Ticker

6/recent/ticker-posts

Hoton Siyasa A Fina-Finan Hausa: Fim Ɗin Masu Gudu Su Gudu Bisa Faifan Nazari.

 Tsakure: Aikin adabi a kullum tafiya yake daidai da yadda rayuwar al’umma ke sauyawa. Dukkan wasu abubuwa da ke cikin ƙunshiyar kayan cikin adabi suna nuna yadda rayuwa wannan abin ya kasance ne a daidai lokacin da ya samu. Wannan ne ya sa masana suka ɗauka cewa, adabi tamkar madubi ne na rayuwar al’umma. Kasancewar siyasa tana daga cikin muhimman al’amura waɗanda suka shafi rayuwar ɗan’adam, wannan ya sa da wuya mutum ya iya rayuwa ba tare da ita ba. Ko dai ya kasance siyasar ta tsarin gargajiya ce, ko siyasar addini, ko kuma siyasar zamani. Dangane da siyasar zamani kuwa, akwai ayyukan adabi da dama da suka shafi waƙoƙi da labaran zube da ma wasannin kwaikwayo da suka nuna ɓirɓishinsa. Waɗanda suka fito da irin wainar da aka toya a baya da halin da ake ciki yanzu, da ma hasashen abin da zai iya faruwa a nan gaba. Wannan takarda za ta dubi irin wainar da aka toya ne a fagen siyasar Nijeriya, musamman lokacin da zaɓen shekarar 2015 ya matso, da irin abubuwan da suka faru wanda tarihi ba zai manta da su ba. Za a yi wannan nazari ne ta hanyar yin nazarin fim ɗin Masu Gudu Su Gudu, tare da kwatanta shi da gaskiyar abin da ya faru zahiri.



Hoton Siyasa A Fina-Finan Hausa: Fim Ɗin Masu Gudu Su Gudu Bisa Faifan Nazari.

Na

Jibril Yusuf
Department of Nigerian Languages and Linguistics
Kaduna State University,Kaduna.
Phone no: +2347030399995
Email: jibreelzango@gmail.com

1.0  Gabatarwa

Tun bayan ɓullar Fina-finan Hausa, masu shirya su sun riƙa kallon waɗansu al’amura na yau da kullum waɗanda suke faruwa a cikin al’umma wajen shirya fina-finan nasu a kai. Waɗannan al’amura sukan kasance ta fuskoki mabambanta na rayuwar ɗan’Adam, inda akan riƙa ɗaukar su a matsayin abin da fim guda zai kalla. A wani shirin kuma sai a dubi wata fuskar daban.

Masana da manazarta sun sha yin nazarce-nazarce da bincike-bincike a kana bin da ya shafi fim ɗin Hausa, tun daga kan yadda ake shirya shi, da masu shirya shi, da ma nazarin ƙunshiyar fina-finan. Masana da manazarta irin su; Larkin (2004) da Adamu (2003) da Dunfawa (2002) da sauransu, sun yi nazarin abubuwa da dama da suka shafi fina-finan Hausa, kuma sun kalli abubuwa da dama da suka shafi fim, sai dai a duk cikin nazarin nasu ba a samu wanda ya dubi irin abubuwan da suka faru cikin a cikin siyasa shekarar 2015 ba, duk kuwa da cewa an samu wani fim ɗin Hausa wanda ya hasko wasu muhimman abubuwan da suka faru a lokaci. Wannan fim kuwa shi ne; Masu Gudu Su Gudu.

A cikin wannan nazarin za a dubi irin abubuwan da suka faru ne a cikin fim ɗin tare da duban yadda abin yake a zahiri, da kuma nazarin irin yadda fim ya kasance kundin adana tarihi, musamman kan abin da ya shafi tarihin siyasar Nijeriya.

2.0  Tsakanin Adabi Da Siyasa

Siyasa na nufin neman ra’ayin jama’a ta hanyar amfani da lafuzza masu daɗi da suka ƙunshi tausasawa da nuna jin ƙai da rangwame da ƙarya, domin samun biyan wata buƙata wadda ka iya kasancewa na neman shugabancin al’umma ko cimma wani buri na rayuwa. Yusuf, (2018:9). Kodayake, a yau al’umma sun fi kallon siyasa a matsayin wayo ko zance mai daɗi ko lallashi ko ƙarya ko danne haƙƙi ko yaudara. Funtua, (2003:18). Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da irin salon da shugabanni suka ɗauka wajen gudanar da shugabancin al’umma a yau ba.

Kowane zamani da irin siyasar da yakan zo da ita, wadda ta dace da irin tsarin rayuwar da ake gudanarwa a wannan zamanin. Kasancewar adabi hoto ne da yake nuna rayuwar wata al’umma, wannan ya sa a kowace gaɓa ko yanki na rayuwa da aka riska ba a taɓa rasa ɓurɓushin siyasa a cikin adabin al’ummar wannan lokaci.

