Wani sa'in ko unguwarku ɗaya da
mace ba dole ba ne ka san ainihin haƙiƙanin kalar jikinta, bare kuma a ce ba
gari guda ba. Matan
na kallon ma'aunin da muke auna su da shi ne. Da a ce muna kallon kyawun hali ne sama da
hasken jiki, to da ba
yadda za a yi su riƙa
kashe kuɗinsu
wajen gyaran jiki. Na taɓa jin
wanda ya ce Allah ya ba shi farar mace ko ya take. Ganin irin wannan fahimtar
ya sa mata suke ƙoƙarin komawa farare, ko da kuwa duk mazan baƙaƙe ne. Duk wani aure da za a ɗaura ka kalli mijin da matar....
Zan Ƙara Aure 32: Kafar Sadarwa
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Za mu iya cewa hanyar salula
hanya ce ta ƙarin aure amma ba ta
isa ta zama ingantacciyar hanya ita kaɗai
ba. Akwai abubuwa guda
biyu da ake la'akari da su wurin zabin mace, wato kyawun ɓoye da na sarari. Kowa na fatar na ɓoyen ne. Su
kuma suna iya nuna na sararin ne kawai. Shi ma ɗin duk
an yi coge a ciki. Duk kyakkyawar
da za ka gani a kafofin sadarwa rabi ba gaskiya ba ne. Maɗi ake
wa talla ba zuma ba. Wannan
ya sa maza suka fara ɗari-ɗari da zaɓin mace a kallo ɗaya, masamman na ranar salla ko wani biki ko
suna. Idan mace ta sami
dilka mai kyau irin na mutanen Borno ɗin nan sai ka rantse da Allah fara ce sal, ashe
a-cuci maza ta yi.
Wani sa'in ko unguwarku ɗaya da
mace ba dole ba ne ka san ainihin haƙiƙanin kalar jikinta, bare kuma a ce ba
gari guda ba. Matan
na kallon ma'aunin da muke auna su da shi ne. Da a ce muna kallon kyawun hali ne sama da
hasken jiki, to da ba
yadda za a yi su riƙa
kashe kuɗinsu
wajen gyaran jiki. Na taɓa jin
wanda ya ce Allah ya ba shi farar mace ko ya take. Ganin irin wannan fahimtar
ya sa mata suke ƙoƙarin komawa farare, ko da kuwa duk mazan baƙaƙe ne. Duk wani aure da za a ɗaura ka kalli mijin da matar.
To ya batun hotunan da ake
liƙawa a kafofin sadarwa na zamani don
neman dace da wanda za a aura? A nan
akwai mahangu guda biyu waɗanda galibi su aka saba da
su:
a) Mahangar addini wacce
ita kullum laluɓen
abubuwan da shari’a ta
gindaya take yi. Ta halasta na ƙwarai
ta haramta na banza ko da
kuwa yawacimmu muna jin daɗinsa ko kuma muna ganin
kyawunsa, masamman bayyana ado na ƙarshe har ta kai ga nuna abubuwan da za su tayar da
sha'awa ba tare da damuwa da abin da
zai biyo baya ba.
b) Mahangar al'ada, wacce ita kuma ta fi karkata ne zuwa ga abubuwan
da aka saba tun tale-tale ko aka gada iyaye da kakanni har zuwa yanzu. Galibi ana auna kyawun abin ne ko muninsa da
al'ada da kuma hankali. In bai
saɓa musu ba to yana da
kyau. Mu Hausawa waɗanda
galibimmu Musulmai ne al'adarmu na tafiya da addini ne. In ta saɓa masa to dole ne a yi watsi da ita a riƙi addinin. Shin za mu ce neman aure a
kafofin sadarwa ya dace? In muka duba bayanan sama za mu fahimci cewa in dai ba
za a yi bincike ba, to za a iya zaɓo tumun dare. Hakan kuma bai dace ba.
Na yi zamani da wacce ta ce min ta san wani da ke hanyar gidansu wanda ya fara nemanta. Sai da suka saba da juna ta
san cewa manemin mata ne.
Wata
ma ana dab da ɗaura
aure ta fahimci cewa ba namiji ba ne.
Ta
fasa auren. Ta yi
bincike ke nan. Wata kuwa an ɗaura
auren amma makonta guda ta fito. Ita ma
matsalar rashin mazantaka ce.
Wata
ta ce baƙin mugu ne. Ba za ta iya zama da shi ba. Wata tana so ne ta sani in
za ta iya rabuwa da shi, ƙazami
ne. Wata
tana kukar fitina ne a shinfida. Duka
dai za ka taras matsalar rashin bincike ce.
To kamar wanda zai ga hoton
mace a WhatsApp ko Facebook ya ji kawai ya kamu da sonta, har ma ya gaya mata
cewa shi fa wallahi yana jin in bai aure ta
ba rayuwarsa sam ba ta da amfani...
Irin
wannan in ta yarda gaskiya ta ga dama ne, domin sha'awarta yake ji. Bai ga surarta a zahiri ba. Wato lafiyarta lau ko tana da naƙasu, haskenta na shafe-shafe ko ma na'ura ce ta ƙara mata? Wata ma ƙila ta yi gyarar fata ne! Sannan ɗabi'u
da addini waɗanda tun asali su ne manyan dalilan da
suke sa mutum ya so mace za ka taras ba abin da
ya sani a ciki. Ta yaya za ki karɓi cewa ƙaunar
gaskiya ce ba sha'awa ba?
Sha'awa lokaci ɗaya tal
take shiga,
kuma mutum kan iya yin komai a dalilinta. Kafofin
sadarwa kaf ɗinsu
tallanta ta suke yi.
Mu
maza sai su tallata mana kyau.
Mata
kuma a tallata musu wadata. In na
sha shadda mai mugun tsada ta sha aiki sai na jingina da babbar mota a gaban
wani tsararren gida ga waya mai mugun tsada a hannuna na ɗauki hoto na turo kafofin sadarwa. Da mace ta gani sai ta ce
wannan wankan na manya ne.
Cikin
sauƙi abubuwa za su gyaru.
An yi haka barkatai! Ina son na ce kafofin
sadarwa a yau su ne a sahun farko wajen sada ma'aurata masu ƙoƙarin
yin auren fari ko ƙarawa. A nan ba cewa muke halas ko haram ba. Muna nuna cewa sun zama hanyar da ma'aurata
suke bi a yau wajen tabbatar da aurensu ya ɗauru. Na
san ma'aurata da dama waɗanda kafofin sadarwa suka haɗa su. Wasu
daga nisan duniya, wasu a kusa.
Akwai
wata Ba'amurkiya da ta so ɗan
Somaliya kuma ta aure shi ta
wannan hanyar. Akwai kuma wani Ba'amurke
da ya haɗu da
wata a Iraƙi ta hanyar kuma ya
aure ta. To bare
a Nijeria daga Borno zuwa Legas!
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.