Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa karo na huɗu da Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato ta shirya a kan Daular Zamfara. Wanda aka gudanar a ƙarƙashin jagorancin Farfesa A.H. Amfani a Zauren Lacca na Tsangayar Fasaha da ke Jami’ar, a ranar 26-2-2020.
Masarautar Bakura A Daular Zamfara
Dr.
Adamu rabi’u bakura
08064893336
TSAKURE
Sanin abubuwan da suka shuɗe ta kowace fuskar rayuwar ɗan Adam yana da muhimmancin gaske. Wannan ne ya sa masana tarihi ke iƙirarin cewa duk wanda
bai san abin da ya faru kafin haihuwarsa ba, zai zama tamkar jinjiri har abada.
Domin zai kasance da ilimin abin da ya sani ko ya gani, ba tare da fahimtar
musabbabin wanzuwarsa ba. Tarihi yakan ɗauki fuskoki mabambanta kamar na ƙasa ko al’umma ko addini ko managartan magabata da taƙadirai. A waɗannan fannona, tarihi yana amfani wajen ilmantar da
al’umma yanayin cikin da jiya ta ɗauka, domin sanin abin da gobe za ta haifa da kuma daraja ko ƙasƙancin abin da aka haifa zai samu a
cikin rayuwa. Ganin an yi wa tarihin wasu al’ummomi riƙon sakainar kashi a farfajiyar ƙasar Hausa, alhali kuwa
irin waɗannan al’ummomi ne suka aza
harsashen abubuwan alheri da ‘yan baya suka riska har suka kasance suna cin
moriyarsa. Dalilin haka ne wannan maƙalar ta ƙuduri aniyar kawo bayanai game da asali da ma’anar kalmar
Bakura da yanayin ƙasar da iyakokinta da asalin mutanenta tare da bin diddigin asalin sunan
masarautar da al’ummarta. Za a kuma zo da abubuwan da suka taimaka wajen bunƙasar masarautar da
sarakunanta da dangantakarsu da masu masaukinsu.
1.0 Gabatarwa
Taskace tarihin kowace al’umma abu ne
wanda ya wajaba a wuyan ‘yan asalin al’ummar, matuƙar sun mallaki ilimin
karatu da rubutu1. Sau tari ta hanyar rubutun ce ake adana tarihin
al’ummomin daban-daban don kare tarihin daga gurbacewa. Duk da haka al’umma kan
zaɓi wasu rukunin
al’umma da aka tabbatar da suna da kaifin basirar kiyaye abubuwan da suka ke
wanzuwa a tsakanin al’umma, a ɗora musu alhakin taskace su cikin ƙwaƙwalwarsu maganin ko
taka taso a sakamakon salwantar kundin tarihin al’ummar saboda ta’adin gobara
ko harin yaƙi ko ambaliyar ruwan sama2. Zuwan Turawa ƙasar Hausa wanda ya haifar
da yaƙe-yaƙe, ya zama sanadin salwantar kundayen
tarihin wasu al’ummomi, musamman Musulmi. Wasu kayan Turawan Mulkin Mallaka ne
suka kwashe su, su kai ƙasar Turai, musamman waɗanda aka taskace cikin harshen Larabci
da rubutun ajami. Abin da ya rage gun ‘yan ƙasa sai waɗanda ke taskace a ka
da abubuwan da Turawan suka rubuta domin biyan wasu buƙatun kansu. Domin ƙoƙarin adana ɗan abin da ke cikin ƙwaƙwalwar fasihan
magabata, wannan takarda ta yi ƙoƙarin kawo taƙaitaccen tarihin
wannan al’umma, kamar yadda aka ambata a cikin tsakuren da ya gabata a
sama.
2.0 Bakura: Asalin
Kalmar da Ma’anarta
Akwai ra’ayoyi da dama dangane da
asalin samuwar wannan suna na Bakura. Sai dai kowane ra’ayi da aka bayyana za a
tarar cewa, masu ra’ayin sun yi ƙoƙarin bayyana hujjar
da za ta iya tabbatar da nasu ra’ayi. Daga cikin irin waɗannan ra’ayoyi akwai
wanda ke nuna cewa, an samo asalin sunan “Bakura” daga sunan wanda ya kafa
garin, kuma shugaban Ɓurmawa na farko mai suna Muhammadu Kura, wanda Turawan
Faransa suka yi wa laƙabi da mayaƙi wato ‘WARRIOR’.
An nuna cewa sunan Bakura ya samo
asali ne a yayin da jama’ar Muhammadu Kura ke ƙoƙarin bayyana
rasuwarsa, sai suka ce, “Ba Kura” a madadin su ce, “Kura ya mutu ko ya rasu”.
Masu wannan ra’ayi sun bayyana cewa daga waɗannan kalmomi ne guda biyu aka haɗe suka koma kalma ɗaya wato “Bakura”,
wadda aka yi amfani da ita aka laƙaba wa mazaunin
Muhammadu Kura, kamar yadda Bunu (2003) da Muhammad (1988:16) suka bayyana.
Idan aka dubi wannan ra’ayi za a ga
ya sami gindin zama ta la’akari da al’adar ƙasar Hausa a inda akan yi amfani da
kalmar girmamawa da nuna tausayi ga duk wani babban mutum da Allah ya yi wa
cikawa. Domin
a kunnen ɗan ƙasar Hausa da ya ji
an ce: “ Wane ya mutu” zai ɗauki an nuna hutsanci da rashin ladabi da rashin nuna
tausayi ko damuwa, musamman ma idan wanda Allah ya yi wa rasuwa shugaban jama’a
ne.
A wani ra’ayi na daban kuma an
bayyana cewa, sunan Bakura ya samo asali ne daga sunan wani mafarauci da ake
kira “BAKKU”, kamar yadda Harris (1938:93) da Johnson (1953:3) da Malam Yahya
(2003) suka bayyan. Masu wannan ra’ayi sun nuna cewa, “an samo wannan suna ne a
lokacin da Ɓurmawa suka yi ƙaura daga Tukunawa3,
suka dawo mazaunin da garin yake a halin yanzu. A nan ne suka sami mafaraucin
da ake kira “Bakku”, wanda ke zaune kusa da hanyar da Fulani ke wucewa in za su
je mashayar dabbobi. An ce a duk lokacin da za su ɗaukar ruwa, sukan ce,
“Ra – Bakku”, wato “ga Bakku”. An ce daga nan sai kalmomin suka yi musayar
gurbin wurin zama, sai suka dawo “Bakku – Ra”. Daga baya sai aka haɗe kalmomin guda biyu
tare da shafe harafin “K” da aka ɗaura a gaɓar farko Bak, sai ta dawo “Ba+ku+ra”,
daga nan sai aka sami sunan “Bakura” da ake kiran wannan ƙasa ta Ɓurmawa da shi.
Yayin da a wani ra’ayi aka nuna
cewa, sunan “Bakura” ya samo asali ne, alokacin da aka fara kafa mazaunin da
Bakura take, a inda ake son a bayyana wa sauran jama’a cewa wurin lafiyayye ne
ba ya da kuraye, sai aka ce “Ba kura”, kamar yadda Marafa Alh. Bello Yusuf III
(2003) ya bayyana. An ce daga waɗannan kalmomi ne guda biyu aka haɗe suka zama “Bakura”.
Masu wannan ra’ayin sun nuna cewa, kafin a kafa garin a wannan wurin, ya
kasance mai yawan kuraye. Amma a yayin da al’umma suka soma kai musu farmaki,
suna farautarsu, sai duk kurayen suka watse. Don haka, a wajen ƙoƙarin nuna sun watse
ba sauran da suka rage, shi aka taƙaita aka ce “Ba
kura”, wanda daga waɗannan kalmomi ne aka
game su waje ɗaya suka bayar da
asalin sunan garin “Bakura”.
Ta kowane irin hali dai za a iya
fahimtar cewa, an kafa wannan gari mai albarka tun wajen farkon ƙarni na goma sha
bakwai (ƙ.17). Kuma sunan garin ya samo asali ne tun daga wancan
lokacin.
3.0 Yanayin Ƙasar Bakura Da
Iyakokinta
Kasancewar Allah ya yi mutanen
wannan ƙasa zarumai ne, shi ya haifar da maƙwabtansu na kusa da
na nesa suke yi wa wannan gari kirari da cewa:
Bakura garin Jandamo
Garin Na-abu da Ɗankwai
Garin da ba a haihuwar ɗa raggo.
Garin Bakura na ɗaya daga cikin manyan
garuruwa masu cikakken tarihi da aka kafa a farfajiyar Daular Zamfara, ya kuma
kasance cikin jahar Zamfara ta yanzu. Yana tsakanin Sakkwato da Talata Mafara,
kimanin nisan kilomita 105 ne daga Sakkwato zuwa Bakura. Daga Gabas ta yi iyaka
da Ruwan Gizo da ke cikin ƙasar Talata Mafara. Daga Arewa kuwa ta
yi iyaka da ƙasar Gandi. Ta yi iyaka da ƙasar Rara ta wajen
Yamma, sannan ta yi iyaka da ƙasar Anka ta ɓangaren Kudu, a inda
ta gangara ta faɗaɗa har ta kai Gulbin
Rangam. Yayin da a Kudu Maso-Yamma ta yi iyaka da Tureta.
Yamma arewa gabas Zahirin Taswira Ƙasar Bakura (gamers,
Aug 11,2018).
Taswirar
Jahar Zamfara, Nijeriya
Garin Bakura na ɗaya daga cikin manyan
gundumomin Zamfara guda goma sha huɗu da suka haɗu suka yi yankin Sakkwato ta Gabas a
lokacin mulkin mallaka. A wannan zamani kuwa tana ɗaya daga cikin manyan
masarautun jahar Zamfara masu daraja ta farko.
Ƙasar Bakura, ƙasa ce shimfiɗaɗɗiya wadda take kan
tudu. Ba ta da yawan kwazazzabai, haka kuma ba ta da duwatsu, sai dai akan sami
tsaunuka jefi-jefi a wurare daban-daban kamar: Dutsin Damɓo da Dutsin Yami da
Dutsin Jauga. Gulbin Sakkwato ya ratsa ƙasar ta Bakura, wanda
ya fito daga Gusau ya zarce zuwa Sakkwato. Shi wannan gulbin ya saki fadamu da
dama a ƙasar, saboda wasu ƙoramu da suka haɗe da shi a cikin
yankin, kamar na Ɓoɓo wanda kan kai wa
tabkin Natu ruwa. Haka kuma tana da yanayin ƙasar noma mai
albarka, tudu da fadama. Ƙasar da ke kan tudu akasari jigawa ce wadda ake iya noma
kayan abinci da na sayarwa. Kayan abincin da ake nomawa sun haɗa da gero da dawa da
maiwa (dauro). Su kuma kayan sayarwa waɗanda ke taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, sun ƙunshi auduga (kaɗa) da gyaɗa da wake. Fadama
kuwa kamar yadda aka sani tana da ƙasa mai laka da damɓa-damɓa, wadda ake amfani
da ita wajen noman rani da na damina, a inda akan shuka shinkafa da rake da
masara da rogo da dankali da sauran kayan lambu. Hasali ma kusan noman rani da
ake yi a madatsar ruwa ta Bakalori kusan kashi sittin da biyar a ƙasar Bakura ake
gudanar da shi.
Irin wannan yanayi na ƙasar noma mai albarka
shi ya jawo hankalin wasu mashahuran mutane har suka zo Bakura suka yi gonaki,
cikin su kuwa akwai Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato. Haka ma Jami’ar
Ahmadu Bello Zariya ta gina wata haraba a Bakura domin nazari da binciken dabaru
da hanyoyin noma na zamani. Allah Ya albarkaci yankin da wadatattun ruwan ƙarƙashin ƙasa fiye da sauran
makwabtanta.
Ƙasar Bakura tana da
daji mai yawan gaske, sai dai bai cika sarƙaƙiya kamar na ƙasar kurmi ba. Amma
akan sami namun daji a cikinsa can ba a rasa ba. Haka kuma ƙasar tana da itace da
ke taimaka wa jama’ar ƙasar wajen inganta tattalin arzikinsu, kamar itacen kuka
(murna ko miyar kaɗi) da ɗorawa da tsamiya da
mangwaro da bagaruwa da kaiwa da kaɗe da ɗunya da sauransu.
4.0 Asalin Mutanen
Bakura
Akwai saɓanin ra’ayi dangane
da takamaiman ƙasar da mutanen ƙasar Bakura suka fito
da dalilin ƙauratowarsu daga ƙasarsu ta asali da
yadda aka yi har suka iso a mazaunin da suke a halin da ake ciki. Duk da haka,
ba za a rasa madafa ba, domin kuwa masana sun yi ƙoƙarin bayyana
ra’ayoyinsu gwargwadon hujjojin da suka zo a hannunsu.
Da farko, an nuna cewa, asalin
mutanen Bakura Barebari ne da suka ƙaurato daga Barno5
a farkon ƙarni na goma sha huɗu (ƙ.14), kamar yadda
Bakura District Assesment Report (1916:9) da Bakura District Note Book; SSHCB
Sokoto (1980:22) suka nuna. Suka zo suka zauna a yamma da mazaunin da suke
zaune a yau. Bisa wannan ra’ayin an nuna cewa ba wani mahaluƙi da ya taɓa zama a wurin kafin
zuwansu daga ƙasar Barno. A da can ana kiran mutanen Bakura da sunan
Barebari ne, sai daga baya aka yi musu laƙabi da Ɓurmawa.
A wani ra’ayi da Harris (1938) da
Magatakardan Sarkin Ɓurmin Bakura, Malam Yahaya suka bayar, ya nuna cewa, Ɓurmawa sun yi ƙaura ne daga wani
wuri da ake kira LARABA-GARDA a can cikin ƙasar Barno, ɗaruruwan shekaru da
suka shuɗe. Wannan ya faru ne
a sakamakon wata rashin jituwa da ta auku saboda neman sarautar da ta faɗi. Domin kauce wa
wulaƙanci da tsangwama daga Sarkin da ya hau karaga, sai
abokan takarar su uku suka yi ƙaura tare da mabiyansu. A kwana a
tashi har Allah ya kawo su mazaunin da suke yanzu. A wannan bayanin an nuna
cewa, su waɗannan mutane uku
‘ya’yan sarki ne, hasali ma uwarsu ɗaya, ubansu ɗaya da wanda ya hau karagar mulki,
wanda kuma shi ne babbansu.
