ne wanda
ake yi ta hanyar Intanet domin a wannan hanyar miliyoyin daloli ake kwashe a
asusun ajiya a sauya masu wuri cikin ɗan
ƙananen lokaci. Akasari masu gudanar
da wannan damfara ana kirasau da suna, “Yah[12]oo
boys”. Haka kuma binciken ya fahimci abubuwan da ke haifar da damfara da
dalilan yin damfara da illolin damfara. Daga ƙarshe
bincike ya gano cewa ba wani abu ke sa a damfari mutum ba sai kwaɗayi
wanda Hausawa ke yi wa kirari da mabuɗin
wahala. Domin kwaɗayi ya haifar da mutane
sun yi hasarar dukiyoyi masu tarin yawa. Don haka ya kamata mutane su kiyaye a
duk lokacin da suka ga wani wanda ba su fahimci shi ba, ka da su yi saurin faɗawa
cikin wannan lamari sai sun tuntuɓi
masana.
5.0 Kammalawa
Damfara
ruwan dare ne game duniya. Domin babu lokaci ko yanayin da ba a gudanar da ita.
Haka kuma a wancan zamani ana amfani da siddabaru wajen aiwatar da damfara.
Sannan kuma `yan kore sun taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da damfara. Domin
damfara ba ta yi yuwa dole sai an samu ƙwararren
ɗan
kore wanda zai taimaka wajen turo mutane a damfara su. waɗannan
`yan damfara sun haɗa da bokaye da malaman
tsibbu da gardawa da sauransu Amma yanzu da aka samu wayewar kai sai damfara ta
ɗauki
sabon salo. Wato da shiga sahun amfani da abubuwan da zamani ya kawo. Waɗannan
na’urorin zamani su ne suke matsayin `yan a sigar damfarar zamia, saboda ta
amfani da su ne ake samun bayanai da za a yi amfani da su wajen damfara. Wannan
ya ba `yan damfara damar shiga cikin rigar zamani su ci karen su babu babbaka.
Waɗannan
nau’o’rorin zamani sun taimaka wajen aiwatar da damfara ta yadda wanda aka
damfara babu yadda zai gane sai bayan aikin gama ya gama. Damfarar zamani ta ɗauki
fuskoki da dama kama daga damfarar satar sirrin banki da ta satar kuɗi
a asusun banki da ta amfani da wayar hannu da sauransu.
[1] Hira da Malam Aminu wani wanda `yan dafara
suka samu sa’arsa a ranar 16/10/2018
[2]
Bunza, (1994) “Damfara Da 419 A Bahaushiyar Al’ada” (Nazarin Nasonsu da
Damabalarsu A Rubutattun Ƙagaggun
Labaran Hausa). Takarada da aka gabatar a taron ƙara
wa juna sani a jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.
[3]
Kundi wani littafi ne wanda
ya ƙunshi hatimai na zane-zane da baƙaƙen Larabci ko aƙaluna
iri-iri.
[5] Idan an ce sirri ana nufin wasu
abubuwa ne da sai wanda ka yi da abinsa sai ko wanda sai ko in an nemi
taimakonsa ya bayyana.
[6] Yana da alaƙa da asiri sai dai shi naƙali sai wanda aka naƙaltawa mutum kawai zai iya sarrafa
shi.
[8] Na’ura da ake liƙa wa a bango a bakin baki wanda
mutane ke zuwa suna cire kuɗi. Da Turanci a cewa, Automated
Teller Machine.
[11]
Hira da Malam Munir Sidi a UDUS ranar 20/10//2019.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.