Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Koyar da Harsuna da Al’adu, Tsangayar Fasaha da Ilimi, Jami’ar Tarayya, Gusau don neman digiri na farko.
Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (5)
NA
HIZBULLAHI ƊANLAMI
BABI NA HUƊU:
TASIRIN SANA’AR GINI GA BUNƘASA ARZIƘIN KWATARKWASHI
4.0 Gabatarwa
Wannan babi zai tattauna ne akan tasirin sana’ar gini ga
Bunƙasa arziƙin kwatarkwashi, wanda a ƙarƙashinsa za a yi bayanin ci gaban da aka samu ta ɓangaren samar da aikin yi ga matasa, da bunƙasar kiyo da Noma da
kuma saye da sayarwa (kasuwanci) a garin kwatarkwashi.
A gargajiyance akwai hanyoyi da yawa da Bahaushe ke bi
don haɓaka ko kawo ci gaban arziƙinsa. Waɗanda suka haɗa da sana’o’i tare da yanayin tsarin zamantakewarsa. Idan aka dubi wannan
sai a ga cewa wasu muhimman hanyoyi ne da Bahushe ke bi don bunƙasa hanyoyin arziƙi.
Sana’o’in gargajiyar Hausawa su ne mafi yawa da bunƙasa arziƙi da Bahaushe ke bi ya
samar wa kansa abubuwan da yake buƙata don gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum.
A bisa haka ne, sana’ar gini da magini (Birkila) ta
taimaka ƙwarai da gaske a yankin garin kwatarkwashi a bisa ga tasirinta wajen bunƙasa arziƙi. Sana’ar ta yi ƙoƙari ainun wajen bunƙasa arziƙin garin kwatarkwashi ta
hanyoyi kamar haka: -
4.1 Samar da Aikin yi ga
Matasa
Haƙiƙa, sana’ar gini da magini (Birkila)
ta ba da gudunmuwa ta musamman wajen wanzar da ayyuka mabambanta, a dai dai
lokacin da ake fama da rashin ayyukan yi, musamman ga matasan da suka kammala
karatu a makarantun gaba da firamare (Primary), waɗanda ba su sami wucewa ba zuwa manyan makarantun gaba da
sakandare. Sabod rage raɗaɗi na zugin talauci da kuma zaman
kashe wando a cikin gari.
Sana’ar gini da magini (Birkila) a garin kwatarkwashi ba
ta tsaya a nan ba, har ma da waɗanda suka kammala karatun N.C.E, a cewar Musa Ɗanbarno Sankalawa inda ya ba ni
misali da ɗansa. Kuma ya tabbatar mini da cewa
matasan da ya koya wa aikin gini a ƙasar kotorkoshi da ma wajenta kamar irin su Damɓa da Gusau, to bai san adadinsu ba.
Har ila yau, sana’ar gini da magini (Birkila) a garin
kwatarkwashi ba ta tsaya a kan waɗancan matasan ba a’a, har ma da marasa ilmin zamani duk sana’ar ta janyo su
a jiki domin samar da aikin yi ga matasan domin rage zaman banza da bangar
siyasa da shaye-shaye da sata da fizge da fyaɗe da kuma faɗa wa wasu ƙungiyoyin ta’addanci da sauransu.
Tabbas, bayanai sun nuna cewa a halinm da ake ciki a garin kwatarkwashi da wuya a sami
wata sana’a ta gargajiya ko ma ta zamani da ta kwashi kason jama’a mai yawa
kamar sana’ar gini da magini (Birkila). Saboda sana’ar ba ta buƙatar fidda wasu kuɗi masu yawa wajen
yinta, ba kamar irin sauran sana’o’in ba.
4.2 Bunƙasa Kiyo a Garin
Kwatarkwashi
Kiyo/kiwo: sana’a ce ta sayen dabbobi domin a kula
da abincinsu, lafiyarsu, a kuma ririta su domin samun naman ci da kuma
biyan buƙatun rayuwa.
Sana’ar kiwo/kiyo daɗaɗɗiyar sana’a ce a ƙasar Hausa, kusan sana’ar ta na kafaɗa da kafaɗa da tsohuwar sana’ar nan ta gargajiya
wato Fawa (hwawa) ko ma ta ɗan girme mata.
Kasancewar ƙasar kwatarkwashi shimfiɗaɗɗiya ga kuma sarari da ciyayi a ko’ina ya sa kusan kowane gida ana kiwon
dabbobi ko tsuntsaye. Mutanen
kwatarkwashi na tsare dabbobi da tsuntsaye a gidajensu ta hanyar ba su
abinci ko kuma a kora su zuwa daji don
su sami abinci a can. Ire-iren dabbobin
da mutanen kwatarkwashi suke kiyo/kiwo sun haɗa da shanu, da
Tumaki da Awaki don cin namansu da kuma sayarwa. To haka su ma maginan
(Birkilan) ƙasar kwatarkwashi ba a bar su a baya ba, duk suna yin wannan sana’a domin
bunƙasa arziƙin garin ko yankin na kwatarkwashi.
Sannan kuma, ana sayar da fatunsu da ƙiragansu don yin amfani
da su. Ana kuma ɗaukar kashin da suka yi don kai wa
gona a matsayin takin da zai ƙara wa gona albarkar
ƙasa.
Bayan dabbobi, mutanen ƙasar kwatarkwashi suna kiwon
tsuntsaye irin su kaji da agwagi da zabbi don cin namansu da ƙwaya-ƙwayinsu da kuma sayarwa.
Maginan (Birkilan) ma suna a sahun gaba wajen kiwon ire-iren wɗannan tsuntsayen
domin bunƙasar arziƙin garin na kwatarkwashi ta hanyar kuɗaɗen da suke samu daga tasu sana’ar.
4.3 BUNƘASA NOMA A GARIN
KWATARKWASHI
Noma hanya ce ta amfani da ƙarfe domin a zafafa ƙasa a gino ko tono
amfaninta ta hanyar shuke-shuke tare da amfani da ruwa domin a sami tsiro na
ci da na tsotsawa da kuma wanda za a
sarrafa zuwa kayan tufafi ko kayan ado.
Noma wata daɗaɗɗiyar sana’a ce ko safara
wadda Bahaushe ya fara yi a doron ƙasa. Ana amfani da dabbobi ko ƙarfi wajen aiwatar da ita wannan
sana’a.
Noma sana’a ce wadda Bahaushe yake bugun gaba da ita, tun
daga kaka da kakanni. Domin kuwa babu gidan
Bahaushe da ba a noma. A ƙasar Hausa a kan fahimci mutum mai arziƙi ne idan yana da ‘ya
‘ya da yawa, masu taimaka masa ga yin
noma a gonaki (wannan bisa ga al’ada ke nan) (Gusau, G.U. 2014).
Hausawa kan ce “Noma na duƙe tsohon ciniki kowa ya zo duniya
kai ya tarar”. Wannan kirari yana bayyana sana’ar Noma daɗaɗɗiya ce a wannan duniya ba wai ga Hausawa ba. Wannan ya sa idan ana maganar
bunƙasar tattalin arziƙin al’ummar garin kwatarkwashi to noma ne za a fara kawowa don kuwa shi ne ƙashin bayan bunƙasar tattalin arziƙin wannan gari (kwatarkwashi).
Inda sana’ar gini da magini (Birkila) ta yi tasiri sosai wajen haɓaka da bunƙasar noma a garin (kwatarkwashi). Wannan ya faru ne
saboda sana’a ce wadda kowa da kowa yake yi talaka da saraki, attajiri da
matalauci, maza da mata, babba da yaro, don a sami abin da za a ci da kuma
wanda za a sayar don yin hidimomin yau da kullum. Tasirin da birkilanci ya yi
ga noma shi ne idan matasa suka sami kuɗi wajen gini sai su je su ƙara faɗaɗa noma da waɗannan kuɗi da suka samu ga aikin gini. Ta haka har noma ya bunƙasa a Kwatarkwashi kowa ya sami
abinci da abin sayarwa/ sana’a.
Al’ummar garin kwatarkwashi na yin noma iri biyu na ci da
na sayarwa. Kayan noma na abin ci sun haɗa da gero da dawa da masara da shinkafa da sauransu, na
sayarwa kuma sun haɗa da auduga, da gyaɗa da waken suya da sauransu. Haka, a ɓangaren magina (Birkila) sana’ar
gini ta yi tasiri sosai, wajen noma ire-iren waɗannan amfanin gona domin bunƙasa arziƙi mai ɗorewa a garin kwatarkwashi.
4.4 BUNƘASA
SAYE-DA-SAYARWA A GARIN KWATARKWASHI
Saye-da-sayarwa: wata hanyar hulɗa ce, ta kasuwanci tsakanin jama’a.
Saye-da-sayarwa (Kasuwanci) yana ɗaya daga cikin muhimman sana’o’in garin kwatarkwashi, domin
ta hanyarsa ne kusan dukkan sauran kayayyakin buƙatar rayuwar ɗan Adam suke shiga hannun jama’a.
Tun kafin wannan zamani al’ummar Hausawa suna da irin
nasu tsari wajen tafiyar da harkokin kasuwanci su. Wannan tsari ana iya dubansa
ta fuska biyu; kasuwancin cikin gida da kuma na waje. A cikin gida akwai
kasuwanni na garuruwa waɗanda ake tafiyar da harkokin
kasuwanci ana musayar abubuwan sayarwa ne, misali Manomi ya ba masaƙi kayan gona don ya
amshi kayan saƙa, ko ya ba makiyayi don ya amshi wata dabba da sauransu. An daɗe ana yin irin wannan tsari na cinikayya a ƙasar Hausa har zuwa ƙarni na goma sha takwas
da aka shigo da kuɗin wuri da biringizau don yin saye da sayarwa a duk faɗi n Afrika ta yamma (Nadama, 1977: 137-138 cikin Sallau, 2017).
Babu shakka wannan nau’in kasuwanci na cikin gida na saye
da sayarwa, al’ummar garin kwatarkwashi suna gudanar da shi, wanda hakan ya
sa sana’ar gini da magini (Birkila) ta
yi tasiri matuƙa wajen bunƙasa arziƙin garin kwatarkwashi.
Sannan kuma, hanyoyin kasuwanci suna da yawa a wajen
mutanen garin kwatarkwashi, yawancinsu na saye da sayarwa ne. Kowane abin
sayarwa yana da tasa hanyar da ake bi a
sayar da shi. Sai dai kasuwancin yana da wani mataki ɗaya, wannan kuwa shi ne jari da mai sana’a yake son ya mallaka kafin ya fara kasuwanci, saboda haka ta hanyar gini matasa sun sami jarin yin kasuwanci ta wannan hanya.
A cewar Gusau, G.U. (2012) “Jari wasu kuɗi ne da mai niyar yin kasuwanci ko sana’a ke tarawa,
domin gudanar da kasuwancinsa ta yadda
zai ɗore ta hanyar jujjuya shi”.
Haƙiƙa, sana’ar gini ta yi tasiri sosai ga magini (Birkila) ta hnayar samun jari
na gudanar da kasuwanci irin na saye da sayarwa domin ƙara bunƙasa arziƙin garin kwatarkwashi.
4.5 NAƊEWA
Wannan babi ya tattauna ne game da tasirin sana’ar gini ga bunƙasa arziƙin garin kwatarkwashi,
wanda a ƙarƙashinsa aka fara bayyana gabatarwa, aka
shiga cikin bayanin muhimman abubuwan da suka yi tasiri wajen bunƙasa arziƙin garin kwatarkwashi,
kamar irin su: samar da aikin yi ga matasa da bunƙasa kiyo da noma da kuma bunƙasa saye da sayarwa duk
a garin kwatarkwashi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.