Siyasa ta samo asali tun lokacin da ɗan Adam ya samu hanyar neman abinci da kuma bayyanar makaman yaƙi, Idris, (2016:35-26). Wannan ya sa ake ganin cewa har a wancan zamani na rayuwar gargajiya ma an samu ɓurɓushin siyasa a cikin adabi. Kafin bayyanar hanyar rubutu, adabin baka shi ne hanyar bayyana fasahohin al’umma. Don haka idan aka samu tasirin siyasar gargajiya cikin nau’o’in adabin ba abin mamaki ba ne. Misali, a cikin zube na baka, ana samun tatsuniyoyi masu ɗauke da hoton tsarin siyasar ƙasar Hausa, inda akan nuna tsarin gudanar da mulkin sarakuna da kuma yadda ake gudanar da al’amuran shugabanci, yadda akan nuna shugaba da irin ƙarfin ikonsa a cikin jama’ar da yake mulki. Wasu kuma akan nuna irin tsarin zamantakewar Hausawa ne na zaman gandu, da aikin gayya, da yadda tsarin shugabancin yake tun daga cikin gida, ta yadda akan samu shugaban gida wanda yakan kasance dattijo ne wanda ya fi kowa shekaru, da kuma sauran mabiyansa waɗanda suka haɗa da ‘ya’yansa da surukansa da jikoki da sauransu. Baya ga tatsuniyoyi, akwai karin maganganun Hausawa da dama da suka fito da tasirin siyasa waɗanda su ma yawanci sun shafi tsarin gudanar da shugabanci ne, waɗanda suka fito da falsafar rayuwar al’umma ta fuskar tsarin mulki da shugabanci da yadda shugaba ya kamata ya zama da halayyarsa da ɗabi’unsa, kai har ma da siyasar zamani da sauransu. Ɗanhausa, (2012:43).

Haka kuma a cikin waƙoƙin baka na Hausa, nan ma tasirin siyasa ya fito ƙarara, domin kuwa an samu waƙoƙin siyasa na sarakuna waɗanda aka kira su waƙoƙin fada, waɗanda ake nuna irin ƙarfin mulkin sarakuna da ƙarfin faɗa a ji, da kuma yadda suke juya akalar al’ummarsu a tsarin gargajiya. A cikin waƙoƙin kuma akan ga yadda abokan adawar sarki ko shugaba kan kasance cikin rashin jin daɗi, ko dai wanda suka so ya zama sarki ba shi aka naɗa ba, ko kuma dai wani abin daban wanda ya sa suke ganin ba za su iya yi wa wannan sarki mubaya’a ba. A wasu lokuta har wasu sukan bar gari idan sun rasa sarauta tare da mabiyansu. Su kuwa makaɗan, sai su riƙa jifar su da habaice-habaice da gugar zana a kan irin rashin nasarar da suka yi da kuma nuna musu cewa mulki na Allah ne da sauransu. Irin wannan duk tasirin siyasa ne ya kawo samuwar waƙoƙi irin na fada. Haka kuma, akwai waƙoƙin baka da dama waɗanda suka shafi siyasar kanta, misali; murnar samun ‘yancin ƙasa da na siyasar jam’iyyu da ma waɗanda aka yi wa ‘yan takara. Gusau, (2008:290).

Bugu da ƙari, wasannin kwaikwayon Hausa da dama sun fito da irin wannan tasiri na siyasa, domin kuwa sau da yawa akan samu wasannin da suka fito da tsarin sarautun gargajiya. Misali akwai wasannin tashe waɗanda ake nuna yadda sarki ke nuna mulki, da rayuwar cikin gidan sarauta da sauransu. Kai hatta a cikin bori wanda wasu irin su Ahmed, (1985:6) suke ganin wasan kwaikwayo ne, an samu tasirin siyasa a cikinsa, domin kuwa an samu iskoki waɗanda daga jin sunansu ka san cewa tasirin siyasa ce ta samar da su. Misali, iskoki irin su Amiru da Gwamna, da Bature da Kwamanda kai har ma akwai sarautar sarkin bori da akan samu. Waɗannan duk za a iya iya cewa tasirin siyasa ne cikin adabin Hausa.