A wata faɗar kuwa an nuna cewa,
mutanen Bakura malamai ne masu tsoron Allah da ke aiki da ilminsu, sun baro ƙasarsu ta asali wato
Barno a sakamakon buɗin da Allah ya yi
musu na busharar cewa Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da zai
bayyana a wannan nahiya ta ƙasar Hausa. Samun wannan fatahi, sai
suka ƙaurato daga mahaifarsu, suka dawo wannan nahiya suna masu
jiran bayyanarsa domin su taimaka masa wajen jaddada addinin Allah a bayan ƙasa. Wannan ya so ya
yi kama da irin abin da kakan Barebari wato Tubba’u ya aikata dangane da imani
da Annabi Muhammadu (SAW), tun kafin bayyanarsa fiye da shekara dubu (Gana,
1965:39). Su ma al’ummar wannan ƙasa haka suka aikata,
musamman idan aka yi la’akari da yadda Sarkin Ɓurmin Bakura Wakaso
ya bar sarautar na wani lokaci, ya tare wurin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo domin ya
bayar da gudummawa wajen jaddada addinin Musulunci. Haka kuma wannan ra’ayi na
iya samun madafa idan aka yi la’akari da yadda sauran al’ummar ƙasar suka tsunduma
wajen neman ilmin addini da kuma yaɗa shi a farfajiyar ƙasar Hausa. Malam
Yahaya ya ƙara da cewa, a lokacin da suka taso daga LARABA-GARDA
tun a ƙarni na 14, sun fara yada zango a Kura ta ƙasar Kano. Daga can
ne suka koma wani wuri a ƙasar Katsina5. Amma saboda fargabar hare-haren
Katsinawa da rashin tabbas na samun kwanciyar hankali, sai suka yi ƙaura daga ƙasar Katsina har suka
iso mazaunin da suke a yau.
Da farko an bayyana cewa, sun fara
zama ne a wani wuri da ake kira “AJI GISHIRINKA”, kimanin mil biyar daga garin
Bakura a halin yanzu. Ganin cewa, wannan wuri ya zama mashiga ce ga dakarun
Gobirawa, wannan ya tilasta musu yin ƙaura suka koma sabon
garin Bakura. Daga nan kuma suka koma garin Jabo da ke cikin jahar Sakkwato ta
yanzu domin su kare kansu daga hare-haren Kanta. Bayan shekaru da dama, sai
suka yanke shawara a kan su dawo inda garin Bakura yake a halin da ake ciki
yanzu domin su kafa mazauni na din-din-din.
Saboda haka za mu iya cewa al’ummar ƙasar Bakura sun zauna
wurare daban-daban kafin daga ƙarshe su zauna a Bakura da Tureta. Sai
dai tarihi ya bayyana mana cewa wani ɓangaren mutanen Tureta sun cigaba da
yawace-yawace kafin daga baya su zauna a Tureta ta yanzu, kamar yadda Bakura
District Note Book (1980:23) ya nuna. Daga cikin wuraren da mutanen Bakura suka
yada zango sun haɗa da: 1. Ɗunɗaye, 2. Gumyu, 3.
Gwamatse, da cikin jahar Sakkwato ta yau, daga ƙarshe suka zarce
mazaunin da suke a halin da ake ciki yanzu.
A wani ra’ayin kuwa ya nuna cewa
tushen al’ummar Bakura daga wasu shahararrun mutane ne su huɗu, waɗannan mutane kuwa su
ne: 1. TULU, 2. WARKU, 3. JANDAMO, 4. BUREMA. Waɗannan mutane sun ƙaurato daga ƙasar gabas6
ne, suka zo suka kafa garuruwa huɗu waɗanda duk sunan sarautarsu yana ɗauke da laƙabin Sarkin Ɓurmi. Hasali ma idan
aka duba fuskokinsu za a ga suna da alama ta fashin-goshi, wadda ke bayyana
al’ummar da suka fito daga cikinta. Garuruwan kuwa sun haɗa da garin Bakura da
Tureta da Jabo da kuma Moriki.
Lokacin da Bakurawa suka isa ƙasar da suke zaune a
cikinta, sun tarar da wani ɓangaren ƙasar yana ƙarƙashin mulkin Kabawa,
yayin da ɗaya sashen ke ƙarƙashin kulawar
Zamfarawa7. Bayan sun yi cikakken nazari sai suka yada zango a cikin
ƙasar
Zamfara. A daidai wannan lokaci ne suka taimaka wa Zamfarawa a fagen fama a
matsayin sojojin haya, wato lokacin da Zamfarawa ke yaƙi da Kabawa, kamar
yadda Bakura Disstrict Note (1980:22) ya nuna. A sakamakon taimakon da al’ummar
Bakura suka bayar wajen yaƙar Kabawa, wanda ya haifar da samun
gagarumar nasara, wadda ta samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya, ya sa
Sarkin Zamfara ya ba al’ummar Bakura wani ɓangaren ƙasar da suke zaune a
ciki a matsayin ladar yaƙin da suka taimaka (‘Yarkufoji, 1994 : 45).
5.0 Asalin Sunan
Sarautar Bakura Da Na Al’ummarta
Abu ne mai matuƙar wuya, mutum ya
fito gaba-gaɗi ya bugi ƙirji farar ɗaya ya ce zai bayyana
asalin samuwar sunan wata al’umma da sarautarta, ba tare da ya waiwayi abin da
magabata suka bayyana ba. Ko ba komai, ai Hausawa sun ce, da tsohuwar zuma ake
magani. Saboda cimma wannan manufa ne, ya zama tilas a koma baya don kalato
ra’ayin magabata.
Sunan al’ummar Bakura wato “Ɓurmawa” ya samo asali
ne tun kafin su yi ƙaura daga ƙasarsu ta asali,
Barno. Masu wannan ra’ayin sun bayyana cewa, Galadiman Barno ne na wancan
lokaci ya laƙaba musu suna “Ɓurmawa”, kamar yadda
Harris (1938:119) ya nuna. Yayin da Danial (1916:9) ya ce Sarkin Kukawa. Masu
wannan ra’ayin sun nuna cewa, da Sarkin Kukawa zai tafi yaƙi, sai ya bar wa
jikansa alhakin kula da lamurran ƙasar. Sarkin ya
kwashe tsawon shekara bakwai wajen yaƙi. Bayan ya dawo, sai
ya tarar da jikan nasa ya huda (ɓurme) taskarsa ya kwashi wasu abubuwa daga
cikinta. Daga lokacin ne ya kira jikan nasa Sarkin Ɓurmi.
A wani ra’ayi an nuna cewa an samo
sunan ne daga sunan ɗaya daga cikin
shugabanninsu mai suna “Bureme”, kamar yadda Bakura District Note (1980:119) ya
nuna, wato mutanen Burema ko Buremawa.
Da tafiya ta yi tafiya, sannu a hankali sai sunan ya sauya ya koma Ɓurmawa.
