Ticker

Adawa A Dimokuraɗiya: Tubalin Gina Ƙasa

 Tsarin mulkin siyasa wani salon mulki ne na farar hula da ke baiwa yan ƙasa yanci da damar tsoma albarkacin bakinsu ga yadda ya kamata shugabanni su tafiyar da salon mulkinsu don cigaban ƙasa da bunƙasa ilimi da tattalin arziki. Adawa wata hanya ce da yan siyasa ke amfani da ita wajen yiwa shugabanni hannunka mai sanda domin su tunnatar da su bisa ga alkawurran da suka ɗauka a lokacin yakin neman abe. Kowace jam’iyya tana da manufofin da aka kafa tad a su waɗanda manufofi sun e suke yi ma yan siyasa jagora ga samun nasarar kafa kyakkyawan mulkin dimokuraɗiya. Gudanar da mulki na adalci shi ne ginshiƙin zaman lafiya da cigaban ƙasa ta fannoni daban-daban na rayuwar yau da kullum. Yan adawa suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyin salon mulkin dimokuraɗiya ta fuskar bunƙasa ilimi, tattalin arziki da tsaro don cigaban ƙasa.

Adawa A Dimokuraɗiya: Tubalin Gina Ƙasa

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

GSM NO. 07032567689

E-mail: aliyurabiu83@gmail.cim

Gabatarwa

Mulkin dimokuraɗiyya wani tsarin salon mulki ne wanda jama’a ke zaɓen shugabanninsu da kansu. Wannan irin salon mulki shi ne wanda yake bai wa duk ɗan ƙasa damar faɗin albarkacin bakinsa. Ana kafa mulkin dimokuraɗiyya ta hanyar kafa jam’iyyu bisa ga dokar tsarin mulkin ƙasa. Kowace jam’iyya tana da manufofin da aka kafa ta da su domin su zama jagora ga jama’ar ƙasa ga samun nasarar gudanar da zaɓen shugabanni tun daga ƙananan hukumomi, jihohi da kuma Gwamnatin tarayya.

Duk lokacin da wata jam’iyya ta sami damar kafa Gwamnati, to akan sami sauran jam’iyyu su zama masu soke-soke da korafe-korafe game da yadda jam’iyyar mai mulki take tafiyar da salon mulkinta. Waɗannan soke-soke da korafe-korafe sune ake kallo a matsayin adawa. Wannan takarda za ta tattauna game da adawa da tasirin da take da shi a fagen mulkin dimukoraɗiyya da cigaban ƙasa.

 

MA’ANAR ADAWA

Adawa tana nufin nuna rashin gamsuwa da yadda wani mutum ko wasu mutane ake gudanar da salon mulkinsu. Wani lokaci Bahaushe yakan kalli adawa a matsayin hassada ko kushewa zuwa ga wani mutum da ake tunanen baya bin ƙa’ida wajen tafiyar da mulkin jama’a ko mulkin ƙasa.

 

Hornby (8th Edition): Adawa tana nufin rashin yarda da wani tsari ko shiri na wani mutum ko wasu mutane da ke jagorancin jama’a da nufin kawo canji mai ma’ana. Bargery G.P (1993): Adawa tana nufin ƙiyayya ko kushewa da wani mutum zai nuna ga wani tsari ko shiri da hukuma ko wasu shugabanni ke aiwatarwa. Mariam Webstarts (10th edition): Adawa tana nufin rashin amincewa ko yarda ga wani abunda ya saɓawa ra’ayin sauran jama’a a cikin shugabanci domin a maye gurbinsa da abinda mafi rinjayen jama’a suke da ra’ayi.