Haka kuma, a cikin Hiskett, (1975:13) an ga irin yadda tasirin cuɗanyar da aka samu da baƙin al’ummu ya haifar da samuwar hanyar rubutu, wanda ake ganin ya taimaka ƙwarai wajen samuwar rubutaccen adabi, ciki kuwa har da adabin Hausa. Domin kuwa, bayan samuwar tsarin rubutun Larabci da na Ajami ne aka fara samun rubutattun waƙoƙi, tun kafin jihadi da kuma bayan jihadi, inda tun a wannan lokacin ake ganin an fara samun waƙoƙi masu ɗauke da ruhin siyasa. Haka kuma an samu wasiƙu da sarakuna suka riƙa aike wa junansu wanɗanda suke ƙunshe da abubuwan da suka shafi mulki da siyasa da al’amuran jagorancin al’ummominsu. Duk da cewa ba a samu rubutaccen wasan kwaikwayo a daidai wannan lokacin ba, kasancewar lokaci ne da aka yi jihadin gyaran halaye, wanda Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo ya jagoranta, haka kuma addinin Musulunci addini ne, da bai zo da irin wannan wasan ba, amma dai an samu rubuce-rubuce da dama waɗanda za a iya alaƙanta su kai tsaye da siyasa, musamman ma waƙoƙi waɗanda su ne aka ɗauka hanya mafi sauƙi wajen isar da sako fiye da komai. Waɗannan waƙoƙin sun kasance suna kira ne ga yin ɗa’a ga Allah da manzonsa da kuma shugabannin Musulmi na wancan lokaci, waɗanda ba wai sarakuna ne, domin ci gaban tsarin mulkin da Shaihu ya shimfiɗa bayan jihadi da kuma wayar wa al’umma kai kan abin da ya shafi addini. Hiskett, (1975:17). Daga bisani kuma, bayan samuwar rubutun boko, an ci gaba da samun waƙoƙi masu ɗauke da wannan ruhi na siyasa. Domin kuwa duk da lokacin ba a fara batun siyasar jam’iyyu ba, amma kuma siyasar neman ‘yancin kai da ta tsarin mulki da tsarin shugabancin sarakuna, da tsarin mulkin Turawa su ne cike cikin waƙoƙin. Hiskett, (1975:13-19). Ko kafin waɗannan waƙoƙin masu ɗauke da ruhin siyasa, an samu littattafan zube na Hausa na farko da aka rubuta, a cikin wasu daga cikin littattafan an samu waɗanda suke ɗauke da ɓurɓushin siyasa a cikinsu, duk da cewa dai ba shi ne babban saƙon da littattafan ke ɗauke da shi ba, amma dai ko ba komai an samu abin da za a faɗa kuma a danganta shi da siyasa. Misali, littafin Ruwan Bagaja na Abubakar Imam ya ɗan hasko yadda tsarin sarauta da shugabancin al’umma a gargajiyance take. Shi kuma littafin Ganɗoki na Bello Kagara ya fito da irin yadda siyasar Turawan mulkin mallaka ta gudana.

Daga bisani, an samu littafin Magana Jari ce na Abubakar Imam wanda a cikin labaru da dama na cikin littafin an nuna tasirin sarautar gargajiya da mulki da ƙarfin iko irin na sarakuna, da kuma yadda ake girmama su.

Da tafiya ta yi nisa, lokacin da aka fara hada-hadar karɓar mulkin kai, nan ma an samu tasirin siyasa ƙwarai cikin rubuce-rubucen adabin wannan lokacin, domin kuwa ɓullar jam’iyyun siyasa ya ƙara wa abin armashi, kasancewar kusan dukkan ayyukan adabi na wannan lokacin suna ɗauke da wannan ruhin. Misali, an samu waƙoƙi da dama na siyasa tun daga waɗanda aka yi wa jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa a wannan lokacin da ma sauran zamunnan siyasar da suka biyo baya. Baya ga waƙoƙi, an kuma samu littattafan zube da suka fito da tasirin siyasa wasu ma har da ɓirɓishin siyasar jam’iyyu a cikinsu. Misali; littafin Tura Ta Kai Bango na Sulaiman Ibrahim Katsina da Ƙarshen Alewa Ƙasa na Bature Gagare. Haka kuma, ta fuskar wasan kwaikwayo ma an samu wasannin da suka fito da ruhin siyasar jam’iyyu na wannan lokacin. Misali littafin wasan kwaikwayo na Kukan Kurciya na Mahmud Barau Bambale da sauran su.

Haka ma ta fuskar sauran rassan adabi duk inda aka duba siyasa ta ɓulla, kuma ta yi tasiri ƙwarai cikin dukkan rassan na adabi, ciki kuwa har da fina-finan Hausa waɗanda suka kasance wani nau’i ne na wasan kwaikwayo na zamani.

Ke nan, idan aka duba za a ga cewa dangantakar adabin Hausa da siyasa ba abu ne a ɓoye ba, domin kuwa ta bayyana ƙarara cewa siyasa da adabi tamkar hanta ce da jini, domin kuwa ba a iya raba su, kuma duk yadda aka so a ga an cire siyasa cikin adabin Hausa ba zai yiwu ba, ba don komai ba sai kasancewar siyasa tana tafiya ne da tsarin rayuwar al’umma, shi kuma adabi shi ne ke nuna hoton rayuwar al’ummar. Ashe ke nan idan aka tashi nuna hoton dole a hango siyasa a cikinsa.

3.0  Fina-finan Hausa Da Samuwarsu A Taƙaice

Samuwar fina-finan Hausa yana da alaƙa da samuwar majigi a ƙasar Hausa. Kamar Larkin (2004:47) ya bayyana, tun a wuraren shekarar 1933 ne aka fara nuna hoton majigi a gidan Shettima a Kano, inda aka rika yaɗa manufar Turawan mulkin mallaka da suka shafi noma da kiwon lafiya da yadda ya kamata a riƙa girmama sarakunan gargajiya da Sarauniya da dai sauran wasu manufofin da Turawan suke son shigarwa cikin al’ummar Hausawa. Majigi ya ci gaba da zama wata hanya mai sauƙi ta yaɗa manufofin gwamnati da wayar da kan al’umma har zuwa tsakankanin shekarar 1970 zuwa 1980, inda aka samu ɓullar tashoshin talabijin waɗanda aka kafa su da manufofin siyasa, waɗanda kuma aka riƙa nuna wasannin kwaikwayo a cikinsu domin wayar da kan al’umma kan waɗansu sababbin abubuwa. (Larkin, 2004: 51).

Fina-finan Hausa na bidiyo sun samu ne a wuraren shekarar 1980 zuwa 1984 lokacin da wasu ƙungiyoyin wasannin kwaikwayo suka haɗu suka shirya wasu fina-finai guda huɗu, sai dai daga cikin huɗun biyu ne kawai suka shiga kasuwa. (Ali, 2004: 30). Sai dai Ali, (2004: 31) yana da ra’ayin cewa, fim na farko da aka nuna ƙwarewa wajen shiryawa kuma aka sayar da shi, shi ne fim ɗin Turmin Danya wanda ya fito a shekarar 1990. Sauran da suka biyo bayansa su ne Rikicin Duniya a shekarar 1991 da kuma Gimbiya Fatima kashi na 1 zuwa na 5 daga 1992 zuwa 1995. Sai kuma fim ɗin In Da So Da Ƙauna da wani fim Munkar waɗanda suka fito a shekarar 1995. Duk da cewa akwai saɓani wajen tantance wane fim ne ya riga wani, amma dai an tabbatar cewa fim na farko da aka fara shiryawa shi ne Turmin Danya.

Daga bisani, harkar fim ta ci gaba da bunƙasa, inda aka riƙa samun ɓulɓulowar sababbin kamfanonin shirya fina-finan, da kuma ƙarin sababbin ‘yan wasa da suka yi ta kunno kai, kasancewar ana samun ɗan abin masarufi. An ci gaba da samar da sababbin fina-finai waɗanda suke dauke da saƙonni daban-daban har zuwa wannan lokacin da muke ciki. Daga cikin irin abubuwan da akan shirya fina-finan a kansu akwai; ƙarya da cin amana da auratayya, da zamantakewa da sarauta da soyayya da siyasa da sauransu.

4.0  Dangantakar Fina-finan Hausa Da Siyasa

Tun bayan ɓullowar fina-finan Hausa an ci gaba da samun fina-finai waɗanda aka riƙa shirya su bisa mabambantan al’amura waɗanda suka shafi rayuwar yau da kullum. Kasancewar siyasa aba ce mai muhimmanci a cikin rayuwar ɗan’Adam, wadda ta kasance cikin kusan kowane ɓangare na rayuwar yau da kullum. Wannan ya sa a cikin fina-finan Hausa ma an samu wasu da dama da aka shirya su bisa tsarin siyasa, ko dai siyasar gargajiya ko na addini ko kuma na zamani wato siyasar jam’iyyu. Misali, fina-finai irin su; Sangaya da Juyin Sarauta da Ƙasata da Siyasa ko Ƙabilanci da Mahdi da Shugabanci da Rayuwa da Ga ni Ga ka da Wuta sallau da Masu Gudu Su Gudu da dai sauransu, duk fina-finai ne da aka shirya su kan siyasa. Ke nan idan aka duba za a ga cewa fim da siyasa suna da dangantaka mai ƙwari, kasancewar kowane fim kan yi ƙoƙari ne wajen nuna wata irin rayuwa ta al’umma, ko dai domin ya faɗakar ko kuma ya nishaɗantar. Wannan ne ya sa aka samu fina-finai na siyasa waɗanda ke nuni da irin rayuwar siyasa da ta wanzu a wani zamani ko kuma take gudana a yanzu, domin wayar wa da al’umma kai, ko kuma faɗakar da su kan illolin waɗansu miyagun ɗabi’u da ‘yan siyasa ko ma mabiyansu kan tsunduma a ciki.

Irin wannan dangantakar ce da ke tsakanin fina-finan Hausa da siyasa ta samar da fim ɗin Masu Gudu Su Gudu wanda a kansa wannan nazari zai gudana domin ganin irin yadda rayuwar siyasa ta kasance a shekarar 2015. Mu je zuwa!

5.0 Ɗaurayar Fim Ɗin Masu Gudu Su Gudu

Fim ɗin Masu Gudu Su Gudu fim ne da kamfanin A.D.A Film &Distribution Company LTD ya shirya tare ɗaukar nauyin Isma’il Na’abba(Afakallahu). Falalu A. Ɗorayi ne ya ba da umarni.

Fim ne wanda aka shirya shi kan irin wa-ka-ci-ka-tashin da aka yi lokacin da babban zaɓen ƙasa na shekarar 2015 ya ƙarato. An shirya fim ɗin ne ta hanyar nuna irin shirye-shirye da irin lissafin da ‘yan siyasa kan yi domin ganin sun yi nasara a zaɓe.

Tun da farko, an nuna wasu gungun ‘yan siyasa a wurin taron yaƙin neman zaɓe, inda aka nuna a cikin fim ɗin cewa sun tafi yaƙin neman zaɓe a wata da aka da jihar Laushi a fim ɗin. An cikin gudanar da jawabai sai aka jifar su da ruwan leda (Pure water) da takalma da duwatsu tare da yi musu ihu cewa “Ba ma yi! Ba ma yi!! Inda babu shiri suka sauka suka ranta a na kare. Daga nan sai aka nuna inda wani da aka kira shi da suna Maidawa yake magana ta waya da shugaban ƙasa daga wani gari da aka kira shi Sabon Gari, inda shi shugaban ƙasar yake nuna masa irin rashin  jin daɗinsa kan jifar da aka yi musu a garinsa (Maidawa). Inda shi Maidawa yake nuna wa Shugaban ƙasa cewa akwai wani jigon jam’iyyarsu, wanda kuma shi ne ma shugaban jam’iyyar na ƙasa da ke yi wa jam’iyyar zagon ƙasa a jihar.

