Da
yawa mutane masu himma sun sami abin da suke buri. Wani
zai gaya maka shi babban soja ne, kuma wallahi tun yana ƙarami bai da buri sai
aikin sojan. Wani
zai ce maka likita ne shi. Tun yana ƙarami burinsa ke nan. Wasu
lamuran Allah kan dubi zuciyoyimmu ne ya...
Hanyoyin Cin Nasara 10:
Ba Wa Ƙwaƙwalwa Damar Aiki
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Mutane sun karkasu zuwa
gidaje daban-daban, akwai masu ƙoƙari waɗanda
kullum cikin tunanin bunƙasa
ayyukansu suke yi, in dan kasuwa ne wanda yake sayar da gwanjo, yakan fara
tunanin cewa nan gaba fa zai iya tsallake wannan sana'ar zuwa wace ta fi ta,
kamar sayar da sabbin kaya waɗanda
aka yiwo odarsu daga ƙasashen
waje, in mai sayar da takalma ne a bakin titi yana bin motoci da gudu, zai fara
tunanin cewa nan gaba fa jarinsa zai yi yawa zai kama shago, zai zama babban
dan kasuwa har a mutane zu riƙa
zuwa suna sarin kaya a wurinsa.
.
In kuma malamin makaranta ne
zai fara tunanin zai zama babba har ya yi fice a fagen ilimi, zai gina makaranta
tasa mai cin gashin kanta, in karen mota ne yana tunanin zai zama direba zai
sami mota tasa ta kansa, zai zo ya sayi motoci nan gaba ya dauki direbobi yana
biyansu, waɗannan
abubuwa ba su rabuwa da zuciyoyin gwarazan mutane, waɗanda
duk abin da za su yi suna tunanin gaba, kamar mutum mai ƙaunar ibada kullum a masallaci, har ya
fara burin a ce shi ne ladanin masallacin, yau da gobe ya zama na'ibin limamin,
ko a ba shi limanci a wani masallacin, da yawa in mutum zai kama haya saboda
zai yi aure za ka ga ya fara tunanin inda yaransa za su riƙa kwana da tarbiyar da za su samu a
matattarar, bayan ko auren ba a daura ba, tsari ke nan.
.
Da yawa mutane masu himma
sun sami abin da suke buri. Wani
zai gaya maka shi babban soja ne, kuma wallahi tun yana ƙarami bai da buri sai aikin sojan. Wani zai ce maka likita ne shi. Tun yana ƙarami
burinsa ke nan. Wasu
lamuran Allah kan dubi zuciyoyimmu ne ya biya mana buƙatummu. Dubi dai waƙa da
ake ganin abar banza ce, na dubi Hauwa Kululu wace Mamman Shata ya yi wa waƙa, tana cewa tun tana yarinya ba ta
aikuwa sai in mutum zai yi mata waƙar
Shata, asali ita yariya ce ƙarama,
ba ita ce mai sayar da tuwon ba babarta ce.
.
Lamarinta ya riƙa ba masu sayen tuwon babarta al'ajabi,
kwatsam sai ga Mamman Shata din wata rana ya sauka wurin babarta, aka ba shi
labari kuma aka nemi ya yi mata waƙa,
Shata ya zauna ya waƙe ta
fes, burinta ya cika, amma fa ba arha ta sami wannan daukakar ba, sai da ta
tsaya kan burinta har ta kai ga gaci, sauran lamura da kake gani a rayuwa duk
haka suke, ba yadda za a yi mutum ya kai ga biyan buƙata ba tare da ya tsaya ƙyam kan abin da yake so ba, kullum
tunaninsa shi ne ya zan kai ga wannan ƙudurin
nawa?
.
Burina a ce na zama malami,
na fara koyarwa ne a makarantar Islamiyya ta dare, a hankali har na dawo ta
safe, na koma furamare, na fara karantarwa a sakandare da ta manyan mutane, na
karantar a kwaleji kafin yanzu na komo jami'a, tafiyar ba mai sauƙi ce ba kamar yadda na karanto haka,
akwai jarabowoyi a tsakiya kala daban-daban, wasu har ba ka son ka tuna su, ba
ka ƙaunar ka ga wanda ya san su, burin mutum
a zuciya kawai ya isa wurin da yake hari, kuma zai isa din amma sai da taimakon
Allah SW, ke nan tun farko shi ne mutum zai fara kamawa, in ya amince maka dole
a baka, duk abin da za ka yi kar ka manta da mahaliccinka.
.
A cikin mutane akwai waɗanda
suke son ci-gaban, kuma suna ganinsa tare da wani, amma ba sa ƙaunar su motsa, ba sa iya yin tunanin
cewa za su zama wani abu nan gaba, wanda yake yankar farce dole ya saka cewa
zai zama wani abu yadda nan gaba shi ma za a zo a yanke masa, bunƙasa sana'a dole ne in ba haka ba nan
gaba za a rasa mai yi, amma ci-gaba ma wajibi ne, ba yadda za a yi ka ce kaza
na gada kansa zan mutu, bai zama dole sai ka canja sana'a ba, amma ka yi
tunanin ya za ka bunƙasa
shi har mutane birjik su ƙaru
da kai?
.
Ba yadda za ka bunƙasa gadon mahaifinka sai ka yi tunanin
kawo na'urorin da za su sauƙaƙa aiki su inganta shi ta yadda za a riƙa yi da yawa, ko a canja salo, duk abin
da ka sani a duniyannan za a iya inganta shi, na san wani yaro da ya taso a
gaban mahaifinsa tela, yanzu ya zama babban tela ya kawo manyan kekuna masu yi
wa kaya ado, da haka ya mallaki gida na kansa da ma'aikata masu yawa, sana'ar
dinkin ce dai ba a canja ba, amma an ƙawata
ta, an habbaka ta, an inganta ta, wannan ya sa aka ƙara samun dafifin jama'a dake burin
ganin an yi musu dinki a shagon.
.
Duk wani babban mutum da
kake gani wanda ya ci nasara a rayuwarsa ta hada-hada, ko cinikayya, ko wani
fanni na aiki ko sana'a in zai gaya maka hanyoyin da ya bi don ganin ya cimma
burinsa za ka taras sai da ya ci baƙar
wahala, anan akwai abubuwa guda biyu:-
1) Ya sa abin a ransa don
ganin ya cimma burinsa, ya yi ta bin hanyoyi daban-daban don ganin hakan ya
wakana, ko dai karatu, ko mutanen da yake ganin za su taimake shi, ko bibiyar
shawarwarin da za su isar da shi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.