Wani abokina na kusa ya
taba gaya min cewa ya yi mu'amalla da wata 'yar gabashi, har ya kusa zuwa
gidansu sai ta gaya masa cewa ita fa ba sa zama da kishiya. Ya ce to da ma yana da mata biyu. Sai ta
ce ai da sauƙi tun da ba su kai 3 ba, kuma za ta iya riƙe yaran gaba ɗaya. Da ya
tambaye ta ma'anar maganarta, sai ta ce ya sallami sauran matan kawai ta ishe shi komai! Auren
da ba a yi ba kenan, domin ta kai ga uwayen tsohuwar matar sun...
Zan Ƙara Aure // 29: Kwaɗayi
Ma Dalili Ne
Baban Manar Alƙasim
Zauren
Markazus Sunnah
Koda-yake kwadayi
kala-kala ne, akwai na sama da na ƙasa, na saman kan kasance kwadayin nau'o'in
sanadari da ababan masarufi, na ƙasan kuma ido a kan 'yammatan dake gilmawa ko
matan da suka sha ado ko yanayin halittarsu, na sha ganin masu mata guda-guda
wadanda ciyar da su ma matsala ce, amma kyakkyawar yarinya ko wace ta san
matsalar maza na gilmawa sai ta dauke hankalinsu ka ji suna buƙatar ƙarin aure, shi ya sa za ka
ji mata da dama a wannan lokacin suna ta
laluben hanyoyin da za a hana maza ƙarin aure sai an tabbatar cewa za a iya riƙe su gaba daya.
.
Shekarun baya ne aka yi
wani abin kuwa a daya daga cikin jahohinmu na Arewa, inda wata yarinya ta
tallata kanta tare da cewa za ta tallafa wa mai aurenta da gida da mota, haka
samari da masu neman ƙarin aure suka yi dandazo kowa na ƙoƙarin ganin shi ya lashe
wannan gasar ya dauke ta, da a ce ba ta yi maganar tallafi ba ƙila da zancen aurenta bai
shigo tunanin manemanta ko kadan ba, kenan kwadayin abin hannunta shi ne sila,
na sha jin samari na cewa "Don Allah in aka sami wata hajia mai neman miji
a tuntube su" kar ka ce ko suna neman su yi aure a bagas ne, abin hannunta
suke kwadayi.
.
Shi ya sa za ka yi mamaki
idan na ce maka mata na yaudarar maza don su aure su, kamar yadda kowa ya san
maza kan yaudari mata, wallahi yanzu mace talaka za ta gyangyanda da ƙyar ta sayi mota da kayan ƙawa, ta sami namijin da ya
yi mata ta yi masa ƙaryar arziƙi, ta nuna masa tana da kudi da dukiya mai
dimbin yawa amma custom sun riƙe, da dai sauran maganganu, sai ta samu ta
aure shi daga bisani ya gane cewa ashe ba da gaske ba ne ga shi kuma ya riga ya
kama kansa dole ya haƙura, kwadayi ya zama dalilin ƙara aure.
.
Da yawa mazan dake neman
yaran masu kudi ba don tsabar sha'awa da soyayyar dake tsakaninsu ba ne kawai,
har ma da lissafin cewa in mutum ya auri wance to fa ya warke , na taba jin
wata hajiya da wani matashi ya tsaya sai ya aure ta, ba ta ƙi shi ba, sai dai ta
gindaya masa wani mummunan sharadi ne na sai ya rabu da matarsa, wato uwar
'ya'yansa, ya jujjuya maganar kuma ya yi shawara da abokai da iyaye a ƙarshe aka tsaya kan ya haƙura kawai tunda iyalinsa
ba su yi masa komai ba, abin baƙin ciki ya yarda kan ya haƙura din, sai kuma can daga
baya ya sake dawawa ya saki matarsa ya auro ta.
.
Wani abokina na kusa ya
taba gaya min cewa ya yi mu'amalla da wata 'yar gabashi, har ya kusa zuwa
gidansu sai ta gaya masa cewa ita fa ba sa zama da kishiya. Ya ce to da ma yana da mata biyu. Sai ta
ce ai da sauƙi tun da ba su kai 3 ba, kuma za ta iya riƙe yaran gaba ɗaya. Da ya
tambaye ta ma'anar maganarta, sai ta ce ya sallami sauran matan kawai ta ishe shi komai! Auren
da ba a yi ba kenan, domin ta kai ga uwayen tsohuwar matar sun taka masa burki
gami da gaya masa irin matakin da za su ɗauka matuƙar ya saka musu 'ya. Allah
ne dai Masani. Wata ƙila ba su ne kaɗai dalilin fasa auren ba.
.
A hadisin Annabi SAW dai
mun fahimci cewa dukiyar mace ma kan zama babban dalilin da kan sa mutum ya yi
aure, koda yake ba wannan ne shahararre a matattararmu ba amma tabbas yakan
faru, wasu kan ƙara aure a dalilin abin hannun mace, ba wai don suna da buƙatar ƙarin auren ba, har ma ka
ji abokansa suna masa murna wai ya auna arziƙi, wasu ma sukan yi
sha'awar a ce sun sami wannan damar koda kuwa abokansu ba su ji dadin nasu
auren ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.