Alƙalami



Wannan waƙa na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin da “Fasihi Usman Mai Riga Jega” ya rubuta. Usman matashi ne da Allah ya zuba wa basirar gudanar da abubuwa daban-daban. Ciki har da baiwar rubuta waƙoƙi masu matuƙar ilimantarwa da faɗakarwa. Yana zaune a garin Jega da ke jahar Kebbi a Nijeriya.

Usman Mai Riga Jega
07067998315
Mairigajega@gmail.com

ALƘALAMI

1- Farko ni sai na kira gwanina,
    Allah sarki mai biyan buƙatu.

2- Roƙonka na ke yi dare da rana,
    Ka ban baiwar da zan wadatu.

3- To zan yi salatina wurin ma'aki,
     Muhammadu Abban su Bintu.

4-  Alihi da sahabbansa suna raina,
    Da duk wanda ya bisu za ya ƴantu.

5-  Ku zo ku ji yau ga sabon bayani
     Wanda na tsara kan abin rubutu.

6-   Matuƙar dai yanzu ana karatu,
     To ashe dai tilas ne a yo rubutu.

7- kunsan ai Alƙalami iri-iri ne,
   Amma ai kowane yana rubutu.

8-  Alƙalami amfaninsa fa ba iyaka,
    Domin ta silarsa ne na fahimtu.

9- In har ko kwalba ce uwar turare,
     To ashe Alƙalami ne uban karatu.

10-  Sam ba a zuwa gona in ba fatanya,
       Makaranta ko a je da abin rubutu.

11- Mu kam Shi ne zamu ƙanƙamewa,
     To meye amfanin kiɗan na shantu.

12- Kai! Jahillci shi ne ke ta yaudararmu,
      wallahi rashin ilimi ke sa a cutu.

13- Kai! Tabbas Alƙalami abin yabo ne,
      Lambu gun ka kowa ya ke ta hutu.

14- Ku duba ko zamani na manzomu,
      To ko lokacin ma ai na ji ana rubutu.

15- Dubi san da duk wahayi ya sauka,
       Anan lokacin wasu na yin rubutu.

16- To wanda ba ya yi ya ba mu hanya,
       Ni yanzu ma za ni fara yin rubutu.

17- Wanda ya riƙeshi ai  ba ya kunya,
      Tabbas zai ɗaukaka cikin halittu.

18-  Wayyo! Ni yau wai mi za ni cewa,
        Ni ina tausan wanda bai rubutu.

19- Kai kowane yare na duniyar nan,
     Idan kun bincika suna yin rubutu.

20- Samun Alƙalami mun yi murna,
     Don ga shi muna ta yin rubutu.

21- Ya Yan'uwa ni ina kiranku,
     Ku san darajar abin rubutu.

22- Ni Usman Mai Riga ake kirana,
     Garin Jega na ke kar ku zautu.

23- Waƙar nan to zan tsaya nan,
      Na gaida Alƙalami abin rubutu.

24- Godiya gun sarkinmu Allah,
     Wanda shi ne ya yi duk Hallitu.

Post a Comment

0 Comments