Daga nan kuma an nuna inda shugaban hukumar zaɓe yake yiwa ‘yan jarida bayanin irin shirin da suka na zaɓen da ke zuwa, inda yake nuna cewa ba za su yi aiki da masu ƙarancin ilimi ba, maimakon haka za su yi aiki ne da manyan masana waɗanda suka kai matakin Farfesa, sannan kuma za su yi aiki da na’urar tantance masu jefa ƙuri’a da sauransu. An kuma ci gaba da nuna irin halin da jam’iyya mai mulki ta DPD (kamar yadda suka kira ta a fim din) take ciki tare da magoya bayanta a dukkan jihohi musamman ma jihohin Arewacin ƙasar.

Bugu da ƙari, an kuma nuna wata ganawa da jagororin jam’iyyar DPD mai alamar rumfa, ta jihar Dabo (kamar yadda suka kira ta) suka yi, inda suka riƙa tattauna irin ƙalubalen da ke gabansu a wannan kakar siyasar. Tattaunawar dai ta gudana ne tsakanin Malam da Ɗanfari da Aunty da kuma Baba Tsoho. Inda suka riƙa nuna irin fargabar da suke da ita akan irin yadda farin jinin Madugu ya bi ko’ina cikin jihar, da kuma barazanar da na’urar tantance masu jefa ƙuri’a ke yi wa nasarar lashe zaɓensu, domin kuwa babu damar yin aringizon ƙuri’u. A wani ɓangaren kuma, an nuna ‘yan ɓangaren adawa na jihar Dabo ƙarƙashin jagorancin Madugu suna tattaunawa da jagoran adawa na jihar Mai Ruwa wanda aka kira shi da suna Ɗanmeci, wanda yake ba su ƙwarin gwuiwa cewa, duk da dai matar shugaban ƙasa daga jihar Mai Ruwa ta fito kuma jama’ar jihar sun fi raja’a ga jam’iyya mai rumfa, amma dai duk da haka zai yi iyakar ƙoƙarinsa.

Haka kuma, an nuna uwargidan shugaban ƙasa tana umartar wani da aka kira Aruguje wanda kuma ya fito a matsayin minista ne a fim ɗin da cewa duk yadda zai yi ya tabbatar cewa jam’iyyarsu ta yi nasara a jihar Mai Ruwa ya tabbatar ya yi ko da kuwa hakan zai zubar masa da mutunci. Domin su tabbatar Ɗanmeci bai yi nasara ba. An kuma nuna wanda ya fito a matsayin mataimakin shugaban ƙasa tare da Maidawa na jihar Laushi, inda suke tattaunawa kan ƙalubalen da ke gabansu. Inda a cikin tattaunawar tasu Maidawa yake nuna cewa ɗantakarar jam’iyyar adawar nan fa da ake yi wa laƙabi da ‘Mai Gaskiya’ ya samu karɓuwa ƙwarai da gaske a wurin al’ummar ƙasa, yadda har ta kai ga ba shi ke ba su kuɗi ba, maimakon haka ma su ne suke tara masa kuɗin da zai yi takara. Sannan an nuna inda mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron ƙasa yake shawara da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro ta yadda za a ɓullo wa batun zaɓe, don ya lura cewa ba za su yi nasara ba. Daga bisani kuma sai aka nuna inda shuwagabannin harkokin tsaron suka gana da shugaban hukumar zaɓe kan cewa su ba su shirya ba domin kuwa ƙasa babu tsaro. Kuma ba su da jami’an tsaron da za su kula da tsaro lokacin zaɓen. Wanda tilas hakan ya sa aka ɗage zaɓen da aka shirya gudanarwa har zuwa sati shida.

An kuma nuna inda manyan masu riƙe da madafun iko suka zauna wani taro domin shawo kan matsalar da take tunkaro su, inda suka cimma matsayar cewa za su ciwo bashi daga ƙasar waje domin rabawa talakawa don su zaɓe su. Sannan za su yi amfani da kafafen watsa labarai domin ɓata abokan adawa da dai sauran batutuwan da suke ganin su ne za su kai su ga nasara, wanda suke iƙirarin samun ta ko ta halin ƙaƙa.

An kuma nuna wata jiha da aka kira Jihar Sarauniya, inda aka nuna gwamnan jihar wanda ke neman wa’adin mulki karo na biyu yana jawabi a wurin yaƙin neman zaɓe, inda yake nunawa a cikin jawabinsa cewa su ke da mulki a hannu, kuma duk wanda suka bar shi to sun ga dama ne.

Sannan an nuna inda wasu masu faɗa a ji a cikin jam’iyya mai mulki suka riƙa raba wa junansu buhunan kuɗi da sunan waɗanda za a yi amfani da su wajen yaƙin neman zaɓe. A jihar Dabo an nuna an fito da jakar kuɗi daga gidan Malam an ba wa Aunty Da Baba Tsoho domin a yi wa jam’iyya aiki.

