Ticker

Zan Ƙara Aure // 31: Zuwa Wurin Bokaye


Na taɓa zuwa wata unguwa zan wuce sai na ga tarin jama'a ana tsattsaye kamar akwai wani abu dake faruwa. Na ɗan leƙa na ga ko meye sai na ji wasu na ta zage-zage wai ƙanwarsu ta zo neman magani a wurin bokan don ta auri wani saurayi da suka yi cuncurundo a ƙofar gidansa. A maimakon ya yi mata aikin da ta saka shi sai ya yi mata aika-aika, inda ya...


Zan Ƙara Aure // 31: Zuwa Wurin Bokaye

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Wani abu ne da ya kamata a ce mutum ya yi nazari a kai, amma wanda ya yi nisa zai yi wahala ya ji kira, wata ce take ta ba wa wani oganta shawarar cewa lallai su ga wani malami saboda taka wa mahassada burki, ta ce irin wannan matsayi da Allah SW ya kai shi dole ya tara mahassada, wadanda in ba su yi tunanin tunkude masa ni'imar da Allah ya yi masa ba za su yi masa wani ƙullin da ba zai ji dadin wannan alkhairin da ya samu ba, to da yake an ce masa ba boka ba ne ya ji dadi sosai.
.
Amma me zai faru? Lokacin da ya sami bokan aka ba shi maganin da yake buƙata sai kuma aka gaya masa cewa in yana so za a gaya masa inda arziƙinsa yake, da ya buƙaci hakan sai ya ce masa kar ya rabu da wannan matar, arziƙinsa yana tare da ita, ya yi ƙoƙari ya aure ta, sai ga magana ta canza, bayan wani dan lokaci sai ta zama matarsa ta biyu, boka ya zama dalili, duk da cewa ƙaryarsa ya kantara amma dai ta cika burinta na mai da mutumin mijinta ta hanyar bokan, wai kuma tana son auren ya yi albarka.
.
Sai dai wani lokacin abin yakan zo da akasi, an sami wani lokacin da na kawo labarin wata mata da ta je wajen boka tana son ta sami maganin haihuwa, don ta yi na Baturen har ta gaji ba wani labari, daga bisani sai ta yanke cewa kawai ta je wurin malam zai taimaka, ashe kai malam ya ƙyasa, a maimakon ya ba ta maganin haihuwa sai ya shiga dura mata maganin da za ta bar gidanta, rana tsaka ta ce gidan ya yi mata baƙi, kowa ya yi rarrashi har ya gaji amma ta ce sam ba za ta zauna a gidan ba, ai kuwa ta fita, bayan dan wani lokaci sai malam ya aure abarsa, daya daga cikin illolin zuwa wurin boka kenan, ya yi ta biyu da ita.
.
Na taɓa zuwa wata unguwa zan wuce sai na ga tarin jama'a ana tsattsaye kamar akwai wani abu dake faruwa. Na ɗan leƙa na ga ko meye sai na ji wasu na ta zage-zage wai ƙanwarsu ta zo neman magani a wurin bokan don ta auri wani saurayi da suka yi cuncurundo a ƙofar gidansa. A maimakon ya yi mata aikin da ta saka shi sai ya yi mata aika-aika, inda ya ɗirka mata ciki. Ta kawo maganar aure don su samu su rufa wa kansu asiri ya ce bai san wannan maganar ba, har sai da 'yan uwanta suka ji abinda ya faru suka biyo shi da sanduna za su ba shi kashi, an ce dai dole ya aure ta a matsayin matarsa ta biyu.
.
Boka bai isa ya saka wani mutum ya ƙaunace ki saboda Allah ba, ko kin tsaface shi kin aure shi za a sami lokacin da zai karye, ke kuma kin shiga uku kenan, kar ki yarda da zuwa wurin wani ƙato don neman taimako kamar yadda suke fada, wata ke ba da labarin tafiyarta zuwa wurin wani malami neman yadda ba za a yi mata kishiya ne ba, a ƙarshe aka raba auren kuma bokan ya ƙara da ita, wasu sai bokan ya aikata ma-sha-ansa da ita sannan ya biya mata buƙata, buƙatar da ma ba dorarriya ba, akwai bokan da zai ce wa mace buƙatunta ba za su taɓa biya ba sai ta bar gidan da take, ko tana son gidan haka za ta bari.
.
Ga ma wasu matan da bokaye ke aurensu ba ta hanyoyin ganinsu a makarantu ko kasuwanni ko wuraren sana'a ba yawancinsu ma suna da aurensu, in suka je neman taimako kamar yadda suke fadi sai bokayen su raba aurensu da mazansu su yi na biyu ko fiye da su, to matan aure ma kenan bare wace ta je neman maganin farin jini, shekarun baya wata bazawara ta tafi wurin boka neman maganin farin jini, ko ya aka yi oho, sai muka ji ana shirye-shiryen daurin aure, mun ji labarin wani tsoho da ya auri mata sama da guda hudu, na yi ta mamaki wai ba musulmi ba ma malami ne da aure sama da hudu! Sai na ce mata yanzu kwadayi ya yi musu yawa, nan da nan wani abokin aikina ya ce ai ba da son ran matan yake aurensu ba, duk wace ya ƙyalla ido ya gan ta sai ta ji ba wanda take son zama da shi irinsa.
.
A dunƙule dai bokaye masu amfani da sunan malanta suna siye hankalin mata daga ƙarshe su sa matan su kashe aurensu ta wurin tsaface su, wannan zuwan da mata ke yi wurin bokaye babban dalili ne da malaman kan yi amfani da shi wajen auresu, babban gargadin da za a yi wa mata anan shi ne su sani cewa ba fa dole ne su sami biyan buƙata a wurin bokayen ba, zai yuwu ma su fitar da su a gidajensu su raba su da masoyansu da 'ya'yansu su aure su a ƙarshe, ribar ƙafa kenan wai kura ta taka kwado.

Post a Comment

0 Comments