Ticker

Ɗan Boko


Wannan waƙa na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin da “Fasihi Usman Mai Riga Jega” ya rubuta. Usman matashi ne da Allah ya zuba wa basirar gudanar da abubuwa daban-daban. Ciki har da baiwar rubuta waƙoƙi masu matuƙar ilimantarwa da faɗakarwa. Yana zaune a garin Jega da ke jahar Kebbi a Nijeriya.

Usman Mai Riga Jega
07067998315
Mairigajega@gmail.com
Ɗan Boko

1. Bari in fara zancena da sunan Allah,
Allah ka ƙara salati ga ɗan Abdallah,
Manzona shugaban duka Annabawa.

2. Alihi da sahabbai ina ƙaunarsu Raina,
Wanda duk ke zaginsu ya ɓata Raina,
Wallahi ni barinsu ai sam ba na iyawa.

3. To ɗan boko mai ganin ubanai wawa,
Kai ni haka na ke ji ai ana ta yin cewa,
Wasu ne ke haka ai ba a cewa kowa.

4. To boko dai an samoshi daga turawa,
Shekaru da yawa da sun yo wucewa,
Yanzu bokon kowa shi ya ke Riƙewa.

5. Dubi ancne kakaninmu suna gudunsa,
Amma yanzu ga mu muna ƙaunarsa,
Ƙarshe ya lalata tarbiyarmu da yawa.

6. Kai! na ji wani malami ya na ta cewa,
Ƴan boko gida uku sun ka yo tsayawa,
Ku biyo ni ku ji su ni fa ba ni ɓoyewa.

7. Na ɗaya ɗan boko aƙida ai ya fi kowa,
Gu na wawanci shi kam ba a wucewa,
Kai a dabbobi ya fi jakin da ake hawa.

8. Duk abin da boko ya ce ba ya musawa,
Ko fa kafirci ne shi sai ya yo riƙewa,
 In ka ce Allah fa ya ce to ba ya kulawa.

9. Ƴaƴansa har matansa ya ba su dama,
Su yi fita ta tsiraici wace babu ƙima,
Ai ko ya gani dolo shi ba ya hanawa.

10. Ga rashin mutunci ya ɗauka a kansa,
Ba ya son kowama ya nema wurinsa.
Ko maƙwabtansa shi fa ba ya kulawa.

11. Kuma bai da aiki sai karatun jarida,
To ba ya bambanta tilawa da hadda,
Sai ya kai Prof Ƙur'ani ba ya biyawa.

12. To fa kun ji kaɗan daga boko aƙida,
Amma akwai masu dama na shaida,
A Boko aƙidar wasu na kwatantawa.

13. To na biyu Akwai mai boko sana'a,
Wanda shi kuɗi ɗai ya kewa ɗa'a,
In dai ga kudi ne komai yana iyawa.

14. In har kana neman masu cin Hanci,
Ga su sai zalunci ba sa da karamci,
In ka zo wurinsu to ai ba ka wucewa.

15. Su fa don kuɗi kawai su ke ta Boko,
Babu niyyar ƙwarai dama tun farko,
To arziki ai Allah ne ke ƙaddarawa.

16. Dubi su sun ƙware a wurin dabara,
Kai su Burinsu dai ai kullum su tara,
Halal da haram ai sam ba sa rabewa.

17. To kaɗan a cikin halin boko sana'a
Akwai na ƙwarai su nakewa addu'a,
Ni fa ba ya hallata garan in zargi kowa.

18 Kai mu je na ukun su boko fahimta,
Kun ga wanga ai shi ne ke da tsafta,
Kar ku damu lallai zan bayyanawa.

19. Mai boko fahimta fatansa ya gane,
Ga shi kuma shi damuwarsa mutane,
ba ya cewa komai ya yi amincewa.

20. Gashinan mai tausayi gun mutane,
 Fatan da yake fa ci gaban mutane,
 Yanzu ai irinsu lallai ba sa yin yawa.

21. Kuma na ji wani malami yana cewa,
Wajibi ne muyi Boko dalilan da yawa,
Amma a hankali wasu zan yo faɗowa.

22. To ga tambayoyina gare ku ƴan'uwa,
In mun ƙi yin boko wa zai yo hayewa?   
Likkitoci da yawansu ina su ke fitowa?

23. Sojoji ƴan'sanda sauran muƙamai,
Duk su zam ba na mu ina su jarmai?
In dai da kuɗi to boko kana iyawa.

24. To wanga sako ne dai ba ni na ce ba,
Kuma ni tunani ba shirme ba ne ba,
Don Allah hankalinku ku yo tattarawa.

25. Ni zan tsaya wata nan don in taƙaita,
Dukkanin waƙoƙina in za ku fahimta,
Fatana kuskurenmu mu yo dubawa.

26. Usman Jega Sunana na ke biyawa,
Mairiga inkiyana bana yin rufewa,
Ku yi ta yi min addu'a ya ku ƴan'uwa.

27. Alhamdu lillah ni na godewa Allah,
 Na kammala baitukana fa jimillah,
 Allah ka sa Aljanah mu yo shigewa.

Post a Comment

0 Comments