A al’adance, Hausawa mutane ne masu zamantakewa irin ta cuɗe-ni-in-cuɗe-ka, ba zamantakewa irin ta kaɗaici ba, irin wanda kowa kansa kawai ya sani sai kuwa iyalansa. Irin zamantakewar da al’ummar Hausawa ke yi irin wannan ce ta, mu gudu tare, mu kuma tsira tare.
Hausawa al’umma ce da take zaune a yankin arewa maso
yamma na ƙasar Nijeriya, da kuma wani sashe na kudancin ƙasar
Nijar. Wannan yanki ya kasance ne tsakanin sabana ta sudan da kuma sahel. Waɗannan yankunan a wani
lokaci kan yi fama da ƙamfar ruwan sama a lokacin damina wanda wani sa’ili kan
haifar da rashin kyawon kayan amfanin gona da ake nomawa. Sakamakon haka akan
sami aukuwar yunwa ko ƙarancin cimaka, lokaci-lokaci.
Misali, ‘Yar Gusau yunwa ce da ta addabi wani sashe na ƙasar Hausa a shekara ta 1943. An yi fama da yunwar Muɗa a shekara ta 1953. Yunwar Bankaura kuwa, a shekarar 1973. ‘Yar Buhari, ta faɗawa ƙasar Hausa ne a shekara ta 1984. Nufin wannan muƙala ne ta yi tsokaci kan yadda lamarin zamantakewa a tsakanin al’ummar Hausawa kan kasance a lokacin yunwa, musamman kamar yadda wasu mawaƙan baka suka ƙyallaro shi, suka kuma suranta hoton zamantakewar a cikin waƙoƙinsu na baka, musamman waƙoƙin da aka yi a baya-baya wato daga 1984 da aka yi ‘Yar Buhari, ya zuwa yunwar da aka yi a wajajen 1996.
Zamantakewar Al’umma a Lokacin Yunwa:
Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Baka na Hausa
DR. MUSA
FADAMA GUMMI
Email: gfmusa24@gmail.com
Phone No.: 07065635983
1.0 Gabatarwa
Adabi madubi ne ko
hoto na rayuwar al’umma. Abu ne da ya game dukkanin rayuwar al,umma musamman
fasaharsu, da hikimominsu. Fasahohi da hikimomin al’umma kan haɗa da maganganun
hikima kamar kirari, da take, da habaici, da gugar zana, da baƙar magana, da Karin magana,
da tatsuniyoyi, da labarai, kai har da uwa uba, waƙa. Waƙar baka wani rukuni
ne daga cikin rukunan adabin baka sannan waƙa wani ma’adani ce ko
rumbu na tarihi kuma tana nuna hoto na rauyar al’umma.
Wannan dalili ne ya
sanya wannan muƙala ta ƙuduri anniyar duba wannan rumbu na
ajiyar tarihi domin duba yadda zamantakewa tsakanin al’ummar Hausawa kan
kasance a lokacin yunwa, kamar yadda wasu mawaƙan baka suka hanga,
suka kuma bayyana a cikin waƙoƙin yunwa na baka da
suka rera a lokuta daban-daban. Yunwa bala’i ce don haka takan shafi yadda
al’umma kan gudanar da rayuwarta. Abin dubawa a gani a nan shi ne shin yunwar
kyautata zamantakewar take yi ko a’a zamantakewar gurɓata take? Duba waƙoƙin zai ba da haske a
kan yadda lamarin kan kasance. Kafin duba wannan lamari a cikin waƙoƙin baka, ya dace a
kalli ma’anar yunwa da kuma waƙar baka.
1.1 Ma’anar Yunwa
Masana daban-daban
sun yi ƙoƙari a wurare daban-daban, su bayyana
abin da ake kira yunwa. A ƙamus
na Longman cewa aka yi yunwa ita ce tsananin rashin abinci ga jama’a masu yawa.
Bargery (1933:1117) a
cikin Ƙamusun Hausa da Turanci, cewa ya yi yunwa tana nufin jin
buƙatar
cin abinci irin yadda aka saba idan an ɗauki lokaci mai tsawo ba a ci abinci, wato
abin da a harshen Ingilishi ake kira ‘Hunger’. Ɗaya ma’anar da Ƙamusun ya kawo shi ne
cewa kalmar yunwa tana iya ɗaukar ma’anar wani bala’i na ƙaranci abinci ga wata
al’umma ta wani yanki ko ƙasa, wato abin nan ake kira ‘famine’ a harshen Ingilishi.
A cikin kundin Encylopidae
Brittanica, cewa aka yi yunwa ita ce matsanancin ƙarancin abinci a wani
yanki ko wata ƙasa baki ɗaya, wanda ke sa a tagayyara har ma da mace-mace.
Watts, (1983:1) cewa ya yi yunwa tana nufin
wani bala’i da kan shafi al’umma, wanda ke haddasa ƙarancin abinci ta
yadda jama’a masu dama za su tagayyara.
Umar, (1992:5) gani yake cewa yunwa ita ce
matsanancin ƙarancin abinci. Watau mutane su rasa abincin da zai
wadace su.
Malumfashi, (2002), cewa ya yi wasu za su ce
ai ba komi ba ne yunwa face zafin ciki da mutum kan ji idan bai ci abinci ba,
ko rashin isasshen abinci mai sa ƙoshin lafiya. Haka ne
amma yunwa ta wuce nan. Duk wanda ya ɗauki yunwa a matsayin rashin cin abinci ko
ramewa saboda rashin ƙoshi to bai fahimci yunwa sosai ba. A ganinsa yunwa ta haɗa da talauci da
fatara.
Fadama (2008), cewa
ya yi idan Bahaushe ya ce yunwa to tana iya ɗaukar ɗaya daga cikin ma’anoni biyu. Na farko dai
tana nufin zafin cikin da mutum kan ji idan bai ci abinci ba na wani ɗan lokaci, ko da kuwa
yana da abincin. Ma’ana da zarar mutum ya ji yana matuƙar buƙatar abinci to kuwa
yana jin yunwa. Irin wannan yunwa ta yi daidai da abin da wani mawaƙin noma, Makaɗa Illon Kalgo, a
jihar Kebbi ya ce a wata waƙa tasa ta gonar Sardauna.
Jagora: Shehu Kalgo taho rakkan
ni
: Mu zo waƙar gona
: Ni kam gona can nika wasa
: In kwan can
: In yini can in koma hantci
: Raina kwal
: Gonar Sardauna
: Ba ka jin yunwak komi
: Kowa shiga gonar Amadu
: Has shi wuce duniyag ga
‘Yan Amshi: Bai yunwa
ko ɗai.
( Makaɗa Illon Kalgo Waƙar Gonar Bakura gonar
Sardauna)
Ɗaya ma’anar kuwa ita ce hali na matuƙar ƙarancin abinci ga mafi yawan jama’a na wata
al’umma wanda ke sa a tagayyara, wani lokaci har da mace-mace. Irin wannan
bala’i na yunwa ya yi daidai da abin da wani mawaƙi, Amali Sububu na ƙasar Maradun a jihar Zamfara yake
cewa:
Jagora: “Rani
wanga ya yi rani
Ya sa maza lage,
Tafiya
wagga ta yi nisa
Ta
sa maza gaba
Yunwa
wagga ta yi yunwa
Ta ba mu arkane
Ga mata da ‘yan ɗiya
Ka ji ƙatonta
ya yi lalata
Ya ba ta wuri
Yara: Ya tcere yana ta kai nai”.
( Amali Sububu: ‘Noma Ba ya Sa Ka Rama’)
Watau ke nan yunwa
iri biyu ce, akwai ta al’ada wadda aka saba da ita yau da kullum da kuma ta
bala’i wadda kan sami al’umma lokaci-lokaci.
1.2 Ma’anar Waƙar Baka.
Masana da dama sun yi namijin ƙoƙari wajen bayyana
abin da waƙar baka take nufi. Bisa ma’ana, Yahya, (1997:4) yana
kallon waƙa a matsayin tsararriyar maganar hikima da ta ƙunshi saƙo cikin zaɓaɓɓaɓun kalmomi da aka
auna domin maganar ta reru ba faɗa kurum ba. Masanin ya ce ita waƙar baka ana rera magana
ne tare da amfani da kayan kiɗa bayan zaɓen kalmomi da tsaru su.
A wurin Gusau (2003: xiii), waƙar baka wani zance ne
shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da
daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da kiɗa da amshi.
Idan aka yi la’akari da abin da masana suka faɗa
dangane da abin da suke ganin ake kira waƙar baka, to ana iya cewa waƙar baka wani zance ne na hikima ko
magana wadda aka shirya ta hanyar tsara kalmomi zaɓaɓɓu
kuma zaunannu, a rera su gutsure-gutsure cikin azanci da salon armashi, tare da
yin kiɗa, da amshi, da
nufin isar da saƙo.
Yanzu ya dace a duba
yadda zamantakewar al’umma kan kasance a lokacin yunwa kamar yadda wasu mawaƙan baka suka hango.
2.0 Yanayin Zamantakewa A Lokacin Yunwa
A al’adance, Hausawa
mutane ne masu zama irin na cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. Ba zama irin na kaɗaici wanda kowa kansa
ya sani ba. Irin zaman da al’ummar Hausawa ke yi irin zaman nan ne na ‘mu gudu
tare mu tsira tare’. Wannan ya sa tun fil azal Hausawa suke irin zaman nan na
gandu wanda uba tare da iyalansa da iyalan danginsa har da barori suke zaune a
wuri ɗaya. A irin wannan
zama komai tare ake yi. Bayan an fitar da mutum daga gandu sai ya kama aikin
kansa. To amma duk da haka, ranar da ya kasa, watakila sakamakon wata rashin
lafiya ko wani abu mai kama da haka, to kuwa ana taruwa a taimaka masa. Irin
haka, na ɗaya daga cikin abin
da ya sa ake yin aikin gayya. Irin zaman cuɗe-ni-in-cuɗe-ka da Hausawa ke yi ya sa idan lalurar
bukin aure ko na haihuwa ta sami ɗan’uwa ko ma duk wani makusanci, akan taru
kowa ya ba da tasa gudunmawa ko ta kuɗi ko ta abinci. Yin haka, ga dukkan alamu,
shi ya haifar da al’adar nan ta buki. Ko ma ba wannan ba, duk wata matsalar da
ta sami wani wadda ake ganin ta fi ƙarfinsa, to taruwa
ake yi a haɗa ƙarfi don a warware
masa ita.
Irin wannan
zama da Hausawa ke yi wanda har ya zame masu al’ada, wani lokaci akan kauce
masa, musamman a lokacin matsuwa. Watau lokacin da wani bala’i, na rashin
abincin da za a ci, ya auka wa wata al’umma. Tarihi ya nuna irin wannan kan
auku daga lokaci zuwa lokaci. A lokacin yunwa akan sami akasi na kyakkyawar
zamantakewa da aka san Hausawa da ita. Zamantakewa sai ta gurɓace,
a sami rayuwa ta kaɗaici, da
rowa, zama da ƙazanta,
da kisan aure, da hali na talaucewa, da yaudara, da uwa uba ƙaura. Yanzu sai a bi su ɗaya
bayan ɗaya, a ga yadda
suke aukuwa kamar yadda aka kawo su a cikin waƙoƙin baka daban-daban.
2.1 Rayuwar Kaɗaici
Da Rowa.
A lokacin
yunwa, musamman ma dai idan ta yi tsanani, akan sami rayuwa ta kaɗaici.
