Ticker

Faskare A Garin Faskari (1)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara.

Faskare A Garin Faskari (1)

NA

ABUBAKAR HASSAN

faskare

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan kundin digiri ga mahaifiyata Hama, Allah ya jiƙanta ya gafarta mata dukkan kurakuranta, da kuma babana malam Hassan faskari da yayata Maryama da Kabir da Maharazu da Rabi’atu da Hadiza da kuma Jafar.

TSAKURE

A wannan bincike da ake gudanarwa, za a yi ƙoƙarin binciko asalin sunan faskare da ma’anar faskare da kuma yanda ake gudanar da faskare a cikin garin Faskari. Bugu da ƙari, a wannan ɗan ƙwarya-ƙwaryar bincike, za a yi ƙoƙarin gano illolin da ke tattare da sana’ar faskare da kuma muhimmancin sana’ar. Haka kuma, a wannan bincike, za a yi ƙoƙarin binciko ire-iren itatuwa masu sauƙin faskare da masu wahalar  faskarawa. Daga ƙarshe kuma za a kammala wannan aiki tare da shawarwarin da malamai suka bada da kuma sauran mutane.  

GODIYA

            Ina mai godiya ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komi mai rahama mai jin ƙai zuwa ga bayinsa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da sahabbasa da zuri’arsa da dukkan wanda ya bishi har zuwa ranar sakamako.

            Bayan haka,  ina miƙa godiya ta da jinjina zuwa ga mahaifina Malam Hassan bisa jajircewa da ya yi na ganin cewa na kammala karatuna, kuma na gode da irin addu’o’in da ya yi ta yi man dare da rana. Allah ya saka masa da mafificin alkairi, kuma Allah ya saka masa da gidan aljanna Amin.

            Bayan haka, ina miƙa godiyata ta musamman zuwa ga yannena da kuma ƙannena, bisa ga gudunmuwar da suka bani da kuma tayani da  addu’o’i da sukyi, kamar Maharazu da maryam da Kabir,  da Rabi’atu da Hadiza da Jummai Allah ya gafartamata da Jafar da Musa da  Ibrahim da Nasir. Allah ya saka masu da mafificin alkairi amin summa amin.

            Ba zai yiwu in yi tuya in manta  da albasa ba, ina miƙa godiya da ban jinjina zuwa ga Mama (Asabe) bisa gudunmawar da ta ba ni tun daga lokacin da na fara karatu har zuwa lokacin da Allah ya sa na kammala, tabbas ta yi namijin ƙoƙari, