Muƙalar da aka gabatar a babban taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa karo na huɗu (4) wanda Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Da Kimiyyar Nazarin Harshe, Jami’ar Jahar Kaduna ta Shirya a kan wasan kwaikwayon da lamurran finafinan gargajiyar Hausa a ƙarni na 21. A harabar Tsangayar Fasaha da ke Jami’ar Jahar Kaduna daga ranakun 28 zuwa 30 ga watan Maris na shekarar 2019.
Ginuwa Da Bunƙasar Rubutaccen Wasan
Kwaikwayon Hausa A Kan Mizanin Manazartan Ƙarni Na 21
Dr.
Adamu rabi’u bakura
08064893336
Tsakure
Wasan Kwaikwayo yakan
kasance wasa ne wanda yake ba gaskiya ba
a lokacin da ake gudanar da shi. Kuma wasan yakan zama maƙasudinsa faɗakar da al’umma da ilmantar da su ta hanyar
sake-kama. A wajen sake kaman nan, mai wasa ko ‘yan-wasa za su canza kamanninsu
na yau-da-kullum. Sake Kaman nan na iya zama ta sigar tufafin ‘yan-wasan ne, ko
ta abubuwan da suke amfani da su, ko kuma ta abubuwan da suke yi. Wato kamannin
mai-wasan, ko ‘yan-wasan ya zan ya bambanta da halayyar mai-wasan ko ɗabi’ar ‘yan-wasan. A
kan iri wannan turba ce aka gina wasan kwaikwayo na kowace al’umma da ta tsira
a farfajiyar wannan duniya tamu. Hasali ma ta hanyar kwaikwayon ne aka aza
ginin wasu al’adun al’umma. Misali al’adar nan ta rufe mamaci wato yi masa
kabari ta wanzu ne a sakamakon kisan gillar da Ƙabila ya yi wa ɗan’uwansa Habila.
Saboda haka ne Allah Ya turo hankaka domin a koya masa yadda zai binne gawar ɗan’uwansa (Alƙur’ani, 5:31).
Manufar wannan maƙala ita ce ta waiwaya fagen tarihi domin bin diddigin
silalen harsashen ginuwar rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa da bunƙasarsa. Yin haka zai
bayar da damar rairaye tsakuwa daga cikin aya, hasali ma Hausawa na cewa,
waiwaye adon tafiya. Sai dai za a ƙoƙarta kawo ma’anonin
tubalan ginin wannan maƙala, waɗanda suka haɗa da: Ginuwa, Bunƙasa, Wasa da kuma
Kwaikwayo.
1.0 Gabatarwa:
Wasan Kwaikwayo ya shafi dukkan
harkokin rayuwar al’umma ta yau da kullum, domin yana bayyana wa ɗan kallo ko mai sauraro
ko karatu hanyoyin rayuwar al’umma ta fuskar sana’o’insu da yanayin
zamantakewarsu da al’adunsu.
Ta fuskar ma’ana kuwa, muna da
kalmomi guda huɗu, wato ginuwa,
bunƙasa, wasa da kwaikwayo, waɗanda suka kasance
tubalan ginin sunan wannan maƙala wadda kowace na da ma’ana kamar
yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya:
1.1 Ginuwa: An samo Kalmar ne
daga Kalmar aiki wato ginaa, wadda ke iya ɗaukar ɗafa-ƙeya ƙwayar sautuka kamar “e,
o, u,” . Kalmar na ƙunshe da ma’anar: ƙaga wani abu, kamar
yadda Ƙamusun Hausa (BUK, 2006:165) ya nuna.
1.2 Bunƙasa: Kalma ce daga cikin
kalmomin da ke nuna wanzuwar aiki, wato aikatau. Kalmar na ɗauke da ma’anar
gawurta ko ƙasaita. A wata ma’anar tana nufin girmama. Haka tana ɗaukar ma’anar:
arzurta, a wani Karin harshen akan kira ta da burunƙasa, (BUK, 2006:53).
1.3 Wasa : kalma ce ta suna
da ke cikin jerin kalmomin Hausa jinsin
maza, jam’i kuwa wasanni. Ita wannan kalma tana ɗauke da ma’anoni
kamar haka:
(i)
Abu
da akan yi don raha ko nishaɗi, ko don motsa jiki.
(ii)
Wani
taron biki da kaɗe-kaɗe da raye-raye.
(iii)
Abu
wanda yake ba da gaske ba.
1.4 Kwaikwayo : kalma ce ta suna da
ke cikin jerin kalmomin Hausa jinsin
maza. Kalmar na ɗauke da ma’anar “
Koyon abu da wani ya yi ko yake yi”.
Ta la’akari da waɗannan ma’anonin
tubulan kalmomin da aka gina wannan take (suna) masana adabin Hausa da suka
nazarci wasan kwaikwayo sun bayar da ma’anoni gwargwadon fahimtarsu. Kaɗan daga cikinsu:
Ɗangambo (1984) ya
bayyana ma’anar wasan kwaikwayo da cewa:
“Wasa ne da ake gina
shi kan kwaikwayon wani labari,
Ko wata matsala ta
rayuwa da ake son isarwa ga jama’a.
Akan aiwatar da
labarin, matsalar da sauransu cikin siffar
“Yaƙini” wato zahiri”.
Shi kuma Umar (1987)
ya bayyana ma’anar wasan kwaikwayo da cewa:
“ Wasan kwaikwayo
kamance ne na wasu halaye ko yanayin
Rayuwa da akan shirya
yinsa musamman, akasari cikin raha.
Wannan kamancen na
iya zama na wasu zayyanannun halaye
Sanannu, wato
abubuwan da aka san sun faru a rayuwa ta haƙiƙa,
Misalin yaƙi ko wani abin da ya
gudana a tarihi”.
Yayin da ‘Yar-Aduwa (2007) ya bayyana ma’anar wasan kwaikwayo da cewa:
“Ginshiƙin rayuwar al’umma
ne, saboda ta hanyarsa ce
Mutum yake koyon
yadda zai rayu. Ta hanyar kwaikwayo
ne mutum yake koyon
abubuwan rayuwarsa. Masana ilmin
Halayyar ɗan’Adam sun tabbatar
da cewa hanyar farko ta
Koyon rayuwa ita ce
ta kwaikwayo”.
2.0 Musabbabin samun
Wasan Kwaikwayo A Tsakani Al’umma
Yana da wahala a sami wani mahaluƙin da zai bugi ƙirji ya ce ga ranar
da aka soma wasan kwaikwayo a doron ƙasa. Abin da kawai
aka sani shi ne, wannan rukunin adabi ya daɗe sosai ana aiwatar da shi a doron ƙasa.
