Kowa buri yake ya haɗa biyu;
ga kuɗi ga ilimi. Hakan kuma ba zai haɗu ba sai da karatu. Duk ɗan
kasuwan da yake da ilimi ya fi sanin yadda zai bunƙasa kasuwancinsa, to bare...
Hanyoyin Cin Nasara 12:
Karatu Fa Dolone Ne
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Ko ni nakan fadi haka, amma
kuma wanne? Karatun addini ko na boko? Ga wanda ya san akwai bambanci ke nan,
ni a iya sanina ba ilimin da addini bai zo da shi ba sai dai in ba shi da
mahimmanci ko amfani ga dan adam, ilimin rayuwannan da kake gani shi ne mafi
mahimmanci a wurin kowa don haka dole ka yi shi in kana son cin nasara a
rayuwarka, za ka taras wani ya yi Furamare ne ya tsaya, tsakani da Allah ba za
ka hada shi da wanda bai taba taka makaranta ba, wani ya yi Sakandare ne ya ce
"Nan zan tsaya".
.
To irin wannan da ya tsaya a
Sakandare ba za ka taba tunani a zuciyarka zai iya zama malamin jami'a ba, ko
malamin Sakandaren da ya yi ba zai zama ba sai in ya dawo ya ci gaba da karatu
zuwa gaba da Sakandaren, haka mutumin da a rayuwarsa matuƙin mota ne da ya koya a tasha ya iya, ya
kwashe kimanin shekara 25 yana tuƙi
rana daya ba zai ce kai na gaji yanzu jirgin sama zan koma tuƙi ba, iliminsa bai kai nan ba, komai
gwanancewar mutum a tuƙin
keke rana guda ba zai hau babur ya tuƙa ba
sai in ya koyi yadda ake yi a karance ko a aikace.
.
Kamar bakanike ne, don mutum
ya yi shekaru yana gyaran keke ba zai ce yau na koma gyaran mota don dukansu
biyu hawansu ake yi ba, kamar yadda ka san ni da kai shekarummu guda ni ina da
mata 2 kai ba ka taba aure ba ba za ka ce masaniyarmu da mace guda ne ba, shi karatu
komai kasawarsa dole sai an yi shi, in ba ka taba aure ba tashi guda aka ba ka
mata biyu, ni kuwa na taba zama da su a lokaci guda matsalar rayuwa ta sa na
rabu da daya ko dukansu biyu dole yadda zan tafiyar da sabbin matan ya bambanta
da yadda za ka yi, ba komai ne ba sai karatun da na yi a baya, sau da yawa
kallon baya kan taimaka wa mutum ya san yadda zai tafiyar da gaba.
.
Amma fa gaba daban baya
daban, mai son cin nasara a rayuwarsa kar ya taba raina ilimi don koya yake, a
lokacin da mutum ya yi Furamare ya ce daganan na gaji ke nan abokan karatunsa
za su wuce gaba, Ƙur'ani
kuma ya tambayemu a sifar ƙalu-bale
ya ce: "Shin masana da marasa sani za su yi daidai?!" Ya ce "Ko
a kwatance ba daidai suke ba" duk wanda ya wuce ka har abada ya sha
gabanka, sai dai ka fi shi a wani abin ko ka dawo ka shiga gabansa, yadda ka
san jahilan masu kuɗi ba su sha'awar su zama
talakawan masu ilimi, haka talakan malami bai da burin zama jahilin mai kuɗi.
.
Kowa buri yake ya haɗa biyu;
ga kuɗi ga ilimi. Hakan kuma ba zai haɗu ba sai da karatu. Duk ɗan kasuwan da yake da ilimi ya fi sanin yadda
zai bunƙasa kasuwancinsa, to bare babban
ma'aikaci, gwamnati kanta takan ƙimanta
mutum ne da yanayin matakin karatun da ya taka, ba cewa muke kowa sai ya yi
zurfi a karatun boko ba, amma iya karatun mutum iya inda zai tsaya, wanda ya
tsaya a facin keke bai yalwata tunaninsa zuwa na babura da manyan motoci ba
tabbas zai mutu a facin keke, domin iyakarsa ke nan.
.
Wanda yake ganin yana da
kayan facin keken ƙila
yana buƙatar inji ne kawai da manyan sifanonin
da za su taimake shi wurin kwance tayar mashin, sai ya fara tara kuɗin
inji, ya sayi kayan aiki tabbas wata rana za ka ji ya fara facin babur, ƙila kuma ya bar wa yaransa facin keke,
daganan zai fara saka wa mota iska ana biyansa masu motoci su fara zuwa a
tsammaninsu har faci yana yi, daganan zai fara tunanin to me zai hana ya fara
facin ma? Ƙila ya fara tattauna
wasu batutuwa da masu facin mota din, wata rana sai dai ka ji ya fara sayo
kayan aiki, kamin ka ankara sai dai ka ga motoci har ya fara facin tayoyinsu,
ya fadada tunaninsa ke nan.
.
Duk abin da mutum yake
sha'awa a rayuwa ya yi karatu kawai, kar ya damu da abin da yake karantawa idan
ya saki layi tun farko, ya fara tunanin yadda zai kai ga burinsa kawai matuƙar yana tunanin cewa rayuwarsa ba za ta
yi masa dadi ba sai da cikan burinsa, na san wani babban dan jarida wanda
kimiyar noma kawai ya karanta sai ga shi ya sami kansa a fagen jaridar da ya
jima yana haƙilo, na san wanda
addinin muslunci ya karanta, ba harshe ba bare a ce suna kusa, shi ma dai ya
zama babba a harkar jarida yana gogayya da manyan 'yan jaridu a yau, na kuma
san wanda ya karanta aikin likita kuma yana da buri game da harkokin addini,
shi ma yau daya ne daga cikin manyan mutanen da ake alfahari da su a duniya ta
fannin ilimin addinin.
.
Duk
waɗannan
sun cimma burinsu ne ta wajen karatu koda kuwa abin da suke nema bai yi daidai
da karatun da suka yi ba, sai dai kuma karatun ya ba da gudummuwa gwaggwaba
wurin cimma burinsu na samun abin da suke so a rayuwa, shi karatu ko ba ka riƙe biro ba, ba ka zauna a aji ba sunansa karatu,
ba kuma za a taba hada ka da wanda bai yi ba har abada, kusan kowa ya san haka,
shi ya sa in mutum ya yi kwaba za ka ji ana cewa "Ka ji, wai Dr ke nan!"
Duk kuwa da sanin cewa kwabar da ya yi ba a fanninsa ba ne, ma'ana karatun da
ya yi bai taimaka masa da komai ba a wannan wurin.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.