Babban
jigon waƙar shi ne Adalcin mulkin Musulunci da
zaluncin mulkin kafirci. Dalilinda suka sa na tabbatar da haka su ne kamar
yadda marubucin ya zayyana a cikin wassu baitoci da suka ratsa waƙar tun daga farko har ƙarshenta.
Waƙar
Tsarin Mulkin Musulunci
Ibrahim Mohammed
08060287141
1.
Mu
gode Wanda yay yi mu musulimina,
Na Ahamadu Ƙadirawa masu
Sunna.
2.
Salati
nai da taslimi su duma,
Ga Ahmadu Shugabanmu zuwa ga dina.
3.
Da
Allai nai Sahabbai nai Fiyayye,
Da Atbai da Tabi’i-Tabi’ina.
4.
Ku
saurara gabatam muslimina,
Ku bi ta ku bar sarautak kafirina.
5.
Musulmi
manya-manya da salihansu,
Ka zaɓen mai gabatat muslimina.
6.
Su
taru su ɗauki alwashi na ɗa’a,
Ga foron nan na Alƙur’an da Sunna.
7.
Shari’a
ko’ina tat tausa kowa,
Ta shuɗe ya ƙi ya so kowane na.
8.
Shi
zan yarda da al’amarinsu ya zan,
A ba shi shi hanƙure nauyin abin
nan.
9.
Shi
ƙarfafa
wajibi shi hana haramun,
Kamas salla masallaci shi gina.
10. Riyoji kasuwa
hanya tafukka,
Kusheyi don shi sa matsaran abin nan.
11. Talakkawa marayu
sa gwagware,
Abin matafa shi nura da alhakin nan.
12. Tsaron aumi tsaron
matafa jihadi,
Shi kore masu aikin zalimina.
13. Shi sa matsara
gari duka masu gyare,
Da alƙallai su zam masana na Sunna.
14. Shi aiki a tar da
zakka kowace ta,
Shi sa a raba talakkawan garin nan.
15. Idan saura a kai
ta a ba waɗansu,
Talakkawa a ba ta mujahiduna.
16. Shi aiki a tar da
Baitul-mal gari duk,
A sa ta ga maslahatu kan garin nan.
17. Idan saura a kai
ta a gyarta wansu,
Kamat gyaran birane don a zamna.
18. Masallatai ribaɗi don karatu,
Ibada don a samo addu’an nan.
19. Makamayyen jihadi har dawaki,
Da nasu rabo akwai shi ga dukiyan nan.
20. Da mallammai da alkalai da sauran,
Musulmi
duk shi nura da maslahan nan.
21. Shi sa wani
shugaban yaƙi shi zamna,
Iyakat muslimina da kafirina.
22. Shi zam shimgi shi
daidai ganima,
Shi ɗau humusi shi nisanta amana.
23. Gululi duk shi bar
shi shi tsorci Allah,
Ku saurara sarautak kafirina.
24. Saraki su ka ƙarfafa fada zaɓe,
Ga ‘yan sarkinsu wane a juye suna.
25. A ce sarki a ba
shi abin sarauta,
Su zuzzuge gaisuwa da kiɗi na murna.
26. Ga al’adunsu kowaz
zo shi duƙa,
Waɗansu suna afi ku ji wane dai na.
27. Su gangunma da
algaitu kalangai,
Da tabburra abin wasa na sunna.
28. Da jan kaya da
gwarje alharini,
Azurfa su abin girmansu ke nan.
29. Galadima magaji
uban dawaki,
Yarima sayen kaza manyansu kenan.
30. Shi ɗauki wanda yas so
kowane na,
Shi
ba shi gari a ce sarkin gari na.
31. Su zage gaisuwa
tare da ƙwace,
Su kai ma uban wuta nasu, duk su ƙuna,
32. Dawaki nai da
sarki nai na yaƙi,
Su kai mai dukya shi ad da wannan.
33. Su ce doki tufan
girma takobi,
Na manya na su amshe duk abin nan.
34. Su bar humusi su
tausa sunka saba,
Su ce ko way yi kamu nas kenan.
35. Barori ag gare su
da ‘yan barade,
Lifidda ba su tarac cin amana.
36. Gululi ba su
istibra ga mata,
Su samu a nan su sa ɗaka, ha wutan nan.
37. Muna roƙonka kai Sarkin
sarauta,
Ka sa mu cikin gabatar muslimina.
38. Mu zamna salihina
mu sami tsiran,
Sarautak kafirina da fasiƙina.
39. Ka gafarta jama’aƙ Ƙadirawa,
Ka sa mu ciki ga hanayn nan ta Sunna.
40. Mu ƙara godiya mu zubo
salati,
Ga Ahmadu mun cika bisa arba’ina.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.