Waɗanda suka sayi
filaye, motoci da sauransu in ba sa'a aka yi ba nan da nan za su kadar da su su
bi kan kuɗin
su lashe. Da
a ce kansilanmu malamin makaranta ne, lokacin da ya sami kuɗinnan kamar ana zubo su da bakin ƙwarya sai ya sayi
wani...
Hanyoyin Cin Nasara a
Rayuwa 18: Rashin Girman Kai
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Na isa wata ƙasa a 2002 inda na kammala digirorina a
2015, idan muka lura da cewa na dan jima a can, kuma ko tun farko karatun ne
dai ya kai ni, sannan a matakin digiri wanda ko kafin na tafi ina da diploma
kuma na dan jima ina koyarwa waɗannan abubuwa za su iya ba
ni damar da zan dan lura da wasu abubuwa waɗanda
sun dan saba wa yadda na saba gani a ƙasata,
ba ina cewa sun fi mu hikima ne da jajurcewa ba, amma akwai wasu abubuwan da in
an koya za a iya magance zaman banza, bambadanci, ubangidanci, neman alfarma da
ƙarfa-ƙarfa,
a can ne na ga wanda yake aiki a gidan jarida da majalla ta ƙasa da rana, in dare ya yi ya koma wata
jami'a a matsayin mai-kula da yara yana kwana da su, yana dan samun na cefane.
.
Na ga soja a matsayin major
kuma malami ne a wata jami'a, na shiga ajinda da yake koyar da addinin
kiristanci, tsakanina da Allah bayan na gabatar da wata ƙasida sai da ya nuna min cewa ban san
komai a ƙasata ba, ni kaina na yarda da hakan,
masamman irin hujjojin da ya bayar, na ji labarin wani babban sojan sama da
yake koyar da konfuta a wata jami'ar, ni da kaina na taba ganinsa a cikin kaki
ina ta mamaki, na ga wasu masu dafa abinci a wata jami'a ashe 'yan sanda ne,
suna aikin ne idan sun cire kaki don su ƙara ƙarfin abin da suke samu a wata.
.
A lokacin da muke dalibai na
ga wani ministan ilimi wanda shi ne shugaban tsangaya ta ilimi a wata jami'ar,
akwai wani dan sanda da muka san shi, sai ga shi yana kamisho, ban sani ba in
wannan yana da alaƙa da
tsaro ko baida shi, ina kuma da masaniyar cewa ƙasata
ba ta ba da hurumin da ma'aikacin gwamnati zai yi aiki biyu ba, amma kuma ba a
hanaka ka nemi na rufin asiri a wani wurin ba, babban abin da yake ba ni
sha'awa da su shi ne babban aikin da kake yi ba zai hana su su yi wani da ake
ganin ƙasƙantacce
ne ba, tabbas akwai masu yin haka anan amma ba su ne suka fi yawa ba.
.
Zai yi wahala mutumin da ya
yi kansila a same shi ya koma ajinsa na furamare kamar yadda yake da, to bare
kuma wanda ya hau matsayin shugaban ƙaramar
hukuma, da ya koma aikinsa na baya ya gwammace ya riƙa bin 'yan uwansa 'yan siyasa su ba shi
ko su hana, matsalar da muke fama da ita kenan, na ga kansiloli a baya da suka
riƙa sayen filaye da gina gidaje suna wadaƙa da kudi yadda suke so, abin takaici ba
sa iya aiki da damar da suka samu ta wurin gina ƙaramin
kamfani ko wata ma'aikata ko shagon kayayyaki yadda in suka sauka za su koma
can don rufin asiri, da sun sauka da dan ƙaramin
lokaci sai ka ga sun lashe abin da suka tara.
.
Waɗanda
suka sayi filaye, motoci da sauransu in ba sa'a aka yi ba nan da nan za su
kadar da su su bi kan kuɗin
su lashe. Da a
ce kansilanmu malamin makaranta ne, lokacin da ya sami kuɗinnan
kamar ana zubo su da bakin ƙwarya
sai ya sayi wani fili ya gina makaranta tun da ya san kan abinnan, yana sauka
ya ƙara fadada ta ya sami hanyar da zai riƙe rayuwarsa ya dauki wasu ma aiki, yau a
ce mutum tela ne aka ciro shi aka nada shugaban ƙaramar
hukuma, da sai ya yi kamfacecen shagon teloli, ya zuba kekunan da ba ko'ina ake
samunsu ba, ya dibi ma'aikata, sannan ya yi ofis dinsa na masamman saboda
ko-ta-kwana, yana sauka ya san inda zai je.
.
Hana ƙarya na ga wani kansila wanda tun asali
shi manomi ne, dan abin da yake samu a gwamnatance ya riƙa ƙara
shi cikin abin da yake birnewa a ƙasa,
ya ƙara zama babban manomi, koda ya sauka ba
wani abu nasa da ya canja, don ko tun yana kai yakan dibi 'yan ƙwadago su shiga daji, nan ma ya taimaki
wasu, duk da cewa rayuwa ta dan sauya da ya sauka din, amma bai wani shiga
halin ni-'ya-su ba, wani tela da na sani ya sami aiki babba, kuma yana samun
kudi ba shakka, a maimakon ya ƙawata
sana'arsa ta farko ya habaka ta bai yi ba, a ƙarshe
damar da yake da ita ta kubuce masa, har muka rabu shagonso ba a daina murza
zare a cinya ba, bayan na ga wasu suna amfani da wani dan inji ƙarami.
.
Matuƙar babban matsayin da ka samu a yau na
dan wani taƙaitaccen lokaci ne da
yatsun hannunka za su iya ƙirgawa,
me zai hana ka yi wani shiri da za ka dade kana jansa bayan saukarka ko bayan
gushewar wannan damar? In ka yi hakan aikin da ka samu zai dada taimakonka ne
zuwa ga nasarar da kake sa rai da ci a rayuwarka, tabbas wasu suna da tsari,
sukan waiwayi halin da suke ciki kafin su sami kansu a irin wannan halin na
yau, sukan yi tunanin cewa in fa suka sauka za su iya komawa gidan jiya, sai su
yi wa kansu tsari.
.
In
a baya mutum ya karanci likitanci ne amma bai fara aiki ba saboda halin da ake
ciki na ƙarancin gurabun aikin, sai Allah ya tarfa wa garinsa
nono ya sami wani muƙaddashin
ƙaramar hukuma na riƙo, me zai
hana ya ririta dan kuɗin
da yake samu wurin gina ƙaramin
asibiti, ya riƙa kawo kayan da ake buƙata a hankali yadda kafin ya sauka ya gama
tanadar duk abubuwan da ake buƙata?
Da farko dai in ya sauka zai ci gaba da aikin da ya karanto a wurin da shi ne
shugaba, sannan kuma zai samar wa bayin Allah da aikin yi, ga riba ga lada.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.