Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Koyar da Harsuna da Al’adu, Tsangayar Fasaha da Ilimi, Jami’ar Tarayya, Gusau don neman digiri na farko.
Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (2)
NA
HIZBULLAHI ƊANLAMI
BABI NA ƊAYA: - SHIMFIƊA
1.0 Gabatarwa
Wannan babi yana ɗauke ne da bayanin tsarin yadda aka shata binciken da kuma yanayin gininsa. Masana harshen Hausa
tun farko sun yi ƙoƙarin karkasa harshen (Hausa) ta fuskar koyo da koyarwa da kuma bincike da
nazari zuwa manyan fannoni uku wato, harshe, adabi da kuma al’ada.
Tushen wannan bincike mai
suna “Magini (Birkila/messin) a garin Kwatarkwashi”, yana ƙarƙashin fannin al’ada ne, kuma yana ɓangaren sana’a ne, fannin
samar da muhalli da sauran ababen da magini (Birkila) ke ginawa domin
inganta rayuwar Bahaushe.
A ɗan hasashena, al’ada tana da muhimmanci daga cikin
fannonin uku, wato harshe, adabi da kuma al’ada. Saboda al’ada, ta shafi
rayuwar ɗan’ Adam ne baki ɗaya tun daga haihuwarsa har zuwa ƙabarinsa. Magini (Birkila/messin)
yana cikin sahun gaba daga cikin mutanen da suke cin gajiyar al’adar
garagajiya. Wato sana’ar gini da magini (Birkila/messin) ke aiwatarwa wani
babban reshe ne na al’ada. Kuma birkila yana da tasiri ƙwarai da gaske wajen bunƙasa da haɓaka al’adar Bahaushe tun ba a fannin sana’o’in gargajiya
ba.
Wannan bincike za a
gudanar da shi ne a kan “Birkila/Messin a garin Kwatarkwashi”, sannan za a yi ƙoƙarin bayyana yadda magini (Birkila)
yake a garin Kwatarkwashi, da ci gaban da sana’ar ta samar ga shi kansa
(Brikilan) da matasan garin kwatarkwashi. Haka kuma harshen Hausa ya sami bunƙasa gwargwadon hali.
Domin ganin an cimma nasarar kammala wanann bincike, an karkasa aikin
binciken zuwa babuka biyar.
Babi na farko yana ɗauke da shimfiɗar wannan bincike da gabatarwarsa, wanda zai tattaro bayanai a kan manufar
bincike da dalilinsa. Akwai kuma farfajiyar bincike, muhimmancin bincike da
kuma hanyoyin gudanar da binciken. Haka kuma da hujjar ci gaba da bincike, da
bitar wasu ayyukan da suka gabata.
A babi na biyu kuwa, nan
ne za a bayyana tarihi da al’adun garin Kwatarkwashi, wanda ya ƙunshi gabatarwa da taƙaitaccen tarihin
Kwatarkwashi da tsarin gine-ginen Kwatarkwashi. Bayan wannan akwai bayanin
al’adun garin Kwatarkwashi da kuma shigowar baƙin al’adu a garin Kwatarkwashi. Har
wa yau, da tasirin shigowar baƙin al’adu a garin Kwatarkwaahsi, duk dai a wannan
bincike.
A babi na uku, za a
bayyana sana’ar gini a garin Kwatarkwashi, inda ya ƙunshi gabatarwa da ma’anar gini da
ire-irensa, da kuma ma’anar magini (Birkila/Messin) da kuma bayanin maginin
gargajiya da maginin zamani. Sannan a ƙarshen wannan babi za a kalli gini a garin Kwatarkwashi
da kuma irin gudunmuwar da magini (Birkila/messin) ke bayarwa wajen bunƙasa kalmomin Hausa.
Babi na huɗu, ya ƙunshi tasirin sana’ar gini ga bunƙasa tattalin azikin Kwatarkwashi. A ƙarƙashinsa akwai ya haɗa da gabatarwa da samar da aikin yi ga matasa da bunƙasa kiyo da noma a garin
Kwatarkwashi. Haka kuma da bunƙasa saye da
sayarwa a garin Kwatarkwashi.