Daga nan ne aka rinƙa kiran jagoransu da
sunan shugaban Ɓurmawa. Daga bisani sai aka rinƙa kiransa Sarkin Ɓurmawa. Saboda tsawon
zamani da sauye-sauyensa da aka samu, sai sauyin ya yi tasiri matuƙa har ya kai ga
shafuwar tsarin ginin kalmar ta koma Ɓurmi. Sai aka cigaba da
kiran jagoran al’ummar da suna “Sarkin Ɓurmi”. Ke nan wannan
ra’ayin yana nuna mana cewa sunan al’ummar Bakura da na shugabansu wato “Ɓurmawa” da “Sarkin Ɓurmi”, sun samo asali
ne daga sunan shugabansu na farko da ake kira da suna “Burema”.
A wani ƙauli kuma an bayyana
cewa Sarkin Zamfara ne da kansa ya bayar da sunan sarautar, ta “Sarkin Ɓurmi”, kamar yadda
Yahaya (1993) ya bayyana a Rima Rediyo (‘Yarkufoji, s1994). Masu wannan ra’ayin
sun bayyana cewa, Bakurawa sun taimaki Sarkin Zamfara a lokacin da yake yaƙi da Kabawa, inda
suka nuna bajinta da jaruntaka, suka fatattaki Kabawa. Bayan Wari ya nuna
bajinta ne, sai Sarkin Zamfara ya mallaka musu mazaunin da muƙamin “Sarkin Ɓurmi”. Sai dai su ma
masu wannan ra’ayin ba su bayar da wata hujja da ta sa Sarkin Zamfara ya kira
wannan sarauta ta Bakura da laƙabin Sarkin Ɓurmi ba.
Wani ra’ayi kuwa ya nuna cewa Shehu
Usmanu Ɗanfodiyo ne da kansa ya raɗa wannan suna na Ɓurmawa, sarkinsu kuma
Sarkin Ɓurmi, kamar yadda Alhaji Shehu Bunu (2003) ya bayyana.
Wannan ya auku ne saboda irin jaruntakar da Sarkin Ɓurmin Bakura
Son-Allah da jama’arsa suka nuna wajen fasa rundunar abokan gaba a Tabkin
Kwatto, a lokacin da ake yin jihadi (‘Yarkufoji, 1994 : 42).
Saboda haka, idan aka yi la’akar da
kalmar Ɓurmi, za a tarar an samo ta ne daga kalmar aikatau da ake
kira da ‘Ɓurma’ wadda a luggance tana ɗauke da ma’anar ‘yanke
daga ƙarshe’, haka kuma tana nufin “hudawa” ko “fasawa”, wato
kamar a ce: “Ya ɓurma masa wuƙa a ciki”,
ma’ana, ya huda masa ciki da wuƙa, ko ya fasa masa
ciki da wuƙa”.
Saboda haka, ta
la’akari da ma’anar kalmar a iya cewa sunan ya samo asali ne bayan an ga irin
yadda suka nuna jaruntaka ta wajen yi wa rundunar yaƙin abokan gaba,
yankan batta. Domin kuwa a tsarin kalmomin Hausa akan samu sunan ma’aikaci daga
sunan aiki. Kuma ina kyautata zaton cewa, ta haka ɗin ne aka samar da
sunan al’ummar, wato Ɓurmawa, abin nufi masu iya karya kowace irin rundunar yaƙi ta abokan gaba.
Ita kuma sunan sarautar, wato Sarkin
Ɓurmi,
an laƙaba wa jagoran Ɓurmawa ne domin
kasancewar sa ƙwararre jarumi mai dabarun yaƙi iri-iri, wanda bai
da fargaba in ya so ya fasa rundunar abokan gaba, ta yadda za su gigice, su
tarwatse. Haka kuma idan muka yi la’akari da yadda Barebari ke yi wa mai suna
Ibrahim laƙabi da Buraima ko Burema ko Bura, ma iya cewa an samo
sunan ne daga sunan Sarkin Ɓurmi na uku wanda ya yi mulki daga
shekara ta 1375 zuwa 1407. Hasali ma laƙaba wa al’umma sunan
shugabansu don a nuna cewa su mabiyansa ne abu ne da ya daɗe, akwai Malikawa da
Shafi’awa, waɗanda ake nuni da cewa
mabiyan mazhabobin Imam Maliki da Shaf’i ne.
6.0 Haɓakar Garin Bakura
Idan aka ce haɓaka, a nan ana nufin
abu ya girma, ya bunƙasa, ya kai wani mataki na gawurta har ya zama ya ƙasaita kowa ya san da
zaman abin.
Saboda haka, nan
bayani ya zo ne game da yadda garin Bakura ya girma, ya gawurta har ya samar da
wata ƙasaitacciyar masarauta da za a iya bayyana ta da
shahararriyar masarauta da ta samar da manyan bayin Allah da suka yi fice a
doron ƙasa. Wannan ƙasa ta samu yin fice
ta fuskoki da dama da suka haɗa da fannin yaƙe-yaƙe da kuma fannin
ilimin addinin Musulunci da ke tattare da tawali’u da gudun duniya.
6.1 Gina Ganuwar
Bakura
Ganuwa, wata babbar katanga ce da
ake zagaye gari da ita domin bayar da kyakkyawan tsaro da kariyar rayuwa da
dukiyoyi da mutuncin al’umma. Samuwar ganuwa ga kowane irin gari wata alama ce
da ke iya nuna tabbatar da bayar da cikakkiyar kariya ga al’ummar da ke zaune a
wannan gari, domin takan ƙara jawo masa haɓaka da Bunƙasa ta fuskoki da
dama.
A lokacin mulkin Sarkin Ɓurmin Bakura Mayaƙi 1691 zuwa 1736 ne
aka fara gina ganuwar garin Bakura. Sarkin ya aiwatar da wannan aiki ne domin
ya samar da cikakken tsaro da kwanciyar hankali ga al’ummarsa. Ganuwar dai tana
da ƙofofi
huɗu ne kamar haka:
·
Ƙofar Bai: Ita wannan ƙofa tana Gabas ga
gari ne, ita ce mashigin mutanen Rini.
·
Ƙofar Acale: An yi ta ne a Yamma.
·
Ƙofar Baici: An gina ta ne a Arewa.
·
Ƙofar ‘Yan Sarki: Ita kuwa an yi ta ne a ɓangaren Kudu.
Samuwar
ganuwa a Bakura ya sa aka rinƙa samun mtane suna ƙauratowa daga ƙasashensu suna zuwa
Bakura domin su sami cikakkiyar kariya da kwanciyar hankali. Wannan ne ya
haifar da wanzuwar Gobirawa da Zamfarawa a cikin garin Bakura. Zuwan waɗannan rukunin al’umma
ya sa Bakura ta bunƙasa tun a lokacin da ake yaƙe-yaƙe ta hanyar amfani da
ƙarfin
cin hatsi.
6.2 Bunƙasar Masarautar
Bakura Ta Fuskar Yaƙe-Yaƙe Da Zuwan Baƙi
Sau tari idan aka sami wani
shahararren mayaƙi da ya kai wa gari harin yaƙi bai sami nasara ba,
wannan kan sa a sami wasu jinsin mutane su yo ƙaura daga mazauninsu
na asali su dawo wannan gari domin su sami cikakkiyar kariyar rayuwa da ‘yanci
da dukiya ta yadda za su sami walwala da kwanciyar hankali. Haka kuma idan aka
kai wa gari harin yaƙi aka laƙume shi, sai al’ummar wannan gari su
watse su je su nemi mafaka a wasu garuruwan da suka tabbatar za su sami
kyakkyawar kariya da tsaro na duk wani farmakin mayaƙa da ka iya tasowa.
