Ticker

    Loading......

Gudummawar Zogale Cikin Sha’anin Magunguna a Kasar Hausa

zogale

Gudummawar Zogale Cikin Sha’anin Magunguna a Ƙasar Hausa

Dr. Adamu rabi’u bakura

arbakura62@gmail.com
08064893336

Shimfiɗa

Ma’anonin Tubalan Ginin Take

 Kalma ce Bahaushiya da ke cikin jerin sunayen jinsin mata. Ana faɗar ta da lafazin gudunmawa a Karin harshen Sakkwatanci da na Kananci da kuma zazzaganci, kamar yadda Bargery (1993:402) ya nuna. Shi kuwa Abraham (1975:337) ya nuna cewa, a Karin harshen Sakkwatanci ne ake faɗar ta da lafazin gudunmowa wato akan saka wasalin /o/ a gaɓa ta uku maimakon wasalin /u/da wasu Karin harsuna ke amfani da shi. Har ila yau Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero (2006:171) ya nuna ana furta gaɓa ta uku da wasalin /a/ ko /o/, misali gu-dum-ma-wa. Kalmar gudummawa tana ɗauke da ma’anar taimako na aiki ko kuɗI ko abinci ko sutura ko wani abu. Kuma daidai take da agaji ko ceto daga wahala kamar yadda Garba (1990:4) ya bayyana.

 ZOGALE:-

 Wata itaciya ce da ake shukawa ko dasawa a gida ko gona, wadda ake tsigar ganyenta ana dafawa a kwaɗanta a ci ko a yi dambu ko fate ko a yi miya da shi. Haka kuma akan yi danga da itaciyarta. Tana da furanni farare.Ana kuma yin yaji da saiwarta (Garba, 1990:167).Ita zogale matsakaiciyar itaciya ce, wadda girmanta ya kama daga tsawon mita biyar (5) zuwa mita goma (10). Saboda yawan amfanin da ake da ita ya wanzar da nomanta a duk kusan sassan duniya. Ana samun ta a yammacin duniya da ƙasashen Asiya musamman a yankunan tsaunukan Himalaya da ƙasashen Indiya da Pakistan da Afirika da kuma ƙasashen Larabawa.

 Al’ummomi daban-daban kamar Romawa da Girkawa da Misirawa kan tatso mai daga ‘ya’yan zogale wanda sukan sarrafa shi wajen aiwatar da turare da man shafawa. A cikin ƙarni na goma sha tara (19), gandayen zogale da ke Yammacin Indiya sun fitar da man zogale zuwa ƙasar Turai domin yin turare da giris don amfanin na’urori.

 Al’ummomin ɓangaren ƙasar Indiya sun daɗe suna amfani da kwasfan zogale wajen abinci. Shi kuwa ganyen zogale ya kasance wani muhimmin abu da ake ci a duk farfajiyar ƙasashen Afirika ta Yamma da wasu sassan Asiya.Abin ƙayatarwa ne ƙwarai dangane da jerin nau’o’in magungunan da ake yi da zogale waɗanda ke ƙunshe da muhimman sinadaran gina jikin ɗan-Adam. Sakamakon amfanin da ake yawan yi da ita ne ya sa aka gano tana maganin cuwurwuta da dama. Wannan ne ya haifar da mayar da hankali wajen binciken irin cutar da take magani.

Zogale A Farfajiyar Ƙasar Hausa

 A farfajiyar ƙasar Hausa akan kira ta da sunaye dabam-daban. Wasu yankunan na kiran ta zogalagandi ko zogale ko kuma tamakka. A wani yanki na ƙasar Zamfara kuwa, kamar Bunguɗu da Maru suna yi mata laƙabi da ɗanhaki. Yayin da ake kiran ta dakable a yammacin ƙasar Gummi. A ƙasar Ruwan Ɗoruwa da kewayenta ana kiran ta ‘yarmakka. A yankin ƙasar Nijar kuwa akan kira ta da sunan bagaruwar makka.

 Ana kyautata zaton wannan itaciyar ta zo ƙasar Hausa ne ta hannun mahajjata, kamar yadda sunayen da aka yi mata a ƙasar Hausa da ƙasar Nijar suka yi ishara. A wani hasashen kuwa, zogale ta zo ƙasar Hausa ne daga Misira. Tarihi ya nuna, ƙasar Masar na daga cikin ƙas- ashen da aka fara kai zogale daga Indiya. Misirawa sun daɗe ƙwarai suna amfani da zogale wajen magungunansu na gargajiya, musammam ma mai da ake samu daga ‘ya’yan zogale wanda aka ce Misirawa na shafa shi a fatar jiki don kariya daga illar da iskar Hamada ke yi wa fatar jiki.

 A ra’ayin Hambali Junju, Hausa ta samo asali ne daga Misira. To idan muka ɗauki wannan ra’ayin za a iya cewa, ke nan koda Hausawa suka zo ƙasar Hausa, sun zo ne tare da abarsu. Ai ko banza masara ma daga Misira ta zo ƙasar Hausa. Saboda haka ba abin mamaki ba ne idan aka ce zogale daga can ta zo. Sai dai ba wani mahaluƙi da zai fito fili ya ce ga ƙayyadadden lokacin da ta zo ƙasar Hausa da kuma wanda ya fara shigowa da ita, sanin wannan sai Allah.

 

Asalin Zogale:

 Masana da dama kamar (Nickon & others 2003) da (Ndong, 2007) da (Agrawal da wasu, 2008) da (Busani da wasu, 2012) sun nuna cewa, zogale tun can asalatan itaciyar ƙasar Kudancin Indiya ce, wato ƙasar Sirilanka. In kuwa haka ne, za mu iya cewa, Allah cikin ikonSa da hikimarSa da iradarSa, Ya samar da zogale a can ne domin Annabi Adamu da zuriyarsa na farko su sami abin yin riga-kafi da maganin cututtuka da ita. Musamman idan aka yi la’akari da irin sinadiran ban mamaki da ta’ajibi waɗanda Allah Ya halicce ta da su, da ke da muhimmanci a cikin jikin ɗan-Adam, ta fuskar waraka da garkuwa daga wasu nau’o’in cuwurwuta da kan addabi jiki. Masana tarihi sun nuna an saukar da Annabi Adamu (A.S.) a farfajiyar ƙasa da ke yankin Sirilanka, yayin da Matarsa Hauwa’u aka saukar da ita a Jidda. In kuwa haka lamarin yake, za mu iya cewa, zogale na ɗaya daga cikin itatuwan Aljanna. Musammam idan muka yi la’akari da irin ɗinbin sinadiran da take kunshe da su, da kuma yadda take maganin cututtuka fiye da ɗari uku (300) tun ƙarnukan da suka shuɗe kamar yadda za a gani nan gaba. Sai dai sanin gaskiyar lamarin yana wajen Allah.

 Wata hujjar da ke tabbatar da hasashen ita ce, za a tarar cewa, itaciyar zogale ta sha bamban da sauran itatuwa ta hanyoyi da dama. Da farko dai takan tsiro (toho) a lokacin rani da damina, muddun tana samun danshin sanyi. Haka kuma tsananin fari da sara bai haddasa ta mutu, sai ko in har an haƙe saiwarta gaba ɗaya, ba kamar wasu itatuwan ba. Abu na biyu da ya bambanta ta da sauran itatuwa shi ne tana rayuwa a ƙasashe masu tsananin zafi da matsakaita da masu danshi da ni’ima, har ma a cikin yankunan rairayi.

 

 Magani: Ma’anarsa Da Asalinsa

 Masana da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ma’anar Kalmar magani gwargwadon fahimtarsu. Kano (2006: 316) sun bayyana ma’anar magani da cewa:

Magani, yana nufin duk wani abu da ake sha ko shafawa ko

Kuma ɗurawa a jiki ta hanyar yin allura, don neman samun

Lafiya ko kariya daga wata cuta.

Shi kuwa Ahmad (1984) ya bayar da ma’anar magani da cewa:

Magani shi ne duk wani abu da za a yi, ko wata hanya ko

kuma wata dabara da aka yi don gusar da cuta daga jikin

mutum ɗungurumgun ko kuma kwantar da ita don kawo

jin daɗI ga jiki ko ga zuciya da sauƙaƙa duk wata wahala

ga jiki da damuwa da ita cutar kan iya haifarwa.

Bakandamiyar ma’ana ta magani ita ce wadda Bunza (1989:134) ya bayyana inda yake cewa:

Magani wata hanya ce ta warkar da ko kwantar da ko rage wata

Cuta ta ciki ko ta waje ko wadda aka samu ta haɗari. Ko kuma

Neman kariya daga cuta ko abokan hamayya ko neman ɗaukaka

Ta daraja ko ta buwaya ta hanyar siddabaru da sihirce-sihirce na 

ban al’ajabi.

 Asalin Magani

 Magani ya samu ne tun bayan da Allah Maɗaukakin Sarki Ya halicci Annabi Adamu (A. S.) sai ya sanar da shi dangogin ilmomi masu yawan gaske cikin yardarSa ( Alƙur’ani, 2: 31). Daga cikin ilmomin kuwa har da ilimin cututtuka da yadda za a magance su. Haka ya halitta wasu tsirrai a doron ƙasa domin amfanin Annabi Adam da zuriyarsa. Aka kuma fahimtar da su hanyoyin sarrafa su a matsayin maganin yunwa da na cututtuka.

 Yayin da zamani ya shuɗe, mutane suka ƙara yaɗuwa zuwa sassa daban-daban, sai Allah cikin jinƙanSa da rahamarSa Ya jefa wa ɗan Adam, a ransa, in aka yi amfani da abu-kaza zai yi maganin ciwo kaza da kaza.

 Wasu lokuttan kuma a mafarki za a gayawa ɗan-Adam, ya yi amfani da wani abu don maganin wata cuta. Wani zubin kuwa, murya kawai mutun zai ji kamar daga sama, ana umurtarsa, ya yi amfani da abu kaza domin magance cuta kaza.

 Akan kuma sami magani ta hanyar gwaji da kwatantawa, musamman ta la’akari da yadda dabbobi da tsuntsaye ke amfani da’ya’yan itatuwa da hakukuwa da ganyaye yayin da suke cikin yanayin rashin lafiya, da yadda suke nuna halin ko’inkula da su a lokacin da suke cikin ƙoshin lafiya ( Adamu, 2003:10).

 Yaɗuwar al’umma da nuna kyakkyawar biyayya, ya wanzar da ɗorewar mallakar asirran magani daga hannun masana magunguna na haƙiƙa. Kyakkyawar biyayya ta sau- da ƙafa kan sa a sanar da waɗansu daga cikin zuriya ko waɗanda suka yi barance, asirran magungunan da Allah Ya sanar da su. Ta waɗannan hanyoyi ne aka cigaba da gadon asirran magungunan gargajiya a ƙasar Hausa. Kuma ta irin wannan hanya ce ilimin sirrin magungunan da zogale ya bi ya cigaba da bunƙasa.

 Rabe- Raben Magani a Bahaushiyar Al’ada

 Kamar yadda aka faɗa a bay akaɗan, magani abu nemai daɗaɗɗen tarihi wanda al’ummomi daban-daban na duniya ke bin hanyoyi mabanbanta domin samar da shi da kuma amfani da shi. Nau’uka ko ire-ire ko rabe-raben magani abu ne da ya ja hankalin masana al’adun Hausawa, kuma sun yi tsokaci a kan wannan batu. Sarkin Gulbi (2014:86) ya kawo rabe-raben magani kamar haka:

i. magungunan riga-kafi.

ii. Magungunan waraka.

iii. Magungunan cutarwa

iv. Magungunan biyan buƙata

v. Magungunan camfi

Zogale A Fagen Magani

 Zogale, nau’in itaciya ce wadda Allah Ya tsirar a bisa doron ƙasa domin amfanin mutane da dabbobi da Aljannu. Ita kanta ƙasa ma tana amfana da ita. Wani abin mamaki da ta’ajibi shi ne, irin yadda halittun da ke ruwa suke amfani da saiwar zogale da ke kusa da gulbi ko ƙorama.

,‘Yanmagori da bokaye da sauran wasu daga cikin masu sana’o’in gargajiya kamar wanzamai da masunta da makamantan su, duk suna amfani da zogale a gargajiyance domin yin magunguna nau’i-nau’i a farfajiyar ƙasar Hausa da ma wasu sassan Nijeriya.