Babi na biyar, kuma na ƙarshe shi ne babin da ya
ƙunshi kammalawar wannan bincike, wanda da ya ƙunshi gabatarwa da jawabin sakamakon
bincike da shawarwari da kuma naɗewa, da kuma manazarta.
1.1 Manufar Bincike
Manufar wannan bincike ita
ce samar da wani kundin bincike wanda zai
zama a matsayin wani ɗan yunƙuri da aka gabatar a ɓangaren al’ada, domin raya al’adun Hausawa.
Manufofin wannan bincike
suna da yawa, amma ga wasu daga cikinsu: -
(a)
Samar da ɗan abin dubawa ga mai nazari ko karatu.
(b) Farfaɗo da al’adun Hausawa, musamman ɓangaren sana’ar gini da magini (Birkila). Ganin, yadda
sauran takwarorin sana’a’oin sukayi masa fintinƙau ta fannin bincike da nazari.
(c)
Zaburar da masana al’adu
da masu bincike zuwa ga sana’ar gini da magini (Birkila). Saboda gefen yana
cikin jerin gwanon al’adu da suka kusa mutuwa. Saboda rashin bincike mai zurfi
a wannan fanni.
(d) ƙoƙarin tattara bayanai waɗanda suka fayyace tsakanin maginin gargajiya da na
zamani.
(e)
Bayyana muhimmancin
magini (Birkila) da tasirinsa da kuma irin gudunmuwarsa ga al’umma.
(f)
A ƙarshe an bayyana tsintsar rawar
da Magina (Birkila) suke takawa wajen bunƙasa tattalin arziƙi da kuma inganta
rayuwar matasa.
1.2
Dalilin
Bincike
Dalilin da ke sa a gudanar da bincike suna ɗauke da manufofi daban-daban kamar yadda ake aiwatar da shi binciken.
Saboda haka, dalilan da suka sa aka gudanar da wannan bincike suna da yawa,
amma ga wasu kamar haka:
(a) Babban dalili na ɗaya ga aiwatar da wannan bincike shi ne, cike wani gurbi
da masana suka manta da shi cikin littafan da suka rubuta, waɗanda ba su yi magana a kan su ba.
A fannin al’ada Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, ya rubuta
littafi a fannin al’adar, amma bai ambaci sana’ar gini da magini (Birkila) ba
duk da sanin kowa ne al’umma ba za ta iya rayuwa babu muhalli ba.
(b) Dalili na biyu kuwa,
shi ne, rashin tsayuwar masana su yi zuzzurfan bincike a kan sana’ar gini da
magini (Birkila), sai dai a shafi wurin sama-sama a wuce, misali kamar:
Farfesa, Ibrahim Yaro Yahaya da wasu (1992), sun kawo
sana’o’in Hausawa na gargajiya, inda suka ambaci sana’ar gini a ciki, amma ba a
yi bayanin sana’ar tiryan-tiryan ba, kamar yadda ya kamata. Madogarata ita ce littafin
nasu mai suna “Darussan Hausa don manyan makarantun sakandare (1992). A nan ne
suka kawo sana’o’in.
(c) Dalili na uku,
fannin al’ada sashe ne da yake da fatara irin ta ƙarancin masana a gefen. Saboda ko a ɓangaren wasu al’adun za a ga cewa al’adun suna cikin
hatsari (endangered) kamar gini da magini (Birkila).
(d) Zaburar da masana da
masu bincike a kan al’ada, domin karkatar da hankalinsu zuwa fannin sana’ar
gini da magini (Birkila), domin haɓɓaka bincike a gefen.
Dukkan al’amurran duniya baki ɗayansu da ke gudana akwai dalilin kasancewarsu da kuma na
faruwa, kuma dalilan na iya zama a sarari ko a ɓoye. A taƙaice, waɗannan ne da wasu dalilan da ya sa aka gudanar da wannan bincike.
1.3 Farfajiyar Bincike
Magini (Birkla/ Birkilanci) wani babban rukuni ne a cikin
sana’o’in al’ummar Hausawa jiya da yau. Saboda kowace irin halitta ta duniya ba
za ta iya rayuwa ba tare da muhalli ba. Hasali ma yana ɗaya daga cikin abubuwa uku da ake buƙata a rayuwa. Wato muhalli (shelter). Wannan bincike zai
taƙaita ne a kan “Sana’ar birkila (messin) a garin Kwatarkwashi”.