Masarautar Bakura na ɗaya daga cikin ƙasashen da bajinta da
gwarzontaka a fagen fama (yaƙi) ya kawo mata bunƙasa ta hanyar zuwan
baƙi
don su tsira da mutuncinsu. Hasali ma idan aka bi diddigin tarihi za a tarar
cewa tun kafuwar wannan gari har zuwa lokacin Turawa ba wata ƙasa da ta taɓa cin ƙasar Bakura da yaƙi, sai dai ƙasar ta kuɓutar da makwabtanta
daga harin fin ƙarfi.
Wannan ne ya haifar da son wasu
sarakuna na neman su ƙulla ƙawance da wannan masarauta, misali
kamar ƙawancen Banaga Ɗanbature8
da Sarkin Ɓurmi Bahago9. Duk da kasancewar Banaga Ɗanbature ya shahara
da sanin dabarun yaƙi iri-iri, amma yana shakkar Bahago, don haka, sai ya rinƙa aika wa Sarkin Ɓurmi Bahago da wasu
wurudda domin ya ƙara tabbatar masa da ƙaunar da ke tsakanin
sa da shi. Banaga ya yi haka ne kamar yadda bincike ya nuna, domin Sarkin Ɓurmi da jama’arsa su
ba shi haɗin kai wajen yi wa
Shehu Usmanu Ɗanfodiyo tawaye (Bagobiri, 1985).
Jaruntakar Bahago da yawan roƙon Allah sun sa har
Bawa Jangwarzo ma bai taɓa izgilin kawo wa
wannan masarauta yaƙi ba. Hasali ma har an yi lokacin da Sarkin Ɓurmi Bahago ya ƙwaci al’ummar Tureta
daga hannun Bawa Jangwarzo, (Bagobiri, 1985). Don haka muna iya cewa, al’ummar
wannan masarauta zarumai ne, kuma duk inda zarumai suka kai, su ma sun kai.
Masarautar Bakura ta kafu ta kuma
bunƙasa
ta kuma wuce tsara da wasu siffofi da suka keɓanta ga al’ummar wannan ƙasa na zamansu
zarumawa, ta hanyar nuna ƙarfin hali da juriya da son zumunta da riƙon addini tare da ƙoƙari yaɗa shi. Haka kuma ga
su da tawali’u da tsoron Allah wanda ya sa musu gudun abin duniya. Irin waɗannan halaye sun
taimaka musu ainun wajen kafa ƙasarsu tare da faɗaɗa ta har aka wayi
gari ta kasance ta bunƙasa ta hanyar ciye wasu ƙauyuka da garuruwa da
suke zagaye da ita, waɗanda yaƙe-yaƙe suka auku a
tsakaninsu a yayin da suka takale ta.
Daga cikin garuruwan da ta ciyo a
zamanin da ake yaƙe-yaƙe, sun haɗa da: 1. Gandi, 2.
Rara, 3. Nasarawa, 4. Damɓo, 5. Rini, 6. Ɗankadu, 7. Birnin
Tudu, 8. Ruwan Ɓora, da kuma 10.Gorar
Daji, kai har ma sai da ta cinye rabin garin Talata Mafara, wanda ya kai har Ɗankura, bakin tsohon
gidan sarautar garin, wannan ya auku ne a zamanin mulkin Sarkin Mafara Ɗambaƙi , kamar yadda Edgar
(1911) da Bunu (2003) suka nuna.
Amma daga baya sai
aka kafa iyaka a ‘Yargeda, maimakon a tsakiyar garin Talata Mafara kamar yadda
sharuɗɗan yaƙi suka tanada. Wannan
ne sanadin wasa a tsakanin Mafarfari da Ɓurmawan Bakura. Haka
a karon batta da masarautar ta yi da masarautar Anka, Bakura ta fatattaki Anka
a inda ta laƙume garin Damri da sauran garuruan da ke ƙarƙashinsa. Sai dai daga
baya an sami ƙulla zumunta a tsakani, a inda Sarkin Ɓurmin Bakura Isan
Na-Abu ya aurar da ‘yarsa mai suna Maimuna ga Sarkin Zamfaran Anka Abubakar
Bawa Adam wanda ya yi mulki daga 1829 zuwa 1853. Ya samu haihuwa da ita ta ɗa namiji mai suna
Muhammadu Farin Gani wanda ya yi sarautar Anka har sau biyu. Na farko daga 1896
zuwa 1899, karo na biyu daga 1928 zuwa 1946. Shi ma ya auro ma ɗansa da ake yi wa laƙabi da Sardauna Yaro,
mata mai suna A’ishatu daga shahararren gidan nan na Magazawa Bakura. Matar ta
haifa wa Sardaunan ɗa da aka sani da
Malam Sulaiman Anka (Magatakarda Malam Sule Anka).
Babu shakka, za a iya cewa al’ummar
wannan masarauta ba kanwar lasa ba ce, domin sun nuna bajinta da ƙwazo da jaruntaka
tamkar yadda Fulani suka nuna a ƙoƙarin da suka yi na
tabbatar da kalmar Allah. Wannan shi ya sa har suka kai ga kafa garuruwa na ƙashin kansu tare da
samun cikakken iko a kan ƙasashen da suka ci da yaƙi. Samun nasarar ragargaza
ƙasashen
da suka laƙume ya ba su damar maye gurbin gidajen sarautar da nasu,
ta hanyar naɗa wasu sarakuna daga
cikin zuriyarsu. Da tafiya ta yi tafiya sai aka rinƙa ƙulla dangantaka ta
hanyar auratayya a tsakani. Saboda haka ne aka sami garuruwa guda takwas a
cikin masarautar da suka zama suna da kusan asali ɗaya da jama’ar
Bakura, har ma hakan ya ƙara taimakawa wajen samar da haɗin kai da wanzuwar
zaman lafiya a tsakanin al’ummar da kuma sarakunan da ke wannan masarauta.
Hasali ma sai aka wayi gari suna ganin sun fito ne daga tsatso ɗaya.
A sakamakon tsawon zamani da
wanzuwar mulkin masu jihadi da na Turawan mulkin mallaka sun haifar da rage faɗin ƙasar masarautar
Bakura. Misali an fitar da garuruwan Gandi da Ruwan Ɓorai da Ruwan Gizo da
Gorar Daji da Barikin Daji daga cikin ƙasar. Wasu aka mayar
da su ƙarƙashin masarautar Talata Mafara, Gandi kuwa ta sami
‘yancin kanta.
6.3 Bunƙasar Masarautar
Bakura A Zamanin Turawan Mulkin Mallaka
Kasancewar masarautar Bakura na ɗaya daga cikin masarautun
da ke ƙarƙashin Daular Usmaniyya tun kafin zuwan Turawa, kuma
Sarkin yana daga cikin muƙaraban daular, ya sa Gwamna Lugga ya yi taro na musamman
da muƙarraban daular, domin su fitar masa da wanda ya dace ya
zama Sarkin Musulmi, bayan Sarkin Musulmi Attahiru na 1 ya yi hijira. Jagoran
wannan masarauta, Sarkin Ɓurmi Ahmadu Bafillace yana ɗaya daga cikin waɗanda aka gayyata a
wancan zama (Kani & Gandi, 1990: 31). Saboda sarakunan yankin sun kasance
cikin Majalisar Sarkin Musulmi tun zamanin jahadin Shehu Usman har zuwa lokacin
Sarkin Musulmi Abubakar III ya kawo wasu
sauye-sauye a 1945 da suka haifar da cire sarakunan da ke majalisar tun
zamanin Shehu, kamar: Sarkin Ɓurmin Bakura Yahaya (1937-1960) da
Sakin Katsinan Gusau Marafa Ibrahim (1945-1948) da Sarkin Kiyawa Muhammadu Asha
(1929-1952). Wannan ita ce farkon ƙulla dangantaka
tsakanin Turawa da masarautar.
Aikin farko da Turawa suka fara ƙaddamarwa a
masarautar shi ne buɗe ofishin gunduma,
wanda suka aika da jami’i don ya kula da ayyukan da sarakuna ke aiwatarwa. Haka
kuma sun gina titin mota da ya tashi daga Bakura zuwa lamba wanda ya haɗe da babban titin da
ya fito daga Sakkwato zuwa Gusau.
Idan aka karkato ta ɓangaren ilimin zamani
za a tarar cewa, a shekarar 1945 Turawa suka gina makarantar Boko ta farko a
garin Bakura. Haka sun gina ƙaramin ɗakin shan magani don amfanin jama’ar
da ke masarautar.
6.4 Bunƙasar Masarautar
Bakura Bayan Samun Mulkin Kai
al’ummar masarautar Bakura, su ma
kamar sauran kowace al’umma suna sane da irin yadda Turawa suka fakaice da
mulki domin tsotse arzikin ƙasa tare da yin katsalanda a harkokin
da suka danganci addini da makamantansu. Wannan shi ya sa suka tashi
gadan-gadan suka tsuduma wajen yunƙurin ganin cewa,
Turawa sun bayar da mulkin kai. Domin sun fahimci cewa, ta hanyar fafutukar
neman ‘yanci ne kawai za a iya samun bunƙasar tattalin arziki
da cigaban addinin Musulunci a cikin wannan ƙasa. Wannan magana a
bayyane take, domin kuwa Sarkin Ɓurmi Yahaya ya fito
fili ɓaro-ɓaro ya bayyana
ra’ayin al’ummarsa a yayin da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya ziyarci
masarautar a cikin shekara ta 1955 (Yahaya, 1993) kamar yadda ‘Yarkufoji (1994)
ya nuna. Sarkin ya gabatar da jawabinsa a inda yake cewa:
Ni Sarkin Ɓurmi da mu da
jama’armu, muna ba da
goyon baya ɗari bisa ɗari a kan yunƙurin da kuke
yi na ganin
cewa, ƙasarmu ta samu ‘yancin kai.
Samun mulkin kai ke
da wuya sai masarautar Bakura ta fara bunƙasa ta fannoni
daban-daban. Misali a fannin ilmin zamani, an sami cigaba, domin kuwa an sami
damar gina makarantar firamare a ƙarƙashin Ƙungiyar
Jama’atul-nasru Islam. Ta ɓangaren gwamnati kuwa, a shekarar 1960 ne aka ɗaukaka makarantar
farko da Turawa suka gina zuwa makarantar firamare ta cikin gari da ƙara gina wasu azuzuwa
domin a sami damar ƙara yawan ɗalibai. Haka an sami damar giggina wasu
makarantun a wasu sassa da ke faɗin masarautar. A cikin shekara ta 1975 ne aka
kafa Makarantar Horon Malamai a cibiyr masarautar. Makarantar ta fara zaman
wucin-gadi a Talata-Mafara.
Haka huma an sake buɗe ƙananan makarantun
sakandare guda biyu a yankin masarautar a cikin shekara ta 1980. A cikin
shekara ta 1983 aka sake buɗe wata makarantar firamare a Sabon Garin Bakura. Haka
kuma an buɗe ofishin ilmi don ya
kula da yadda ake tafiyar da lamurran ilimin makarantun firamare.
A fannin noma kuwa, idan aka duba za
a iya cewa duk faɗin masarautun da ke
jahar Zamfara ba wata masarauta da ta bunƙasa fiye da
masarautar Bakura ta wannan fuska. Domin kuwa a wannan masarauta Sardauna ya yi
gona wadda aka shuka abubuwan da a wancan lokacin ba gonar da za a same su a
duk faɗin lardin Sakkwato,
sai a gonar. Haka kuma an gina asibitin dabbobi a Bakura. Noman rani ya bunƙasa matuƙa a farfajiyar wannan
masarauta a sakamakon gina madatsar ruwa da aka yi a masarautar Maradun. Wannan
ya sa masarautar ta zama mafi rijaye daga cikin ƙasashen da ke noman
shinkafa a duk faɗin jihar Zamfara.
Manoman yankin ba sun tsaya kaɗai ga noman shinkafa ba ne, har da wasu kayan ci da na
sayarwa, wato kamar masara da alkama da wake da rake da tumatir da dankali.
Masarautar ita ce gundumar da ta fi kowace ƙasa noman dankali a
duk faɗin Nijeriya. Ganin
irin yadda noma ke haɓaka a wannan
masarauta shi ya sa aka kafa makaranta don inganta noman rani a masarautar
wadda ake kira da SCHOOL OF IRRIGATION AND EXTENTION SERVICES. An yi haka domin
a koyar da manoma dabarun noman rani na zamani. Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta
buɗe haraba ta Kwalejin
Aikin Noma a cikin gundumar, daga baya ne gwamnatin jihar Zamfara ta karɓi wurin domin nazarin
kimiyyar fasahar noma ta zamani.
Bayan samun mulkin kai, gwamnati ta yi ƙoƙarin inganta harkokin
kiyon lafiya ta hanyar gina ƙananan ɗakunan shan magani a wasu sassan
wannan masarauta. A cibiyar masarautar kuma aka gina asibiti domin kula da
lafiyar al’ummar wannan ƙasa.
Ta fuskar sufuri kuwa, abubuwa sun
bunƙasa
a inda aka sami hanyoyin mota da suka haɗa wannan masarauta da wasu yankuna da ke maƙwabtaka da ita.
Misali an gina hanyar da ta fito daga Sakkwato ta biyo ta Raɓa da Gandi ta faɗo Bakura ta zarce
lambar Bakura a inda ta haɗe da titin da ya fito daga Gusau zuwa Sakkwato. Yin titin
ne ya haifar da wanzuwar gina gadar Bakura. A ɗaya hanyar kuwa da ta fito daga sashen
‘Yarkufoji da Birnin Tudu da Rini ita ma ta sami bunƙasa a inda aka gina
gada tare da shimfiɗa wa wani sashe
kwalta. Haka an zuba kwalta a cibiyar masarautar.
