Ashe
gogan naka ya bi ta kan kuɗin ne. Auren da bai ɗauru
ba ke nan.
Sai ga shi
ana ta...
Hanyoyin Cin Nasara a
Rayuwa 34: Bambancin
Hanzari da Gaggawa
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Hanzari yana nufin ka ƙara saurin tafiyarka ne don ka isa zuwa
ga nasara a daidai lokacin da ake buƙatarka,
gaggawa kuwa na nufin ka yi saurin aikata abu tun lokacin aikin bai yi ba,
kenan hanzari ake buƙata
ga mai son cin nasara ba gaggawa ba, domin abin da ake so shi ne mutum ya iya
samun abin da yake buƙata
da surar da yake buƙata
din, mun taba zuwa tambayar wani karatu na NCE sai aka ce mana akwai
"regular" shekara 3, part time shekara 4 sai kuma long vacation
shekara biyar, in mutum zai iya sai ya dauki ta shekara 3 don ya yi hanzari ya
gama, in ba zai iya ba kuma ya dauka to ya yi gaggawa kenan.
.
Duk wata sana'a ko aiki da
mutum zai kama ya tabbatar hanzari zai yi ba gaggawaba, wata mata da aka kawo
mata kishiya sai ta fara nuna wa kishiyar cewa ita keda mijin, tana saka ta
ayyuka daban-daban, har amaryar ta goge idanunta ta ce ita ba baiwa ba ce, daga
ranar ta dena yin komai, har da wanda ya dace ta yi din ma, ta ce matsayinsu
guda ne, na ce gaskiya uwargidan ma ta yi gaggawa, da ta yi haƙuri ta janyo yarinyar a jiki, ta nuna
mata abin da ya dace, koda an gaya wa amaryar ƙarya
da gaskiya in ba ta ga abin da ake gaya mata ba za ta sauko ta yi abin da ya
dace, ba abin da mutum zai bi a hankali sai ya ga ribarsa ko meye kuwa.
.
Na ga wani mai aski yana ta
fada, da yake rigimar ba tawa ba ce sai na ja bakina, wai yaron da ya zo koyon
aiki ne ya tsaya sai an riƙa
raba kuɗin
da ya samu kashi biyu ana biyansa, alhali ogan yana ganin yaron ne ma zai riƙa biyan koya masa da ake yi, ni dai ban
sa baki ba, amma na san mai koyon aiki a wasu wuraren shi ne ma yake biya ba
shi ake biya ba, kamar dai yaron ya yi gaggawa, tun da ba a ce ya biya ba bai
dace ya ce a biya shi ba, a ƙarshe
dai sun rabu, ina da tabbacin cewa indai yaron zai ci gaba da haka ko ina ya je
irin wannan rabuwar za a yi.
.
Wadansu sun shirya yin wani
kamfani sai suja tara kuɗin
farko a hannun daya daga cikinsu, kusan shi ake so ma ya riƙa ajiye kuɗin,
a ƙarshe dai wannan kuɗin
bai fito ba, sai a albashinsa aka riƙa
cirewa a hankali, kuma an amshe tarin daga hannunsa, saboda bayyanar rashin
gaskiya ƙiri-ƙiri,
na ce ya yi gaggawa ne, da ya yi haƙuri
akwai wasu kudi na masamman da ake bai wa duk mai tarin kudi, da ya rabauta da
shi, wanda ya fi ba ni mamaki shi ne wanda ya je neman auren wata yarinya, an
ba shi ita kuma an saka masa rana, sai da ya rage saura 'yan kwanaki kadan sai
ta yi maganar kayan daki ya ce yana da wani ƙwararren
kafinta.
.
Ashe gogan naka ya bi ta kan
kuɗin
ne. Auren da bai ɗauru
ba ke nan. Sai ga shi
ana ta wasan kurar boyo tsakaninsa da amaryar, gaskiya ya yi gaggawa, da ya
bari ya aure ta tukun, komai nata inda soyayya nasa ne, gajin haƙuri ne, wata kuma maigidanta ne ya auro ƙawarta ba tare da saninta ba, ya ce in
ta sani za ta iya dagula lamarin, a taƙaice
dai ba ta sani din ba sai bayan an daura, nan fa uwargidan ta tada bala'i har
ya kai ga ta bar wa amaryar mijin, da dakinta da ma yaran da ta haifa, saboda
kishi, na ce ta yi gaggawa, da za ta bi a hankali da ta riƙe kayanta gaba daya.
.
Akan yi gwaji ne don
tabbatar da ko mutum zai yi gaggawa, duk da cewa ina tababar maganar gwaji a
neman aure, wasu matan sukan yi asarar miji na gari a dalilin gwaji, na tabbata
ba shi ne hanya ta ƙwarai
wurin zabin miji na gari ba, don da shi din ne da Annabi SAW ya zabar mana,
amma bincike shari'a ta tabbatar, in dai namiji ne to mace ta bar shi da
kininsa kawai, maƙwabta
abokan aiki, 'yan uwa duk za su iya taimakawa wurin bincike, kuma su din ne za
su kawo abin da ya dace.
.
Wani ɗan abu
ne ya shiga tsakaninsu ita kuma ta nemi saki a matsayinta na mace, gaulan naka
ya ba ta duk da cewa namiji ne, a kullum suna tare, bayan ba aure a tsakaninsu,
sai ya zamanto duk bayan 'yan kwana biyu sai ta dauko yaro ta zo gidansa wai ta
kawo masa dansa ya gani, amma sai su kwashe sa'o'i biyu zuwa uku bai gama ganin
yaron ba, na ce sun yi gaggawa, da sun yi haƙuri
za su fahimci junansu, haka dai suka ci gaba har wanda tsautsayi ya fada masa
ya aure ta, ba ta jima ta fice abinta ta koma inda ta fito.
.
Wasu kuma duk an yanke musu
hukunci mai tsanani akan kashe wani da suke zargin cewa ya kashe musu ƙani, alal aƙalla da sun danƙa shi a hannun hukuma, a tunanina ba
mutumin da zai wuce kwanakin da Allah SW ya diba masa, matuƙar dai za su iya kashe shi a wannan
lokacin to sun yi gaggawa, domin ko ba su tabe shi ba mutuwa zai yi, akwai
abubawa da dama da muke rasawa a dalilin gaggawa irin wannan, ba laifi ba ne su
yi hanzarin miƙa maganar koto kafin
bincike ya kai gare shi, amma kashe shi kam gaggawa ne
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.