Ticker

Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 31: Duk Abu Naka Naka Ne


Idan ka gama sanin komai, ya za a yi wani mutum ya zo maka daga waje ya mallake ka? Ba zai yuwu ba! Na ga wata makaranta da wani ya...


Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 31: Duk Abu Naka Naka Ne

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Sakaci da rashin kulawa ko rashin sani su ne manyan abubuwan dake sanyawa mu rasa damar dake hannunmu ko mu bar ta wani ya ƙwace mana, da farko fara gina kanka tukun, yi ƙoƙari ka sami ginshiƙi mai ƙarfin gaske, kar ka yarda ka yi abu a kan jahilci, in kamfanin gyaran mashin za ka gina binciki kanka tukun, shin kana da  kuɗin da zai ba ka damar aiwatar da wannan aikin? In ba ka da shi to ya za a yi ka samu? Ilimin aikin dai yana kanka  kuɗin aiwatarwan ne ba bu.
.
Da farko tsaya ka karanci sana'ar da za ka fara, shiga ciki a matsayinka na mai koyo, yi ƙoƙari ka san komai nata, kayan aiki, abubuwan da ake buƙata, masu kyau da jabu, kudadensu, dadewarsu, bambance-bambancen dake tsakanin kamfanoni, lokutan da suka fi dacewa da inda ya kamata a yi saboda yawan mabuƙata, ya zamanto dai a matsayinka na mai koyon aiki ba abin da ba ka sani ba, albashi in ka zo daukar ma'aikata da za su yi maka bayani kan kayan aiki da sauransu ba abin da ba ka sani ba, kuma ba wanda zai yi ƙoƙarin cutarka ko bata maka aiki.
.
Na koyar a wata makaranta ta Misho, inda na ga hedimastan koyaushe yana zagawa azuzuwa yana ganin darussan da ake koyarwa, da lokutan da ake koyarwan, wata rana ya amshi wani aji ya koyar ko ya yi musu tambayoyi don ganin shin abin da suke buƙata malaman suke ba su kokuwa? Na yi mamakin ƙwaƙwalwar mutumin yadda ya san komai kai har da sunan daliban, ba abin da malami zai fada wanda bai sani ba, sai na tambaya, ya aka yi ya san duk waɗannan abubuwan? Sai aka ce ya koyar na tsawon shekaru da dama kafin ya kai ga riƙe makarantar a hannunsa, ashe asali ma ba ɗan ƙasa ba ne, amma yana tsari mai ƙarfin gaske, koyarwar ta taimake shi sanin komai.
.
Idan ka gama sanin komai, ya za a yi wani mutum ya zo maka daga waje ya mallake ka? Ba zai yuwu ba! Na ga wata makaranta da wani ya so gudanar da ita. Ya tanaji komai amma bai da kudi, sai suka hada hannu da wani mai abin hannunsa, a ƙarshe aka fara rigimar shin wa ma yake da makarantar tukun? Wanda ya fi ƙarfinka sai ya dauki hannunka ya mare ka da shi, kusan abin da aka yi kenan, mutumin farko da a ce yana da  kuɗinsa sai ya ci gaba da gudanar da lamuransa shi kaɗai ba zai jawo kowa ba.
.
Duk abin da za ka yi in dai kai da ƙarfinka za ka yi aiki wani da dukiyarsa kar ka yarda a ce komai shi zai yi, wani zai ce kar ka damu, ko nawa kake so ni zan dauki nauyi, in ka yarda da wannan to ko shakka babu ka sayi wuƙar yanka kanka, sanya taka dukiyar kuma ka yi aiki da ƙarfinka, ba yadda zai dawo wata rana ya yi farfagandar cewa komai nasa ne don shi ya yi, kai ma ka sanya  kuɗinka, ka yi aiki da ƙwaƙwalwarka sannan ka ba da lokacinka daidai gwargwado, abubuwan dake faruwa a duniya yanzu yadda ka san ba lahira a gaban mutane.
.
Akwai wata makaranta da wani ya so gudanarwa, shi ya ke da wuri a hannunsa, sai ya jawo wani babban malami wanda ya yarda da shi sosai, ya danƙa komai a hannunsa, sai mutumin ya yi aiki da wannan damar ya maida mai wurin yaronsa ya yi ta yi masa bauta na tsawon shekaru, sai dai ya ɗan gutsuro a wata ya miƙa masa, ba wanda ya san abin da ake ciki, a ƙarshe da yake mai wurin shi ma ba nasa ne na kansa ba sai mutumin ya kori shi wai bai gamsu da irin gudummuwar da yake badawa ba, idan kana da rai ba abin da ba za ka ji ba, waɗannan su ne abubuwan da ni na gani da idona Allah ne kaɗai ya san abubuwan dake faruwa a wasu wuraren.
.
Da a ce mutuminnan ya koyo aikin, ya fara da kansa bai janyo kowa ba, shi yake gudanar da komai ba wanda zai zo rana tsaka ya mamaye masa wuri, balle ya tuhume shi da rashin gaskiya har a ƙarshe ya ce zai kore shi, duk sana'ar da za ka shiga yi ƙoƙari ka san gabanta da bayanta yadda ba wani abin da zai boyu maka, kana da cikakken 'yanci, kana da duk wata dama da za ka dauki matakin da kake so, ba tare da wani ya yi aiki da ƙwaƙwalwarka ya cuce ka ba, in kana gaya wa kanka cewa ba za ka iya kaza ba ina tabbatar maka daga lojacin da wani ya karbe maka wannan damar sai yadda ya yi da kai.
.
Za a kai yadda ba za ka iya zartar da komai ba sai abin da ya so, shi kuma abin da ya ce ka yi ba ka da makawa, ko kafin ka farga ya yi maka babbar illa, don duk abin da zai amfane ka ba zai yarda da shi ba, duk kuma wata hanya da za ka bi wace za ta nuna maka hanyar daidai ba zai yarda ka san ta ba, taka ta ƙare kenan, ka bude idanunka, ma'ana duk lokacin da ka gano cewa nasararka tana kan dakinka ne to ka gina matakalanka da kanka, ka hau da kanka ka ciro, ka sani in ka tura wani ya ciro maka to shi ma fa yana so.

Post a Comment

0 Comments