Ticker

Zan Ƙara Aure 33: Wurin Buki

A wuraren biki kuwa abubuwa biyu ne ko uku a haɗe. Na farko dai ka san cewa budurwa ce, sannan akwai dalilin da zai sa ka iya yi mata magana ko ma ka bayyana muradinka kai tsaye. Na uku kuma samun damar...


Zan Ƙara Aure 33: Wurin Buki

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Wuri ne da yake tara mutane daban-daban masamman 'yammata da samari. Su samarin sun san da 'yammatan don haka suke shan ado sannan su sami ɗan abin da da su za su iya janyo hankalin matan da shi. Su ma matan saboda yau da kullum sun san abubuwan da mazan ke buƙatar gani a jikinsu. Ba su cika kula da hanin addini ko na al'ada ba a irin wannan lokacin. Buƙatarsu kawai su samo wanda za su rayu da shi.

Biki ko na salla ne 'yammata kan sha ado da sabbin kaya, bare bukukuwan aure da aka mai da su wuraren samun samari. Idan da za a ƙirga matan da suka haɗu da mazansu a wuraren bukukuwa Allah ne kaɗai ya san iyakarsu. Shi ya sa wani sa'in akan tura wasu yaran su yi wa wata ƙawance. Ko dai su sami mazan a cikin abokan ango ko kuwa mahalarta bikin. Yarinya kan sha ado na wuce imanin maza, ta riƙa rangwaɗa tana ririta ajinta daidai da yanayin wurin. In ustazai ne ta sha hijabi ƙila har da niƙabi. In ta je wajen 'yan boko kuma gyale ga ɗaurin ture-ka-ga-tsiya.

Irin wannan in namiji ya ga kwalliyar da ta tuno masa rayuwar makaranta sai ka ga ya fara ɗan matsowa kusa. A ƙarshe sai labari ya canza. Maza da yawa cikin waɗanda muka tattauna wannan batun da su sun tabbatar da cewa gidajen biki hanya ne mai ƙarfi na samun damar ƙara aure. Ba ma batun 'yan mata kaɗai ake yi ba, hatta zawarawan, sun sami damar ƙara auren ta haka. Wata dama ce da namiji kan samu ta keɓewa da mace wacce ba don bikin ba da wahala hakan ta faru.

Na zauna cikin wasu matattarun na ga al'adunsu sun ɗan bambanta da namu. Mu ɗauki ƙasashen Larabawa a matsayin misali. Lalle duk da cewa adon mace ne amma ba kowace mace take da hurumin yi a lokacin da ta so kwalliya ba. Lalle adon matar aure ne. In tana so, kuma takan yi shi a hannu biyu har ya yi baƙi. Budurwa ba ta yin lalle sai ja a lokacin biki, kuma sama-sama a hannu ɗaya, wato hannun hagu. Kana ganin ta ko a ina ne ka san ba matar aure ba ce. Namiji na da hurumin da zai tsaya da ita masamman a lambun bakin hanya ko a makarantu.

Mu kuwa ba wata alama da za ka iya rabe matar aure da budurwa. Babu a suturar jikinta ko yanayin lalle. 'Yammata kan yi adon lallensu a duk lokacin da suka ga dama, da duk launin da suke so a kowani hannu. Rashin bambance budurwa da matar aure ya sa maza ba sa iya tunkarar mace in ba su santa ba. Ko gilmawa ta yi sai dai ka ji ana tambaya "Wannan budurwa ce ko matar aure?" In wani ya sani shi ne yake iya yin bayani dalla-dalla. Har da haka tunkararta ba tare da wata 'yar sila ko da ƙanƙanuwa ce ba akwai wahala.

A wuraren biki kuwa abubuwa biyu ne ko uku a haɗe. Na farko dai ka san cewa budurwa ce, sannan akwai dalilin da zai sa ka iya yi mata magana ko ma ka bayyana muradinka kai tsaye. Na uku kuma samun damar tsayuwa wuri guda na wasu 'yan kwanaki. Ka bar batun jahar Jigawa da Kano da suke kusa-kusa, har daga Barno, Adamawa da Taraba 'yan mata kan zo biki. In Allah ya yi da rabonsu sai ka ga wanda suka yi magana da shi ya biyo sawu.

Bar batun 'yan mata, zawarawan ma na ga suna yin wani abu. Ana zaune sai ka ji wata ta ce wa wani ɗan uwanta "Wane! Zo nan na yi maka mata. Ga wata bazawara ka rufa mata asiri." Ko wata magana makusanciyar haka. Sai ka ji tana ta ƙoƙarin kuɓutar da kanta cikin raha. A haka ne wasu mazan suke gane cewa ba fa matar aure ba ce. Tana kasuwa. Wanda Allah ya tsaga da rabonsa ya ɗauka. Ita da kanta takan nemi dalilin da za ta bayyana cewa ba fa matar aure ba ce.

A taƙaice gidan bikin aure ko na suna wurare ne da ke komawa filin baje kolin ma'aurata. Da in ka ji bikin suna to manyan mata ne, amma yanzu har da 'yan mata, kuma dai muraɗin kenan. Mai son yin aure ko ƙari sai ya gwada, in Allah ya tsaga da rabonsa sai ya ɗauka. Ko dai namiji ya sami mata, ko kuma ita matar ta sami mijin aure. Na ga misalai a kan haka da dama.

Post a Comment

0 Comments