Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 29: Ma’aikaci da Wayoyinsa

Shi ya san matsalarka kuma zai yi maka hanzari. Kwanaki wani ke ba mu labarin cewa mai yi musu aikin kafinta ya karɓi...


Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 29: Ma’aikaci da Wayoyinsa

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Wasu ayyukan sam ba sa yuwuwa sai da wayar, kenan ita ce jigon sana'ar gaba daya, wani sa'in za ka taras ba a buƙatar wayar dole ka haƙura ka ajiye ta matuƙar kana son sana'arka ta ci gaba, da yawanmu ba mu san haka ba, in kai ne babba a wuri kuma kana da yara masu taimaka maka ba matsala ka daga wayarka kuma ka yi maganarka yadda kake so, in ba ka son yaran su riƙa yin abin da kake yi to su sani fa cewa kai kaɗai kake da wannan hurumin, don kar su gan ka kana yi su ma su kwaikwaye ka, wani abokina ya taba gaya min cewa masinjansa kan shigo masa ofis ya yi ta waya yana dararrakunsa ya manta cewa a ofishin na gaba da shi yake.
.
Na zauna da wasu masu sana'a waɗanda kiransu aiki ake yi daga wurare, in sun dawo wani ya sake kiransu, wani sa'in suna kan wani aikin za a kira su, kuskuren dake faruwa anan sai mutum ya kama waya ya kashe wai an dame shi, sai a yi ta kira ana samunta a kulle, har mutum ya yi shawarar canja abokin sana'a, wani kuma ba kashewar zai yi ba amma ba zai daga ba, kuma abokin kasuwancinsa ne sun dade suna tare, sai ya duba ya gani can ya yi tsaki ya jefa wayar wani wurin, a maimakon ya daga ya gaya masa gaskiya cikin sauƙi "Wane na fito aiki ina wuri kaza tun lokaci kaza, ƙila na gama zuwa ƙarfe kaza, in na gama ban gaji ba zan kira ka" shikenan cikin sauƙi.
.
Shi ya san matsalarka kuma zai yi maka hanzari. Kwanaki wani ke ba mu labarin cewa mai yi musu aikin kafinta ya karɓi ƙaramin aikinsu bai gama da wuri ba, suka ce sun yi masa hanzari saboda salla ta matso ƙila ya shiga wata saugar ne, sai aka sami wani kwantaragi da kudi mai tsoka aka yi ta kiransa ya ƙi daga wayar, wai ya sani cewa maganar baya za a yi masa, a ƙarshe dai ya yi asarar wannan aikin, ba yadda za ka ce ka san abin da mutum zai gaya maka, ko maganar zai yi maka ƙila akwai wata sabuwa.
.
Akan gaza kaiwa ga yin nasara a kan rashin sanin yadda za a tafiyar da waya, mutum ne zai nemi aiki ya kai cv dinsa wani wuri mai ɗauke da lambarsa, amma in aka buƙace shi sai a sami wayar a kulle, wasu wuraren ba su da lokacin kiran mutum sai cikin dare, kai kuma za ka yi barci ka kama waya ka kulle, ina laifi ka sanya ta yi tsit yadda ko an kira ka ƙarar ba za ta dame ka ba, in ka shi ka ga kiran? An taba ba ni kudi a wata makaranta ta share fagen jami'a aka ce na gayyato waɗanda suka sami nasarar tantancewa don su shigo su zana jarabawar da za ta ba su damar tsallakawa cikin makarantar, ashe a cikinsu akwai wasu mutane masu dabi'ar in ba su san lamba ba ba za su daga ba.
.
Na yi ta kiran wani bawan Allah amma ya ƙi dagawa, lokacin da na gama na juyo kansa na kira shi, da dagawarsa sai ya ce "Wrong number" bai ma ko ji muryata ba, har na haƙura da shi saboda fusatar da na yi, sai na sake tunani, na san bai san ni ba bare na ce raini ne, gidadanci ne kawai irin na mutanemmu, ka ba da lambarka a kira ka bisa wani abin da kake so, ko wannan ya isa ka ɗan saurara ko ka canja dokarka, tun da ba ta Allah ba ce, na ɗan wani lokaci, albashi in ka sami abin da kake so sai ka dawo da ita,  na sake kiransa amma sai ya dode ni, sai da na rubuta wasiƙa na tura masa cewa daga wuri kaza ne ake magana kan abin da yake nema.
.
Ko minti daya ba a yi ba sai ga shi ya bugo yana ba da haƙuri da wasu hujjoji na banza, sai na ce masa ya yi haƙuri mun raina hankalinsa mun ba wani, hankalinsa ya yi matuƙar tashi ya biyo baya a guje, sai da na gurza shi sosai don ya goge kafin na ce kar ya ƙara irin wannan sakacin a rayuwarsa, wanda yake neman aiki kashe waya ba tasa ba ce, na taba neman wani abu, amma na kasa canja wayata da na yi niyyar saye, duk tsoron kar a kira ni a ɗan mintocin da ba su kai biyu ba ba a same ni ba, na ga wata mata da za ta canja waya sai da ta zo wurimmu ta kawo kuka kar mu kira ta ba mu same ta ba, in mutum ba zai iya daga waya ba to ya saka ta ta yi tsit, yadda in ya waiwaye ta zai ga duk masu kiransa.
.
Maganin bera da na siya a wurin wani Inyamuri sai da ya ba ni lambar wayarsa ya ce bai zama wuri daya amma in na ji dadin maganin to na kira shi kawai, duk inda yake zai waigo ni ya kawo min, waɗannan sun san kan sana'a, mutanemmu da dama suna yin sana'ar da zai yuwu a neme su, ana buƙatar hidimarsu, amma abin haushi sai ka ji wai mutum bai da waya, wani yana da itan amma in za ka buga sau dubu ba za ka same shi ba, ga hanyar cin nasara ta wurin bunƙasa sana'arsa amma abin haushi bai san yadda zai yi ba, akwai wani mai sayar da rake yakan zo masallaci gab da Magariba, ana buƙatarsa sosai wani sa'in yakan yi salla a masallatan kewayen, duk buƙatarsa da kake yi sai dai ka haƙura ko ka ce wani wurin ba za ka same shi ba, bai da waya, in ma ya na kusa ba za ka hage shi ba gari ya yi duhu bai da haske.
.
Kamar masu sana'ar yawo irin wanzamai, masu tallar magunguna, kai harda ma'aikata kamar kafintoci, kanikawa, masu gyaran wuta duk ya kamata a ce suna aiki da waya, to bare masu hayar ababan hawa, hatta mahauta akan kira su su gyara wa mutum dabba in akwai sha'ani, bai dace ba a ce ka bar jama'a na ta jiranka kai kuma kana can kana ta waya da wasu, amma don ka saurari mutum na minti daya wannan na da matuƙar mahimmanci, akwai mutanen da bai dace suna tsayuwa ga waya ba saboda yanayin sana'ar tasu, kamar dai direbobi, amma in suka sami wuri suka tsaya za su yi wayarsu yadda suke so ba tare da wata matsala ba.

Post a Comment

0 Comments