Rayuwa irin wadda kowa kansa kawai ya sani. Rayuwar da idan mutum ya sami ɗan
abin da zai ci sai ya manta da wasu makusantansa. Irin wannan hoton rayuwa ne
Amali Sububu na ƙasar
Maradun a jihar Zamfara, ya ambata a cikin wata waƙa tasa. Amali Sububu, yana cewa:
“Ashe yunwag ga na
sa,
Mutum ya gaza da
mata,
Ya sa a yi mai jiƙo,
Ba ya ce mata tashi
ga shi”.
(Amali
Sububu, waƙar Mai batun yaƙi da sabra).
A wani ɗan waƙa da Shayau
Maizari Gayari, ƙasar Gummi a
jihar Zamfara ya rera, yana cewa:
“ Yunwa bala’i ta Shaya
Mai sa a kama gudun dangi.”
( Shayau Maizari, ‘Maiƙwandama’)
Hoton da Amali Sububu ke son ya nuna mana a
cikin wannan ɗa na waƙarsa shi ne cewa, saboda yunwa mutum
zai kasa cika wani haƙƙi
da addininsa da kuma al’adarsa suka ɗora
masa na ciyar da matarsa. Ya sa a jiƙa masa garin rogo/kwaki amma kuma ya manta ba
zai ba matarsa ba. Wannan rayuwa ce irin ta lokacin yunwa. Shayau kuwa cewa ya
yi yunwa tana sa a guji dangi.
2.2 Yawan Fushi Da Kisan Aure
Aure
halacci ne na zamantakewa tsakanin mace da namiji su kasance mata da miji domin
samar da zuriya ta halat ta yadda za a sami danƙon zumunci a tsakanin al’umma da kuma mutane
nagartattu. Al’ummar Hausawa ta rungumi al’adar aure tun gabanin saduwarta da
kowace al’umma ta duniya walau daga gabas ko daga yamma. Hausawa kan ƙulla aure ne da niyar ɗorewarsa
har abada face in lamurra sun dagule ne ake samu rabuwa tsakanin ma’aurata. A
lokacin yunwa akan sami yawan hushi saboda zafin rai da yunwar take haddasawa
wanda wani lokaci kan haifar da yawan kisan aure. A kan yawan husata da zafin
rai wanda yunwa take haddasawa, wani mawaƙi a wani ɗan
waƙa tasa yana
cewa:
Jagora: Hunger is very danger
If you
are feeling hunger
It will
make you anger.
Yara: Wai yunwa bala’i ta
In
yazzan kana jin ta,
Zahin rai take sa wa.
(Alh. Sani Da’aino
Gyalange Waƙar Sarkin Noma Maigayya).
A kan kisan aure
kuwa, wata Mawaƙiya mai waƙar begen Manzon
Allah, Gwamma Maibege Iyaka, ƙasar Gummi a Jihar Zamfara ta faɗa a wani ɗan waƙa tata, cewa:
“ In hwaɗa maka
Yunwam Muɗa marar albarka
Ta sa maza sakin matansu
Ta sa maza su tudda ɗiyansu
Abdu an wani ɗa sai lahira ya gane gidansu.”
( Gwamma Maibege, ‘Yunwar Muɗa’)
Shayau Maizari Gayari
kuwa cewa ya yi:
“ Maikwandama zakkay yunwa
Ta bi wake ta ride
Ta bi maiwa ta ride
Ta bar mazanmu cikin ragga
Koyaushe mata na kotu
Kowa a kai mashi sammace
Kowace a ce mata na bakki.”
( Shayau Maizari, ‘Maiƙwandama’)
A wani ɗan waƙa na daban, cikin waƙarsa ta ‘Maiƙwandama’, Shayau na
cewa:
“ Maiƙwandama babbay yunwa
Ko mai idanu ta kamtce
Yau kam makahi tah hwarma.”
“ Maiƙwandama ka kashin
arme
Don kak ku ce mana mata na.”
“ Ga mace ba komi na kari
Macce babu hurak kurɓi
Waken Adar ya ƙare
Ɗan hanƙurin nan guntu na.”
( Shayau Maizari, ‘Maiƙwandama’)
2.3 Zama Da Ƙazanta ko Rashin
Tsabta
Tsabta masu iya
Magana suka ce cikon addini. Hausawa mutane ne da al’adarsu da kuma addininsu
na musulunci suka tanadi a yi tsabta ta jiki da ta sutura. Wannan ya haɗa kwalliya ta hanyar
saka sutura kyakkyawa, da ɗaura lalle tare da shafe-shafe a fuska ga mata, Wannan
kyakkyawan al’amari kan sami naƙasu a lokacin da al’umma ke fama da
yunwa. Makaɗa Shayau maizari
Gayari ya ambaci wannan a wani ɗan waƙa tasa ta ‘‘Yar wara’ inda ya ce:
“ ‘Yar wara Shayau in gaya ma
Mai hana mata shafa kwalli
Ɗarmin lalle ba a yi
nai.”
“ Haba ‘yar wara!
Shayau yunwa ba ta tausai
Ka tcinkai mata sun yi gungu
Kowace na shafah hawaye
Ɗarmin lalle ba a yi
nai
Har da kitso bana ba su yi nai.”
( Shayau Maizari, Waƙar ‘ ‘Yar wara’)
Wara wake ne da aka
fi sani da waken soya. Ana sarrafa shi a yi wani abinci na ƙwalama da ake kira
wara. A shekara ta 1996, zamanin mulkin soja na Janar Sani Abaca, mutane sun
shiga cikin matsi na tattalin arziki da ta kai har wasu suna cin dusa ta waken
soya, bayan an haɗa ta da ƙuliƙuli da gishiri.
Wannan matsi na rayuwa ne Shayau Mai zari Gayari a ƙasar Gummi, jihar
Zamfara ya waƙe, ya kuma saka wa wannan yunwa suna ‘Yar wara.
Ɗaurin lalle kwalliya
ce da matan Hausawa kan yi ta hanyar kwaɓa garin lalle a saka a hannu da ƙafafuwa domin jiki ya
kasance ja. Ana saka gishirin lalle domin a samu baƙi a ƙafa da hannu, abin
gwanin sha’awa. Kitso ma kwalliya ce da ake wankewa tare tsefe gashin mata a
kuma shirya ta hanyar tufƙa. Lalle da kitso gyaran jiki ne da al’adar Bahaushe ta
tanadar wa mata. A lokacin yunwa kamar yadda wannan Mawaƙi ya nuna mata ba
sukan damu da yin irin wannan kwalliya ba saboda sai ciki ya cika ake zancen
kwalliya.
2.3 Yaudara Da Sata
Yaudara da sata
miyagun halaye ne da al’adar Bahaushe da kuma addinin musulunci ba su ba gurbin
zama ba a cikin al’umma. Don haka ne ma ya sa duk wanda yake yin waɗannan ɗabi’u, akan yi masa
wani kallo na mutumin banza kuma ma akan yi masa kyara, wani lokaci akan yi
hukunci ga wanda ya aikata ɗaya daga cikin ɗabi’un. Duk wannan matsayi da ɗabi’un suke da shi a
al’umma, a lokacin da rayuwa ta shiga cikin ƙunci na matsanancin
talauci da yunwa sai a tarar wasu suna aikata halayen ba don suna da muradin
yin haka ɗin ba sai don halin
matsi da ƙunci na rayuwa da suka sami kansu a ciki. Halin ɓera ne Shayau Maizari
Gayari ya kawo a cikin wani ɗan waƙa nasa. Wai wani ya saci ƙullin garin kwaki a
wurin wata Bayaraba amma sai ta gan shi.
“Ya tai wurin garin kwaki
Sai da yah hizgo ƙulli
Mama sai tas sa kuwa
‘Soho’ a zan ‘soron’ Allah
Koyaushe sai ke dau kulli.”
