Ticker

Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (6)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Koyar da Harsuna da Al’adu, Tsangayar Fasaha da Ilimi, Jami’ar Tarayya, Gusau don neman digiri na farko.

Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (6)

NA

HIZBULLAHI ƊANLAMI

 

guni

BABI NA BIYAR: KAMMALAWA

5.0 Gabatarwa

            Wannan babi shi ne kammalawar wannan bincike kuma anan ne za a tattauna abubuwa gabatarwa da sakamakon bincike da shawarwari da kuma naɗewa har ma shata tartibin jerin manazarta.

5.1 Sakamakon Bincike

            Bayan kammala wannan bincike, an gano cewa sana’ar gini da magini (Birkila) muhimman abubuwan ne ƙwarai da gaske a cikin kowace al’umma da ma shi kansa harshen Hausa, kuma wannan sana’a ta gini ana amfani da ita matuƙa wajen gina  al’umma da kuma bunƙasar tattalin arziƙin al’umma ta fannonin rayuwa daban-daban. Har ila yau  wannan bincike ya gano wasu muhimman bayanai da suka shafi sana’ar gini da magini (Birkila) ke yi kafin, da kuma bayan kammala aikin gini.

            Bugu da ƙari, wannan bincike ya gano irin gudunmuwar  da sana’ar gini da magini (Birkila) suke bayarwa ga bunƙasa harshen Hausa tun daga kayan aiki har zuwa ababen da suke samarwa a sana’ar, duk wannan bincike ya tarkato su, kama tun daga ɓangaren na gargajiya har zuwa na waɗanda zamani ya samar. Misali, samar da kalmomin da sana’ar ta yi waɗanda harshen Hausa yake amfani da su a maganganun yau da kullum.

 

5.2 Shawarwari

            Hausawa kan ce “Mutum mai shawara aikinsa ba ya ɓaci, amma kuma ba bu sirri ga al’amurransa.

            Haƙiƙa abin alfahari ne ga harshen Hausa da al’ummar Hausawa, ganin irin yadda harshen ke daɗa bunƙasa a duniya gaba ɗaya ba wai a Afirika (Africa) ba; Ya kutsa gabas  da yamma kudu da arewa. Kamar yadda farfesa Aliyu Muhammad Bunza ke cewa a cikin waƙarsa:

                        “Yau harshenmu ya zamo gagara badau,

                        Furce Afrika har ƙasashen Turawa.” (Bunza, 2004)

Da kuma irin karɓuwar da ya samu a kafafen yaɗa labarai da sauran jami’o’in duniya da  ake nazarin Hausa.

Don haka, za a iya amfani da wannan dama domin bayar da shawarwari tare da jan hankali game da bunƙasa harshen  Hausa.

            Shawara ta ta farko ita ce ga masu aikin gudanar da bincike irin mu (ɗalibai), idan za a yi nazari ko bincike kan wani abu daga sassan Hausa uku wato (Harshe, Adabi da kuma Al’ada) ya kamata a tsaya a natsu tare da bin ingantattun hanyoyi domin gudanar da bincike. Tare da yin amfani da harshe mai sauƙi ta yadda aikin zai zama mai amfani da nagarta.

            Shawara ta biyu ita ce ina ƙira ga ɗalibai baki ɗaya da suke karatu a faɗin duniya ba wai Nijeria ba, ko Jami’ar gwamnatin tarayya ta Gusau (FUGUS) ba, da mu riƙa yawaita bincike a ɗakunan karatu (Libraries) musamman idan an ba mu aikin jinga (Assignment), domin zai taimaka muna ƙwarai wajen samun bayanai cikin sauƙi ba tare  da wahala ba.

            Haka kuma ina bai wa malamanmu shawara, musamman na wannan  sashe mai albarka, wato sashen Hausa da su matsa ƙaimi ga ɗalibai domin su riƙa nazarin ɓangaren al’ada, domin yana daga cikin tubalan ginin al’umma, musamman a ɓangaren al’adun samar da muhalli  wanda al’umma ba ta iya rayuwa sai da shi, kasancewar fannin na fuskantar ƙalu-bale.

            Sannan ɗalibai ‘yan uwana ina ba su shawara da su yi amfani da wannan ɗan aiki nawa, su karanta, insha Allahu zai zame masu jagora idan buƙata ta taso. Saboda Hausawa na cewa “don baƙar rana, ake baƙar ajiya”.

            Bugu da ƙari, mutanen ƙasar Kwatarkwashi ban bar su a baya ba, ina ba su shawara da su tashi tsaye wajen bincike da nazarin al’adunsu, domin ganin sun bunƙasa su ta hanyar sauya su ta yadda za su dace da zamani.

            Shawarata ta ƙarshe, zuwa ga masana domin su ke da alhaki wajen faɗakar da al’umma da gwmanati, ta daure ta riƙa ɗaukar nauyin wasu ɗalibai tana tura su jami’o’i daban-daban na gida da na ƙetare domin nazarin harshen Hausa, da kuma ɗaukar nauyin buga kundayen da rarraba su zuwa wuraren da ake buƙata.

 

5.3 Naɗewa

 Komai ya yi  farko tabbas zai yi ƙarshe. A nan ne Allah cikin iyawarsa  da ikonsa ya ƙaddareni da zuwa inda zan naɗe tabarmar wannan bincike, wanda yake sharaɗi ne daga cikin sharuɗɗan wannan karatu nawa na neman takardar shaidar digiri na farko a fannin Hausa mai taken “Birkila/Messin a garin Kwartarkwashi”.

            A babi na farko, wato shimfiɗar binciken an yi tsokaci a kan gabatarwa da manufar bincike da dalilin binciken da farfajiyar binciken da muhimmancinsa da hanyoyin gudanar da shi da hujjar ci gaba da bincike, sanna aka rufe da bitar ayyukan da suka gabata.

            Sai babi na biyu, wanda yake shi ne Tarihi da al’adun garin Kwatarkwashi. Inda a ƙarƙashinsa ya haɗa da gabatarwa da tarihin garin Kwatarkwashi da tsarin gine-ginen garin Kwatarkwashi da al’adun garin Kwatarkwashi da bayanin shigowar baƙin al’adun harma da tasirinsu a garin kwatarkwashi.

            Shi kuwa babi na uku, wato sana’ar gini a garin Kwatarkwashi, wanda ya ƙunshi gabatarwa da ma’anar gini da ire-iren gini da bayanin magini (Birkila) da kuma bayanin maginin gargajiya da na zamani da bayanin yadda ake gini a garin Kwatarkwashi har ma da gudunmuwar da magini (Birkila) ke bayar wa wajen bunƙasa kalmomin Hausa.

            Yayin da babi na huɗu yake a matsayin  tasirin sana’ar gini ga bunƙasar tattalin ariziƙin garin Kwatarkwashi. In da ya ƙunshi gabatarwa da samar  da aikin yi ga matsa da bunƙasa kiyo da noma da kuma saye-da-sayarwa a garin Kwatarkwashi.

            Sai babi na biyar kuma na ƙarshe, wanda ya ke kammalawa inda a ƙarƙashinsa akwai gabatarwa da sakamakon bincike da shawarwari  da naɗewa da kuma manazarta.

5.4 Manazarta

Tuntuɓi Amsoshi.

Post a Comment

0 Comments