Ta fuskar samar da abubuwan jin daɗi inganta walwalar
jama’a, a cibiyar masarautar ta sami rijiyar burtsatse, haka kuma garuruwan da
ke cikin masarautar sun sami fanfunan tuƙa-tuƙa, haka a mafi yawan ƙauyuka. Wani muhimmin
abu da ya taimaka wajen haɓaka masarautar shi ne ƙirƙiro ƙaramar hukuma da aka
yi. Da farko ƙaramar hukumar tana ƙunshe da masarautu
biyu ne, masarautar Tureta da masarautar Bakura. Amma bayan ƙirƙiro jihar Zamfara,
masarautar ta sami ɗaukaka a inda aka bar
ta a matsayin ƙaramar hukuma ita kaɗai. Samar da ƙaramar hukuma ya
wanzar da samuwar sashen ilmi da kuma wata sabuwar kasuwa. Duk waɗannan abubuwa da suka
faru a wannan masarauta sun taimaka wajen haɓakarta ta kowace fuska da suka haɗa da ƙaruwar yawan al’umma
da tattalin arziki da ƙarin shigowar baƙi. wannan ya sa
masarautar ke ƙunshe da ƙabilu daban-daban da ke zaune a
cikinta kamar:
Ɓurmawa (Barebari) da
Fulani da Zamfarawa da Gobirawa da Buzaye da Yarbawa da Igbo
(Inyamurai).
7.0 Gidan Sarautar
Bakura
Daga abin da muka gani za a lura da
cewa, asalin sarakunan masarautar Bakura sun fito ne daga tsatso ɗaya tun ranar da aka
fara sarautar Bakura. Shi wannan babban gida, Muhammadu Kura ne ya kafa
shi, wanda Turawa ke yi wa laƙabi da WARIOR a Turance, wanda ke
nufin “Gwarzo” ko “Zarumi” ko “Mayaƙi” ko kuma “Barde”.
Abin kula a nan shi ne wannan gidan sarauta na Bakura ya sha bamban da wasu
gidajen sarakuna da aka kafa su a lokaci ɗaya, domin an ɗora harsashinsa ne a kan tubalan
addini da jaruntaka da kuma gado, musamman idan aka koma baya aka dubi tarihin
kafuwar masarautar da samuwar sunan masarautar.
Hasali ma ko da al’ummar ƙasar suka zo
mazauninsu sun kasance Musulmi tsantsa da ke ƙoƙarin koyo da koyar da
addinin Musulunci. Wannan shi ya sa har kwanan gobe al’ummar wannan masarauta
suke cikin sahun gaba a wajen ilmin addinin Musulunci. Za a iya ganin haka a
zahiri a cikin gida da kuma waje. Misali, mutanen Bakura sun tare a Tudun Wada
Zariya a sakamakon gayyatar da Sarkin Zazzau Ibrahim ya yi wa jagoransu Malam
Aliyu Ɗan Muhammadu Kayi ( Liman Alu) ta hannun Malan Sani Na-Ƙofar Doka, don neman
yaɗa ilmi da bunƙasa shi10.
Haka ma lamarin ya kasance a wasu garuruwan kusa da na nesa da al’ummar suka
je, kamar Gusau, da Ƙaura Namoda da T/Mafara da Kano da Katsina da sauransu.s Don haka neman
ilmin addinin Musulunci kusan abu ne wanda talaka da Basarake kowa ke nemansa
tun kafin su zauna dindindin a wannan farfajiya.
7.1 Salsalar
Sarakunan Bakura
An riga an fahimci cewa, Muhammadu
kura shi ne wanda ya fara zama a wurin da aka kafa Bakura tun lokaci mai tsawo
da ya shuɗe. kafin garin ya
tabbata, sai da mutanen farko suka sha fama da gwagwarmaya domin ganin sun
tabbatar da ‘yanci tare da samar da cikakkiyar walwala da jin daɗi ga zuriya mai zuwa.
Tarihi bai bar komai ba a sake, domin ya tabbatar mana da abubuwan tunawa da ke
nuna salsalar gidajen sarautar Bakura ya danganta zuwa ga mutum ɗaya ne. Ita wannan
zuriya ta sarakunan Bakura tana tattare da abubuwan da suka aiwatar na tarihi
da ba za a manta da su ba. Wannan ne ya sa a daidai lokacin da aka raba
zarumawan Ribaɗi da aka ba Abubakar
Atiku yanki Zauma (Zamfara) wadda Bakura na ciki, sai ya tare a garin Bakura
saboda amincin da ke tsakaninsu da al’ummar ƙasar.
7.2 Tsarin Sunayen
Sarakunan Bakura da Shekarar da Aka Hau Karagar Mulki:
1. Sarkin Ɓurmi Zara 1319 - 1337
2. Sarkin Ɓurmi Wari 1337 - 1375
3. Sarkin Ɓurmi Ibrahim (Ilo) 1375 - 1409
4. Sarkin Ɓurmi warku Jan-Damo 1409 -1445
5. Sarkin Ɓurmi Ango 1445 -1493
6. Sarkin Ɓurmi Dodo 1493 -1529
7. Sarkin Ɓurmi Tulu 1529 -1574
8. Sarkin Ɓurmi Alje 1574 -1621
9. Sarkin Ɓurmi Bagobiri 1621 -1646
10. Sarkin Ɓurmi Aliyu AL’aje 1646 -1691
11. Sarkin Ɓurmi Mayaƙi 1691 -1736
12. Sarkin Ɓurmi Son Allah 1736 -1794
13. Sarkin Ɓurmi Wakaso 1794 -1825
14. Sarkin Ɓurmi Bahago 1825 -1836
15. Sarkin Ɓurmi Bawa Na-Maibarau 1836 -1856
16. Sarkin Ɓurmi Yusufa Ɗankwai 1856 -1885
17. Sarkin Ɓurmi Isa Na’abu 1885 -1901
18. Sarkin Ɓurmi Amadu Bafillace 1901 -1905
19. Sarkin Ɓurmi Amadu Maijirgi 1905 -1909
20. Sarkin Ɓurmi Manu Maikasada 1909 -1916
21. Sarkin Ɓurmi Muhammadu Taude 1916 -1919
22. Sarkin Ɓurmi Ibrahim Ima 1919 -1937
23. Sarkin Ɓurmi Yahaya 1937 -1960
24. Sarkin Ɓurmi Yusuf II 1960 -1970
25. Sarkin Ɓurmi Muhammadu Mailafiya 1970 -1981
26. Sarkin Ɓurmi Yusuf III 1981 -2001
27. Sarkin Ɓurmi Engr. Bello M.
Sani 2001 -2010
28. Sarkin Ɓurmi Hasan Damri 2010 -2011
29. Sarkin Ɓurmi Engr. Bello M.
Sani 2011 -
8.0 Kammalawa
Daga waɗannan bayanai an
fahimci cewa tushen al’ummar Bakura ta
samo asali ne daga wasu shahararrun mutane huɗu ne wato Tulu da Warku da Jandamo da
Burema, waɗanda suka ƙaurato daga ƙasar gabas suka zo
suka kafa garuruwan Bakura da Jabo da Moriki da kuma Tureta. Hasal i ma duk
sunan sarautarsu na ɗauke da laƙabin Sarkin Ɓurmi. A sifa kuwa
suna da alamar fashin goshi da ke bayyana al’ummar da suka fito daga cikinta.