( Shayau Maizari, waƙar “ Maiƙwandama”)
Ita ma Gwamma Maibege
Iyaka ta kawo hoton yaudara a cikin wani ɗan waƙa tata ta
‘Shahwa’atu’ inda take cewa:
Jagora: Ba ka san ƙabdogala ba
Shiga mota babu kuɗɗi
Yara: Muhammadu Ɗanlarabawa
Jagora: Yaro ba ka san ƙabdogala ba
A shige mota babu kuɗɗi.
Wai a lokacin wata
yunwa ce da ake kira ‘Shahwa’atu’ mawaƙiyar da yaranta suka
shiga motar haya ba tare da suna da kuɗin biya ba. Sai da aka kai su wajen da za su
sauka aka tambayi kuɗin mota shi ne take
yi wa yaron mota wannan tambayar .
2.4 Talaucewa
Yunwa da
talauci, abokan tafiyar juna ne, wato Ɗanjumma ne da Ɗanjummai. A lokacin yunwa, ba ƙarancin abinci kawai ake fama da shi
ba, har ma da talauci. A sakamakon matsanancin rashin abinci da na kuɗi,
mutane kan sayar da kayayyakinsu har ma da dabbobi don su sayi abinci. Matan
aure kuwa sukan sayar da kayan ɗakinsu kamar
kwanoni da gadaje, don su sami kuɗin
sayen abinci, lokacin da mazajensu suka kasa. Waƙoƙin yunwa sukan ƙunshi bayani irin wannan. Misali, wani ɗan
waƙa na waƙar ‘‘Yar Zanhwara’ yana cewa:
‘Yaz
zanhwara ba ki barin kanta
Ke canye
kabid da tasohi
Balle kwalla
abin banza
Hwanteka ba
a ko magana
Kai hadda
zanen gado an kai
An canye ɓula
da ɗan sululuf
(Hira
da sa’a Maiƙosai
Gummi, ranar 6/11/04).
Zamfara jiha
ce da aka ƙirƙiro a watan Oktoba na shekarar 1996,
lokacin mulkin soja ƙarƙashin jagorancin Janar Sani Abaca. A
daidai wannan lokaci, mutane suna cikin wani hali na ƙaƙa-ni-ka yi soboda matsi na tattalin arziki da
kuma ƙarancin
abinci. Wannan matsin shi ne wasu suke kira ‘Yar Zamfara”. Wannan waƙa ta nuna yadda matan aure suke kwashe
kayan ɗakinsu kamar
kwanoni, da tasoshi, da katifu domin sayarwa a sami kuɗin
sayen abin da za a ci.
A wata mai
kama da wannan, Shayau Maizari yana cewa:
Nit tai bara
Shayau ƙauye
Ni iske mata
na shiƙa
Nit tai bara
Shayau ƙauye
Manu na
kukan yunwa
Ga ni ba ni
gani Shaya
Dac can guda
tac ce shaya
Shaya koma
birninku
Koyaushe
birni, birni na
Na sai da
hwanteƙa
shidda
Na ba miji
ya sai tsaba
Sai guda
tacce shaya
Ko ni awaki
sun ƙare
Saura na
ga-kiwo ɗai an nan
(Shayau
Maizari: ‘Maiƙwandama’).
A wani ɗa
na waƙarsa ta “‘Yar
Wara” ’, Shayau yana cewa:
‘Yar wara Shayau
in gaya ma
Ta ci awaki,
ta ci kaji
Ta amshe
shanun talakka
Ta bar ƙato na hawaye
Ta amshe
shanun talakka
To Allah ka
jiƙam Musulmi
(Shayau Maizari: ‘‘Yar wara’).
Ita ma
Gwamma Maibege tana cewa a wani ɗa
na waƙarta ta ‘Shahwa’atu’.
