Ticker

6/recent/ticker-posts

Marubuci Dan Baiwa: Rubutu Da Marubuci A Fuskar Masu Mulki Da Al’umma

Takardar Da Aka Gabatar A Wurin Bikin Karrama Haziƙan Marubutan Da Suka Samu Nasarar Lashe Gasar Marubuta A Matakai Daban-daban, Wanda Ƙungiyar Marubuta Littattafan Hausa, Wato Hausa Authors Forum, Reshen Jihar Kano Ta Shirya, Ranar Lahadi 29 Ga Watan Disamba, 2019, A Ɗakin Taro  Na Laburaren Jihar Kano.

rubutu

Marubuci Ɗan Baiwa: Rubutu Da Marubuci A Fuskar Masu Mulki Da Al’umma

 

NA

Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya)

Shugaban Ƙungiyar Inuwar Marubuta ta Jihar Yobe (Yobe Authors Forum),  Nguru Writers’ Association of Nigeria (NWAN).

07066366586, 08125351694.

Instagram: ibrahimgarbanayaya

E-mail: ibrahimba182@gmail.com

1.0 Gabatarwa

Babban abin da yake jagorantar rubuce-rubucen littattafan Hausa ita ce fasaha, domin da ita ce marubuta suka bambanta da sauran gama-garin jama’a. Tare da wannan fasahar tasu, sukan samu matsaya mabambanta a wurin jama’a, kowa da irin kallon da yake musu. Amma rubutu, abu ne da yake fito da kyawun al’umma ta zama tamkar fuskar kyakkyawar budurwar da take da dogon hanci da idanu farare abin so ga kowa. Haka rubutun marubuta yake a tsakankanin al’umma, wannan sai ya sanya marubutan sun samu ƙauna da soyayyar al’umma. Babu yadda za a yi rayuwa ta yi wa kowa daidai yadda yake so, wannan ya sanya a gefe guda za a ga akwai masu nuna ƙiyayya ga marubuta, wannan kuma shi ke sanya rayuwa ta yi kyau; amma ga wanda ya fahimce ta.    

2.0 Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Littattafan Ƙagaggun Labarai Na Hausa

          Tarihin kagaggun littattafai bai daɗe ba sosai idan aka kwatanta da tarihin samuwar wakokin baka da kuma rubutattu. Waƙoƙi sun samu kulawa tun shigowar Musulunci ƙasar Hausa, da yake an yi amfani da su wajen yaɗa addinin Musulunci, su kuwa ƙagaggun lattattafai sai bayan da Turawa suka shigo ƙasashenmu na Afrika ta Yamma ne suka fara samuwa.

          Yawancin rubuce-rubucen da Turawa suka yi ba na ƙagaggun littattafai ba ne. Littafin da Schon J.F. ya rubuta mai suna Farawa Letafen Magana Hausa, shi ne littafin Hausa na farko na zube cikin boko, kuma duk rubuce-rubucen da Turawan suka yi babu wanda ya yi kama da ƙagaggun labarai wato Noɓel, sai dai a bugun ƙarshe a shekarar 1886, ya tabo tatsuniyoyi. Kuma yawancin littattafan na yaɗa addinin Kiristanci ne.

           Amma rubuce-rubucen zube na ‘yan ƙasa ya samo asali ne sakamakon kafa Hukumar Talifi ta Arewa (Northern Literature) a shekarar 1933, inda ta sa gasar rubuce-rubuce ga ‘yan Ƙasa, inda suka samar da littattafai guda shida kamar haka:

1. Ruwan Bagaja na Abubakar Imam 1935

2. Gandoki na Bello Kagara 1935

3. Jiki Magayi na Tafida Umar da Dr. R.M. East 1935.

4. Idon Matambayi na Muhammadu Gwarzo 1935.

5. Shehu Umar na Abubakar Tafawa Balewa 1935.

6. Iliya Danmaikarfi na Ahmadu Ingawa. 1968. (Gidan Dabino, 2010:2-3).

           Bayan samar da waɗancan wallafe-wallafe a mataki na farko na ‘yan ƙasa, an ci gaba da samun wasu, musamman ta hanyar hukumomin da aka rinƙa kakkafawa da kuma kamfanoni har zuwa wajajen shekarar 1980, wato lokacin da aka fara samun ɓulluwar wani salo na rubuce-rubucen littattafan ƙagaggun labarai, saboda dalilai na sauyin zamani da ɓulluwar baƙin al’adu da kayan zamani zuwa ƙasar Hausa. (Nayaya, 2019:2).

            An samu maganganu da dama daga masana daban-daban game da samuwar Adabin Kasuwar Kano, ko kuma sajewar littattafan Hausa zuwa ga komawa ga abin da Malumfashi (1984) ya kira da Adabin Kasuwar Kano. Amma a taƙaice, ga abin da Mukhtar (2010:21) ya bayyana, “A cikin shekarar 1984 ne wata al'adar rubuce-rubuce ta ƙagaggun littattafai ta kunno kai wadda aka sa wa suna Adabin Kasuwar Kano, a Turance " Kano Market Literature". An sami wani jigo na soyayya inda ya yi tasiri sosai da sosai cikin wannan adabin. Daga cikin waɗanda suka share fage akwai irinsu:

          -Rabin Raina, littafi na ɗaya (1984) na Talatu Wada Ahmad

          -Soyayya Gamon Jini (1986) na Ibrahim Hamza Abdullahi.

          -In Da Rai (1987) na Idris ImamImam.

          - Buduwar Zuciya (1987) na Balaraba Ramat Yakubu.

          -Kogin Soyayya (1988) na A M. Zahraddeen.

          -Idan So Cuta Ne (l989) na Yusuf M. Adamu”.

            Daga cikin abin da ya gabata, za mu fahimci Adabin Kasuwar Kano ba wata gamammiyar ƙungiya ba ce ko wata hukuma da aka yi taro aka sanya mata wannan suna, sunan ya biyo bayan la'akari da Adabin Kasuwanni makamantansa ne ya samar da shi, wannan ya sanya Malumfashi (1994) da ya kira shi da wannan suna. Kuma shi Malumfashin ya yi haka ne daga abin da ya gani masu kama da juna tsakanin littattafan da irin waɗanda aka samar a Kasuwar Onisha wanda ake kira Adabin Kasuwar Onitsha, kuma irin haka ne ga abin da ya wakana ga abin da ake kira da Adabin Elizerbert da na Kitsh na Jamus. (Nayaya, 2018:55).

2.1 Wane ne Marubuci?

            Masana sun bayyana ma’anar marubuci ta fuskoki mabambanta, misali: Wikipedia ta bayyana cewa, "Marubuci shi ne wanda yake amfani da rubuta kalmomi ta hanyar mabambantan salo da dabara domin sadarwa ta hanyar hikimarsu". A wani wurin kuma, ta bayyana da cewa, "Marubuci shi ne mai shirya mabambanta ayyukan adabi da rubutun hikayoyi kamar rubutattun labaru, gajerun labarai, tatsuniyoyi, wasanni, tsara labarai, insha'i da kuma rahotanni da labarai, da muƙalu waɗanda suka yi dai-dai da ra'ayin jama'a. Rubutun marubuta ana buga shi a ɗaukacin wuraren watsa labarai".

            Collins English Dictionary ta bayyana da cewa, "Marubuci shi ne wanda yake rubuta littattafai, labarai, da muƙalu a matsayin aiki".

            Kafar yaɗa bayanai ta Difference Between ta bayyana marubuci da "Shi ne wanda yake rubuta littafi, muƙala, da kuma dukkanin aikin adabi".

            Shi kuwa Gidan Dabino (2006)  ya bayyana marubuci da, "Marubuci shi ne wanda ta hanyar amfani da fasahar rubutu yakan ƙirƙiri wani yanayi na gaske ko na almara ko tunani ya kuma yi amfani da shi don gina wasu mutane da abubuwa wadanda yake amfani da su don isar da sako ga al'ummar da ke karatun rubutunsa. Shi wannan sako ana tsara shi ne ta hanya ta musamman mai cike da hikima da hazaka don isarwa a saukake, kamar ta hanyar yin amfani da haruffa zuwa kalmomi zuwa jimloli zuwa siɗarori da shafuka har zuwa cikakken littafi".

            Nayaya (2018:53), wajen taƙaita waɗannan ma’anonin, sai ya ce, “Marubuta su ne ire-iren mutanen da suke sarrafa fasaharsu wajen ƙago ko gyara wani labari da ya afku ko ake jin zai iya afkuwa a rayuwar jama’a, domin faɗakarwa da yin hannunka mai sanda, shin su ɗin za su samu wani abu ne ko a’a”.

2.2 Wasu Cikin Marubuta Litattafan Hausa

             Baya ga bayanan da suka gabata, yana da kyau a bayyana wasu cikin marubuta littattakan Hausa a matsayin misali. Daga cikin marubuta akwai:

-Ado Ahmad Gidan Dabino                    - Ɗan Azumi Baba

-Bilkisu Ibrahim Nabature                      -Fauziyya D. Suleiman

-Ruƙayya Abdullahi Dangado                -Kabir Yusuf Fagge Anka

-Maimuna Idriss Sani Beli                       -Ayuba Muhammad Ɗanzaki

-Abubakar Auyo                                       -Hadiza Nuhu Gudaji

-Amina Dauda Abubakar                         -Naja'atu Haruna Saleh

-Maryam Kabir Mashi                              -Jiddah Haulat Nguru

-Maryam Rabi'u Ado                                  -Muhammad Lawal Barista

-Sadiya Garba Yakasai              -A'isha Abdullahi Bagwanje, da dai sauransu.

            Wani abin la’akari, mafi yawan marubuta littattafan ƙagaggun labarai na Hausa, ba Hausa suka karanta ba, ƙila ma ba su haɗa layi da darasin day a shafi Hausa ba, walau a babbar sakandare har zuwa manyan makarantu. Misalai na nan da dama, daga ciki: Marubucin littafin Idan So Cuta Ne, wato Farfesa Yusuf M. Adamu malamin Nazarin Labarun Ƙasa ne (Geography), Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, (Mass Commuhaka abin yake har zuwa yanzu wanda ga misali nan a nan gabanmu ga wadda ta samu nasarar zuwa ta ɗaya.    

2.3 Misalan Littattafan Ƙagaggun Labarai Na Hausa

Nayaya da Baba (2018:54) sun haƙaito ire-iren littattafan ƙagaggun labarai na Hausa, cikin waɗannan litattafan akwai:

i.          In da Alƙawari (1992) na Bala Anas Babinlata.

ii.         Duniya Sai Sannu (1997) na Ado Ahmad Gidan Dabino, MON.

iii.       Mafarkin Khadija (2014) na Maimuna Idriss Sani Beli.

iɓ.        Rayuwar Bilkisu (2016) na Ayuba Muhammad Ɗanzaki.

ɓ.         Firgita Samari (2005) na Kabir Yusuf Anka.

ɓii.       Amon ‘Yanci (2013) Halima Ahmad Matazu.

ɓiii.     Jarrabi (2014) na Abubakar Auyo.

ɗ.         Me Zan Yi Da Ke (2016) na Maryam Rabi’u Ado.

ɗi.        Marubuciya (2019) na Jiddah Haulat Nguru.

ɗiii.     Rumaisa (2014) na Fauziyya D. Suleiman.

ɗiɓ.      Adon Dawa (2011) na Jamila Umar Tanko.        

3.0 Marubuta A Idon Masu Mulki Da Al’umma

              Marubuta wasu keɓantattun mutane ne da suke rayuwa a tsakankanin al’umma suna masu hidimta wa al’umma ta hanyar sarrafa basira da hikima gami da fasahar da Alllah huwace musu. Har wa yau, ta wannan hanya ce suke taimakon kansu da taimakon al’umma wajen wasu ɗawainiyar da suka shafi kuɗi. Saboda wannan muhimmanci nasu, sai ya kasance suna da matsaya a idanun al’umma, sawa’un masu mulki ne ko kuwa ɗaiɗaikun mutane ne cikin masana da ɗalibai da sauran gama-garin mutane cikin masu karanta littattafan marubuta. 

3.1 Marubuta A Idon Masu Mulki

           Masu mulki a nan, sun ƙunshi dukkanin ayarin da suke riƙe da madafun iko; musamman a ƙololuwa, wato jagorancin jama’a. Waɗannan rukuni na mutane sun ɗauki marubuta da muhimmanci dubi da yadda suke karrama ɗaiɗaikunsu da lambobin yabo da kambunan girmamawa. Har wa yau, waɗannan mutane sukan bai wa marubuta dukkanin gudumawar da suka nema domin gabatar da muhimman taruka na marubuta. Tare da wannan muhimmanci nasu, sukan samu wasu matsaloli na rashin kyakkyawan tallafi wajen yin ɗab’in littattafansu, hakan ya sanya ake samun yawaitar waɗannan littattafai suna yawo a soshiyal mediya, domin ba a samu an buga su an fitar da su kasuwa ba. Ke nan, idan dad a masu mulki za su ware wani ofishi domin yin wannan aiki, da harkar rubuce-rubuce za ta ƙara ɗaukaka.

           A taƙaice dai, marubuta littattafan Hausa suna da wata daraja ta musamman a idanun shugabanni, domin ƙoƙarinsu na seta rayuwar al’umma da ɗora ta a kan tsari mai kyau.   

3.2 Marubuta A Fuskar Al’umma

           Al’umma a nan, na nufin dukkanin jama’a, musamman masu karanta littattafan Hausa da waɗanda ake karanta musu da waɗanda suke kallon masu karatun. A wannan ɓangare akwai matsaya guda uku:

i. Waɗanda ke karanta litattatafan Hausa kuma suke samun nishaɗantuwa daga littattafan. Ire-iren waɗannan mafi yawa ‘yan mata ne masu shekarun tsaka-tsaki, sai matan auren da ba su jima a gidajen aure ba, sai kuma manyan mata; wato matan alhazai ko kuma hajiyoyi. Galibi irin waɗannan mataye sun yi nutso cikin karance-karancen waɗannan litattafai, wannan ta sanya lokacin da guguwar karanta littattafanan Hausa ta kunno kai a wasu gidajen radiyo a ƙasar Kano, suka mayar da hankali wajen sauraron radiyo, har ma ɗalibai mata sukan tafi makarantunsu da ƙaramar radiyo ko waya domin sauraren wannan shiri na karatun littattafan Hausa.

         Don haka a wurin waɗannan makaranta, marubuta na da matuƙar daraja da ƙima a idanunsu, har ma suna ganin daina yin rubuce-rubuce kan iya jefa su cikin wani kogin dab a zai ɓulle da su ba. Idan kuwa wata musifa ta samu wani/wata marubuci/marubuciya, sukan damu matuƙa, har ma su ji kamar su abin ya sama. Yayin da suke matuƙar jin daɗi da farin ciki a duk lokacin da abin farin ciki ya samu marubuta.

ii. Kaso na biyu, su ne masu karantawa idan sun samu, a gefe guda kuma suna ganin baiken marubutan. Don haka, marubuci kan iya zama mai daraja a idanunsu, a wani lokaci kuma ya zama akasin haka. Irin waɗannan mutane, ba su da wata alƙibla guda ɗaya da suke kan ta. Su dai idan sun samu su karanta, su yaba, ko su kushe. Ba kasafai suka fiye damuwa da halin da marubuta ke ciki ba, walau mai kyau ne ko akasin haka.

iii. Wannan kaso, su ne waɗanda kwata-kwata sun tsani marubuta, ba sa son su ji ko ganin ayyukan marubuta, domin sun ɗauki harkar ɗab’i a matsayin shiririta da ɗirkaniya da rashin aikin yi. Irin waɗannan nan, ba su da wani aiki face zagi da kushe ga marubuta a kowane lokaci.

3.3 Marubuta A Idon Malamai, Manazarta Da Ɗalibai

          Malamai su ne masu sanya ɗalibai yin nazarin ayyukan marubuta, sawa’un su umarce su domin su ciro wani kuskure ne, ko kuma su zaƙulo wani darasi ne da ke cikin littafin ko kuma su waiwaici matsala ta ƙa’idojin rubutu. Haka zalika manazarta, aikinsu ne nazartar ayyukan marubuta tare da sanya su a ma’aunai daban-daban. Manazarci kan iya zaƙulo matsala a cikin littafi amma ba lalle ya iya kawo mafita daga wannan matsala ba, domin wannan aiki sai wanda ya rubuta.

          Ɗalibai kuwa, su ne masu tsayuwa wajen nazartar waɗannan ayyuka na marubuta, hakan kuwa ba zai yiwu ba; har sai sun tattauna da marubutan, domin mafi yawan nazari ba ya yiwuwa da littafi kawai, dole sai an nemi marubucin littafin.

          A wurin waɗannan ayari na masana, marubuta na da muhimmiyar gudumawa acikin rayuwar al’umma, domin ta fuskar nazarin nasu ne suke zaƙulo wasu sabbin ilimin da su kansu marubutan ba su san as u ba. Don haka, su ma sukan bibiyi rayuwar marubuta da son farin cikinsu, da kuma damuwa da damuwarsu.              

5.0 Kammalawa

           Kamar yadda waɗannan bayanai bayanai suka gabata, babu tantama marubuta na da muhimmiyar rawa a cikin rayuwar al’umma. Ke nan, kafa ofis domin ƙoƙarin tafiyar da ayyukansu a gwamnatance abu ne da zai ƙara gyara wannan harka. Sannan jami’o’i su zama mahaɗa ta waɗannan marubuta domin tattauna batutuwan da suke addabar ƙasa gami da fitar da rubuce-rubucen da suka fi dacewa da zamani. Misali, a irin wannan zamani, rubuce-rubucen da suka shafi haɗin kan ‘yan ƙasa, zaɓar shugabanni ba domin kuɗi ba, sanya kishin gari da yare da addini da al’adu, matsalolin shaye-shaye da barace-barace (duk da an yi rubuce-rubuce a kai) rubutu ne da zai taimaki al’umma. Idan muka kalli al’amari na jagoranci da siyasa, da ilimin matasa da zaman kash-wando, da bangar siyasa, akwai buƙatar a samar da sabbi wallafe-wallafe waɗanda suka fi dacewa da wannan zamani da irin alƙiblar da al’umma ke kai. Har wa yau, malamai a manyan makarantu har ma da sakandare su mayar da hankali wajen sanya ɗalibai nazartar ire-iren waɗannan wallafe-wallafe, da kuma gabatar da jawaban fiɗar waɗannan litattafan a taruka mabambanta.

Manazarta

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments