Jiya Ba Yau Ba : Takaitaccen Nazari A Kan Bikin Haihuwa A Al’adarHausawa.


Haihuwa ko samar da ‘ya’ya shi ne babban manufar yin aure ga al’ummar Hausawa, kamar yadda yake a mafi yawan al’ummun duniya. Shi kuwa lamarin haihuwa yana samuwa ne ta hanyar yin aure, kuma ta hanyar haihuwa ne ake samun wanzuwar al’umma tun daga farkon wannan duniyar har zuwa ƙarshenta. Mai yiwuwa dangane da hakan ne al’ummar Hausawa ke  faɗi-tashi wajen yin aure domin neman haihuwa. Ba sai an faɗa ba, ana iya ganin irin darajar da Bahaushe ya ba wa lamarin haihuwa idan aka dubi irin damuwar da yake nunawa idan ya yi aure bai sami haihuwa ba. Bisa ga wannan matsayi na haihuwa ne, a wannan maƙala  za a yi taƙaitaccen bayani a kan nason zamananci a cikin al’adun haihuwar Bahaushe. Za a yi ƙoƙarin kawo yadda nason wasu baƙin al’adu ya haifar da taɓarɓarewar waɗannan al’adu na haihuwa. Daga cikin abubuwan da muƙalar  za ta yi nazari a kansu sun haɗa da: goyon ciki da kayan ƙauri da zanen suna da wankan jego da gara da reno.

Jiya Ba Yau Ba : Takaitaccen Nazari A Kan Bikin Haihuwa A Al’adarHausawa.

Rabiu Aliyu Rambo
Sashen Koyar Da Harsunan Najeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo; Sakkwato.
Email: rabiualiyurambo@yahoo.com
GSM:08125507991

1.0 Gabatarwa


Haihuwa na ɗaya daga cikin manya-manyan ginshiƙan dalilan yin aure a cikin al’ummar Hausawa. Duk da yake lamarin haihuwa lamari ne da ya bambanta daga wannan al’umma zuwa waccan. Domin wasu al’ummu ba su buƙatar haihuwa kamar yadda wasu suke da. A ƙasar Hausa ɗa (mace ko namiji) baiwa ce da kowa ke burin ya samu. A al’ada, yaro ko ba kai ka haife shi ba muddin ka girme shi zai yi maka ladabi (C N H N . 1981 :16) Wannan ya nuna ‘ya’ya suna da muhimmanci a cikin al’ummar Hausawa.

A al’adance, a duk lokacin da aka sami  ƙaruwa ta haihuwa a ƙasar Hausa, ana aiwatar da wasu al’adu waɗanda ke nuna murna ko farin cikin ƙaruwar da aka samu. Don haka , wannan maƙala za ta yi ƙoƙarin nazarin wasu daga cikin al’adun da ake aiwatarwa a lokacin gudanar da bikin haihuwa a ƙasar Hausa. Daga cikin abubuwan da za a yi nazari sun haɗa da al’adar goyon ciki da ta kayan ƙauri da ta zanen suna da ta wankan jego da ta kayan gara da ta shayarwa.

Bisa haka ne a wannan maƙalar za a yi ƙoƙarin kawo irin yadda zamananci ya yi tasiri a cikin al’adun haihuwar bahaushe a yanzu . Ma’ana,  za a dubi yadda nason baƙin al’adu ya taimaka wajen taɓarɓarewar  al’adun haihuwa na Bahaushe.  A ƙarshe maƙalar ta yi ƙoƙarin ba da shawarwari  yadda za a tsare a kuma inganta waɗannan al’adu  musammam a cikin al’ummar Hausawa domin muhimmamcinsu.

2.0  Ma’anar Haihuwa


Dangane da abin ya shafi ma’anar haihuwa kuwa, a nan ana iya cewa akwai ra’ayoyi daba-daban dangane da ma’anar haihuwa . Domin wasu sun ɗauki ma’anar ne ta fuskar samun da wani ya  yi  na wani abu. Misali a ce ‘yawan dariya barkatai na haifar da hauka’ A nan haihuwa na matsayin musabbabi. Amma idan muka ce ‘Aisha ta haifi Musa’ A nan wannan na nuna a sanadiyyar saduwa da Aisha ta yi da mijinta ta ɗauki ciki har ta haifi Musa.

Ta  wannan fuska, ana iya cewa haihuwa tana nufin samuwar ɗa namiji ko mace da mutane kan yi ta hanyar saduwa tsakanin namiji da mace musammam ta hanyar aure. Ga kaɗan daga cikin abin da masana suka tofa dangane da ma’anar haihuwa. Abdullahi  ya rawaito Alhassan da wasu suna cewa ‘-----yayin da miji da mata suka ƙaru da samun ɗa ko’ya ‘ (Abdullahi  2008:225)

A ma’anar ƙamussan Hausa na C N H N an  bayyana ma’anar haihuwa da cewa: ‘samun ɗa ko ‘ya bayan mace ta yi ciki wata tara’ (kamussan Hausa C N H N .2006:189) Haka kuma a wani ra’ayin cewa aka yi:

Ƙaruwa ce ta hanyar fitowar wani abu mai rai daga jikin wata halitta jincin mace wanda ya ɓoyu a wani wuri na musammam na wani ƙayyadadden lokaci don samun kamanni ko siffa kwatankwacin na zuriyarsu,wanda ke aukuwa a sakamakon saduwa da jinsin namiji na wani halittar.

(Abdullahi, 2008:228)

Bisa ga waɗannan ma’anoni, ana iya fahintar haihuwa a wannan muhalli tana nufin irin ƙaruwar da matan Bahaushe kan samu na ‘ya’ya musamman bayan sun yi aure. Domin a al’adar Bahaushe ana iya samun ƙaruwa ta haihuwa amma maimakon a yi farin ciki sai ya zama na baƙin ciki,wannan kuwa  a fili yake idan aka dubi irin ƙyamar da ake nuna wa matar da ta haihu ba tare da miji ba, ma’ana samun ɗan da aka Haifa ba tare da aure ba.


3.0 Wasu Al’adun Haihuwa a Al’ummar Hausawa


Idan ana maganar  ƙasar Hausa, ana nufin wata farfajiya wadda take shimfiɗe, tare da gulabe da duwatsu da tsaunuka da suka ratsa ta jefi-jefi. Ƙasar Hausa tana da manyan birane da ƙananan ƙauyuka da suka haɗa da Kano da Katsina da Daura da Gobir da Zazzau da Rano da Garun gabas         da Gaya da sauransu.

Ta fuskar harshe kuwa, Yahaya da wasu  (2001:95) sun ce:

                      Harshen Hausa shi ne wanda Hausawa suke amfani da shi,

                     kuma shi ne babban jigo wanda ya haɗa dangantaka

                  da kasuwanci tsakanin waɗannan garuruwa, sai kuma

                  harakokin kasuwanci da ciniki da saye da sayarwa  

Don haka, mazauna ƙasar Hausa kamar sauran ƙabilun duniya, suna da ɗabi’unsu da al’adunsu da suka keɓanta da su, wasu daga cikin al’adun suna tattare ne da wasu bukukuwa da suke aiwatarwa a tsakanin su. Waɗannan bukukuwa suna ƙara danƙon zumunci da kawo annashawa a tsakanin su. Kuma waɗannan bukukuwan su ne ƙashin bayan jin daɗin zaman al’ummar Hausawa.  Waɗannan bukukuwa sun haɗa da; haihuwa da aure da sallah da kalankuwa da shan kabewa da sauransu.

A  wannan muƙalar za a yi bayani ne a kan wasu al’adu da ake aiwatarwa lokacin bukin haihuwa a cikin al’ummar Hausawa.

3.1 Al’adar Goyon Ciki

A ƙasar Hausa, ana da al’adar mayar da yarinya haihuwa a gidansu idan cikin ya kai wata bakwai, kuma galibi wannan na faruwa ne ga mace mai haihuwar fari. Wannan al’ada ana yin ta ne domin mai ciki ta sami kulawa na musammam a gidansu .A wannan lokacin ana kula da lafiyarta, kuma ana sanya mata wasu sharuɗa na hani ko horo ga aikata wasu ayyuka ko cin wani abu musammam waɗanda za su taimaka mata sauka lafiya.

Haka za ta ci gaba da zama gidansu har lokacin da naƙuda ta taso mata. Naƙuda ita ce wata alama da mai haihuwa za ta fara ji ko gani kamar ciwon mara da baya da fitar  ruwa fari a gabanta . Lamarin naƙuda wani abu ne mai matuƙar wahala .Wannan ya sa har waƙa aka yi mata kamar haka:

Wayyo naƙuda ta tashi

Ciwon naƙuda ya tashi

Kuma ciwon naƙuda ya motsa

Yau kam babu zama zaure

Wayyo Inna ki cece ni

Wayyo naƙuda ‘yar ziza

Ciwon naƙuda bori ne

Ko ko naƙuda hauka ce

Amshi ki ɗan kurɓa

Ba toka ce ba rubutu ne

Ko Allah nai maki sauƙin ta

(Yahaya  da wasu 2001:99)

Ga al’ada, da zarar mace ta je goyon ciki iyayenta za su rinƙa tanadin wasu kayan goyo. Haka kuma shi ma miji zai tanadi nasa kayan ,wani lokaci ana kai mace ne gidansu, wani lokaci kuwa iyayenta ne ke zuwa su ɗauke ta. (CNHN. 1981:17)

Kamar yadda aka ambata a baya, idan naƙuda ta fara ana kiran wata tsohuwa a unguwa mai ɗaukar biƙi (ungozoma). Ita ungozoma tana da masaniyar dabarun karɓar haihuwa. Bayan an sauka lafiya ungozoma za ta yanke cibiyar abin da aka haifa, ta wanke jinjiri ta kuma taimaka wurin gyaran ɗakin mai haihuwa. Tana kuma taimakawa da wasu ‘yan saƙe-saƙi wadanda za a  ba jariri da uwarsa domin gyaran jiki da kariya ga wasu cututtuka. Kuma za ta ci gaba da yi wa jariri da uwar jaririn hidima har sai bayan uwar ta gama wankan jego.

3.2 Kayan Ƙauri

A al’ada ana kai kayan ƙauri ne bayan an yi kwana huɗu da haihuwa . Kuma mafi yawa ana amfani da ƙafafun sa ko kai haɗe da kayan yaji kamar citta da kanunfuri da masoro da barkono da kanwa da hatsi da sauransu. A kwana na biyar za a yi rabon ƙaurin bayan an cire wa mai jego nata, inda za a ba maƙwabta da sauran dangi da abokan arziki. A lokacin wannan rabon ƙaurin,  ana haɗawa da kunun kanwa duk a raba wa maƙwabta. Kuma a al’ada, duk namijin da matarsa ta haihu ba a yi bikin shan ƙauri ba, to wannan ya yi abin kunya a cikin  al’umma.

3.3 Bikin Suna

Kamar yadda sunan ya nuna , bikin suna wani yanayi ne da ake haɗa ’yan uwa da abokan arziki a ci a sha, kuma a yi annashuwa da raha. Ana aiwatar da bikin suna ne idan ranar da aka haifi jaririn ta zagayo; ma’ana bayan mako guda. Ranar suna, rana ce da za a raɗa wa jaririn da aka haifa sunan da za a riƙa kiran sa da shi. Galibi a ƙasar Hausa ana sanar da ‘yan ‘uwa da abokan arziki su haɗu musammmam da safe lokacin kalaci domin gudanar da wannan al’ada.

A ranar suna, ana yanka rago a raba goro, liman ya yi wa jariri huɗuba galibi bayan kwana bakwai da haihuwa, duk da yake ana iya huɗuba tun ranar da aka haifi jinjiri a raɗa wa yaro suna sai dai ba za a bayyana sunan ba sai ranar suna. Kuma galibi da yake Hausawa mabiya addinin Musulunci ne, don haka, ana zaɓen sunan ne daga cikin sunayen addinin Musulunci.

Ranar raɗin suna ,za a taru tsakanin dangin mai

 haihuwa da mijinta .Idan waɗanda duk ake jira ya

                             taho, za a raba goro ga jama’a inda za a fara fitar da

                             na malamai da wanzamai da mata . Daga nan sai

                             liman ya yi wa abin haihuwar addu’a da ita kanta

 mahaifiyar da uban da sauran jama’a baki ɗaya

(Yahaya da wasu . 2001:99)

Shi kuwa (Gusau, 2012:42) Yana da ra’ayin cewa:

Zanen suna ko raɗin suna ana gudanar

da shi ga abin da aka haifa, bayan mako

ɗaya da haihuwa. Zanen suna ko raɗin

suna ya kasu kashi biyu, akwai zanen

 suna a gargajiyance, akwai kuma zanen

 suna a addinance.

Ta kowace fuska dai za a fahinci bikin zanen suna yana haddasa haɗuwar dangin mace da na namiji wuri ɗaya domin taya juna murnar samun ƙaruwa ta haihuwar da aka samu.

3.4 Wankan Jego

Wankan jego wanka ne da mace mai haihuwa kan yi da tafasassun ruwa har na tsawon a ƙalla kwana arba’in bayan ta haihu safe da marece. Daga nan sai ta ci gaba da yi da safe ko da yamma kawai zuwa kwana sittin ko ma fiye. A lokacin wannan wankan, ana yin amfani  ganyen sabara ko na doka ko na geza ko darbejiya ko sanga-sanga. Ana amfani da waɗannan ganyayyaki ne saboda muhimmancinsu wajen samar da waraka daga cututtuka daban-daban. A al’adance mace mai haihuwa tana fara wankan jego ne tun daga ranar da ta haihu. Wannan wankan yana matsayin wata hanya ta jinyar raunin da ta samu lokacin haihuwa. A wannan lokacin ne ake ba jinjiri dauri domin kula da lafiyarsa.

A al’adance idan mai jego ta yi aƙalla kwana arba’in tana yin  wankan, har  ɗan ƙwarya-ƙwary an biki ake yi,  inda za a toya waina a ci a yi sadaka. Bayan wannan lakacin ne mace za ta fara kwalliya.

3.5 Kayan Gara

A ƙamussan Hausa, an bayyana ma’anar gara da cewa:

Kaya, musamman na abinci da iyayen

 amarya kan kai wa ‘yarsu bayan an

 gama bikin aure ko haihuwa.

(CNHN.2006;157.)

A zahiri ana iya fahintar ana amfani da wannan kalmar ta gara a muhalli biyu ne lokacin bikin aure da haihuwa. Ana kai garar haihuwa a ranar suna , wato kayan toye-toye  wani lokaci har da kuɗi . Sannan ana kai gara lokacin da mai haihuwa za ta koma ɗakinta bayan ta ƙare wankan jego. A nan ana haɗa mata kayan abinci irin su shinkafa da dawa da mai da daddawa da gishiri gwargwadon ƙarfin iyayenta. Wani lokaci har  makaɗi ake kira ya raka su, ana tafe ana waƙe-waƙe kamar sabuwar amarya.

3.6  Renon Abin da aka Haifa

Bayan an raɗa wa jinjiri suna da sauran hidimomin al’ada kamar wankan jego da gara,  al’ada ta gaba mai muhimmanci ita ce renon shi abin  da aka haifa. Reno shi ne ci gaba da kulawa da shi, ta hanyar ba shi dauri da nono sau da yawa wannan yana faruwa har tsawon wata shida . Daga nan ne za a fara ba shi kunun hatsi  yana sha, duk da yake ana yi mashi ɗure ne. A lokacin da jariri ya kai wata takwas zuwa tara ne  za a fara bashi abinci , sannu a hankali har ya fara ci da kansa.

Haka a wannan lokacin ne ake koya wa jinjiri zama daga nan sai rarraife da ta-ta-ta (koyon tashi tsaye) daga nan ya fara koyon tafiya . Abin lura a nan shi ne, kusantar da jinjiri yake yi da uwarsa a lokacin reno. Wannan kuwa yana taimakawa wajen samun shaƙuwa da soyayya a tsakanin jinjiri da uwarsa. Duk da yake, a ƙasar Hausa akwai al’adar ɗan reno, inda uwar jinjiri tare da amincewar mai gidanta za su samo wata ‘yar yarinya domin ta taimaka wa uwar wajen renon jinjiri musamman lokacin da take aiwatar da wasu ayyuka na gida. Bayan reno, abu na gaba ga abin da aka haifa shi ne yaye.  za a cire jinjiri ne daga shan nonon mahaifiyarsa. Galibi ana kai yaron ne wajen kakanninsa zuwa wani lokacin da zai manta da nono. Daga baya sai a dawo da shi wurin iyayensa.

4.0 Nason Baƙin al’adu a Cikin Al’adun haihuwar Hausawa


Tarihi ya nuna  cewa dukkan inda aka sami wata al’umma ta shigar

                   wa wata al’umma, waɗanda yake tilas ne ya zamana al’adunsu

                   sun sha bamban, to za ka taras al’adar al’ummar da ta fi ƙarfi ta yi

                   tasiri a kan rarraunar. Im ma ba a mayar da hankali ba sai a

wayi gari a tarar ƙaƙƙarfar ta mamaye rarraunar baki ɗaya.

(CNHN, 1981:32)     

Kasancewar ƙasar Hausa ƙasa ce  mai daɗaɗɗen tarihi wadda ta sha faɗi-tashi da sauran al’ummu daban-daban na kusa da na nesa wannan ya taimaka wajen kawo wasu sauye-sauye a cikin al’adun haihuwar Bahaushe.  Kasancewarya kullum duniya a cikin sauyi take, wannan  shi  ya haifar da sauyi a cikin al’adun haihuwar Bahaushe. Don haka, ci gaban zamani (wayewar kai) ya taimaka wajen sauya tunanin Bahaushe shi kansa. Haka lalurar kwaikwayon baƙin al’adu shi ma sun taimaka wajen taɓarɓarewar al’adun haihuwar Bahaushe. Don haka, akwai dalilai da dama da suka taimaka wajen taɓarɓarewar al’adun haihuwa a yau, wanda inda an tsaya  tsayin daka aka riƙi waɗancan al’adu na gargajiya da sun taimaka  ainun wajen wanzar da rayuwa mai nagarta fiye da yadda ake a yau.

4.1 Taɓarɓarewar Al’adar Goyon Ciki

Kamar yadda bayani ya gabata , goyon ciki shi ne zuwa gida da mai haihuwa kan yi  gidan iyayenta, musammam a lokacin haihuwar fari, yawanci tun cikin na  wata bakwai. Idan aka lura wannan al’adar an kusan mantawa da ita duk kuwa da irin muhimmancinta ga al’ummar Hausawa. A yanzu za a taras zuwa goyon ciki ya yi  ƙaranci  sosai a cikin al’ummar Hausawa. Masu ɓarɓashin wannan al’adar su ne waɗanda ke bari sai matar ta haihu a mai da ita gida tare da jinjirinta. A nan za a ga irin kulawar da za ta samu idan tana gidan iyayenta ba za ta same ta ba a gidan mijinta musamman ga mazauna birane.