A ƙarshe, binciken zai bayyana ma’anar birkila da kuma
ire-iren abubuwan da magini (Birkila) yake ginawa da kuma irin gudunmuwar da
magini (Birkila) yake bayarwa wajen bunƙasa harshen Hausa, sannan da muhimmancinsa ga rayuwar
al’umma.
1.4 Muhimmancin Bincike
Kamar yadda masana al’ada suka bayyana ta da cewa “hanya
ce da ta shafi rayuwar ɗan Adam tun daga haihuwarsa, har zuwa ƙabarinsa”. Wato ke nan sana’ar gini wata
abu ce mai muhimmancin gaske musamman ta hanyar samar da muhalli ga al’umma.
Saboda haka, magini (Birkila) yana a sahun gaba cikin
mutanen da suke ba da gudunmuwa wajen bunƙasa al’adu da sana’o’in gargajiya da kuma tattalin arziƙin al’ummar Hausawa.
A taƙaice, babban muhimmancin wannan bincike shi ne samar da
bayanai nagartattu game da sana’ar magini (Birkila) da rawar da suke takawa, wajen samar da aikin yi ga matasa da rage raɗaɗin talauci cikin al’umma.
1.5 Hanyoyin Gudanar da
Bincike
Kamar yadda yake a bayyane sanin kowa ne cewa, kowa ne
irin bincike ne za a gudanar ko gabatar, musamman ma na ilmi ba zai
kammalu ba, ba tare da an bi hanyoyi da dabarun gudanar da shi ba. Saboda haka,
kafin a kammala wannan bincike, za a yi amfani da hanyoyin da suka dace tare da
dabaru daban-daban domin ganin haƙa ta cimma ruwa. Za a ziyarci ɗakunan karatu da cibiyoyin ilmi daban-daban domin samun
bayanai daga ayyukan masana daban-daban a kan abin da ake nazari na sana’ar gini. Hanyoyin wannan
bincike sun haɗa da: -
-
Nazarin littafan da aka
wallafa a kan al’ada
-
Nazarin littafan da aka
walllafa a kan fannin Hausa guda uku (Harshe, Adabi da Al’ada) don koyo da
koyarwa.
-
Nazarin maƙalu waɗanda malamai da masana suka gabatar a Jami’o’i da
cibiyoyin ilmi daban-daban, masu dangantaka
da wannan bincike.
-
Tattaunawa ta musamman
da malamai da suaran masana dangane da abin da ake bincike a kansa, domin neman
ƙarin haske da shawarwari.
A taƙaice, waɗannan su ne hanyoyi da dabarun da aka gudanar a lokacin da ake wannan bincike.
1.6 Hujjar Ci Gaba da
Bincike
Bincike a kan “Magini (Birkila) a garin
Kwatarkwashi”. Yana da hujjar da za a ci
gaba da gudanar da shi. Hakan ya tabbata ne la’akari da bitar ayyukan magabata
da aka yi, da sauran ayyukan da suka gabaci wannan bincike. Ba shakka masana da
dama sun yi rubuce rubuce a kan gini da sauran abubuwan da suka danagance shi. Ɗalibai ma sun rubuta
kundaye daban-daban. Amma duk da haka wannan bincike yana da mashiga da hujjar
da za a ci gaba da shi domin ba a ba shi muhimmanci ba a baya sosai. Idan an yi
kuma, to wannan binciken zai fito da wasu muhimman abubuwa waɗanda ba a ambata a
na farko ba.
1.7 Bitar Ayyukan da
Suka Gabata
Al’adun Hausawa sun daɗe ana rubuta su da nazari a kan su, saboda an ɗan sami lokaci ana taskace sassan al’ada daban-daban ta
rubutawa da wallafawa.
Masana da manazarta da marubuta da yawa sun yi ayyuka da
dama da suka shafi sana’o’in Hausawa na gargajiya, da ma yadda ake kallonsu a
al’adance. Dalilin haka ne ya sa gabanin aza tubalin wannan aiki aka yi ɗan ƙoƙarin bitar ayyukan da suka gabaci wannan bincike, masu dangantaka da wannan
aiki gwargwadon hali. Saboda tantance wuraren da aikin ya yi kama, da inda aka
bambanta.