Jagora: Ina
kurin na wanke Jamila
Uba bai sai gado ba
Na za ka na tara kaya
Shahwa’atu taf faɗa
kaya
Tac ce ko ɗai
ba ya saura
‘Yan amshi: Muhammadu Danlarabawa
Jagora: Nic
ce in ke canye kaya
Ga mata na kiɗa
na turmi
Wasu had da kwarya
Suna ɓacin
ki, ni kau
Gwamma nike yaw waziri
Allahu ya taimake ni
In nit tahi bege na Allah
Sai na shiri na tallata ki
(Gwamma Maibege: ‘Waƙar Shahwa’atu’).
Idan aka
dubi waɗannan ɗiyan
waƙa da aka
kawo daga waƙoƙi daban-daban za a ga kowannensu yana ɗauke
da turken sayar da kaya da mutane ke yi a lokacin yunwa domin a sayi abinci.
Wannan kuwa alama ce ta talaucewa.
2.5 Ƙaura
A lokacin
yunwa mutane kan yi ƙaura
daga wuri zuwa wuri, musamman ana barin inda rashin abinci ya fi tsanani zuwa
wurin da ake ganin an fi wadatarsa. Galibi mutanen da ke arewa sun fi yin ƙaura zuwa kudu. Ba abin mamaki ba ne
ko kaɗan don waƙoƙin yunwa sun ƙunshi irin wannan hali don kuwa abu ne da ke
faruwa a zahiri. Tabbacin samuwar irin wannan ya zo ne a cikin waƙar Amali Sububu ta ‘Mai batun yaƙi da Sabra’, inda yake cewa:
Wanga
irin baƙin
zamani Allah kiyaye
Wasu
na ta tashi suna tahiyassu Gwambe
Mu
kam mun tsaya nan muna gyaran gidaje
In
mun cimma gyaranta ba tashi mukai ba
In
ta ɓaci ko Singa ga ba ta rigyam mu Bima
A nan Amali
ya nuna hali na mutane suna ƙaura
zuwa Gombe to amma su kam ba su tafi ko’ina ba, amma idan lamari ya ƙara tsananta to su ma bisa kafafunsu
suke na yin ƙaura.
Ita ma Gwamma Maibege Iyaka, cikin waƙarta ta Muɗa
tana cewa:
Tac
ce ina maza manoma gero
Ina
maza manoma dawa
Ƙaƙa ƙara ƙaƙa kun ji
Kun
gani tsuma, bulala
In
rimbiɗe ku in rabke ku
In
lalabo ku in koro ku
In
gargaɗo ku duk ku yi Bauci
Ita
ta muɗa marar alabrka
Da
tag gargaɗo maza suka watce
Waɗansu
sun wuce Tadurga
Dibo
waɗansu sun kai Kanya
Wasu
ko na Magajiya sun zauna
Wasu
ko sun wuce a Dirin Daji
Duk
korenta na marar albarka
Ta
yamutce maza sun watce
Ta
ce ta yi rantsuwa da ikon Allah
Wani
sai lahira da shi da gidansu
(Gwamma Maibege Iyaka: waƙar Muɗa).
A waɗannan
ɗiyan waƙa, Gwamma ta mutuntar da yunwa cewa ta yi wa
maza bulala ta kuma gargaɗo su duk sun
haura zuwa ƙasar
Zuru. Ta ma rantse wai wani da shi da dawowa gidansu sai lahira. A wani ɗan
waƙa har wa
yau, Amali Sububu ya kawo irin wannan zance na yin ƙaurar jama’a a lokacin yunwa musannan
yunwa ‘Yar Buhari wadda aka yi fama da ita a shekara ta 1984, zamanin mulkin
soja ƙarƙashin jagorancin Janar Muhammadu
Buhari. A ciki yana cewa:
Yunwa
ta taho da gorori
Ta
iske maza
Duk
ƙaton da taƙ ƙuma ga wuya
Sai
ya shantala
Sai
ya hurce Kwantagora
Dan
nan ta waiwayo
Ta
ga katon da bai ɗaga ba
In
taƙ ƙumai bugu
Wajjen
yamma za ya sauka
‘Yan amshi: Riƙa da gaskiya
Rana ba kashi ta kai ba
Yari ɗan
bangi rana ba ta sa ka rama.