Daga nan sai aka nuna jihar Dikko, inda nan ma aka nuna wani babban ɗan siyasa yana yi wa jama’a bayanin cewa ɗan takara na jam’iyyar adawa ya taɓa yin mulki amma bai tsinana wa al’ummarsa komai ba.  Sai kuma aka nuna jihar Ruwa inda nan ne jihar da matar shugaban ƙasa ta fito an nuna ta tana taro da mata, inda take nuna musu cewa shiyyar da ɗan takarar jam’iyyar adawa ya fito duk almajirai ne, kuma suna haihuwar ‘ya’yan da ba su san adadinsu ba, sannan su watsar da su a titi. Inda aka nuna wasu ɓangare na matan da suke halartar taron waɗanda sun fito ne daga shiyyar da ɗan takarar jam’iyyar adawa ya fito suna nuna wa a ɓoye cewa abin da matar shugaban ƙasar take faɗa a kansu bai dace ba, kuma ya sosa musu rai.

Daɗin daɗawa, an nuna inda wasu jiga-jigan jam’iyya mai mulki suke taro kan yadda al’umma suke ƙara nuna musu tsana, har suka nuna rashin jin daɗinsu ga yadda wani da suka kira shi da suna Cif ya yaga katin jam’iyyarsa da kuma kalaman da matar shugaban ƙasar ta yin na cewa suna haihuwar ‘ya’ya suna zubar da su a kan titi. A nan sai Aruguje ya kare ta da cewa ai ba ita kaɗai ce ta yi irin wannan munanan kalaman ba, ya ce ai Gwamna Lema ma ya ce wa mutanen jiharsa kyankyasai.

Daga ƙarshe dai, an nuna cewa dukkan ‘ya’yan jam’iyya mai mulki jikinsu ya yi sanyi inda suka shiga kame-kame don ba su da abin da za su iya faɗa wa shugaban ƙasa don sun kasa shawo kan al’ummarsu waɗanda suka juya musu baya.

6.0 Fim Ɗin Masu Gudu Su Gudu Da Gaskiyar Abin Da Ya Faru A Zaɓen 2015.

Kamar yadda aka riga aka sani ne, shi fim kan kasance wasan kwaikwayo ne wanda akan kwaikwayi wani ko wasu, ta hanyar nuna wata rayuwa da kan iya kasancewa ya taɓa faruwa a gaske ko kuma bai faru ba, ko kuma ma ba zai taɓa faruwa ba. Fim ɗin Masu Gudu Su Gudu ya kasance kwaikwayo ne na rayuwar siyasar da ta wanzu a shekarar 2015, wanda ba wai abubuwan sun faru, sai dai kasancewarsa wasa ne kuma kwaikwayo wannan ya sa wasu abubuwan suka saɓa da abubuwan da suka farun, amma dai an nuna kwatankwacin abubuwan da suka farun ne a gaske. Duk kusan tattaunawar da ta auku tsakanin ‘yan wasa sun faru a gaske, duk kuwa da cewa akan samu ƙari ko ragi ko ma sauyin waɗansu abubuwa, amma dai abu mafi muhimmanci shi ne a dubi irin abubuwan da suka faru wannan lokaci ta la’akari da yadda fim ɗin ya gudana.

Kamar yadda bayanai suka nuna, lokacin da yaƙin neman zaɓe ya kankama a shekarar 2015, jam’iyyu sun riƙa zagawa lungu da saƙo na ƙasar nan domin neman jama’a da ƙarin magoya baya. A wannan lokacin an nuna cewa an riƙa nuna wa jam’iyyar PDP ƙyama musamman a wasu daga cikin jihohin Arewa, inda ta kai ga har jifansu an yi da ruwan leda (pure water) da sauran abubuwa (Yusuf, 2018 : 142-143). Wannan ya yi daidai da abin da ya faru a farkon fim ɗin, inda aka nuna cewa an jefi tawagar shugaban ƙasa lokacin da yake jawabi a jihar Laushi, wanda ko tantama babu, jihar Bauchi ake nufi sai aka sakaya sunan, domin hakan ya faru da gaske a jihar ta Bauchi[1]. Wannan ya nuna irin baƙin jinin da jam’iyyar ta yi ne a wancan lokacin wanda aka nuna zahirin abin da ya faru a Bauchin duk da cewa ba a fito fili a fim ɗin an bayyana ba.

Haka kuma a cikin fim ɗin an nuna inda mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro yake magana da shugabannin tsaro cewa duk yadda za su yi su tabbatar sun yi, domin dai su samu nasara a zaɓen da ke tafe. Watakila wannan ba zai rasa nasaba da furucin da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na wancan lokaci Kanar Sambo Dasuƙi ya yi ba, na cewa ƙasa ba tsaro don haka a ɗage zaɓe sai zuwa wani lokaci. Daga bisani kuwa aka sanar da ɗage zaɓen bayan tattaunawar da shugabannin hukumomin tsaron ƙasa suka yi da shugaban hukaumar zaɓe mai zaman kanta (INEC)[2]. A cikin wannan fim ɗin ma an nuna inda shugabannin hukumomin tsaron suka zauna da shugaban hukumar zaɓe, har daga ƙarshe aka yanke shawarar ɗaga zaɓe zuwa sati shida.