Ana kyautata zaton cewa, an fara
samun wasan kwaikwayo ne sakamakon bauta, wato irin bukukuwan da ake yi wa abin
da al’umma ke bautawa. A daidai lokacin bautar ne, shugabannin addinin ke
kwaikwayon ɗabi’un abubuwan da
suke bauta wa, wai ta wannan hanya ce aka fara samun wasan kwaikwayo
(‘Yar-Aduwa, 2007:4).
A wani ƙaulin an nuna cewa,
akwai waƙoƙi da kirare-kirare da akan yi a lokacin binne jarumai, waɗanda ke bayanin irin
halayensu na jaruntaka. Yayin da lokaci ya yi tsawo sai aka dinga samun wani ko
wasu mutane masu zuwa suna kwaikwayon irin yadda jaruman suke aiwatar da
jaruntakarsu ko a wurin farauta ko a wurin yaƙi. An bayyana cewa,
ta irin wannan kwaikwayo ne da suke yi, sannu a hankali har lamarin ya wanzar
da yin wasan kwaikwayo, kamar yadda ‘Yar-Aduwa (2007:4) ya nuna.
Wani ra’ayin ya nuna cewa, wasan
kwaikwayo ya samu ne sanadin bayar da labarin da ake wa mutane, misali a
dandamali ko kuma idan an je farauta, to a wannan lokacin akan ba mutane
labarin jarumai na wurin yaƙi ko farauta. An nuna cewa ta irin waɗannan labarai ne da
ake bayar da su da baki, a hankali har aka shiga kwaikwayon jarumai. Sannu a
hankali wannan sai ya haifar da wasan kwaikwayo.
3.0 Samuwar Wasan Kwaikwayo
Ana kyautata zaton cewa an fara
wasan kwaikwayo ne a ƙasar Girka, a wajen shekaru 6000 kafin haihuwar Annabi
Isa (A.S.), Girkawa sun fara yin bikin waƙoƙi da raye-raye domin
girmama abin bautarsu da suke kira da suna Dionysus. Suna bikin ne a lokaci
na musamman saboda girmamawa da kuma neman alfarma wajen ubangijin nasu.
Shugaban wannan wasa shi ne Thepis hasali ma shi ya ci gasar, wannan ne
ya ba shi dammar zama ɗan wasan farko a
duniya baki ɗaya.
Haka kuma an samu wasu Girkawa masu
shirya wasannin kwaikwayo kamar su: Acechylus da Sophocles da Euripides
dukkansu sukan shirya was an kwaikwayo musamman na juyayi ( tausayi ).
Saboda
tasirin samuwar waɗannan wasanni daga
bauta ko addini, marubucin wasan kwaikwayo da ya fi shahara a fagen tarihin
wasan kwaikwayo na Girkawa shi ne Aristophanes, wanda aka bayyana yakan shirya
wasanninsa ne domin muzanta manyan shugabannin Girkawa.
A
ƙasar
Ingila kuwa wasan kwaikwayo ya samu shiga sosai a zamanin mulkin Sarauniya
Elizabeth ta farko. Yawancin wasannin na addini ne, saboda goyon bayan da aka
samu a wannan lokaci ne ma ake ganin ba a taɓa samun haɓakar wasan kwaikwayo irin na wannan lokacin
ba, saboda haka ake kiran wannan lokaci da sunan “The Golden Age of Queen
Elizabeth” a tarihin wasan kwaikwayo. An samu marubuta wasan kwaikwayo da
dama kamar su John Lyly da Christopher
Marlowa. A wancan lokaci ne aka samu shahararren marubucin wasan kwaikwayon nan
William Shakespare. Daga baya aka samu marubuta kamar su John Webster da John
Hetcher da Ben Johnson. da Author Jones da Sir Authur Pinero da George Bernard
Shew da sauransu.
A
ƙasar
Hausa kuwa, babu wani takamaiman lokacin da za a ce cikinsa ne aka soma wasan
kwaikwayo. Sai dai akwai tabbacin cewa wannan nau’i na adabi daɗaɗɗen abu ne. Kusan kowace nahiya ta ƙasar Hausa tana da
shi. Ana ganin za a iya raba waɗannan wasannin zuwa
gida biyu. Akwai wasannin da ake yi domin girmama allolin da waɗannan ƙabilu ke yi, wato
kamar bautar da Kanawa ke yi wa Tsunburbura a ƙarƙashin jagorancin
Barbushi, ya ce waɗannan na addini ne.
Akwai kuma na dodo da irin waɗanda ake shirya wa ƙungiya-ƙungiya a kowace
shekara (Clark, 1966).
4.0 Samuwar Wasan Kwaikwayo A Adabin
Hausa
Wasan
kwaikwayo yana ɗaya daga cikin
nau’o’in adabin Hausa da ke ɗauke da hanyoyin nishaɗantarwa tare da sanya annashawa da raha a
cikin zukatan ‘yan kallo ko masu saurare. Idan aka bi diddigin tarihi za a
tarar cewa, adadin shekarun samuwar kowace al’umma a doron ƙasa, shi ne
kwatankwacin shekarun samuwar adabin wannan al’ummar ke nan. Don haka za a ga
cewa, al’ummar Hausawa ma suna da nau’o’in wasannin kwaikwayo tun kafin su fara
cuɗanya da wata baƙuwar al’umma, kamar
Larabawa da Turawa. Da farko za a iya fahimtar cewa, wasu wasannin gargajiya na
Hausawa, kamar wasan kalankuwa da takkai da ‘yan kamanci duk wasanni ne na
kwaikwayo da Hausawa kan aiwatar a wasu lokutta na musamman. Wasu masana na da
ra’ayin cewa, wasannin kwaikwayon Hausa da ake gabatarwa a gidajen rediyo da na
talibijin suna da nasaba da tsarin wasannin kwaikwayon Hausawa na gargajiya;
domin ba rubuta wasannin ake yi kowane ɗan wasa ya hardace lafuzzan da zai faɗa ba. Wannan wasa ya
yi kama da wasan kalankuwa (Ahmad, 1985:7).
Wani
abin sha’awa game da wasan kwaikwayo a adabin baka na Hausa shi ne, yakan ɓullo kusan a kowane
rukuni na adabin Hausa, akan same shi a tatsuniyoyi yayin da mai sauraro zai ji
ana zayyana masa hoton gizo da ƙoƙi da kura da zomo da
sauran irinsu a matsayin ‘yan wasa. Kowane na yin waɗansu ayyukka da
maganganu kamar yadda yakan auku a wani yanayin rayuwa ta haƙiƙa (Umar,1980:1).
5.0 Ire-Iren Wasannin Kwaikwayo A Adabin
Gargajiya Na Hausa
Akwai
wasannin kwaikwayon gargajiya iri-iri da Hausawa suka gada tun kaka da
kakanni kafin bayyanar addinin musulunci
a farfajiyar ƙasar Hausa. Waɗannan wasannin kuwa sun haɗa da:
(i)
Wasannin
kowa da Kowa
(ii)
Wasannin
Matasa.
(iii)
Wasannin
Yara
(iv)
Wasannin
Masu Sana’a
(v)
Wasannin
Lalura
5.1 Wasannin Kowa da kowa
Su
ne wasannin da jama’a na kowane ɓangaren gari na iya yi; wato ba lallai sai ɗan gadon gida ba.
kuma ba sai an yi koyo na musamman ba kafin a riƙa yin wasan. A ƙarƙashin wannan rukuni
akwai wasanni kamar: (a) Giwa Sha
Laka (b) Bukin Buɗin Daji (c) Bukin
Cikar Shekara
5.2 Wasannin Matasa
Wasanni ne na
‘yan-mata da samari, wato mutanen da suke ba ƙananan yara ba ne,
kuma su ba su kai mizilin matan aure ko magidanta ba. Muhimmai daga cikin waɗannan wasanni na
matasa sun haɗa da:
(a)
Wasan Kalankuwa ( magi ko assabano), wannan wasa nau’i – nau’i ne. Akwai wanda
samari ke aiwatarwa da kaka. A kwai kuma wanda samari da ‘yanmata kan kai
ziyara a ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su domin
gudanar da wasan, kamar yadda ‘Yar-Aduwa (2007:9) ya zo da shi. Duk waɗannan wasanni ana
aiwatar da su ne tun kafin bayyanar musulumci a ƙasar Hausa.
(b)
Wowwo (c) Takkai (d) Langa
(e) Nahole
5.3 Wasannin Yara
Wasannin yara sun
kasu kashi biyu, akwai wasannin da ‘yan yara mata ke aiwatarwa na bikin
‘yar-tsana a cikin gida. Haka su ma ‘yan yara maza suna wasan Danda Dokin Kara,
a dandali ko wani fili mai yalwa a ƙofar gida.
5.4 Wasannin Masu Sana’a
Wasanni ne da wasu
mutane da ke gudanar da wasu ayyuka ke yi don samun abinci. Irin waɗannan sana’o’i sun ƙunshi: (a) Bori
(b) ‘Yankama (c) ‘Yanhoto
(Nabiso) (d) Wawan- Sarki (e)
‘Yangambara.
5.5 Wasannin Lalura
Wasanni
ne da ake aiwatarwa a sakamakon wanzuwar wani abu na musamman da ya shafi
rayuwar al’umma ta yau da kullum. Wasannin da ke cikin wannan rukuni sun haɗa da:- (a) Roƙon Ruwa
(b)
Husufi wato zazzaɓin wata ko rana
6.0 Wasan Kwaikwayon Hausa Bayan Zuwan Musulunci
Bayan
da addinin musulunci ya bayyana a farfajiyar ƙasar Hausa, Hausawa
suka karɓi musulunci hannu
bibbiyu, har ya kasance ya yi tasiri a tarsashin rayuwarsu ta yau da kullum.
Irin wannan tasirin shi ya haifar da samuwar wasan kwaikwayo a ƙasar Hausa, wanda ake
yi wa suna da “Wasan Tashe”. Ana gudanar da shi ne a cikin watan azumi, inda
yara samari da ‘yan mata kan shirya wasanni iri-iri da dare bayan shan ruwa,
suna zuwa gida-gida suna yi, manya na kallo ana raha. A irin waɗannan wasannin ana siffanta
waɗansu halaye na jin
tausayi da yin hannunka mai sanda da nuna muhimmancin addinin musulunci. Su ma
irin waɗannan wasannin za a
iya kasa su rukuni-rukuni kamar haka:-
(i)
Wasannin
manya: Wasannin da manya maza ke aiwatarwa sun haɗa da:
Jatau
Mai Magani, Macukule, da sauran su.
(ii)
Wasannin
mata yara: Wasannin da yara mata ke gudanarwa sun haɗa da:
Mairama
Da Daudu, A Sha Ruwa, Mai Ciki, Ragadada, Samodara, da sauran su.
(iii)
Wasannin
yara maza: Wasannin da yara maza ke aiwatarwa sun haɗa da:
Tsoho
Da Gemu, Tashi Wali, Ka Yi Rawa, da sauran su.
(iv)
Bayan
an buɗe makarantar horar da
Alƙalai
a Kano, ƙarkashin jagoranci Sarkin Kano Abdullahi Bayero a
shekarar 1928, wadda aka danƙa wa Malam Sule shugabancinta. A
makarantar ana koyar da littatafai kamar: Risala da Sanusi da Burhama da
Tuhfatul-Hukkami da Li’irabi da Lamiyya da Muɗala’a da Tafsiri da Hadisi da Tarihin
Annabi S.A.W., a bisa tsarin karantarwar gargajiya. Kowane ɗalibi ya zo gaban
malami a biya masa karatunsa, yayin da wani ɗalibi na jan baƙI ana fassara masa.
Bayan da malamin ya tabbatar da cewa, kowane ɗalibi ya haddace Tuhfatul-Hukkami, sai
ya tsara wa ɗalibansa wasan
kwaikwayo domin nuna musu yadda ake bin bahasin shara’a tare da zartar da
hukunci. A wasan an samar da Alƙali da Muhti da masu ƙara domin a yi musu
shari’a tare da yanke hukunci game da wata Magana kamar bashi, ko rabon gado ko
ciniki da dai sauransu, kamar yadda Sufi, (1993:148 – 150) ya nuna. Ta yiyu
daga nan ne Mista Rankin ya gano muhimmancin wannan dabarar koyarwa har yake
bayar da shawarar a samar da rubutatcen wasan kwaikwayon Hausa. Saboda a wancan
lokacin Turawan mulki na kai ziyarar ganin ma ido a kamarantu da sauran sassan
hukumomin En-E.
(v)
Wasan
Gauta: shi wannan nau’i biyu ne, irin wanda ƙwaraƙwaran sarki ke yi a
fada suna kwaikwayon hakimai tare da sanya kayan adonsu na sarauta, an fara
aiwatar da shi ne a fadar Kano a lokacin da ake yaƙin duniya na biyu, Yaƙin Hitila. Bayan da
aka yi sau ɗaya, sai aka dakata
ba a sake yi ba sai da aka gama yaƙin, sannan aka cigaba
da shi. Shi ma ba kowace shekara ce ake aiwatar da shi ba, ana yi ne jefi-jefi,
kamar yadda Sufi (1993:204) ya nuna. Idan kuwa haka ne, kuma ba daga wata
masarauta aka aro ba, za a iya saka shi cikin wannan rukuni. Hasali ma yaƙin an gudanar da shi
a zamanin mulkin Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero ne, wanda ya yi sarautar
Kano daga shekarar 1926 zuwa 1953.
Duk waɗannan wasannin suna ƙunshe da kwaikwayo da
sauya sifar (kamar) masu wasa domin isar da saƙo cikin raha ga ‘yan
kallo.
7.0 Rubutaccen Wasan Kwaikwayo A farfajiyar Ƙasar Hausa Kafin
Zuwan Musulunci
To amma, shi rubutaccen wasan
kwaikwayon Hausa, wanda aka shirya a rubuce don a karanta a fahimta ko kuma a
aiwatar da shi a aikace, ba wani abu da zai tabbatar da samuwarsa ga al’ummar
Hausa kafin bayyanar addinin musulunci.
Wannan ya faru ne a sakamakon rashin ingantacciyar hanyar rubutu a
daidai wanncan lokacin (Bunza,2oo2:11-16). Idan ma akwai wani rubutu na Hausa
da ya danganci ƙagaggun labarai da wasan kwaikwayo, to, ba mu riske shi
ba. Wannan hujja ta rashin samun
ingantacciyar hanyar rubutu na iya zama sanadin rashin rubutaccen wasan
kwaikwayo a ƙasar Hausa. Hasali ma ba
wani bincike da ya yi tsokaci da samuwar rubutaccen wasan kwaikwayo
kafin bayyanar musulunci a ƙasar Hausa.
8.0 Rubutaccen Wasan Kwaikwayo A Ƙasar Hausa Kafin
Tabbatuwar Mulkin Mallaka
Masana da dama sun tafi a kan cewa,
samuwar hanyar rubutun ajami a farfajiyar ƙasar Hausa bai sa aka
samu rubutaccen wasan kwaikwayo a ƙasar Hausa ba, sai
bayan zuwan Turawan Mulkin Mallaka. Masu wannan ra’ayi, sun nuna cewa, ba ma
wasan kwaikwayo kawai ba, har ma duk
wani abu da aka ƙaga wanda ba gaskiya ba ne, bai sami gurbin zama ba,
ballantana har a gina shi a cikin sigar rubutun ajami. Tun da ajamin ɗa ne na tsatson
harshen addinin musulunci, don haka duk wani aiki in ba na addini ba ne, to ba
zai samu karɓuwa ba. Wannan shi ya
haifar da rashin wanzuwar rubutaccen wasan kwaikwayo, kamar yadda Yahaya
(1978:250 ) da ‘Yar-Aduwa (2007:14) suka
nuna. Ta yiwo a daidai lokacin da masanan suka gudanar da bincikensu ba su ci
karo da ayyukan da wasu Turawa suka tattara ba, waɗanda suka samo daga
hannun masu su na asali a cikin sigar rubutun ajami. Irin waɗannan ayyuka sun ƙunshi tatsuniyoyi,
kamar aikin Rattray (1913) da ayyukan da suka ƙunshi ƙagaggun labaran Hausa
da wasan kwaikwayo da waƙoƙin baka na makaɗan Hausa da dai makamantan su, kamar irin
bayanan da kundayen Dokta Rudolf Prietze, waɗanda aka buga a lokuta daban-daban na
shekarun, 1916 da 1917 da 1924 da kuma 1927 suka tabbatar.
Akwai tabbacin wanzuwar rubutaccen
wasan kwaikwayon Hausa tun a wajen shekarar 1902, wanda wani Bahaushe mai suna
Ahmadu Kano da ke zaune a Tunisiya ya rubuta a cikin sigar rubutun ajamin
Hausa. A can Tunusiya ɗin ne ya ba Dokta
Rudolf Prietze wasan kwaikwayon a rubuce. Shi kuma Prietze ya sake juya shi
cikin sigar rubutun Hausar boko, ya yi nazarinsa, ya fassara cikin harshen
Jamusanci, kana ya buga sakamakon binciken nasa a wata mujallar ƙasar Jamus. Wannan
aikin an yi masa suna da: “ Die Medchen Von Gaia”. An buga shi a shekarar 1926,
kamar yadda (Ahmed, 2001:iv-v ) ya bayyana. Wannan bayanin ya kawar da bayanan
da ke nuni da cewa, Hausawa ba su da rubutaccen wasan kwaikwayo, sai bayan
samuwar makarantun boko a ƙasar Hausa da kuma ra’ayin da ke nuni
da cewa, an fara samun rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa a shekarar 1930.
Kamar yadda bincike ya nuna, wasan
kwaikwayo mai suna ‘Yan Matan Gaya
(Labarin 1900) na Ahmadu Kano, wanda shi Amadu Kano ɗin ne ya ƙago labarin da kansa, kana ya cusa lamarin wasan magi
(Ahmad,2001:V). Wato an tsara shi ne a cikin sigar ƙagaggen labari, daga
bisani ne Prietze ya mayar da shi cikin sigar wasan kwaikwayo. Shi ma wasan
kwaikwayo mai suna Turbar Ƙudus (labarin 1898) Prietze ya same shi ne daga Ahmadu Kano,
shi kuma sai ya ba shi suna Der Besuch des deutschen Kaisers 1898 in Jerusalem,
ma’ana Ziyarar Sarkin Jamus zuwa Ƙudus a 1898. Wannan
wasan ya ƙunshi ziyarar da sarkin Jamus William II ya kai a Ƙudus, wanda ya yi hulɗa da Sarkin Istambul
Abdulhamid II. Sai dai Ahmadu Kano ya aiwatar da wasu sauye-sauye a cikin
labarin na asali, domin wasan ya yi armashi, kamar yadda (Ahmed, 2004:V-VI ) ya
bayyana. Prietze ya sami wasan ne daga
hannun Ahmadu Kano a cikin shekarar 1910, bayan shi Amadun ya dawo daga aikin
haji, inda ya yada zango a Ƙudus, har ya shekara huɗu. Dokta Prietze ya
buga wannan wasa a cikin shekarar 1927. Shi kuwa littafin wasan kwaikwayo mai
suna Tarihin Rabeh, wanda ke ɗauke da bayanin yadda
Rabeh ya mamaye wasu manyan garuruwan da ke Tabkin Chadi da wasu garuruwan ƙasar Barno, a wajen ƙarni na goma sha tara
(19). An kuma bayyana irin yadda Rabeh ya aiwatar da kisan gilla ga al’ummar
tare da kamun bayi. Prietze ya buga wasan a shekarar 1924 tare da wasan Turbar Tarabulus.
Daga waɗannan bayanai za a
iya fahimtar cewa, tun kafin kafuwar mulkin mallaka a ƙasar Hausa, an sami
wasu daga cikin Hausawa da suka yi ƙoƙarin rubuta littattafan da suka danganci ƙagaggen labari da na
wasannin kwaikwayo a cikin sigar rubutun ajamin Hausa. Don haka abin da kawai
za a ce ba a yi ba ƙasar Hausa, shi ne a ɗauke shi a matsayin darasi da za a rinƙa koyarwa a
makarantu, kamar yadda aka tsara a makarantun boko.
9.0 Shekarar Ginuwar
Rubutaccen Wasan Kwaikwayo A Zamanin Mulkin Mallaka
Littafin Wasannin Hausa Shida ( Six
Hausa Plays). Shi ne littafi na farko da aka rubuta bayan kafuwar mulkin
mallaka a Nijeriya Ta Arewa. Sai dai daga binciken da aka aiwatar dangane da
takamaiman lokacin da aka wallafa littafin, an sami saɓani a tsakanin masana. Wannan ya auku ne a sakamakon rashin
sanya shekarar da aka buga littafin a jikin liittafin. Hakan ya haifar da mafi
yawan masana suka ɗauki shekarar 1930 a
matsayin shekarar wallafar, kamar yadda Yahaya (1978: 251) da Malumfashi
(1990:1) suka nuna. Sai dai yanzu akwai ƙwaƙƙwarar hujjar da ta
tabbatar da shekarar 1936 a matsayin shekarar wallafar littafin. Da farko Dr.
R.M. East a cikin littafin da ya rubuta da ke ɗauke da jerin sunayen littattafan da
aka wallafa a cikin harsunan Nijeriya, mai suna (take): A Vernacular
Bibliography For The Languages Of Nigeria
wanda aka buga a 1941, ya nuna 1936 a matsayin shekarar da aka wallafa
littafin. Yayin da Baldin (1977:92 ) shi ma ya nuna 1936 a matsayin shekarar da
aka wallafa littafin. An buga wannan littafi ne a kamfanin ɗab’i mai suna WEST AFRICAN
PUBLICITY LTD, LAGOS. Don haka wannan na iya zama wata tabbatacciyar hujjar
zaman shekarar 1936 a matsayin shekarar wallafar SIX HAUSA PLAYS ba 1930 ba. Ta
yiwu masu ra’ayin shekarar 1930, sun fara lissafin ne tun daga shekarar da
Mista Rankin ya ba East shawarar rubuta wasan kwaikwayon ne, domin ya kasance
misali ga ‘yan ƙasa masu sha’awar rubuta wasannin kwaikwayon Hausa
(Ahmed, 2009:82).
10.0 Mawallafin
Wasannin Hausa Shida East ko Imam?
Irin wannan ja-in-ja ba ta tsaya a
kan shekarar wallafa ba, har ma ta shafi neman sanin sahihanin marubucin
littafin. Wasu sun ɗauki R.M. East a
matsayin wanda ya rubuta littafin. Yayin da ɗaya ɓangaren suka tsaya a kan cewa, Abubakar Imam
ne marubucin littafin. Ƙila masu ra’ayin farko sun dogara ne a kan hujjar ganin
sunan R.M.East a bangon littafin a matsayin mawallafi, ba kamar yadda aka saba
gani ba a wasu littattafai irin su Ruwan
Bagaja da Ganɗoki da Magana
Jari Ce da sauran su. Ko kuma sun ɗauki umurnin da shi R.M.East ya ba Abubakar
Imam da masinjan nan mai suna Basankare, na su samar da guntayen labarai da
tatsuniyoyi na ƙasar Hausa, don a mayar da su cikin sigar wasannin
kwaikwayo, a matsayin hujjar danganta littafin da R.M.East. Ko kuma an yi haka
ne a sane, ba don komai ba, sai dan a ƙara wa littafin kwarjini
a idon jama’a, kamar yadda aka yi wa wani littafi mai suna Hali Zanen Dutse, wanda Imam ɗin ne ya rubuta shi, amma sai aka saka sunan
Sarkin Musulmi Abubakar III, don kasancewarsa na tarbiyya. Sai dai akwai
hujjoji ƙwarara da ke iya tabbatar da cewa ba R.M. East ne ya
wallafa wannan littafi ba, Abubakar Imam da Masinjan Makarantar Midil ta
Katsina mai suna Basankare ne suka rubuta littafin, kamar yadda za a gani nan
gaba.
Ita ma muƙaddamar da R.M.East
ya rubuta ana iya ɗaukar ta a matsayin
wata hujjar da za ta nuna ba shi ne mawallafin littafin ba. Idan aka duba
bangon littafin Magana Jari Ce, sabon
yayi za a ga inda aka nuna cewa, Abubakar Imam ne marubucin littafin SIX HAUSA
PLAYS .
Shi ma Abubakar Imam ɗin a wata hira da ya
yi tare da Pweddon, ya fito fili ƙarara ya bayyana cewa
da shi da masinjan Middle School ta Katsina mai suna Basankare ne suka samar da
littafin, ga abin da yake cewa:
“Shi
wannan littafi zan iya cewa ni na rubuta shi tare
da
Wani Masinja na Middle School, wanda ake kira
Basankare; shi ne ya rubuta labarun, ni kuma na mayar
da su cikin sigar wasanni kamar yadda suke a halin
yanzu. Wani ƙarin bayani kuma shi
ne,shi Dr. East
babban aikinsa shi ne ya zama edita mai tace duk abin da
muka rubuta, ya kuma duba kowane littafi ga baki ɗayansa
ya ga dacewarsa da yanayin harkokin duniya da
kuma rukunin jama’ar da aka rubuta shi domin su”
(Pwedden, 1995:89-90).
Wannan bayanin ya
rosa ra’ayin Ahmad (Mrs) (2009:82) da ke cewa, Dakta East ya roƙi Abubakar Imam da
masinjansa mai suna Basankare su samar masa da guntayen labaru da tatsuniyoyi
na ƙasar Hausa waɗanda zai mayar cikin sigar wasan kwaikwayo a rubuce. Ta yiwu a daidai
lokacin da ta gudanar da bincikenta Allah bai ƙaddara hannunta ya faɗan kan wannan bayani
ba. Ƙila ma ta dogara ne a kan abin da ya bayyana zahiri a
bangon littafin da kuma ficen da ya yi a fagen gina rubutaccen adabin Hausa da
rayar da shi.
Daga waɗannan bayanai za a
fahimci cewa, littafin na haɗin gwiwa ne, ba R.M. East ne kaɗai ke da haƙƙin mallakarsa ba. Don
haka, muhimmiyar gudummawar da za a ce an samu wajen gina wasannin ta fito daga
W.S. De G. Rankin wanda ya bayar da
hanyoyin da za a gudanar da wasan, da shi kansa R.M. East da ya tsaya ya tace
wasan da aka rubuta da Basankare wanda ya rubuta labaran da Abubakar Imam wanda
ya mayar da su cikin sigar wasan kwaikwayo.
11.0 Tsarin Gudanar
Da Harkar Wasan Kwaikwyon Hausa
Kamar yadda
rubutacciyar waƙa da rubutun zube suke da tsari haka shi ma rubutaccen
wasan kwaikwayon Hausa yake da nasa tsari da ya keɓanta da shi, tare da ƙara fito da kusancin
kamancen zuwa ga haƙiƙa. Sai dai har zuwa wannan zamanin babu cikakken
tabbataccen bayanin wanda ya aza harsashin tsarin gudanar da harkar wasan
kwaikwayon. Abin da kawai za a iya yin hasashe game da tsarin gudanar da wasan
kwaikwayo shi ne, Turawa sun gina shi ne ta la’akari da wasan kwaikwayon
gargajiyar ƙasar Hausa kamar wasannin tashe, sai suka nazarce shi
suka zayyan ƙumshiyar ayyukan a kan takarda tare da sanya sigar
yanayin ƙasarsu.
Binciken Ahmad (Mrs.) (2009:82) ya
nuna R.M. East ne ya tsara yadda za a gudanar da wasan a aikace. Yayin da Mista
Rankin ya karanta wasan tare da yin wasu gyare-gyare kafin a buga littafin. Ƙila a yayin da ta
aiwatar da nata binciken ba ta samu yin tozali da ainahin littafin Six Hausa
Plays ba, ballantana ta karanta gabatarwarsa wadda a cikinta ne Mista
Rankin ya shata ƙa’idojin gudanar da wasan kwaikwayo a dandamali. Ko kuma
Allah bai nufi hannunta da dafa Baldi (1977:92) wanda ya nuna cewa W.S. de G.
Ranki ne ya zayyana yadda za a gudanar da harkar wasan kwaikwayo dalla-dalla,
ba tare da wata matsala ba. Ya kawo sharuɗɗan ne a cikin gabatarwarsa ta Turanci wadda
aka buga fassararta da Hausa. Da wannan ne za mu fahimci cewa, abubuwan da muka
sani da suna: Sigogin Wasan Kwaikwayo da Ginshiƙan Wasan Kwaikwayo a
wannan zamani Rankin ne ya zayyana su ba East ba.
12.0 Manufar Samar Da
Littafin Wasan Hausa Shida (Six Hausa Plays)
Shi littafin Six Hausa Plays, an samar da shi ne domin a nuna wa Hausawa yadda
za su sarrafa adabinsu na baka su mayar da shi wasannin kwaikwayo domin inganta
adabin da kuma samar da yanayin koyarwa ga ɗalibai cikin armashi da annashawa, da ma masu
sha’awa daga cikin al’ummar Hausawa. Wannan yana ɗauke da ƙudurin bayar da dama
ga Hausawa ‘yan boko don su ƙirƙiro wasannin
kwaikwayo nasu na kansu a cikin harshen harshen Hausa, kamar yadda East ya yi
tsokaci a cikin muƙaddamarsa ga littafin.
12.0 Ƙumshiyar Littafin
Wasan Hausa Shida
Littafin yana ɗauke da wasanni shida
ne, wasa na farko an yi masa suna(take) da:
12.1 Gonar Zomo, inda aka yi amfani da
dabbobi kamar zomo da matarsa da ‘ya’yansa da giwa da raƙumi da iyalansu.
12.2 Gawa Huɗu. A wannan wasa an
nuna irin yadda haɗarin zama wuri ɗaya ya kasance a tsakanin kura da zaki da damisa da
maciji, kamar yadda dila ya haɗa su a cikin wasan.
12.3 Baki Shi Kan
Yanka Wuya,
wanda ya ƙunshi wasu abokai guda biyu, Ali da Tanko. A cikin wasan
an nuna cewa, Tanko ya tsinto gawar Shamakin Sarki, ya ɗauko ya kai ɗakin Ali, domin ramuwar
gayya. Ya yi haka ne a sakamakon cin
amanar da Ali ya yi masa na neman yarinyarsa. A ƙarshe kuma Tanko ya yi iƙirarin cewa shi ne ya
kashe Shamakin, saboda jin wai Sarki ya
ce zai bayar da ladar kuɗu ga duk wanda ya
kashe Shamakin, a sakamakon wani laifi da ya yi masa.
12.4 Larabgana, wadda ke ɗauke da wata al’ada
da ke nuni da cewa, kowace Larabar ƙarshen wata tana
tattare da cuwurwuta. Ita cutar takan sauka da dare ne, kuma duk wanda ya kamu
da ɗayansu ba zai warke
ba har abada. Kuma cutar kan sauka a kan duk wani abin amfani da aka bari a
waje buɗe. Wannan ne ya sa mutane ba sukan fito a daren Larabar
ba, kuma suke rufe abubuwan amfaninsu.
12.5 Makas Sarki. Shi wannan wasa
yana ɗauke ne da bayanin
zuwan Bayajida ƙasar Hausa ne.
12.6 Yanka Masabki Baƙon Sanau. A wannan wasa an
zayyana yadda Korau ya hau karagar sarautar Katsina ne.
13.0 Yunƙurin ‘Yan ƙasa Wajen Samar da
Littattafan Wasan Kwaikwayo
Masana da dama sun nuna cewa, tun
bayan samuwar littafin Six Hausa Plays ba a sake samun wani rubutaccen littafin
wasan kwaikwayon Hausa, sai bayan kafuwar Hukumar NORLA. Wannan ya saɓa wa ra’ayin nan da
ke nuna cewa, yunƙurin farko da ‘yan ƙasa suka fara nunawa
a fannin rubuta wasannin kwaikwayon Hausa ya fito ne daga Malam Aminu Kano,
wanda ya fara rubuta wasannin kwaikwayo tun daga shekarar 1938 zuwa 1939.
Wasannin kwaikwayo na farko da ya rubuta, sun haɗa da : “ Kai Wane Ne A Ƙasar Kano Da Ba Za A
Cuce Ka Ba”, da wani littafi da ya yi wa laƙabi da suna “ Ƙarya Fure Take Ba Ta
‘Ya’ya”. Wannan ra’ayin ya ci gaba da
cewa, tun daga shekarar 1938 zuwa 1941, malamin ya sami damar rubuta wasannin
kwaikwayo kimanin 20 kamar yadda (Xiaomeng, 2004:70) ta bayyana. Sai dai ana
kyautata zaton cewa wasannin da ya rubuta, ba su yi fice ba, domin sun kasance ɗauke da jigogin da
suke sukar halayya da ɗabi’un sarakuna da
shugabannin hukumomin EN-E na wancan zamani, ko kuma tun farko ba rubutattu ba
ne, ko kuma an rubuta sun ɓace ne.
Abin kula a nan, adaidai wancan
lokacin duk wani rubutun da aka yi, wanda ake son a wallafa a rinƙa amfani da shi a
makarantun Arewacin Nijeriya, sai an gabatar da shi ga hukumar ilimi kafin a
amince da aikin. Hasali ma littafin Wasan Marafa sai da hukumar ilimi ta
nazarci littafin kafin a gabatar da wasan a bainar jama’a a farfajiyar
makarantun da ke garuruwa daban-daban tun kafin a yi tunanin buga littafin. A
cikin gabatarwar littafin, Alhaji Abubakar Tunau Mafara ya ce: “Wannan wasa,
mun shirya shi musamman don mu nuna wa jama’a rashin amfanin ƙazanta. Mun yi wannan
wasan a Midil ta Sakkwato sau da yawa. Kuma mun je Talata Mafara da Gusau da Ƙauran Namoda duk mun
yi shi, a cikin shekarar 1943….. (Gabatarwa). Ta yiwu ganin wannan gabatarwar
ce ya sa Ɗangambo (1984:12) ya nuna 1943 a matsayin shekarar da aka
fara samun wasan kwaikwayo, sai dai bai nuna ƙarfafawa ba a cikin
bayanin nasa. Don haka ana iya cewa, kamar yadda jigon littafin farko na ƙagaggen labari mai
suna: Fatima ya hana shi fice a tsakanin al’umma, haka su ma
rubuce-rubucen da Malam Aminu Kano ya aiwatar a kan wasan kwaikwayo, jigonsu ya
hana su samun karɓuwa daga ‘yan mulkin
mallaka. Saboda jigogin nasu ba su dace da yanayin kyakkyawar zamantakewar da
ke tsakanin Turawan Mulkin Mallaka da masu masaukinsu a daidai wancan lokaci
ba. Hasali ma ko littafin Fatima: Hausa Novel wanda Miller ya rubuta, ƙungiyar ‘yanmishan ne
suka ɗauki nauyin buga
littafin wanda shagonsu da Ke Legas mai suna: Missionary Society Bookshop, West
Africa ya buga a shekarar 1933 tun kafin a buga littattafan gasar farko a shekarar
1934 (Bakura,2012).
14.0 Haɓakar Rubutaccen Wasan
Kwaikwayo A Zamanin Mulkin Mallaka
Turawan Mulkin Mallaka sun bayar da gudummuwa
wajen haɓaka rubutattun
wasannin kwaikwayo na Hausa, ta hanyar samar da hukumar NORLA. Ita wannan
hukuma ta NORLA ta yi rawar gani, domin ta ƙara wa ɗalibai da ‘yan ƙasa masu ilimin boko ƙwarin gwiwar shirya
wasannin kwaikwayo da aiwatar da su a makarantu. Hukumar ta buga wasu
littattafan wasan kwaikwayo kamar su Wasan
Marafa na Abubakar Tunau Mafara a shekarar 1949 da littafi mai suna Malam Inkuntum na M. A. Dogondaji wanda
aka buga a shekarar 1955 da kuma littafi mai suna Zamanin Nan Namu na Shu’aibu Maƙarfi wanda aka buga a
shekarar 1959.
Mafi
yawan littattafan da hukumar ta buga sun ƙunshi jigogin ilmantarwa
da faɗakarwa ko wayar da
kan al’umma game da wasu manufofin gwamnati a wancan lokaci. Misali, Wasan
Marafa, an nuna wa al’umma illar rashin tsabta da muhimmancin asibitocin da
Turawa suka gina. Yayin da littafin Zamanin
Nan Namu, ya yi manuniya ga al’umma dangane da muhimmancin ilimi da
tarbiyya ta gari da kuma illar da ke tattare da tallace-tallace. A cikin
littafin Malam Inkuntum, an kawo yanayin dangantakar da ke tsakanin malaman ƙasar Hausa ta ganin ƙyashi da hassada da
son zuciya da neman kunyata ‘yan’uwansu don kawai kwaɗayin tara abin
duniya. An fito da gwarzon wasan mai suna Inkuntum a matsayin ɗan Malam Katakoro.
Sai dai Inkuntum ya kasance ɗan malam ka ƙi halin malam. An
kuma nuna irin karama ta malamai da yadda Inkuntum ya kintsu bayan mutuwar
mahaifinsa.
Don
haka, a taƙaice za a iya cewa kafa hukumar NORLA ya ƙara wa ɗalibai da ‘yan ƙasa masu ilimin boko ƙwarin gwiwar shirya
wasannin kwaikwayo da aiwatar da su a makarantu, wanda sakamakonsa ne hukumar
ta samu damar buga littattafan wasan kwaikwayo da ‘yan ƙasa suka rubuta kamar
haka:-
Sunan Littafi Marubuci Shekarar ɗab’i Maɗaba’a
Wasan Marafa Abubakar
Tunau Mafara 1949 NORLA
Malam Inkuntum M. A. Dogondaji 1955 ,, ,, ,, ,, ,,
Zamanin Nan Namu Shu’aibu Maƙarfi 1959 ,, ,, ,, ,, ,,
15.0 Ƙanfar Littattafan
Wasannin Kwaikwayon Hausa Da Sanadinta
Duk da irin ƙoƙarin da Hukumar NORLA
ta yi wajen samar da rubutattun littattafan wasan kwaikwayon Hausa da na sauran
dangogin adabin Hausa, aka rufe ta a cikin shekarar 1959 sakamakon rashin
isassun kuɗaɗen gudanar da ayyukan
hukumar. Aka danƙa dukkan ilahirin abubuwan da hukumar ta mallaka ga
Kamfanin Gaskiya Ta Fi Kwabo, kamar yadda Ibrahim (1979:40) ya nuna.
Bayan
an rufe hukumar NORLA, Kamfanin Gaskiya bai samu damar sake buga littattafan da
ake da su ba, ballantana ma ya buga wasu
sababbi, idan aka cire littafin Jatau Na Ƙyallu da Shu’aibu Makarfi
ya rubuta, wanda ta wallafa a shekarar 1964 (‘Yar-Aduwa, 2007:12). Ana cikin
wannan yanayi na ƙaracin littafan wasan kwaikwayo har zuwa bayan da sojoji
suka ƙwace mulki daga hannun farar hula a shekarar 1966, kamar
yadda Ibrahim (1979:40) ya zo da bayani.
An fuskanci ƙaranci rubuce-rubucen
littatafan wasan kwaikwayo a sakamakon wasu dalilai da za a gani ɗaya bayan ɗaya kamar haka:
·
Yayin
da aka rosa hukumar NORLA, ba a samar da wata wadda za ta maye gurbinta ba.
Hasali ma ba a ba Kamfanin Gaskiya wadatattun kuɗaɗen tafiyar da harkar littattafai ba.
·
Haka
kuma a daidai lokacin lamurran siyasa sun yi tsanani a Nijeriya ta Arewa, hasali
ma mawallafan littattafan sun kasa cigaba da wallafa komai sakamakon yawan
ayyukan da ke gabansu, wasu sun zama ministoci wasu kuma sakatarori wasu sun
zama wakilai. Uwa-uba kuma lamurran siyasa sun yi zurfi a cikin zukatansu fiye
da komai.
·
Ana
cikin irin wannan yanayi, sai Gwamnatin Jahar Arewa ta wancan zamani ta hana
koyarwa da harshen Hausa a makarantun furamare (Ibrahim, 1979:41). Sakamakon
haka ya haifar da rashin kasuwar littattafan Hausa. Ko da Kamfanin Gaskiya sun
buga ba za su mayar da kuɗinsu ba, balle har su
ci riba. Haka idan mawallafi ya biya aka buga masa littafin babu kasuwar da zai
sayar ya mayar da uwar kuɗinsa har ya yi
tunanin samun riba. Saboda da ma can gwamnati ce ke saya ta rabawa hukumar
ilimi da ke faɗin lardunan jahar
Arewa don amfani da su a makarantun furamare, to, an hana koyarwa da harshen
Hausa, wa zai saya?
Daga waɗannan bayanai za a fahimci su kansu ’yanbokon
farko Hausawa ba su ba harshensu na uwa muhimmanci ba, wanda da shi aka aza
harsashin ginin iliminsu na zamani (boko). Wannan ya nuna ƙarara yadda ‘yan
asalin harshen suka yi wa harshen nasu riƙon sakainar kashi
yayin da mulki ya koma hannunsu.
16.0 Bunƙasar Rubutattun
Littattafan Wasan Kwaikwayon Hausa
Wannan matsalar ta
haifar da damuwa a zukatan wasu mutane da ke kishin harshen Hausa. Saboda haka
a cikin shekarar 1966, sai Gwamnatin Jahar Arewa ta kafa Kamfanin
Shirye-Shiryen Littattafai na Nijeriya Ta Arewa (NNPC) Zariya, wanda ta ɗora wa alhakin sake
buga littattafan Hausa da ake da su tare da samar da sababbi (Ibrahim,
1979:41).
Kafa maɗaba’ar buga littatafai ta Nijeriya ta Arewa
mai suna “ Northern Nigeria Publishing Company” ya taimaka wajen samar da
rubutattun wasan kwaikwayo na Hausa.
Daga shekarar 1971 zuwa 1986
hukumar NNPC ta wallafa littattafan wasan kwaikwayo na Hausa kusan goma
sha huɗu kamar haka:-
Sunan Littafi Marubuci Shekarar wallafa Maɗaba’a
Uwar Gulma A.
M. Sada 1971 NNPC
Tabarbar Kunya Dauda Kano & A. Ɗangoggo 1971 NNPC
Wasannin Yara Umaru Dambo 1971
NNPC
Daren Sha Biyu I. Y. Yahaya (fassara) 1971 NNPC
Bora Da Mowa Umaru
B. Ahmad 1972 NNPC
Malam Mamman Bello
Muhammed 1974 NNPC
Matar Mutum Kabarinsa B.F. Roukbah 1974 NNPC
Shehu Umar Umar
Ladan & Dexter Lyndersy 1975 NNPC, shi wannan littafin “Sheu
Umar” na Sir, Abubakar Tafawa Ɓalewa an fara gabatar da shi a cikin
sigar wasan kwaikwayo a watan Disamban shekarar 1972 ne, a Cibiyar Nazarin
Al’adu, Kwalejin Abdullah Bayero Kano da ke ƙarƙashin kulawar Jami’ar
Ahmadu Bello, a yayin bikin cika shekaru goma da kafa Jami’ar (Baldi,
1977:92)
Kulɓa Na Ɓarna Umaru Ɗanjuma Katsina 1979 NNPC
Zaman Duniya Iyawa Ne A. Yusuf Ladan 1980 NNPC
Matsolon Attajiri D. Idris (fassara) 1981 NNPC
Soyayya Ta Fi Kuɗi H. A. Alƙali 1982 NNPC
Mugunta Guzurin Wuya G.I. Maigari 1984 NNPC
Bar Ni Da Mugu A. Ƙasimu Yero 1986 NNPC
An
sami kuma wasu kamfanoni masu zaman
kansu da suka bayar da gagarumar gudummawa wajen wallafa littattafan wasan
kwaikwayon Hausa. Kamfanonin kuwa sun haɗa da:-
Maɗaba’a Marubuci Shekarar Ɗab’i Sunan Littafi
Ola Printing Press Kano Ibrahim Tajo 1979 Na-Tanko
Oxford University Press T.W.
Harrison 1966 Aikin Mata
Oxford University Press Ahmad Sabir 1978 Mutanen Kogo
U.
D. Katsina 1986 Ai Ga Irinta Nan
Ile Sanmi Press Usman Hassan 1978 Komai Nisan Jifa
Bayan
waɗannan an cigaba da
samun rubutattun wasannin kwaikwayo, sai dai wasun su ba su sami wallafa ba a
sakamakon matsalar tattalin arzikin marubutan. Wasu ma an wallafa su amma ba a
sami ɗuriyarsu ba, balle a
yi tozali da su.
17.0 Kammalawa
A bayanan da suka gabata za a ga
cewa, muƙalar ta yi ƙoƙarin kawo taƙaitaccen tarihin
ginuwa da bunƙasar wasan kwaikwayon Hausa, wanda yake makeken fili ne
mai yalwa. Manufata ita ce zaƙulo harsashen da magabatan ƙasar Hausa suka
assasa a fagen rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa wanda ya kasance ɗaya daga cikin adabin
zamani da magabatan ƙasar Hausa suka samar da shi a cikin sigar rubutun ajamin
Hausa tun kafin kafuwar mulkin mallakar ƙasar Hausa. Haka maƙalar ta zo da bayanan
da suka tabbatar da marubata Wasannin Hausa Shida da iri rawar da East da
Rankin suka taka. Ba a kamala ba sai da aka kawo jerin matsalolin da suka kawo
cikas wajen samar da rubutaccen wasan kwaikwayo da kuma yadda fannin ya bunƙasa. Kafa kamfanin
buga littattafai na Nijeriya ta Arewa mai suna: Northern Nigeria Publishing
Company da Gwamnatin Jahar Arewa ta yi, ya kawo gagarumar gudummawar da ta bunƙasa rubutaccen wasan
kwaikwayon Hausa. A ƙarshe ina kira ga masana da manazarta a wannan fage da mu
yi ƙoƙarin tattara duk
ilahirin sunayen littattafan wasan kwaikwayon da aka rubuta a samar da su a
cure waje ɗaya domin sauƙaƙa wa ɗalibai da manazarta
wannan fanni.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.