 

Shi kuwa Bahaushe yana kallon adawa a matsayin kishi, ko jiyewa ko ƙyashi ko nuna ƙiyayya zuwa ga wani ko wasu mutane wajen aiwatar da wani tsari ko shiri da ya saɓawa al’ada ko ra’ayin jama’a domin akawo sauyi. Idan aka tattara waɗannan ma’anoni gaba ɗaya zasu bada ma’anar adawa a dunkule cewa rashin yarda da wani tsari ko shiri da wani zai kawo wanda ya saɓawa ra’ayin wasu jama’a shi ake kira a dawa. A takaice dai kalmar adawa ta samo asalinta daga kalmar Larabci, a larabce kalmar tana nufi ƙiyayya bisa ga wani abinda ba’a aminta da shi ba, kamar yanda ta tuzgo daga tarihin Annabi Adamu (AS), inda Allah ya ambaci adawa a wurare daban-daban a cikin littafi mai tsailki (ƙur’an 2:30, ƙur’an 3:22-24).

 

Adawa a Hausance tana nufin kulawa da abinda wani mutum ko hukuma ke aiwatarwa da ya saɓawa al’adar ƙasa da ra’ayin jama’a domin a gyara, da wannan takaitacciyar ma’ana ta adawa zan tattauna rawar da adawa take takawa a cikin mulkin demukraɗiyya domin a samar da canje-canje a cikin tsarin shugabanci wanda zai kawo ci gaba a Najeriya.

 

ADAWA A CIKIN SIYASA

Adawa ta siyasa itace wadda ta ke gudana tskaanin yan siyasa da masurike da muƙaman siyasa da na Gwamnati daban-daban. Kowace ƙasa tana kafa mulkinta bisa ga kundin tsarin mulkin ƙasar. Tsarin mulkin ƙasa kan tanadi kafuwar jam’iyyu da za su yi takarar kujeri daban-daban tun daga kujerar kansila har zuwa ta shugaban ƙasa. Misali a Nijeriya akwai jam’iyyun siyasa kimanin 50, amma kaɗan daga cikinsu suka kafa Gwamnati a tarayya har zuwa ƙananan hukumomi. Duk jam’iyyar da ta kafa mulki, ita ce jam’iyya mai mulki, saura kuma su ne yan adawa (Aminu 1987). Da wannan bayani zan danganta wannan takarda da irin adawar da ke gudana tsakanin al’umma da "yan siyasa da kuma masu riƙe da ragamar mulki.

 

ƊAN ADAWA  

Ɗan Adawa wani mutum ne mai nuna ra’ayinsa a fili wajen faɗar gaskiya ga masu riƙe da muƙamin Gwamnati, ko wasu jama’a da yake hulɗa dasu idan ya kalli sun kaucewa al’adar ƙasa ko al’umar da yake cikin su. Abubuwan da ke haddasa adawa tsakaninyan siyasa ko masu tafiyar da mulkin ƙasa sune:

1.         Rashin cika alkawari ga jama’ar da suka zaɓa shugabanni. Kamar yadda kowa ya sani kowace jam’iyya tana da manufofin da aka kafa ta da su. Kuma yan jam’iyyar su ne masu aiwatar da waɗannan manufofi idansun sami damar shiga cikin Gwamnati. Manufofin kowace jam’iyya ba su wuce waɗannan abubuwa ba, da ke biye.

a.      Bunƙasa aikin gona da samar da isasshen takin zamani ga talakkawa.

b.      Samar da wadataccen ruwan sha ga mazauna birare da karkara.

c.       Bunƙasa ilmi da tallafawa makarantu da kayan aiki {Littafai, kujeri, da ajujuwa}

d.     Bunƙasa fannin kiwon lafiya ta hanyar samar da Asibitoci da magani kyauta ga kowa da kowa.

e.      Samar da muhalli {gidaje} ga yan ƙasa domin rage cunkuso a birare da sauransu.

f.        Tabbatar da tsaro a ƙasa, ga rayukka da dukiyoyin al’umma

g.      Bunƙasa kasuwanci da tattain arzikin ƙasa ta hanyar kafa masana’antu da tallafawa yan kasuwa da jari.

Duk waɗannan manufofi da ke sama su ne kowace jam’iyya take fafacakar yakin neman zaɓe da su. Idan Allah ya sa aka zaɓe su da waɗannan manufofi ne al’ummar da suke zaɓe su za su riƙa sukar su ko faɗa masu gaskiya idan suka kasa aiwatar da su. Maganganunda zasu rika faɗi na tunatarwa sune masu muƙamin gwamnati ko yan siyasa ke ɗaukar cewa ana adawarsu.

 

Kasawar shugabanni ga aiwatar da waɗadannan alkawuran da suka dauka lokacinyakin neman zaɓe su ne ummul haba’isun haddasuwar adawa, a siyasance. Jami’iyyar da duk ta kafa Gwamnati a matakin ƙasa ta zama jam’iyya mai mulki, sauran waɗanda ba sukafa Gwamnati ba sun zama jam’iyyun adawa {Dangubi 2003}. Haka suma magoya bayan waɗannan jam’iyyu sun zama yan adawa musamman ga jam’iyya mai mulki. Dukkan abin da ɗan adawa ya furta na magan-ganu to sun zama magan-ganun adawa.

 

A Nijeriya jam’iyyar PDP mai mulkin ƙasa ita ce jam’iyyar da sauran jam’iyyu ke adawa da ita. A wani lokaci takanfaru jam’iyyar da ta kafa Gwamnati a sama {ƙasa} ba ita ke da dukkan jihohi ba. Haka jam’iyyar da ke da jiha ba ita ke da dukkan ƙananan hukumomi ba. A duk inda aka sami irin wannan banbanci na jam’iyyun siyasa a kujeri daban-daban a ƙasa ko a jiha ko a ƙanannan hukumomi da wuya a sami cikakken haɗin kai ga jam’iyya mai mulki. Don haka a matakin tarayya jam’iyyar PDP ita ce ta ƙasa sauran jam’yyu sun zama yan adawa a matakin ƙasa. Haka abin yake a jihohin da PDP ke mulki da sauran jam’iyyu, har zuwa kananan hukumomi {Dangulbi 2003}.

 

TASIRIN ADAWA GA GINA ƘASA

Gina ƙasa da cigabanta ta kowane fanni ya ta’allaka kacokam a kan iya tafiyar da mulki da shugabnni ke aiwatarwa. Maƙasudin yin adawa a mulkin dimokuraɗiyya a ƙasa shi ne; domin faɗakar da shugabanni ta hanyar yi masu hannunka mai sanda bisa ga alkawurran da suka yi wa al’umma lokacin da suke yaƙin neman zaɓe. Koyaushe mutane kan sanya idanu ga yadda shugabnni ke gudanar da mulki domin su ga wuraren da suka yi dai-dai su yaba da kuma inda suka yi kuskure su yi masu nunu su gyara.

 

BUNƘASA AIKIN GONA

“Yan siyasa sukan yi alkawalin taimakawa talakkawa ta fuskar basu bashin noma da wadataccen takin zamani dan su bunƙasa harkar noma, da wannan ne mawaƙan siyasa suke tallata jam’iyyunsu ga jama’a domin a zabesu su kafa gwamnati idan sun kafa gwamnati su aiwatar da duk alkawarran da suka yiwa talakkawa, misali; Muhammad Ɗan Musa Kano yana faɗakar da al’umma game da alkawalin da jam’iyyar APP tayiwa talakkawa cewa zata tallafa masu ga harkar noma ta hanyar basu shanun noma, injin da galma da kuma wadataccen takin zamani. Misali yana cewa a cikin wakarsa ta APP zan zaba dan ta kare haƙƙin talakawa, yana cewa:

Tai nufin baku shanun noma

Har da injin da garman noma

Tai nufin baku takin noma

Zata kare haƙƙin talakawa

Wannan baiti ya nuna mana irin alkawalin taimako da jam’iyyar APP ta yiwa talakawa na wadatasu da takin zamani da galmar noma da kuma shanun noma dan su bunƙasa aikin gona, domin a samar da wadataccen abinci da kayan masarufi don bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Da irin wannan alkawali da jam’iyyar APP tayi ta kuma kasa samarwa jama’a abinda tayi alkawali yasanya jam’iyyar PDP ta ƙalubalanci APP da cewa ta zama mai alkawali bata cikawa. Musa Baban Bege Sokkwato a cikin wakarsa ta PDP yana sukar jam’iyyar APP yana cewa:

Suna da akida dan alkawal sukan yi su tada,

Ko kuma su ce a tada ta’adda

Yau, babu soja, babu dansanda,

Wanda zai hanamu kunar taku ɗiyan masara

Shima da yake nuna tasa a dawa dangane da saɓa alkawali da jam’iyyar MPN tayiwa talakawa a jamhuriya ta biyu, Muhammad Auwalu Isah Bungudu a cikin wakarsa ta PRP jam’iyyar Talakawa, Malamin yana cewa.

Don alkawali fa bashi ne,

Ko waɗ ɗaukeshi cilas ne

Ya cika in dai sahihi ne

Nai alkawali da ɗan jani

Ni ko ba za ni saɓa ba

……………

Ita ƙariya bata haifawa,

Da furenta take ta burgewa

Kai kace bata karewa

To ƙariya bata ɗorewa

Ko anyi bazata dore ba.

Malam Auwal Isah Bungudu ya nuna muna irin alkawurran ƙariya da ‘yan siyasa ke yiwa talakkawa dan su jawo hankalinsu su aminta da manufofin jam’iyyar su a lokacin da suke yekuwar yakin neman zaɓe, dangane da irin waɗannan alkawurran karya da ‘yan siyasa basa cikawa yasanya mawaƙan siyasa na Hausa irin su Auwalu Isah Bungudu suke nuna adawarsu ga jam’iyyar da ke mulki da ta kasa cika alkawurran da tayi wa talakkawa.

 

BUNƘASA ILIMI

A fannin ilimi na addini ko zamani akan sami adawa tayi tasiri musamman wajen kasa cika alkawurran da ‘yan siyasa sukan yi wa talakawa cewa zasu tallafawa makarantu ta hanyar samar masu kayan aiki da ƙwararrun Malamai. Jam’iyyun siyasa da dama sukan yi amfani da dabarun jawo hankalin masu zaɓe ta hanyar shimfiɗa alkawurra lokacin yakin neman zaɓe, kamar yadda muka faɗa a baya ko wa ce jam’iyya tana ɗauke da manufofinta ciki har da manufar bunƙasa ilimi da wannan manuface mawaƙa ke tallata jam’iyyunsu har su kai ga samun nasarar kafa gwamnati, idan sun ɗare kujerar mulki sai su manta da ɗinbin alkawurran da suka yi wa talakawa. Irin wannan rashin cika alkawali ke jawo hankalin yan adawa su riƙa jefa albarkacin bakinsu ta hanyar suke-suke da ƙorafe-ƙorafe game da salon mulkin jam’iyya mai ci; Misali Jam’iyyar PRP tana nuna a dawarta ga Jam’iyyar NPN wadda takasa cika alkawalin da ta dauka na bunƙasa ilimi. Marubucin waƙar jam’iyyar PRP Mugode Allah Babban Sarki, Malam Lawal Isah Bungudu yana maida raddi ga jam’iyyar NPN wadda ta soki yayan jam’iyyar PRP cewa jahilai ne kuma kauyawa kuma jam’iyyar talakawace matsiyata, saboda sai Malam Lawal yake cewa:

An sukemu jahilai bama turanci,

An ce ba’a sonmu dan kada mui ƙauyanci,

Jam’iyyar mu babu kuɗi ba motoci

Kuma ba keke babu babur amma ta ci,

An zaɓeta an ki jam’iyyar turawa.

Ilimi wani abu ne da yake da muhimmanci ga rayuwar kowace al’umma. A baitin da yagabata ya nuna mana cewa wasu suna ganin don kana da ilimin addini in ba ka iya na boko ba to da kai da jahili duk dai kuke, watau duk wanda bai jin harshen turanci ko ba’a iya magana da shi an daukeshi jahili kuma bakauye, wannan ra’ayi ne na ‘yayan jam’iyyar NPN wanda suka kasa cika alkawalin bunƙasa ilimi, amma sun dage ga sukar wasu jam’iyyu.

 

ADAWA TA FUSKAR ƁUNKƘASA TATTALIN ARZIKI

Adawa takanyi tasifin gaske a fannin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, bunƙasa tattalin arzikin kasa shi ne samar da masana’antu da kamfunna waɗanda zasu kawo hanyoyin cigaban ƙasa ta fuskar sana’o’i da samar da kuɗin shiga da kuma samar da aikin yi ga matasa da sauran al’ummar kasa, kamar yanda muka faɗa a baya ko wace jam’iyyar takan yi ƙoƙari ta aiwatar da manufofinta domin tasamu karɓuwa ga jama’ar ƙasa dan azaɓeta ta kafa gwamnati. Da irin wannan mawaƙa kanyi ƙokari su tallata jam’iyyunsu kamar yanda Alh. Muhammad Ɗanmusa Kano ya kambama jam’iyyar APP inda yake nunawa jama’a irin shirinta na buƙasa kasuwanci da bada tallafi ga yan kasuwa domin su bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da dogaro da kai, a cikin waƙarsa ta APP yana cewa:

Malam in rake kake saidawa

Ko da ko ne kake ɗaukawa,

jam’iyyata tana nunawa

Babu banbanci talakawa

 

Malam ko ko mota kake saidawa

Ko jirgi kake tukawa,

jam’iyyar mu yau na nunawa

Babu banbancin talakawa

Wadannan baitoci da suka gabata a sama, sun nuna mana irin shirin jam’iyyar APP da tayi domin ta bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, ta yi alkawarin ba yan kasuwa tallafin kuɗi don bunƙasa sana’o’in su tun daga masu sayar da rake har zuwa gamasu sayar da motoci, harwayau jam’iyyar bata tsaya nan ba ta haɗa har da masu dakon kaya zata tallafa masu.

 

Haka shima Malam Aminu Ibrahim Ɗandago; a cikin waƙarsa ta APP ya ƙara jaddada niyyar jam’iyyar sa ta fuskar kawo cigaba a fannin tattalin arziki yana cew:

Har an zartar ana faɗin ance za a yi,

Sauƙi ga biyan kuɗin hajin bana mai so ya yi

Kuɗin ka ƙalilan idan kaso tafiya sai ka yi

Ba wata matsala da zatazo ta hana don a yi

Cinikayyar arziki ta ɗaukaka Nijeriya

.......................

Anyi mitin jiya ina labe da kunnena na ji

Za a yi oda ta kamfanin haɗa jirgi ku ji

Na ji magauta suna faɗa a gari sun gaji

Ya Allahna Ubangiji ka yi mana agaji

A.P.P bana tazo ta mamaye Nijeriya

Baiti na sama na farko ya bayyana irin shirin da APP tayi  ta taimakawa jama’ar ƙasa wajen aiwatar da aikin haji ta hanyar sauƙaƙa kuɗin kujera domin tausayawa masu niyar sauke farali, haka kuma ta bunƙasa tattalin arziki ta hanyar cinikayya a lokacin hidimomin aikin haji dan daukaka tattalin arzikin Nijeriya.

 

A baiti na biyu a sama, Jam’iyyar A.P.P ta yi gagarumin shiri na shigo da kamfanin haɗa jirgin sama, domin yan Nijeriya su daina yo shatar jirgi daga ƙasashen waje. Yin haka zai taimakawa Nijeriya ta samu kuɗin shiga ta bunƙasa masana’antunta da sauran fannonin kasuwanci, amma magauta, watau yan adawa suna ganin wannan shiri ba zai yuwuba, saboda yan Nijeriya sun gaji da gafara sa basu ga ƙahoba.

 

Akan sami wani lokaci yan adawa basu jiran su ga an aiwatar da abubuwan da aka yi masu alkawari, sai su shiga jefa maganganu na ɓatanci da ganin kasawar shugabanni wajen aiwatar da ayukkan raya ƙasa. Wani lokaci kuwa idan yan adawa bas u sami biyan buƙatunsu ban a ƙashin kansu, sai su hau dokin bakunansu su riƙa jefa kalmomin Allah tsine da Allah wadai ga masu mulki, saboda kawai an kasa biya masu da buƙatunsu. Don haka sai ka ga kazuffa da soke-soke suna kai kawo tsakanin mutane da yan siyasa kawai don su cusa akidar kiyayya da tashin hankali a zukatan sauran al’ummar ƙasa wanda zai hana shugabanni su sami damar aiwatar da ayukkan da suka sa a gaba. Irin wannan adawa it ace wadda babu ruwan masu yinta da ayyukkan raya ƙasa da ayukan alhairi da shugabanni ke yi komi yawansu, kuma komi kyawansu. Irin wannan it ace adawa maras ma’ana. Shi ne ya sa Bahaushe ke yin wata karin magana da ke cewa “Maƙiyinka bai ganin ƙwazonka, ko da ka kama Damisa yana iya cewa Ɓera ce, ko kuma ya ce matatta ka same ta”

 

Marubuta waƙoƙi da makada sukan yi amfani da fasaharsu su riƙa sukar jam’yyn adawa domin kawai su daɗaɗa wa mutanensu rayuwa domin su cimma biyan buƙatar su ta fanning gina ƙasa. Misali wani mawaƙi ya yi suka mai gauni ga jam’iyya adawa da ta kasa samar da abubuwan more rayuwa ga al’umma, Malamin yana suka ne a cikin waƙarsa ta PDP inda yake cewa:

“Babun Babun ta yi yawa na lissaftawa Hausawa

Babu Magani babu ruwan sha, wutar nan bata ɗorewa

Sun ce zasu maida haraji munce ba a maidawa

Ko da za ai ruwan kibiya sai

PDP mazanmu da mata.

 

Kasa samar da irin waɗannan abubuwan more rayuwa da gwamnatoci ke yi ga al’ummar da suka zabe suya kara ririta wutar adawa a ƙasar nan.


KAMMALAWA

Tattalin arzikin kowace ƙasa da cigabanta ta fuskoki daban-daban a duniya ya dogara ga irin cika alkawaran da shugabanni suka ɗauka a lokacin da suke yawon yaƙin neman zaɓe. Dukan manufofin jam’iyyun siyasa na ɓuƙasa ilimi da kiyon lafiya da samar da wadataccen muhalli da tsaro da abinci da kasuwanci manufofi ne da ke buƙatar gogaggu ƙwararrun masana daban-daban domin su ba da shawarwari ga masu mulki ta yadda zasu aiwatar da ayukan cigaban ƙasa.

 

Yan adawa mutane ne da ke kara faɗakar da shugabanni da masu rike da mukaman siyasa ta hanyar maganganun adawa da suke jifar su da su, sai dai adawar tana kasancewa mai ma’ana, watau faɗar gaskiya da yin hannun ka mai sanda ga masu mulki domin su gyara inda yake son gyara. Sai kuma adawa maras ma’ana wadda ita tsabagen kiyayya ce ga masu mulki da soke-soke gare su ko da sun aiwatar da ayuka na raya ƙasa. Haka abin yake ga sauran al’amurran rayuwar yau da kullum. Adawa itace tushen hassada da ƙeta da ƙiyayya. Duk jam’iyyar da ba ta da 'yan adawa za ta kasance 'yar mulkin kama karya, haka kuma idan ba a yiwa gwamnati a dawa to bazata kula da yiwa jama’ar ƙasa ayukkan da suka kamata ba. Don haka adawa itace gishirin siyasa a mulkin demukraɗiyya da ke kawo gina ƙasa.

 

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments