Ticker

Gurbataccen Sako: Nazarin Ka’idojin Raba Da Hade Kalmomi A Rubutun Allunan Sanarwa Da Jikin Manyan Motoci

 Kyakkyawar sadarwa ta ta’allaƙa a kan ingantaccen rubutu, wanda aka yi bisa ga ƙa’idar da rubutu ta tanada. Mutane sukan kasa fahimtar saƙon da rubutu ke son isarwa gare su, saboda rashin biyar dokoki da ƙa’idojin rubutu kamar yadda ya kamata. Mafi yawa daga cikin saƙonnin da ake aikawa a  rubuce domin sanarwa ko gargaɗi, akan kauce wa ƙa’idar rubutu bisa ga kuskure ko rashin sanin ƙa’idojin da rubutun ya ƙunsa. Irin waɗannan rubuce-rubuce a kan gan su ne a manyan allunan sanarwa ko katuttukan gayyatar ɗaurin aure ko suna ko a jikin manyan motocin dakon kaya. Sau da yawa a kan rubuta karin maganganu ko wasu maganganun azanci da nufin yin gargaɗi ko faɗakarwa ko tallace-tallace zuwa ga mutane domin isar da wani saƙo da hukuma ko kamfani ke son jama’a su sani. Amma a saboda rashin bin dokar rubutu ko amfani da ƙa’idojin rubutu da suka dace, sai mutane su kasa fahimtar abin da saƙon ke nufi. A kan haka ne ya sa wannan takarda mai take, “Gurɓataccen saƙo: Nazarin ƙa’idojin raba da haɗa kalmomi a rubutun allunan sanarwa da jikin manyan motoci” za ta mayar da hankali domin gano illar da rashin bin dokokin haɗa da raba kalmomi ke yi a wajen gurɓata saƙo a rubutun da ake yi a kan abubuwan da aka ambata a sama.

sako

Gurɓataccen Saƙo: Nazarin Ƙa’idojin Raba Da Haɗe Kalmomi A Rubutun Allunan Sanarwa Da Jikin Manyan Motoci  

ALIYU RABI’U ƊANGULBI
GSM NO. 07032567689
E-mail: aliyurabiu83@gmail.cim 

1.0  GABATARWA 

Rubutun Hausa wani fage ne mai faɗi da yake buƙatar a nazarce shi kafin a aiwatar da shi. Wannan fage na rubutun Hausa ya haɗa da kowane irin harshe ne da za a yi rubutun Hausa da shi a duniyar masana harshen Hausa. Rubutu shi ke ɗauke da muhimmin saƙon da kowace al’umma ke son isarwa dangane da al’amurran da take gudanarwa na yau da kullum. Idan rubutu bai ɗauki sunansa ba, wato rubutu wanda yake bisa ga kyakkyawar ƙa’idar ta rubutu da zai fitar da ma’anar saƙon da ake son isarwa ba, to an sami tangarɗa. Hakan kan sa saƙon da ke cikin rubutun ya sha bamban da fahimtar masu karatunsa. Biyar ƙa’idoji da dokokin rubutu shi ke inganta ma’ana, kuma mutane su fahimta da saƙon da ake son isarwa gare su.

1.1 MA’ANAR RUBUTU

Rubutu wani zane ne da ake yi a takarda ko allo ko wani wuri da mutum zai iya karantawa kuma ya fahimta. Rubutu wata dabara ce ta yin wasu ‘yan alamomi a kan falalen dutse ko takarda ko allo da za su wakilci magana ta fatar baki (Bunza 2002). A wata fassarar ƙamusun Hausa, cewa ya yi rubutu shi ne, rubutattun kalmomi, ko wasu abubuwa da za su zama a matsayin kalmomi, ko kuma wasu ra’ayoyi, ko fahimta da aka yi shi a wasu abubuwa, ko takarda ko itace, ko dutse, tare da amfani da fensili, ko wani buroshi, ko ta wasu dabaru daban kamar tumbari ko ɗab’i ko huje-huje da zane-zane. Bargeryy (1934).