An nuna cewa a sakamakon gudummuwar da suka bayar wajen yaƙar Kabawa, ta wanzar
da nasarar sarkin zamfara a kan Kabawa. Ita c eta zama silar ba Ɓurmawa ƙasar da ta zama
mallakinsu a madadin ladar yaƙi. An kuma ji yadda aka sami laƙabin sarautar da ma
na al’ummar. Akwai buƙatar manazartan wannan zamani su ƙara ƙaimi wajen taskace
tarihin al’ummominsu da al’adunsu domin amfanin na baya. Zai kuma dace a samar
da makamancin irin wannan fage da zai yi ƙoƙarin taskace
tsofaffin al’adun bukukuwan daulolin ƙasar Hausa saboda
fa’idar da ke tattare da su. Irin waɗannan abubuwa sun danganci jaruntaka da ƙoƙarin yaɗa addinin Musulunci,
musamman idan aka yi la’akari da irin gagarumar gudummuwar da suka bayar a
yayin da ake ƙoƙarin jaddada addinin Musulunci a zamanin jihadin Shehu
Usmanu Ɗanfodiyo.
Ƙarin Bayani
1. Waɗanda ma bas u iya
rubutu da karatu sukan taskace tarihinsu da “ka” su bayar da shi da baki, sai
dai akan sami gurɓatar tarihin a
sakamakon tsufan da ke wanzar da mantuwa ko dagulewar al’amurran tare da giɗimewa. Saboda haka,
sahihiyar hanyar taskace bayanai it ace ta hanyar rubutawa.
2. Saukar ruwan sama
masu yawan gaske ba kafkaftawa kan haifar da cikowar magudanun ruwa, sakamakon
haka kan sa gidajen al’umma su cika su batse saboda rashin wadatattun magudanar
ruwa masu yalwa. Idan haka ta auku, an sami ambaliya ken an a sanadiyyar rowan
sama (Abubakar, 2015:15).
3. Tukunawa na Kudu maso
Yamma da garin Bakura, ta sashen tsohon titin mota mai zuwa Lambar Bakura.
4. Al’ummar Bakura na alfahari da zamansu
Barebari da suka fito daga Barno tun a wajen ƙarni na sha huɗu (K14). Dalilin haka
ne ma Ɗan Majalisar Dokoki mai wakiltar yankin ya gabatar da buƙatar neman ɗaga darajar sarkinsu
domin su sami kyakkyawan wakilci a majalisar masarautu ta jaha. Ya kuma kafa
hujjarsa da cewa, Sarkin Kiyawan Ƙaura yana wakiltar
Filanin Alibawa ne, yayin da Sarkin Katsinan Gusau ke wakiltar Katsinawa.
Sarakunan Anka da Gummi da Talata Mafara duk suna wakiltar Zamfarawa ne. Saboda
haka su ma al’ummar Bakura ya kamata a yi musu adalcin da za su sami wakilci a
majalisar masarautu ta jaha. Ke nan wannan ya nuna suna alfahari da zamansu
Barebari.
5. Tarin ƙasar Bakura bai faiyace
muhalin ba, balle a san ƙaramar hukumar da yake a wannan zamani.
6. Ƙasar Barno, tun a
cikin ƙarni na goma sha huɗu (Ƙ14).
7. Daular Zamfara ta
kasance tun kafin zuwan Gobirawa a Unguwar Alƙali, muhallin da aka
sani da Alƙalawa. Wurin ya cikin farfajiyar Daular Zamfara ne har
zuwa abin da ya kai Sakkwato a inda suka yi iyaka da ƙasar Kabi wajen filin
jirgin sana da ke Sakkwato. Hasali ma ƙasar Dacaɗi duk cikin farfajir
Zamfara ce. Daular ta fara ƙarfi tun a ƙarni na 15 har zuwa
na 16. Ta bunƙasa sosai a tsakanin 1650 zuwa 1750 lokacin da ta dinga
gwabzawa da masarautar Kabbi da Kano da Azbin da Adar ( Nadama, 1977:214).
8. Banaga Ɗanbature ya yi mulki
daga ƙarshen ƙarni na 18 zuwa 1818 a lokacin da masu
jahadi suka kasha shi. Ya kasance mafaɗacin sarki, mai yawan kai hare-hare da ƙone tungage da
rugage. Ya kuma addabi masu jahadi da ke yankin Zamfara ( Jabaka,1985:4, Gusau
da Gusau, 2012:26, Last,1967:68, Usman, 1981:135-137).
9. Sarkin Ɓurmi Bahago ya yi
mulki a farkon ƙarni na 19 zuwa 1836.
10. Malan Aliyu ɗan Magaji Muhammadu
Kayi, ya tafi Zariya a shekarar 1924, bayan ya yi karatunsa a garuruwan Gwadu
da Katsina. A Gwandu ya yi karatu ne a wurin dangin kakanninsa. A Katsina kuwa
ya yi karatu ne a wurin Malan Salihu Mai-gatarin Baƙi. Yayin da ya isa
Zariya, ya sauka a gidan Malan Namalama da ke Tudun Wada Zariya. A daidai
lokaci layi biyu ne kawai, daga Layin Sarki sai Layin Joji. Ya tafi Zariya ne
sakamakon irin labarin da ya samu na ƙwarewar Malan Sani
Na-Ƙofar
Doka a fannin fiƙihu domin su tattauna wasu abubuwa da suka jiɓinci sashen. Malamin
ne ya sanar da Sarkin Zazzau Ibrahim zuwan Malan Aliyu, kuma ya shawarci sarkin
da ya riƙe malan domin yana hangen zamansa a Tudun Wada zai sa ƙasarsa ta bunƙasa. Sakamakon wannan
shawara ne ya sa Sarkin ya nemi malamin da ya zauna a Tudun Wada. Ya kuma ba
shi limancin wannan wuri tare da ba shi jejin (dajin) da ke wurin, don samun
gida da gona, sai dai malamin bai karɓi kyautar ba. Sakamakon haka ne aka sami
makarantar farko da ake koyar da fannonin ilimi a Tudun Wada Zariya wadda
mutumin Bakura ya kafa. A makartar an koyar da ɗalibai masu ɗimbin yawa da suka
halarci makarantar daga sassa daban-daban na nahiyar. Almajiransa sun kakkafa
makarantu daban-daban a Tudun Wada da wasu ƙasashe. Daga cikin
almajiransa da za a iya tunawa akwai: Malan Ibrahim Mai’yammakanta, da Shekh
Malam Mu’azu Na-‘yarkufoji, da Malam Ibrahim Maigandi, da Sarkin Ɓurmi Muhammadu, da
Tudun Birnin Tudu Alhaji Tukur, da Malan Ibrahim Bakura (Na’yarkuta), da Malam
Sulaimanu Bakura, da Limamin Tudun Wada Liman Habibullahi, da Malan Abubakar
Aliyu Fari. Har Malan Muhammadu Marwa (Maitatsine) ya yi karatu a gunsa, amma
da ya ga take-takensa sai ya kore shi. Wannan makaranta ta taimaka wajen yaɗa ilimi da bunƙasa addini da kuma ƙasar Zazzau da ma
Nijeriya baki ɗaya ( Habibullahi,
1989) da (Sa’adu, 1994) da (Ɗanbuzu,1994).
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.