Rabe-Raben Magungunan Zogale

 Ana iya karkasa magungunan da zogale ke aiwatarwa ta la’akari da yadda al’umma ke sarrafa ta wajen biyan buƙatunsu waɗanda suka danganci rayuwar yau da kullum. Daga cikin irin waɗannan buƙatun akwai:

1. Waraka.

2. Kariya Da Buƙatar zuci.

3. Biyan Buƙatun zuci.

 

Zogale A Fagen Maganin Waraka

 Zogale na taka muhimmiyar rawa waje kawar da dangogin cuwurwuta da ke addabar jikin ɗan Adam. Irin waɗannan cututtuka nau’i biyu ne. wadda ake iya gani da wadda ba za a iya gani ba, sai dai kawai maras lafiya ya ji wasu alamomi tare da sauyawar yanayin jikinsa. Daga cikin cututtukan da zogale kan yi maganinsu akwai:

Ƙaiƙayin Ido

 A fagen magance ƙaiƙayin ido, sai a nemo ganyen zogale ɗanye, a murtsuke shi, a sami auduga (kaɗa/ tauhwa) ko wani farin ƙyalle mai tsabta. A tsoma cikin ruwan ganyen, a tatsa (matsa) ɗigo uku (3) a idon har sau uku a rana (jinju,1990:19). Shaihin Malamin ya tabbatar da ingancin maganin ta hanyar gwaji shi da kansa.

Ƙaiƙayin Jiki

 Ta fuskar ƙaiƙayin jiki kuwa, sai a samu ɗanyen ganyen zogale cikin tafin hannu uku (3) a daka, a tarfa ruwa kimanin babban cokali huɗu (4). A tace da ƙyalle fari mai kyau. Ruwan ne za a riƙa shafawa a wurin da ke yin ƙaiƙayin. Za a shafa maganin ne sau uku (3) a rana har tsawon kwana bakwai (7) (Jinju, 1990:73). Malamin ya tabbatar da ingancin maganin tare da rashin wani lahani (aibu/cutarwa) a jikin ɗan Adam.

Ƙaiƙayin Al’aura

 Akwai wata cuta da ke addabar mutane musamman mata, inda sukan fuskanci matsalar matsanancin ƙaiƙayi a daidai farji ko dubura. Irin waɗannan mata kan fuskanci matsalar rashin son saduwa da maigida, a sakamakon mummunan ƙaiƙayi bayan jima’i. Sai a sami saƙe-saƙin zogale a dafa tare da jar kanwa ‘yar kaɗan. Sai a sha kofi ɗaya (1) safe da yamma, ta kuma riƙa yin tsalki da ruwan maganin( hira da Sahabi Kardaji, Gummi). Haka su ma maza masu fama da ƙaiƙayin matsematsi na iya yin amfani da wannan haɗin, don nema samun waraka

Ciwon Ido da Kunne

 Yayin da mutun ke fama da lalurar ciwo ido ko kunne, sai ya ɗebo ɗanyen ganyen zogale. Ya murza, ya matse ruwan ya dinga (riƙa) ɗigawa a ido ko a kunne. Insha Allah za a samu lafiya.

Ciwon Kai

 Ga mai fama da lalurar ciwon kai, sai ya nemi ɗanyen ganyen zogale, ya murtsuka shi ya shafa a goshinsa. Da izinin Allah zai sami waraka.

Ƙurajen jiki

 Idan mutun yana fama da ƙuraje a jikinsa, sai ya nemi garin zogale, ya haɗa da man zaitun ya shafa a jiki. Zai sami waraka insha Allah.

 Idan kuma mutun na fama da kurajen jiki, sai ya nemi garin zogale ya haɗa da man zaitun, ya kwaɓa, sai ya riƙa shafawa a jiki. Da ikon Allah zai sami waraka.

Ciwon Haƙora

 Shi kuwa wanda ke fama da matsalar ciwon haƙori, sai ya nemo ƙaron ( jirrai/ jillan) zogale, sai ya liƙa a inda ke ciwon (Jinju, 1990:23).

Ciwon Ɗankakkarai

 Ciwo ne da ke shafar yatsan hannu ko na ƙafa. A irin wannan yanayi yatsa kan kumbura, ta riƙa ciwo da zogi (raɗaɗi) mai tsananin gaske, har sai wurin ya ja ruwa, wanda ke bayar da damar yin sakiya. Ana amfani da ganyen zogale wajen maganin wannan cuta. Mai fama da wannan lalurar sai ya samo ganyen zogale, ya mutsuka shi, sai a saka kanwa, sai ya kunsa a yatsan da ke ciwo, kamar yadda ake kunsa (ɗaura) lalle. Da izinin Allah, cikin ‘yan kwanaki kaɗan kumburin zai sace ya kuma daina raɗaɗi sai wurin ya ƙafe (bushe).

Harbin Kunama

 Idan kunama ta harbi mutun (Allah Ya tsare), sai a nemo ganyen zogale, sai a murmurza tare da turare sai a saka a daidai wurin da ta yi harbi. In Allah Ya so za ta faɗi ba tare da jinkiri ba.

Ciwon Sanyi

 Mai fama da matsalar sanyi, sai ya nemi ganyen zogale, ya dafa tare da jar kanwa ‘yar kaɗan. A tace, ya rinƙa shan ruwan moɗa (kofi) ɗaya, sau biyu (2) a rana ga babban mutun. Yaro kuwa ya sha rabin moɗa sau biyu a yini (Jinju,1990:66).

 Haka kuma ana tafasa furen zogale tare da albasa, a rinƙa sha kamar shayi, don magance ciwon sanyi.

 Idan ciwon sanyi ya yi yawa, yakan shafi hanyar mafitsara, sakamakon da kan haifar da wahala ainun kafin fitsari ya fito..wani lokaci ma fitsarin kan faskara fita. Maras lafiya na jin fitsari amma ko ya duƙa (tsugunna) domin yin fitsarin sai lamarin ya gagara. A irin wannan yanayi, sai a nemi sayyun zogale, a wanke su sosai domin a tsabtace su. A kuma sami ruwan tsami da aka tsiyayo daga ƙullun gero, sai a jiƙa sayyun a ciki, idan sun jiƙa, sai maras lafiyan ya sha moɗa ɗaya (1) da izinin Allah cikin ɗan ƙanƙanin lokaci fitsarin zai fito ( Fadama,2014: ).

Ciwon Sanyin Mata

 Akan kamu da irin wannan cutar a sakamakon saduwa da mace. Idan namiji ya harbu da ƙwayar cutar, sai a nemo sayyun zogale wadda bata daɗe da tsira ba. Sayyun za a kwanɗare ɓawonsu, sannan a dake su cikin turmi tare da jar kanwa. A yi kunun dawa, sai a ɗebo garin maganin a saka a cikin kunun. Maras lafiya zai riƙa shan kunun domin maganin wannan cutar sanyi. (Sahabi Ƙardaji, Gummi).

 

Sanyin Ƙashi Da Kumburi

 Mai fama da lalurar sanyin ƙashi ko kumburin jiki, sai ya nemo ‘ya’yan zogale a soya, sannan a daka har su zama gari. Sai a haɗa garin da man kwakwa a rinƙa shafawa a wurin da lalurar take.

Sanyin Ƙashi

 A wannan nau’in kuwa, za a sami saiwar zogale da tafarnuwa a kirɓe su. Sai a dinga haɗawa da man tega ana shafawa a ƙafa sau uku (3) a rana, har tsawon kwana bakwai. Za a sami sauki da ikon Allah.

 Ana kuma kwaɓa garin zogale tare da manja, a riƙa shafawa a wurin da ake jin raɗaɗi.

Tsayar Da Zubar jini

 Ta fuskar dakatar da jini daga zubewa kuwa, zogale nan ma ba a baya take ba. Domin in mutun ya yi rauni ta hanyar yanka ko sara ko tuntuɓe wanda har ya haifar da kwararar jini, sai a sami ganyen zogale ɗanye, a murtsika shi, a shafa ruwan ganyen a wurin raunin. In Allah Ya so jinin zai daina zuba.

Rauni Ko Gyambo

 Wanda ya ji ciwo har fatar jikinsa ta fashe tare da zubar jini. Ko kuma yana da wani miki (ciwo) a ƙafa da ya daɗe bai warke ba, lamarin ya kai yana fitar da mugunya (ruwan ƙurji mai launin fari). Sai a nemi garin zogale a zuba a kan raunin ko gyambon. Insha Allahu zai yi saurin warkewa.

Gyambon Ciki (olsa)

 A dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi don maganin gyambon ciki.

Ciwon Shawara

 A dafa ganyen zogale tare da kanwa ‘yar kaɗan. A ci, a kuma sha ruwan don maganin shawara.

Ciwon Sukari

 A nemi furen zogale a gama da citta mai yatsu a dafa, a rinƙa sha kamar shayi. Yin haka yana maganin cutar da ke haddasa yawan fitsari wato Diyabitis.

 Haka kuma, wanda ke fama da irin wannan lalurar, sai ya ɗebo ganyen zogale tun da safe kafin rana ta fito. A shanya shi a wajen da ba hasken rana har ya bushe. In ya bushe sai a rinƙa dafa shi kamar shayi ana sha da madara, sau biyu a rana. A kula da zuwa wajen awo.Idan ba sauran cutar sukari sai a daina sha.

Ciwon Hanta Da Ƙoda

 A nemo ganyen zogale da ‘ya’yan ɓaure, a daka su har sai sun koma gari. Garin nan za a rinƙa sawa a nono ko kunu, a sha sau uku a yini. Insha Allahu za a sami lafiya.

Tsakuwar Ciki (Appendis)

 A sami saiwar zogale a gama da ‘ya’yan kankana a dake su har su zama gari. Sai a rinƙa zuba garin a nono ana sha. Insha Allah za a sami lafiya.

Tsutsar Ciki

 Idan yaro na fama datsutsar ciki, sai a sami ɗanyen ganyen zogale, a wanke a ba mai fama da lalurar ya ci, sau biyu a rana.

Maganin Bugun Aljani

 Idan Aljani ya bugi mutun har ya faɗi, sai a sami garin zogale a shaƙa masa a hanci. Zai yi saurin sakinsa. Wani zubin ma aljanin kan yi magana.

Kariya Da Buƙatun Zuci

 Magunguna ne da akan yi amfani da su don taimakon ɗan-Adam wajen kare lafiyar jikinsa tare da biyan wasu buƙatunsa da suka jiɓinci jin daɗin rayuwarsa. A wannan haujin ma zogale na taka muhimmiyar rawa. Musamman idan aka yi la’akari da amfanin da ake yi da ita ta ɓangarori kamar:

Hawan Jini Da Ƙarin Kuzari

 Sanya (saka/zuba) zogale cikin abinci ana ci, yana maganin matsalar hawan jinni. Yana kuma ƙara wa mutun kuzari a jikinsa.

Kare Kai Daga Cuta

 Magunguna ne da ke taimakawa mutun wajen kare lafiyar jikinsa daga cuta da ke haifar masa da wata illa a jikinsa. Akan yi amfani da zogale domin ƙoƙari dakatar da wata cuta daga shiga cikin jikin mutun, ko kuma hana cutar yaɗuwa. Don haka za a iya cewa zogale na maganin da ya danganci riga-kafi tare da hana yaɗuwar cuta.

Hawan Jini (tashin jini)

 A sami albasa, a kasa ta kasha huɗu, a yanka kashi ɗaya bisa huɗu na albasar a gama da dafaffiyar zogale a ci. A aiwatar da wannan haɗi sau uku ko huɗu a wata. Yin haka na maganin hawan jini, kamar yadda Jinju (1990:32) ya bayyana.

 

Magungunan Biyan Buƙatun Zuciya

 Magunguna ne da suka jiɓinci buƙatun rayuwar ɗan Adam. Ta wannan fuskar ma ana amfani da zogale domin neman samun biyan irin waɗannan buƙatun rayuwa. Misalai daga cikin irin waɗannan buƙatun sun haɗa da:

Ƙara Yawan Ruwan Mama (nono)

 A sami furen zogale a dafa shi tare da zuma. Mace mai shayarwa ta rinƙa ci sau uku a yini. Yin haka na ƙara yawan ruwan mama.

Ƙarin Nishaɗi

 A sami zangarniyar zogale tare da ‘ya’yan da ke ciki, a haɗa da kanunfari da citta da masoro da kimba a dake su, har sai sun koma gari. Sai a riƙa sawa a cikin abinci ana ci. Yin irin wannan haɗin na ƙara wa mata ni’ima da nishaɗi.

 Haka kuma mata ma’aurata na iya samun garin ganyen zogale a riƙa haɗa shi da madara ko nono ana sha domin ƙarin ni’imar kwanciyar aure da maigida. Amfani da wannan haɗin na ƙara sa mace ta ni’imtu, kwanciyar aure da maigida ta yi armashi sosai har kuma a kwaɗaitu da sake maimaitawa. 

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda

Post a Comment

0 Comments