 

Yahaya (1988), ya bayyana cewa ɗan’Adam ya ƙaga rubutu ne domin ya samu damar rattaba saƙonsa, ko tunaninsa ko koyar da wasu darussa da yake son mutane su fahimta, a kan takarda ko don aikawa wani wuri ko kuma don adanawa, ba tare da jin tsoron tauyewar abin nufi ba. Ya ƙara da cewa, rubutu shi ne yin amfani da zayyana wasu alamomi a kan takarda, ko a kan wani abu mai bagire don sadar da magana wadda ɗan’Adam ya fi faɗin ta da fatar baki, a ji shi da kunne, kamar yadda aka bayyana a sama. Wannan hanya ta rubutu ta samu ne a lokaci mai tsawo, kuma ana amfani da alamomin rubutu iri-iri a sassa daban-daban na duniya.

 

Abdullahi (1977), cewa ya yi, mutanen sin (China) suna yin amfani da waɗansu alamomi ne masu kama da surorin mutane da abubuwa wajen isar da saƙo a cikin harshensu tun shekara fiye da 3,500 da suka wuce.

 

Bagari (1986) ya fassara rubutu da wani zanen alamomi na musamman (baƙaƙe da wasula) a kan takarda domin isar da saƙo ga jama’a su fahimce shi.

 

A taƙaice rubutu wata dabara ce ta isar da wani saƙo da ake zanawa a kan takarda, ko wani falalen dutsi, ko ɓawon itace ko wani wuri na musamman ba tare da an furta da fatar baki ba.

 

1.2 SADARWA

Sadarwa tana nufin wata hanya ce da ake yin magana baki da baki tsakanin mutane biyu ko fiye da haka. Sadarwa na iya kasancewa don waɗansu hulɗoɗi ne na zumunci ko na ciniki, ko na aiki ko kuma na waɗansu al’amurran duniya na yau da kullum. Hanyoyin sadarwa da harshe sun kasu gida biyu, furtawa da baki, wato mutum ya ji ta da kunnensa, ko kuma a rubuta a takarda a karanta.

 

1.3 MUHALLIN BINCIKE

Wannan bincike zai yi nazari ne a kan ƙa’idojin rubutu da suka haɗa da raba da haɗe kalmomi a rubutun Hausa da ake yi a kan manyan motocin sufuri da katuttukan sanarwar ɗaurin aure ko suna da kuma kan allunan sanarwar tallace-tallacen kamfanoni da hukumomin gwamnati. Da wannan ne za mu fahimci irin kura-kuran da masu rubutun da aka ambata a sama su ke tabkawa wanda ke zama dalilin gurɓacewar saƙonnin da ake isarwa zuwa ga jama’a.

 

1.4 RA’IN BINCIKE

Bahaushe yakan so duk aikin da zai aiwatar ya sama masa madogara da zai yi tinƙaho da ita. Ƙwararrun masana kuma gogaggu a kan adabin harshe sukan yi yunƙuri na diddige dukkan abin da suka sa a gaba, domin bayyana shi yadda zai amfani jama’a ko waɗanda suka damu da sai sun tantance abu kafin su fara aiki da shi. A nawa gani na ɗora wannan bincike a kan ra’in Prof. Aliyu Muhammad Bunza a kan tantance rubutu da ƙa’idojinsa domin kyakkyawan rubutu da aka tsara bisa ƙa’idojin  da suka dace shi ne tushen fahimtar saƙo. Domin ana fahimtar saƙo idan rubutu ya inganta wanda shi ke bayyanar da manufar marubuci a fili a kan abin da ke a cikin zuciyarsa. Rashin samun haka ke kawo gurɓacewar saƙo, a dalilin saɓawa ƙa’idar rubutu.

 

1.5 DABARUN BINCIKE

Dukkan bincike da za a gudanar musamman irin wannan dole ne yana buƙatar waiwaye da yada zango ga ayyukan da aka yi cikin fannoni daban- daban a fagen ilimi domin ganin yadda fannonin suka fuskanci matsaloli a fagen bincikensu. Bugaggun littattafai, da kundayen digiri da ayyukan da aka wallafa da waɗanda ba a wallafa ba, a zuciyar aikin, dole ne a kai hannu ga sassan da suka shafi adabi daban-daban don kafa hujjar gabatar da wannan bincike nawa. Wannan hanya da binciken ya bi ita ce madogarata ta gabatar da wannan takarda domin fayyace yadda kyakkyawan rubutu yake kasancewa hanyar isar da saƙo kai tsaye cikin sauƙi ga al’ummar da aka nufa da su san abin da ake isarwa gare su, kuma su fahimce shi.