Jagora: Ga hwa kudun muna ta yi
Amma
ba a yin arewa
(Amali
Sububu: ‘Waƙar
Noma ba ya sa ka rama’).
A cikin
wannan ɗan waƙa, Amali ya kawo yadda yunwa take korar
maza, ta tarwatsa su, su warwatse zuwa wurare daban-daban don neman sauƙi a wurin da ake gani ana iya samunsa.
A nan Amali ya mutunta yunwa ya ce tana ɗaukar
gora ta riƙa
dukar maza. Duk wanda ta duke shi komai zamansa ƙato, sai ya sheƙa a guje, ya yi ƙaura zuwa kudanci, wasu har sai sun
zarce Kontagora a jihar Neja. Idan yunwa ta sake waiwayowa, duk wanda bai ƙaura ba, shi za ta sake doka, idan ta
sha shi gora, yamma zai dosa, ya yi tasa ƙaurar.
Kammalawa
Wannan muƙala ta yi ƙoƙarin duba irin halaye na ƙunci da rayuwa kan sami kanta a
zamantakewar Hausawa musamman a lokacin yunwa wadda kan faɗa
ƙasar Hausa
lokaci-lokaci sakamakon rashin wadatar ruwan sama da kuma talauci da ya yi wa
al’umma katutu a wannan ƙasa.
Muƙalar ta yi
waiwaye ne kan irin yadda zamantakewar kan sauya daga abu kyakkyawa zuwa mai
muni a duk lokacin da al’umma ta jarabtu ta bala’in yunwa. Waɗannan
halaye kuwa an zaƙulu
su ne kamar yadda wasu mawaƙan
baka suka ƙyallaro
su, suka kuma bayyanar da hotonsu a cikin waƙoƙinsu daban-daban.
Kamar yadda aka faɗa,
waɗannan abubuwa ko halaye ba abin da
zuciya take muradi ba ne. Hasali ma abubuwa ne masu ɗarsasa
zuciya. Da yake rayuwa juyi-juyi ce, in ji kwaɗo,
wai da ya faɗa ruwan zafi, ba
illa don an yi waiwaye a kansu tun da mawaƙan sun ga dacewar ambaton su a cikin waƙoƙinsu, ba abin da zai hana mai nazari ya zaƙulo su a cikin waƙoƙin. Waɗannan
misalai da aka kawo daga wasu waƙoƙi, ba iyakacin su ke nan ba amma dai duk da
ba a kawo su duka ba, muƙalar
ta yi nasarar tsokaci a kan matsalolin zamantakewa da ake samu a lokacin yunwa
kamar yaudara da sata ko rashin gaskiya, da yadda mutane suke talaucewa, su
karar da abubuwan da suka mallaka domin sayen abinci, da yadda ake samun yawan
kisan aure, da yadda ake samun rayuwa ta kaɗaici
wanda ke haddasa rowa, da kuma uwa uba yadda mutane suke yin ƙaura zuwa inda suke sa ran za su sami
abinci. Wannan ƙaura
ana yin ta ne, wani lokaci ba tare da iyali ba. Wannan kuma sai ya haddasa wasu
matsalolin na daban.
A ƙarshe wannan muƙala tana kira ga gwamnatin tarayya da ta
jihohi da su ɗauki matakai na
tallafa wa manoma ta hanyar samar masu da isasshen takin zamani mai rahusa, da
kuma ba su tallafi na kuɗi ko da
bashi ne marar ruwa, wanda za su biya ko da da kayan gona da suka yi rara ne.
Haka hukuma ta sayi kayan amfani gona daga hannun manoma a lokacin kaka, a
farashi mai armashi ta yadda za a kare lagon ‘yan baranda. Wannan zai taimaka
matuƙa wajen rage
aukuwar yunwa, da rage talauci a tsakanin al’umma.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.