Ayyukan da aka duba lokacin gudanar da bitar sun haɗa da wallafaffun littafai, mujallu da maƙalu da kuma
kundayen bincike. Ga jerin ayyukan da hannu ya sami kai wa gare su kamar haka: -
1.7.1 WALLAFAFFUN /
BUGAGGUN LITTAFAI
Akwai wallafaffun ko bugaggun littafai da dama masu alaƙa da wannan aiki nawa.
Daga ciki akwai littafin:
Rimmer, da wasu (1966) a cikin littafinsu mai suna “Zaman
mutum da sana’arsa”, marubutan sun rubuta littafin ne a kan babuka, wato daga
babi na ɗaya har zuwa babi na biyar, yayin da
babi na biyu suka yi bayanin noma da asalin sana’o’in lambu da noma tsohon
ciniki da gonar gwamnati da noma a Ingila, da noma a ƙasar Masar da kogin Nile da ganuwa
da ƙasar Asiya da manoma a ƙasar Sin da kogunan ƙasar Sin da kuma mutanne Sin.
A babi na biyar suka yi bayanin ginin tukwane a Nijeriya
ta Arewa da kuma faɗi-ka-mutum (Tangaram).
Wannan littafi yana
da alaƙa da wannan aiki nawa, saboda sun yi bayani ne a kan sana’o’in Hausawa,
musamman ginin tukwane, sai dai sun bambanta da wannan aikin, domin littafin
sun gina shi ne game da zaman mutum da sana’arsa, yayin da aikina yana bayani a
kan magini (Birkila/ messin) a garin Kwatarkwashi.
Alhassan da wasu (1982) a cikin littafinsu mai suna
“Zaman Hausawa”. Marubutan sun yi ƙoƙarin kawo wasu sana’o’in Hausawa, waɗanda suka haɗa da noma da ƙira da fawa da Farauta da kiwo da saƙa da kaɗi da rini da fatauci da
sarauta da maƙamai da sauransu.
Aikin yana da alaƙa da nawa aikin,
domin ya shafi sana’o’in Hausawa da al’adunsu. Bambancin da ke tsakanin
aikin nasu da nawa shi ne, aikina yana
magana ne a kan birkila/ messin a garin Kwatarkwashi, su kuwa nasu a kan
sana’o’in Hausawa gaba ɗaya.
East, R.M (1968) a littafinsa mai suna “Labaru na da da
na yanzu”. Marubucin ya rubuta littafin a kan babuka goma.
A babi na farko ya kawo tarihin fitattun sana’o’in
Hausawa na gargajiya, tare da bayaninsu gwargwadon fahimta. Yayin da babi na
biyu kuma ya bayyana wasu fitatun sana’o’in mata na gargajiya. Wannan aiki yana
da alaƙa da nawa aikin ainun ta fuskar
sana’o’i da al’ada. Bambancin da ke tsakaninsu shi ne, aikina yana magana a kan
“Magini (Birkila/ messin) a garin
Kwatarkwashi, da yadda sana’ar ta
taimaka wajen samar da aikin yi ga matasa da sauransu.
Yahaya da wasu (2001) a cikin littafinsu mai suna
“Darussan Hausa don manyan Makarantun Sakandare na biyu”. Marubutan sun yi
magana ne a kan sana’o’in gargajiya, ma’anar ita kanta sana’ar tare da kawo
sana’o’in maza da na mata da kuma na tarayya, sai dai ba su ambaci magini
(Birkila/ Messin) a cikin wannan littafi ba. Amma yana da alaƙa da nawa aikin ta
fuskar sana’o’in gargajiya, duk da haka sun bambanta da nawa aikin domin su nasu yana magana ne a
kan Hausawa baki ɗaya, yayin da nawa aikin yake bayani
a kan birkila/messin a garin Kwatarkwashi.
Shi kuwa Yakasai, (2002) a littafinsa mai suna “Mordern
Comprehensiɓe Hausa Language for Schools and
Colleges”. Marubucin ya yi ƙoƙari wajen tsettsefe sana’o’in gargajiya na maza da na mata, da kuma
tasirin sana’o’in ga al’umma. Babu
shakka wannan aikin yana da alaƙa makusanciya da nawa
aiki. Bambancin da ke tsakanin wannan aikin da nawa shi ne, nawa aikin na
magana ne a kan birkila/messin a garin Kwatarkwashi, yayin da nasa aikin ke
magana kacokan a kan al’adun Hausawa.
Bunza, (2006) kuwa a littafinsa mai suna “Gadon feɗe Al’ada”. Marubucin ya yi magana a kan sna’o’in Hausawa,
musamman maƙera da ma’aska da masunta da manoma da mahauta da kuma maɗora ta fuskar tsafi ko gado, sai dai bai yi magana a kan
sana’ar gini ko magini (Birkila) ba, amma aikin nasa yana da alaƙa da nawa aikin ta
fuskar al’adu. Bambancin da ke tsakaninsa da nawa shi ne, nasa yana magana ne a
kan al’adun Hausawa baki ɗaya, yayin da nawa aikin ke magana a kan magini (Birkila/ messin) a garin
Kwatarkwashi.
Gusau, G.U. (2012) a littafinsa mai suna “Bukukuwan
Hausawa”. Marubucin ya yi ƙoƙari matuƙa, don kuwa ya yi magana a kan sana’o’i daban-daban tun daga kan Fatauci da
noma da Farauta da gini da wanzanci/, da sauransu. Ya bayyana ma’anar gini ne
kawai da ire-irensa da kuma irin sauyin da ginin ya samu tasirin zamani. Bambancin
da ke tsakanin aikina da nasa shi ne, nasa aikin na magana ne kaco-kan a kan
Hausawa baki ɗaya, yayin da nawa kuwa ya keɓanta a kan birkila/messin a garin Kwatarkwashi.
1.7.2 MUJALLU DA MAƘALU
Muhammad (2016) a maƙalarsa mai taken “Gudunmuwar
sana’ar ƙira wajen samar da kayayyakin Hausawa na gargajiya”. Wadda ya
gabatar a cikin mujallar Argungu Journal of Language Studies. Marubucin ya yi
bayani a kan su wane ne Hausawa da ƙasar Hausa da muhimmancinta da sauransu. Wannan maƙala tana da alaƙa da wannan aikin ta
fuskar sana’a, sai dai bambancin da ke tsakanin maƙalar da aikina shi ne, aikinsa ya taƙaita ne a kan sana’ar ƙira kawai, yayin da nawa
aikin yake magana a kan birkila/messin a garin Kwatarkwashi.
Zabi, M.A. da Aliyu (2016) a cikin maƙalarsu mai taken “Tasiri
da barazanar zamani a kan sana’ar noma”, wadda suka gabatar a cikin Mujallar
Argungu Journal of Language Studies. Marubutan sun yi magana ne a kan Hausawa
da sana’ar noma a ƙasar Hausa, da ma’anar tattalin arziƙi da bunƙasar tattalin arziƙin Bahaushe da suaransu. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta
fuskar sana’o’i da al’adu. Abin da ya bambanta tsakaninsu shi ne, aikinsu na
magana ne a kan tasiri da barazanar zamani a kan sana’ar noma ne, nawa kuwa ya
fi mayar da hankali ne a kan birkila/ messin.
Maryam (2015) a maƙalarta mai taken “Sana’o’in Hausawa na gargajiya da
tasirinsu a zamanance”, wadda ta gabatar a cikin mujallar garkuwar Adabin
Hausa. Marubuciyar ta yi ƙoƙari ƙwarai da gaske wajen fito da sana’io’in Hausawa na gargajiya kamar noma da
kiwo da fatauci da ƙira da saƙa da jima da dukanci, da sauransu.
Wannan maƙalar tana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar sana’o’in Hausawa na gargajiya da al’adu, amma
bambancin da ke tsakaninsu da nawa aikin shi ne: Nata aikin na magana ne a kan
sana’o’in Hausawa na gargajiya baki ɗaya, yayin da nawa aikin ya shafi Birkila/ messin.