A nan, za a fahinci mai haihuwar ta yi hasarar irin shawarwarin da iyayenta kan ba ta na hani ko horo ga aikata wani abu, musammam wanda zai taimaka mata inganta lafiyarta da samun sauƙin haihuwa. Don haka, al’adar komawa gida goyon ciki ta ci baya ainun a cikin al’ummar Hausawa a yau. Hakan na faruwa ne saboda nason baƙin al’adu da nuna wayewar kai na zamani.

Bugu da ƙari, idan aka dubi irin hidimar da ungozoma ke aiwatarwa na kula da jinjiri ta hanyar yi masa wanka safe da maraice na tsawon kwana arba’in da ba shi dauri wanda zai taimaka wa lafiyarsa da kula da lafiyar uwarsa duk waɗannan an yi watsi da su. A yanzu an mai da haihuwa asibiti, su kuwa asibiti babu rowan su da dauri.

4.2 Taɓarɓarewar Al’adar Kayan ƙauri

Kayan  ƙauri abu ne mai muhummanci ga uwar jinjiri , domin suna taimaka mata wajen kulawa da lafiyarta . A  halin  yanzu wannan al’adar ta yi rauni ainun a cikin al’ummar Hausawa. Zai yiwu saboda matsalar tattalin  arziki  ko kuma wayewa ta zamani, ta yadda a yanzu kowa yana zaune a gidansa ne babu wanda ya damu da wani.

Baya ga ƙarin lafiya ga mai haihuwa , rabon ƙaurin da akan yi yana ƙara danƙon zumunci a cikin al’ummar Hausawa. Don haka, rashin aiwatar da wannan al’ada ya haifar da wani giɓi a cikin lamarin zumuncin bahaushe. Haka ma, ana iya cewa a  yanzu  a tsakanin al’umma babu  jinkai da tausayin juna, uwa-uba sai tsabar rowa, domin a yanzu maƙwabci na iya ci ya hana  maƙwabcinsa ba tare da wata damuwa ba.

4.3 Taɓarɓarewar Al’adar Bikin Suna

Kamar yadda bayani ya gabata, Hausawa sun ba bikin suna muhimmanci ƙwarai da gaske, musammam idan  aka dubi irin kai –komo da gidan uba da na uwar jinjirin kan yi na shirye –shiryen suna. A al’adance za a ga ranar suna rana ce da ake tara dangin uwa da na uba da ‘yan uwa da abokan arziki domin taya ɗan uwa murnar samun ƙaruwa. Wannan na zaman wata kafa ta ƙara haɗa danƙon zumunci a tsakanin al’umma, inda za a haɗu da wanda aka daɗe ba a haɗu ba . Wata fa’ida ta taron zanen suna ita ce wani bagire ne da ake tattauna wasu matsaloli na al’umma.

Amma a yau, zai yiwu ko dai saboda fahintar addini  ya sauƙaƙa abubuwa. Wannan ya sa al’ummar Hausawa sun yi saku-saku da wannan al’ada.  Ta wata fuskar, ya yiwu matsatsin tattalin arziki da al’umma ke fuskanta ya sa aka  yi saku-saku da wannan  al’ada. Babu shakka, idan aka yi karatun-ta -natsu, za a ga wannan al’ada ta taɓarɓare.

4.4 Taɓarɓarewar Al’adar Wankan Jego

Hausawa na cewa, ‘Zamani riga ce, tana daidai da wuyan kowa’. Duk da yake a al’adance an sani  wankan jego ko biƙi abu ne mai muhimmanci musamman ga mace mai haihuwa, a yanzu al’ummar Hausawa na son ta yi watsi da shi.  A  zahiri a yanzu ta ci baya ainun. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da wayewar kai ba, musamman ganin yadda wasu matan Hausawa suke cewa wai amfani da ruwan zafi yana dafe masu jiki. Wasu kuwa suna jin tsoron amfani da ruwan zafin ne saboda zafinsu. A yanzu saboda yawaitar haihuwa da ake yi a asibiti ba a cika wankan jego ba. Wannan kuwa yana faruwa ne saboda a yanzu  akwai  ƙwayoyin magunguna da allurai da ake yi wa mai haihuwa a asibiti da zarar ta sauka  maimakon wankan jegon. Sai dai abin lura a nan shi ne, duk da waɗannan allurai bai kamata a bar wankan jego ba saboda irin muhimmancinsa a al’ummar Hausawa.

