Ticker

Auren Dole



Wannan waƙa na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin da “Fasihi Usman Mai Riga Jega” ya rubuta. Usman matashi ne da Allah ya zuba wa basirar gudanar da abubuwa daban-daban. Ciki har da baiwar rubuta waƙoƙi masu matuƙar ilimantarwa da faɗakarwa. Yana zaune a garin Jega da ke jahar Kebbi a Nijeriya.

Usman Mai Riga Jega
07067998315
Mairigajega@gmail.com
Auren Dole

1.To Bismillah Allah zan fara
 Taimakeni laifukana in gyara,
  Masoyana ina muku bushara,
Yau wata waƙa ce ni na tsaro.

2.To ku bari dai in fara salatina
  A wurin Manzona mai cetona,
  Alihi da sahabbansa masoyana
  Wajibi ne in zan waƙa sai na jero.

3.Kuma bayanina akan Auren dole,
 Shin Matsalar ta ina ne ta ɓalle?
 Ku biyoni ku ji ku daina ta tsalle,
 Yau zan cire tsakuwa a cikin gero.

4.Ku ma kun san fa auren dole illa ce
 Laifin daga iyaye ne, ni haka zance,
 Ko da fa akwai zumunci zai lalace,
 Shi ne ke sa yarinya yawon kwararo.
      
5.Komai kuɗinka Wata ai ba ta sonka,
 Kan auren dolen ta na iya yankeka,
  Kai za ta iya cin mutuncin iyayenka,
 In ba a sonka to ka daina nuna taro.

6. Da mai sonka da mai ƙin ka wa ya fi?
 Ashe dai ni kam ku zan azawa laifi,
 Kun jefa kan ku cikin rame mai zurfi,
 Wallahi wanga wauta ce ko ga yaro.

7. In ka Aureta ba ta ganinka da ƙima,
 Ballai ta yi sauri Abinci ta girka ma,
 Ai kodayaushe za ka ganta da rama,
 Ba ta ba ka ruwan kofi ballai na faro.
 

8. To shi ke sa yarinya ta kashe kanta,
  Don tunaninta fa shi ne ƙaɗai mafita,
  Ta ce ba ta so iyayen sun ƙi fahimta,
  Iyayen ke gargaɗinta duk ta zaburo.

9. Dubi wurin kwanciya sai ta jayema,
 To daga nan wani bala'i zai soma,
 Ai tamkar mahaukaci za ka koma,
Sarkin ƙarfi ai ba ya kai sarkin taro.

10. Matsalolin kam ai suna da yawa,
 Auren dole shi ne baƙar haduwa,
Wallahi ba nisa auren ke rabuwa,
 Ko da an yi Addu'a an raba goro.

11. Kar dai in ce Auren haramun ne,
 Amma ina ta kiranku ya mutane,
 Ku bar Auren dole don wauta ne,
 Mata da Maza zancena a sauraro.

12. Ta silarsa Yarinya ta na shan duka,
 Koda da cikinta wallahi ba shakka,
In ba sonka wallah kar ma ka ɗauka,
Don da ka Aureta gwara kana gwabro.
     
13. Dubi fa ga wanda ta ke so a zuciya,
 An ɗauketa an ba wawan duniya,
 Kai shi ma ya san babu zama lafiya,
 In dan kuɗi ne to wallahi daina doro.

14. Tabbas  Aure ni'ima ce mai yawa,
  Ta silar Auren dole fa ba a ƙaruwa,
  Ko ciki ta samu ta na iya zubewa,
 Ni fatana in an yi aure a samu yaro.

15. Wata ba ta ko gaisawa da iyayenta,
 Domin ko sun cuci duk rayuwarta,
 Amma su gani suke sun yo bajinta,
Soyayya haɗin Allah ce dubi sauro.

16. To fa duk da ni ilimina bai da zurfi,
Mai haɗa Auren dole ai ya yi laifi,
Domin da hauka ai ba a kama kifi,
 In har ba ta so kar ma a sayi goro.

17. Wata fa ba ta ko kwana gidan miji,
 Kar ma kuce ta saɓawa Ubangiji,
 Kai gare shi ma take neman agaji,
  Alƙali shawarata dai a ɗauko biro.

18. To Alƙalai ku kashe fa Auren dole,
  Da Sarakuna to matsalar ku kulle,
 Malammai duk ku zo  ku daddale,
To ku ɗauki maganar wanga yaro.

19. To Usman Mai Riga ni ake kirana,
  Kun dai ji Matsalar da ke damuna,
 In an ka gyara wallahi zan yi murna,
Alhamdu lilah ta soyayya na gangaro.

20. Zan tsaya nan Ɗan Jega na yi godiya,
  Gun Sarkina mai kyauta ai duniya,
  Wanda ya sanya a Jikinmu soyayya,
  Allah ka sa Usman na zamo tauraro.

Post a Comment

0 Comments