Ticker

    Loading......

Zan Ƙara Aure // 30: Da Kanta


Wata ma da ta lura cewa mijin mai son mata ne, sai ta ba shi shawarar ya auro wata ƙawarta kyakkyawa. Ta tsaya kan sai ya aure ta ɗin. Ita ta haɗa. Da aka tambaye ta dalilin yin hakan, (don ƙawayenta suna ganin wautarta) sai ta ce ta san halin mijinta sarai! Da ya je ya jajuɓo musu abin da zai dame su gwara ta yi maganin abinta tun farko. In ta bar shi ya auro mata wace za ta rikita mata gida fa? Gwara wannan ba mace ce mai son fitina ba. Kuma ta san cewa...


Zan Ƙara Aure // 30: Da Kanta

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunna

Bai cika faruwa ba amma yakan faru ɗin, wato mace da kanta ta ba ka shawarar cewa ka ƙaro aure, duk da cewa duk mace ba ta son kishiya amma akan shiga wani yanayi da ita da kanta za ta ba ka shawarar cewa lallai akwai buƙatar ka ƙara auren masamman in ta dubi amfanin yin hakan, misali ta hango cewa suna da buƙatar da wanda zai riƙa tallafa musu bayan sun girma ƙarfinsu ya ragu, koda yake mata da yawa ba su da wannan tunanin sai dai da yake akan samu, dole mu kawo shi anan, a tarihi ma mun karanta cewa Sara, matar Annani Ibrahim AS, ta sami baiwa mai suna Hajar, sai ta ba wa maigidanta, wato Annabi Ibrahim, tana tsammanin cewa ƙila Allah ya azurta su da samun diya wanda zai tausaya musu nan gaba.
.
A kwanaki ma mun kawo matar da ta riƙe kambu kan cewa ba dalilin da zai sa mijinta ya ƙara aure don cutar da ta samu na rashin haihuwa ba ita ta ba wa kanta ba, amma daga bisani da ta ga ba yadda za a yi sai ta sauko suka daidaita kan cewa ta yarda da wace za a auro ɗin, sai dai tana haihuwa suka sami magaji za a sake amaryar, maigidan ya yarda, aka yi auren kuma ya cika alƙawarinsa na sakin amaryar bayan an sami yara guda biyu, wato dai ƙara auren da yardar matan ne.


Na kuma karanta labarin wata baiwar Allah da aka ce tana azumin rana da sallar dare, ba ta da wata sha'awa ta shimfida ko ta namiji in ba ibadarta ba, kullum dare sai ta yi wanka ta sha ƙamshi ta je ga maigida, in ta ga ya yi barci sai ta lababa ta tashi ta kama ibada, har dai ta fara ba shi shawarar ko zai ƙara aure, domin a ganinta za ta sami wasu 'yan kwanaki da maigidan ba shi tare da ita, za ta yi ta ibadar Allah da bauta masa, shi kuma da ya ga cewa hakan amfaninsu ne su biyu sai ya yarda ta yi masa auren, ashe ma ita ta yi masa ba wai amincewa kawai ta yi ya ƙara ba, mu anan mamaki ake yi idan cikin sauƙi mace ta amince wa mijinta ya ƙara aure ba tare da wata hayaniya ba, sai ka ce haƙƙinta ne sai ta yarda kafin ya ƙara ɗin.
.
Sai kuma wata mata da na sami labarinta, wace tana son haihuwa kuma Allah SW kan ba ta cikin, amma ba a jewa ko'ina sai cikin ya zube, to maigidan yana nuna cewa yana son yara, in ya ga yaran wasu sai nan da nan ya dauke su ya riƙa wasa da su da nunawa a bayyane cewa yana buƙatar Allah ya ba shi magaji, to ganin irin yanayin da suke ciki sai matar ta ba shi shawarar ya ƙara aure kawai, ƙila Allah ya azurta su da wanda zai taimaka musu a gaba, dama ita yake tunani, wannan damar da ya samu sai ta zama dalilin da zai ƙara auren, Allah cikin ikonsa sai ya azurta su da yaran.
.
Akwai wata da take samun cikin amma takan sha baƙar wahala a wurin haihuwa, har likitoci suka fara ba da shawarar lallai a dakatar da maganar haihuwannan, to ita kuma ta lura maigidanta ba abinda yake so kamar yara, don haka ta fara ba shi shawarar ya ƙaro aure, don in aka sami wanda za ta biya masa buƙata zai daga mata ƙafa, duk da cewa ba buƙatarsa kadai ta kalla ba wurin ba shi shawarar ƙarin auren har da lafiyarta ita kanta, amma fa ba shi shawarar ya ƙaro auren ya zama babban dalili na ƙarin auren.
.
Wata ma da ta lura cewa mijin mai son mata ne, sai ta ba shi shawarar ya auro wata ƙawarta kyakkyawa. Ta tsaya kan sai ya aure ta ɗin. Ita ta haɗa. Da aka tambaye ta dalilin yin hakan, (don ƙawayenta suna ganin wautarta) sai ta ce ta san halin mijinta sarai! Da ya je ya jajuɓo musu abin da zai dame su gwara ta yi maganin abinta tun farko. In ta bar shi ya auro mata wace za ta rikita mata gida fa? Gwara wannan ba mace ce mai son fitina ba. Kuma ta san cewa ita ta haɗa auren. Ko don haka za ta sassauta mata ta wani ɓangaren ita da 'ya'yanta.


Kowa da misalin da ya sani, indai game da mata ne, masamman wadanda suke ba da damar a kawo musu kishiya, ba su da yawa saboda kusan duk mata abinda yake zuciyarsu shi ne rayuwa su kadai daga su sai wanda suke nuna cewa suna matuƙar ƙaunarsa, shigowar wata zai kasance ne don bata gidansu ko korarsu ma gaba daya, da wannan suka ƙyamaci maganar kishiya gaba daya, shi ya sa ba sa iya tunanin shigowarta bare har su ba da shawarar a kawo ta, sai dai wadanda ba su da wannan a zukatansu suna ganin sauƙin abin, amma kamar yadda na ce ne: Ba su da yawa.
.
Mace ita da kanta ta ba wa miji shawarar ya ƙaro aure wani sa'i yakan kasance ne don amfaninsa da kwanciyar hankalinsa, tana ganin cewa in hankalin nasa ya kwanta tabbas ita ma nata ya kwanta, wani sa'in kuma tana buƙatar hutu ko yin nesa da shi don magance matsalolinta wadanda ba sa buƙatar sa kullum, sai dai ko wani da ya kwanta rashin lafiya abin ya ƙazanta matar ta ce ya auro wace za ta yi masa wannan hidimar, an ce wai ya warke ya rabu da ita, Allah ne masani, amma a dunƙule, mace ita da kanta za ta iya sanya mijinta ya ƙaro aure, koda kuwa ita ce za ta amfana da auren nasa ko kuma shi.

Post a Comment

0 Comments