Gusau, (2013) a maƙalarsa mai taken “Tsokaci a kan al’adun Hausawa”, wadda ya gabatar a cikin mujallar Harsunna
Nijeriya. Marubucin ya yi ƙoƙari ainun wajen fito da al’adun a sarari kamar yadda ya yi bayani a kan
al’adun al’umma, da al’adun Hausawa da kuma wuraren tanadin al’adun Hausawa.
Wannan maƙalar tana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar al’adu. Abin da ya bambanta aikinsa da nawa shi
ne; Nasa aikin yana magana ne a kan “Tsokaci a kan al’adun Hausawa” yayin da
nawa ya keɓanta a kan birkila/messi.
1.7.3. KUNDAYEN BINCIKE
Bunguɗu da wasu (1999) a kundinsu na takardar shaidar N.C.E mai taken “Bincike a
kan sana’o’in Kaɗi da daddawa da mazanƙwaila da tukanen laka na
da da na zamani a ƙasar Hausa”. Wanda aka gabatar a sashen Hausa na kwalejin ilmi ta Shehu
Shagari, Sokoto. Manazartan sun yi ƙoƙari ƙwarai da gaske wajen bayyana ma’anar kaɗi, kayan aikinta, yadda ake gudanar da ita. Ma’anar
daddawa da yadda ake aiwatar da ita da kuma kayan aikinta. Ma’anar mazanƙwaila, yadda ake yin
mazanƙwaila, kayan aikinta, yadda ake
tukanen laka na da da na zamani da kuma tasirin zamani a kan dukkan
sana’o’in Hausawa da al’adunsu. Bambancin da ke tsakanin aikina da nasu shi ne,
nasu yana magana ne a kan keɓaɓɓun sana’o’in ƙasar Hausa baki ɗaya, yayin da nawa
aikin yake magana a kan magini (Birkila/ messin).
Maru, S.I. da wasu (2012) a kundin bincikensu na takardar
shaidar N.C.E mai taken “Sana’o’in Daddawa a jihar Zamfara”. Manazartan sun yi bayani a kan sana’ar Daddawa da yadda
ake yinta, kayan aikinta tare da muhimmancinta. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta fagen
san’a, amma bambancin da ke tsakain aikinsu da nawa shi ne, nawa yana bayani ne
a kan birkila/messin (magini) a garin Kwatarkwashi.
Mallaha da Atiku, (2014) a nasu kundin na takardar
shaidar N.C.E mai taken “nazarin hanyoyin Bunƙasar mutanen yakin kwatarkwashi”.
Manzartan sun yi ƙoƙari sosai wajen bayyana hanyoyin bunƙasar rayuwar mutanen ƙasar Kwatarkwashi da ma’anar
tattalin arziƙi da albarkatun ƙasar Kwatarkwashi da suaransu. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta ɓangaren al’adu a Kwatarkwashi. Bambanci da ke tsakanin
aikinsu da nawa shi ne, aikina yana magana ne a kan magini (Birkila/ mesin) a
garin Kwatarkwashi.
Yahuza da wasu (2019) a kundin digiri na farko mai taken
“Nazarin Fitattun Al’adun Maguzawa a ƙasar Kwatarkwashi”. Wanda aka gabatar a Jami’ar Ahmadu
Bello, Zariya. Mai reshe a kwalejin kimiya da ƙere-ƙere ta ‘yan mata, Gusau (F.C.E.T).
Manazartan sun yi ƙoƙari matuƙa wajen fito da al’adun garin
Kwatarkwashi ƙwansu da kwarkwatarsu, da muhimmancin al’adun na maguzawan kwatarkwashi da
sauran muhimman abubuwa da kundin ya ƙunsa. Tabbas, wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta
fuskar al’adun garin Kwatarkwashi.
Bambancin da ke tsakanin aikinsu da nawa shi ne; Nasu
aikin yana magana ne a kan “Nazarin fitatun Al’adun maguzawa a ƙasar Kwatarkwashi, yayin
da nawa aikin ya keɓanta a kan magini (Birkila/messin) a garin Kwatarkwashi.
1.8 NAƊEWA/ KAMMALAWA
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.