Wani abu kuma da aka nuna a cikin wasan wanda babu tantama ya faru a gaske shi ne, an nuna wani gwamna da ke neman wa’adin mulki karo na biyu wanda aka kira shi da Gwamna Yaro, wanda ya yi amfani da kausasan kalamai lokacin da yake jawabi a wurin yaƙin neman zaɓe. Dubi abin da ya ce:

“Jama’a ina so in tabbatar muku da cewa, idan mutum uwarsa ta haife shi da jini, idan mun fito ya jefe mu. Idan mutum uwarsa ta haife shi da jini, idan mun fito ya tare, ya ga yadda ake rashin kunya….” (Masu Gudu Su Gudu 2).

Idan aka dubi wannan za a ga cewa ya faru a gaske, domin kuwa muryar gwamna Mukhtar Ramalan Yero ya yi ta yawo a kafafen sadarwa ta intanet waɗanda ke ƙunshe da waɗannan kalaman[3].

Haka kuma akwai batun da aka yi ta yayatawa na cewa uwargidan shugaba tsohon shugaban ƙasa Jonathan ta faɗi miyagun kalamai kan ‘yan Arewa, inda ta kira su ‘almajirai’ waɗanda suke haihuwa babu adadi, sannan su jefar da ‘ya’yansu a kan titi suna barace-barace. Tabbas! Jaridun ƙasar nan da dama sun ruwaito wannan labarin[4]. Ke nan, an yi amfani da gaskiyar abin da ya faru ne aka tayar da zubin labarin fim.

Bugu da ƙari, duk da dai tattaunawa ce kaɗai aka nuna cewa wani da aka kira Cif ya yaga katin shaidar jam’iyyarsa, wato babu wanda ya fito a matsayin Cif ɗin, amma duk da haka za a fahimci cewa ba kowa ne Cif ɗin da suka ambata ba illa tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo. Domin kuwa an bayyana cewa ya fito fili ya yaga katin jam’iyyarsa ta PDP bayan ya ayyana ficewarsa daga jam’iyyar[5]. Haka kuma an nuna wani minister a fim ɗin yana baiwa uwargidan tsohon shugaban ƙasa Jonathan kariya cewa ai doon ta ce wa ‘yan Arewa almajirai ba ta yi laifi ba tun da ɗan yankinsu ma ya ce musu kyankyasai. Batun kyankyasai kuwa idan aka duba za a ga cewa gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema ne ya kira magoya bayan jam’iyyar adawa da kyankyasai, kuma ya ce duk inda aka gan su a buge su[6].

Idan aka dubi hujjojin da aka kawo kan waɗannan bayanan za a ga cewa, dukkan waɗannan nan abubuwan sun faru, kawai dai an yi amfani da wasan  kwaikwayo ne wajen taskace abubuwan ta yadda za su kasance cikin rumbun tarihin siyasa a cikin adabin Hausa.

Tun da ya kasance kwaikwayo ne kamar yadda muka ambata, to su wa aka kwaikwaya?

7.0 Wa Aka Kwaikwaya A Fim Ɗin Masu Gudu Su Gudu?

A wannan bagiren za mu dubi irin yadda aka yi amfani da fim ne wajen kwaikwayo don nuna wasu abubuwa da suka faru a zahiri, wato za mu duba mu ga ko su wa aka kwaikwaya ne a zahiri ta hanyar la’akari da bayanan abubuwan da suka faru, waɗanda kuma an kawo su a baya. Za mu dubi sunayen mutane da na jihohi da aka yi amfani da su a cikin fim ɗin, ta hanyar danganta su da irin rawar da masu sunayen suka taka da kuma garuruwan da abubuwan suka faru. Domin ganin yadda gaskiyar lamarin yake za mu yi amfani da jadawali kamar haka:

Sunan Jiha a Fim

Jihar  Da Aka Kwaikwaya

Dalilan Da Suka Tabbatar Da Haka

Jihar Laushi

Jihar Bauchi

Sunan jihar da aka yi amfani da shi a fim ɗin ya yi kusa da sunan jihar na gaske wajen furuci. Haka kuma, ita ce jihar da aka fara nuna cewa an jefi tawagar shugaban ƙasa lokacin da suka je yaƙin neman zaɓe. An kuma nuna wani da aka kira Maidawa wanda ake nufin Sanata Bala Muhammad (Ƙauran Bauchi) ne, ministan babban birnin tarayya Abuja.

Jihar Dabo

Jihar Kano

Jihar kano ita ce ake ce wa Kanon Dabo. Ana kuma yi mata kirari da “Ta Dabo tumbin giwa…”. Kuma wasu daga cikin ‘yan siyasar da aka nuna a fim ɗin a cikin wannan jihar, suna sanye ne da jajayen huluna. Kuma an yi amfani da sunaye irin su; Madugu ( Rabiu Kwankwaso) Malam (Malam Ibrahim Shekarau) Baba Tsoho (Tanko Yakasai) Aunty (Sanata Baraka) da sauransu.

Jihar Sarauniya

Jihar Kaduna

Idan aka yi la’akari da kalaman gwamnan Jihar Sarauniya lokacin yaƙin neman zaɓe, za a gane cewa gwamnan jihar Kaduna ake kwaikwayo. An kira jihar da jihar Sarauniya ne domin Sarauniya Amina da aka ce wai ta taɓa yin sarautar ƙasar Zazzau. Sannan an kira gwamnan da suna Yaro wanda ke nufin Ramalan Yero, duk wannan zai nuna cewa siyasar jihar Kaduna na wancan lokaci ne aka nuna.

Jihar Dikko

Jihar Katsina

Katsina ta Dikko ɗakin kara. Wannan shi ne kirarin da ake yi wa jihar. Ke nan kiran ta da Jihar Dikko wata alama ce da nuna Katsinan dai ake nufi. Ba ma wannan ba, abubuwan da aka nuna cewa sun faru a jihar kamar bayanin ɗan takarar gwamnan jihar da ya kira ‘yan jam’iyyar adawa da kyankyasai kuma ya ce in an gan su a buge su. Wannan ya ƙara tabbatarwa.

Sabon Gari

Babban Birnin Tarayya Abuja

Domin a nan ne aka nuna shugaban ƙasa (Mainasara) da kuma wasu makusantansa suna tattaunawa.

Jihar Ruwa

Jihar Riɓers

An nuna matar Shugaban ƙasa tana ganawa da minista mai suna Aruguje (Godsday Orubebe) inda ta nuna masa cewa duk yadda zai yi ya tabbatar cewa jam’iyyarsu ta samu nasara a jiharta ta haihuwa wadda ba wai jihar Riɓers ce.

Ke nan idan aka duba za a ga cewa wannan fim ɗin ya kwaikwayi wata irin rayuwar siyasa ce da ta gudana a shekarar 2015, duk kuwa da cewa akwai ƙarin gishiri a waɗansu ɓangarori na fim ɗin, wannan za a iya cewa an sanya ne kawai don dai a samar da nishaɗi ga masu kallo wanda yana daya daga cikin ruhin fina-finan.

8.0 Sakamakon Bincike

Kasancewar siyasa tamkar abu ne mai rai, wanda kuma ke ci gaba da rayuwa daga wani zamani zuwa wani. Wannan ya sa a kusan dukkan fannoni na rayuwa ba a rasa ta. Sakamakon wannan bincike ya nu na cewa fina-finan Hausa sun kasance wani rumbu ne na adana tarihin siyasa, ba ma a ƙasar Hausa kaɗai ba, har da ma Nijeriya baki ɗaya.

Wannann nazarin ya gano cewa ana iya samun hoton ainihin abin da ya wakana a fagen siyasar al’umma a cikin wani zamani, idan aka dubi ƙunshiyar fina-finansu.

Nazarin ya kuma gano cewa za a iya shirya fina-finai kan abubuwa masu muhimmanci na rayuwa waɗanda za a iya dubansu nan gaba a matsayin wanin kundin tarihin al’umma. Domin idan aka dubi abin da ya faru na zaɓen 2015 za a iya cewa fim ɗin ya adana wasu muhimman abubuwan da tarihin siyasar Nijeriya ba zai manta da su ba.

9.0 Kammalawa

Wannan bincike ya shafi tarihin siyasa ne a fina-finan Hausa. Inda aka yi ƙoƙarin nazarin da wasu muhimman abubuwan da suka faru a kakar zaɓen shekarar 2015. Kasancewar nazarin ya shafi fim ɗin Hausa ne, wannan ya sat un da farko sai da aka kawo bayanai kam fim da samuwarsa a ƙasar Hausa. Sannan aka kawo dangantakar siyasa da adabin Hausa, wanda shi ne ya share mana fagen lalubo dangantakar da ke tsakanin fina-finafinan Hausa da siyasa. A ƙarshe, takardar ta yi nazari ne kan ƙunshiyar tarihi siyasa a fim ɗin Masu Gudu Su Gudu na daga abin da ya faru a kakar babban zaɓen ƙasa da aka gudanar a shekarar 2015, tare da kwatanta shi da gaskiyar abin da ya faru a lokacin. An yi ƙoƙarin kafa ƙwararan hujjoji daga bayanai masu tushe domin tabbatar da gaskiyar abubuwan da suka faru.



[1] Dubi jaridar Premium Times ta ranar Alhamis, 22/01/2015, a wannan adireshin https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/175443-youth-attack-jonathan-in-bauchi.html

Dubi Jaridar The Nation ta ranar Juma’a 23/01/2015 a wannan adireshin

 http://thenationonlineng.net/jonathans-conɓoy-stoned-bauchi/

[2] Dubi Ɓanguard ta ranar 09/02/2015 a wannan adireshin https://www.ɓanguardngr.com/2015/02/inecs-postponement-2015-elections/

[5]Shiga wannan adireshin domin ganin  yadda obasanjo ya yaga katinsa na jam’iyyar PDP http://www.nigerianmonitor.com/ɓideo-obasanjo-tearing-his-pdp-membership-card/

Dubi jaridar Ɓanguard ta rana 17/02/2015 a wannan adireshin https://www.ɓanguardngr.com/2015/02/tore-my-pdp-membership-card-obasanjo/

Post a Comment

0 Comments