4.5 Taɓarɓarewar Al’adar Kayan Gara

Kayan gara kamar yadda bayani ya gabata, ‘yan kayayyaki ne da ake kawo wa uban jinjiri a lokacin suna ko lokacin da za a dawo da mai haihuwa daga gidansu zuwa ɗakinta. Wannan al’ada ana yin ta ne domin a ɗan taimaka wa miji da wani abu, ganin  ya yi ɗawainiyar biki. Duk da irin wannan manufa ta kayan gara, a yanzu al’adar ta taɓarɓare sosai a cikin al’ummar Hausawa. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da nason baƙin al’adu ba. Domin a tsarin zamantakewar Bature kowa tashi ta fisshe shi ne, in ba ka yi ba ni wuri. Zamantakewa irin wannan kuwa ba ta buƙatar taimakon juna, sai dai kowa ya yi ta kansa. Zai  yiwu kuma, saboda yanzu akwai matsin tattalin arziki, musamman a Arewacin Najeriya wanda shi ya taimaka wajen raguwar aiwatar da wannan al’ada.

4.6 Taɓarɓarewar Al’adar Reno A Al’ummar Hausawa

A yanzu idan aka lura, za a ga al’adar reno ta taɓarɓare ainun a cikin al’ummar Hausawa, musamman saboda nason wasu baƙin al’adu a cikinta A  zamanance ana ganin wannan a matsayin ci gaba; Amma a zahiri  ci baya ne . Misali idan aka dubi tsawon lokacin da uwa kan samu tana goye da ɗanta ko rungume da shi, Wannan yana ƙara danƙon zumunci da soyayya da jinƙai a tsakanin jinjirin da uwarsa. Haka kuma, nonon da take ba shi yana matsayin kariya ga wasu cututtuka gare shi. Don haka, uwa kan ɗauki ɗan reno domin ya rinƙa taimaka mata da renon.

A yanzu lalurar ɗan reno ya kusa zama tarihi, domin yanzu zamani ya zo da cibiyoyin reno na musamman, inda za a kai jinjiri reno, uwar kuwa ta wuce wurin  aikinta. Bugu da ƙari , a yanzu an samar da magunguna waɗanda suke ƙumshe da abinci. Wannan kuwa na taimakawa sosai wurin rage shan nonon jinjiri. Wata matsala ta zamani da kawo cikas ga harkar reno ita ce rashin gaskiya a cikin al’umma, inda sau da yawa za a tarar an haɗa kai da ‘yar reno an cutar da jinjiri domin wasu buƙatu na duniya.

5.0 Shawarwari


Domin tabbatar da wanzuwar al’adun haihuwar Hausawa da aka ɗan yi bayanin su a wannan maƙalar, za a ga ta la’akari da muhimmancinsu a cikin al’ummar Hausawa bai kamata a bari waɗannan al’adu su salwanta ba wai don kawai nason baƙin al’adu da ya shige mu. Domin duk al’ummar da take watsi da  nata al’ada tana kwaikwayon na wasu, to kul-a jima za ta manta da nata. Bisa ga wannan ne ake kira ga al’ummar Hausawa da mu yi riƙo da kyawawan al’adunmu na haihuwa  babu kama hannun yaro.

Ta fuskar amfani da kayan zamani kuwa musamman kayan kallace-kallace, a yanzu sun maye gurbin hirar da ake yi da dangi a lokacin bikin haihuwa. Domin a yanzu sai dai a shiga kallace-kallacen fina-finan zamani. Don haka akwai buƙatar a yi watsi da wannan al’adar ta kallace-kallace a yi amfani da dandalin suna wanda yakan zama  zauren tattauna matsalolin da suka shafi rayuwar al’umma.

Bayan haka, shigowar hukuma cikin lamarin yana iya taimakawa wajen kauce wa taɓarɓarewar al’adun haihuwa a al’ummar Hausawa. Domin wasu al’adun aiwatar da su na buƙatar kuɗi. A yanzu saboda matsin tattalin arziki mafi yawan  Hausawa suna fama da wannan matsala ta kuɗi. Don haka, hukuma na iya taimaka wa al’umma da bashi ba tare ruwa ba . Hukuma na iya ƙirƙiro  wasu dokoki waɗanda za su taimaka wajen wanzar da al’adun haihuwa. Yin haka, zai taimaka wajen maganin taɓarɓarewar waɗannan al’adu.

Bugu da ƙari, wannan maƙalar na ganin ya kamata a sami wasu ƙungiyoyi na maza da mata da za su taimaka wajen wayar ma jama’a da kai dangane da muhimmancin waɗannan al’adu. Al’adun kuwa sun haɗa da na goyon ciki, da na bikin suna, da na reno, da sauransu. Kuma su waɗannan ƙungiyoyi su  zama a ƙarƙashin kulawar shugabannin kowace al’umma waɗanda suka san darajar al’adun.

Shawara ta gaba ita ce, matsawar ana son kauce wa taɓarɓarewar waɗannan al’adun haihuwa, to akwai buƙatar a ɗan yi ma wasu gyaran fuska ta yadda za su dace da zamani . Misali al’adar yankan rago . Tun da an fahinci ba dole ba ne, to ya kamata jama’a su fahinci rashin rago ba ya hana suna. Domin a yanzu, sau da yawa za a tarar saboda rashin rago an daɗe  ba a yi suna ba. Haka idan aka dubi al’adar shan-ƙauri da gara, sun so su ɗan yi tsauri musamman ga marasa abin hannun su, domin wani ba ya da ƙarfin aiwatar da wannan al’ada. Amma kuma sai al’umma ta zarge shi a kan ya kasa.  Maimakon haka, kamata ya yi a ba mai gida shawara ya riƙa yin haƙuri da duk abin da Allah ya ba shi.

A ƙarshe, bisa ga shawarwarin da aka bayar a sama , za a ga  al’adun haihuwa sun taimaka musamman wajen adana da kuma haɓaka zumunci a tsakanin al’ummar Hausawa duk kuwa da irin barazanar da nason baƙin al’adu yake yi a kansu.

6.0 Kammalawa

Al’amarin haihuwa, al’amari ne mai matuƙar muhimmanci a wurin al’ummar Hausawa. Hasali ma, haihuwa ita ce ƙashin bayan yawaitar kowace al’umma a duniya. Shi kuwa lamarin haihuwa yana samuwa ne sanadiyyar yin aure a tsakanin namiji da mace. Buƙatar wannan haihuwa ya sa al’ummar Hausawa ta ba wa aure muhimmanci domin samun haihuwa.

A wannan maƙala an yi ƙoƙarin nazarin wasu al’adu ne da suka keɓanta ga al’adun haihuwa a al’ummar Hausawa. Daga cikin su akwai al’adar goyon ciki da ta naƙuda da ta kayan ƙauri da ta bikin suna da ta gara da ta reno da sauransu. A nan maƙalar ta yi ƙ      oƙarin bayanin yadda suke a da, da kuma yadda suke a yanzu bayan an sami nason baƙin al’adu a cikin su. Haka kuma, bisa ga binciken da aka gudanar an fahinci  a yanzu waɗannan al’adu sun taɓarɓare a cikin al’ummar Hausawa. Don haka, an kawo shawarwari yadda ake ganin za a iya kare al’adun daga ƙara taɓarɓarewa. Ko shakka babu, waɗannan al’adun haihuwa sun taimaka wa al’ummar Hausawa wajen wanzar da zamantakewa mai nagarta a tsakanin al’ummar Hausawa tare da inganta kiwon lafiya.

Post a Comment

0 Comments