 

1.6 ƘA’IDAR RUBUTU

Ƙa’idar rubutu ita ce bin dokoki da ke inganta rubutu har ya zama abin karantawa, wato ƙa’idar da za ta bai wa mai rubutu damar ya yi rubutunsa yadda daidaitacciyar Hausa ta tanada. Yin haka zai sa rubutu ya inganta ta yadda kowane mutum zai iya karantawa kuma ya fahimci saƙon da rubutun yake ɗauke da shi. Rubutun Hausa ba sake yake ba babu wata ƙa’ida kowa ya rubuta abin da yake so, (Bunza 2002).  Masana da suka tsara dabarar rubutu sun tsara yadda ya kamata a rubuta kalmominsa.

 

Dokar raba da haɗe kalmomi a rubutun Hausa ta taka muhimmiyar rawa musamman ta fuskar tsaftace rubutu da inganta ma’anar saƙo sosai (Sampson: 1985).

 

Haɗe kalmomi yana nufin duk kalmomin da ke da ma’ana ɗaya, ga furucin baki za a ji su sun fita zama ɗaya tare, to a haɗe ake rubuta su (Bunza 2002). Shi kuwa raba kalmomi shi ne inda za a bai wa kowace kalma mai cin gashin kanta damar a rubuta ta ita kaɗai ba tare da an liƙa ta ga wata ba. Sai dai a hasashen masana dokokin raba kalmomin rubutun Hausa sun fi dokokin haɗe kalmomi yawa, kuma sun fi su rikitarwa da wuyar ganewa ga ɗan koyo.

 

Ga alamomin haɗe da rabe kalmomi kamar haka:

Haɗe kalma (< >) raba kalma ( / )

Rashin amfani da waɗannan alamomin rubutu a allunan sanarwa da jikin manyan motocin dakon kaya da makamantansu shi ke haddasa gurɓacewar saƙonni da ake son isar wa ga jama’a. Mafi yawan rubuce-rubucen suna zuwa a cikin sigar maganganun azanci kamar karin magana, habaici da gargaɗi da sauransu. Misali.

Jadawali na : 1 Karin Maganganu.

S/N

Gurɓataccen rubutu Hausa

Daidaitaccen Rubutun Hausa

1.       

Akuya kobata haihuwa tafi kare

Akuya ko ba ta haihuwa ta fi kare

2.       

Ayi yau ayi go be………..

A yi yau a yi gobe

3.       

Ayi dai mugani

A yi dai mu gani

4.       

Abarkaza cikin gashinta

A bar kaza cikin gashinta

5.       

Adawo lafiya

A dawo lafiya

6.       

Agogomaicika aiki

Agogo mai cika aiki

7.       

Ayi salati goma ga annabi

A yi Salati goma ga Annabi

8.       

Allah yamaka jagora

Allah ya yi maka jagora

9.       

Allah gatanbawa

Allah gatan bawa

10.   

Allah bayada dole

Allah ba ya da dole

 

Da wannan ɗan misali na sama za mu iya fahimtar cewa a rubutu na farko ba a yi amfani da ƙa’idar rubutu ta haɗe ko raba kalmomi ba. Saboda haka rubutun ba ya karantuwa ya ba da ma’ana domin ya saɓa wa dokar raba da haɗe kalmomi. Idan aka dubi yadda aka rubuta misali na farko za a ga cewa; “Akuya kobata haihuwa tafi kare”. Wannan jimla ce mai gurɓatacciyar ma’ana, domin tana danganta Akuya da kare, inda jimlar take nufin “Akuya ta tafi wurin Kare”. Amma da an bi ƙa’idar raba kalma, sai jimlar ta ba da ma’ana kamar haka

“Akuya ko ba ta haihuwa ta fi kare”

Wato saƙon wannan karin magana yana nufin fifikon da ke akwai tsakanin Akuya da Kare ta fuskar daraja. A al’ada Akuya dabba ce da ake ci, amma kare dabba ce wadda Bahaushe musulmi ba ya ci. Dalilin haka ya sa Bahaushe ke yin amfani da irin wannan karin magana yana rubuta ta a jikin manyan motoci domin yin habaici zuwa ga wani mutum ko wasu mutane da shi kaɗai ya san wanda yake yi wa habaicin. Amma saboda ba a rubuta ta yadda ya kamata ba sai a kasa fahimtar saƙon.

 

Don haka ana rabawa tsakanin kalmomin, “Kobata, da tafi, kamar haka; “ko ba ta”, da “ta fi”, haka sauran misalai za su kasance a wannan jadawali na farko. Misali kamar Abarkaza cikin gashin ta.

 

Yadda wannan Karin magana take a rubuce, ba haka ya dace a rubuta ta ba. Ga yadda ka’idar take, “A bar kaza cikin gashinta”. Irin wannan misali yakan faru a allunan sanarwa da katuttukan gayyatar ɗaurin aure inda za a ga an rubuta kalmar “Adawo lafiya”, ko “Azo lafiya” da sauransu, cikin kuskure. Misali a daidaitacciyar Hausa ga yadda ya kamata a rubuta waɗannan kalmomi “A dawo lafiya” “A zo lafiya”.

 

Idan aka haɗe kalmar “A dawo”, ko “A zo”, mai koyon karatu ba zai fahimci saƙon ba, cewa ana nufin A dawo ko A zo lafiya ba.

 

Har wa yau za a ga wata jimlar da ke bayani a kan kwarjini ko fayyace darajar wani abu da aka rubuta cikin kuskure da ka iya gurɓace saƙo. Misali, Agogomai cika aiki. Kalmar agogo da mai rabe suke, amma da aka haɗe su, sai saƙon ya gurɓace. Misali Agogomai, haka ya sa kalmar ta zama ɗaya maimakon kalma biyu. Idan aka ce agogo, kowa ya san suna ne, ita kalmar ‘mai’ sifa ce da ke ƙarin bayani ga sunan agogo.

 

A wani misali “Ayi Salati goma ga annabi,” an sami kuskuren rubutu inda ya kamata a raba tsakanin A da yi sai aka haɗe su, wato an haɗe lamiri da aiki. Ko yaushe kalmar aiki ba a haɗe ta da suna ko lamirin suna wajen magana. Don haka ga yadda ya kamata a rubuta ta; A yi Salati. Shi kuwa sunan Annabi da babban baƙi ake rubuta shi. Misali “Annabi’ ba ‘annabi’ ba. To haka dai sauran rubuce-rubucen suke faruwa, waɗanda ke gurɓata saƙonnin da ake aikewa a kan allunon sanarwa da katuttukan gayyatar daurin aure da suna. Idan ana so a fahimci kowace kalma da aka haɗe ko aka raɓe alhali rabe take ko haɗe, to dole ne a yi amfani da ƙa’idojin raba ko haɗe kalma.  Misali ( / ) ko (< >) a  A dawo ko gashin < > ta.

 

Jadawali na: 2: Habaici

S/N

Gurɓataccen rubutun Hausa

Daidaitaccen Rubutun Hausa

1.       

Barewabata gudu ɗan ta yayi rarrafe

Barewa ba ta gudu ɗanta ya yi rarrafe

2.       

Baiwa saiAllah

Baiwa sai Allah

3.       

Busshiya amaryar daji

Bushiya amaryar daji

4.       

Baruwan biri dagada

Ba ruwan biri da gada

5.       

Ba’a kashin wutadawuta

Ba a kashin wuta da wuta

6.       

Ba’a mugunsarki sai mugunba fade

Ba a mugun sarki sai mugun bafaɗe

7.       

Baruwan arzikida mugungashi

Ba ruwan arziki da mugun gashi

8.       

Barimurnar karenka yakama zaki

Bari murnar karenka ya kama zaki

9.       

Badon kurabada kare yanisa

Ba don kura ba, da kare ya nisa

10.   

Yaro mankaza

Yaro man kaza

11.   

bahaka akasoba ƙanemiji yafiimiji kyau

Ba haka aka so ba ƙanen miji ya fi miji kyau

 

Jadawali : 3: Gargaɗi

S/N

Gurɓataccen rubutun Hausa

Daidaitaccen Rubutun Hausa

1.       

Hassada gamai rabo taki

Hassada ga mai rabo taki

2.       

Yakamata auran na gida

Ya kamata auren na gida

3.       

Yaro tsaya matsayin ka

Yaro tsaya matsayinka

4.       

Kowaƙƙi gaskiya rabo nai kunya

Kowa ya ƙi gaskiya rabonai kunya

5.       

Gyara kayan ka bazai zan sauke muraba ba

Gyara kayanka ba zai zama sauke mu raba ba

6.       

Araha tafi bashi

Arha ta fi bashi

7.       

Tahiya sannu sannu kwana nesa

Tafiya sannu- sannu kwana nesa

8.       

Sa a tafi samako

Sa a ta fi sammako

9.       

Yaro daina murna karenka yakama zaki

Yaro daina murna karenka ya kama zaki

10.   

Kyawon tahiya dawowa

Kyawon tafiya dawowa

 

Kamar yadda aka gani a jadawalan da suka gabata a sama, za a iya fahimtar cewa yawancin karin maganganu da habaici da gargaɗi da ake amfani da su, a jikin allunan sanarwa da katuttukan sanarwar ɗaurin aure da sauransu, ana rubuta su cikin kuskure na rashin bin ƙa’idar rubutu. Haka yakan sa mutane su kasa fahimtar saƙon da ake son isarwa gare su. Yakan kasance saboda kauce war ƙa’idar rubutun, sai saƙon ya gurbace; abin da rubutun yake karantawa ya saɓa wa saƙon da yake ɗauke da shi. Misali; “Ba’a mugunsarki sai mugunba faɗe” ba’a na nufin maganar raha, saboda haka ta saɓa wa abin da ake son a isar na cewa “Ba a mugun sarki sai mugun bafade”. Ana nufin fadawa su suka fi sarki mugunta domin su ke kai wa sarki rahoto game da abin da ke faruwa a masarautarsa. Idan aka yi amfani da rubutu na farko, “Ba’a mugunsarki sai mugunbafade, to saƙon ya gurbata ke nan, sai dai a ce “Ba a mugun sarki sai mugun bafade”.

 

1.7 KAMMALAWA

Mafi yawan rubuce-rubucen da ake gani a kan manyan motocin sufurin kaya da allunan sanarwa da katuttukan gayyatar ɗaurin aure da suna, ana rubuta su ba bisa ƙa’idar rubutu ba wanda ya shafi haɗe kalma ko raba ta ba. Dalilin haka sai rubutun ya kasa karantuwa ga masu koyon Hausa. Wasu kuma su iya karanta su, amma su kasa fahimtar abin da ake nufi. Kai har ma waɗanda na iya karatun wani lokaci sukan kasa karanta irin wannan rubutu balle su fahimci saƙon da ake son isarwa ba.

 

1.8 SAKAMAKON BINCIKE

Wannan bincike da aka gudanar a kan ƙa’idojin rubutu da masu rubuce-rubuce a jikin manyan motocin dakon kaya, da allunan sanarwa da katuttukan sanarwar ɗaurin aure da zanen suna, suna rubuta su a kan kuskure ne. Binciken ya gano cewa yawancin mutanen da ke wannan rubutu ba su fahimci yadda ƙa’idar rubutun Hausa take ba;

1.      Ba su da ilimin harshen Hausa da yadda ake rubuta kalmominsa ba.

2.      Ƙabilu ne waɗanda harshen Hausa bai zauna a bakin su ba, balle har su iya rubuta shi kamar yadda ya kamata.

3.      Ko masu ilimin da suke rubuta Hausa, ba su yi nazarin yadda Hausa take bin ƙa’idojin rubutunta ba, shi ya sa ake samun kura-kurai idan suka yi rubutun, saboda sun kasa tsayawa su koyi ƙa’idojin rubutun Hausa yadda ya dace.

4.      Su kansu masu ba da sanarwa a rubuta masu waɗannan saƙonni ba su san ƙa’idojin ba, balantana su gyara kura-kuran da masu rubutun ke tafkawa kafin a rubuta su ga motocin ko allunan rubutun sanarwa.

5.      Ba a ba da horo na musamman ga irin waɗannan mutanen dangane da yadda kowane harshe yake da irin tasa ƙa’idar rubutu.

 

1.9 SHAWARWARI

Idan har ana son a riƙa samun kyakkyawan rubutu da za a iya fahimtar saƙon da yake ɗauke da shi, dole ne a riƙa shirya horo na musamman ga maɗabi’ai da ake kai wa sanara suna bugawa. Haka kuma a riƙa shirya saminoni na musmaman ga masu zane-zane da ake kai wa aiki a bakin tituna ko wuraren sana’ar su domin a inganta rubutun Hausa, a kauce wa aikawa da gurɓataccen saƙo kai tsaye ta hanyar rubutu maras ƙaida. Ƙabilu da ke wannan sana’a su riƙa tambayar masana harshen Hausa yadda ake rubuta wasu kalmomi na Hausa domin kauce wa rubutu maras ma’ana da gurɓata saƙo.

 

MANAZARTA

 

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments