1. Harshe/ Maƙogoro
2. Fatar jiki
3. Hanci
4. Zuciya/ ƙwaƙwalwa
Duk ƙarshensu na ƙarewa ne da wasalin /i/?
To amma ga misalai kaɗan a nan
A hanci ana jin
1. Wari
2. Ƙamshi
3. Ɗoyi
4. Zarni
5. Hamami
6. Gafi
7. Ƙarni
A harshe/Maƙogoro ana jin
1. Ɗaci
2. Tsami
3. Zaƙi
4. Bauri
5. Garɗi
6. Maƙaƙi
A fatar jiki ana jin
1. Sanyi
2. Zafi
3. Ɗari
4. Turiri
5. Ƙaiƙayi
6. Raɗaɗi
7. Tsanani
8. Sauƙi
9. Ɗumi
Sai kuma waɗanda ake jinsu cikin zuciya ko ƙwaƙwalwa. Kamar
1. Daɗi
2. Haushi
3. Takaici.
4. Ƙyanƙyami
5. Ɗoki
6. Marmari.
7. Shauƙi
8. Nishaɗi
9. Fushi
10. Tunani, da sauran su.
NB.
Ban ce ba za a iya samun wasu kalmomin da suka saɓa da wannan tsarin ba. Amma dai yawanci na ce. Na gode.
Mallaka: Hausa Club
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.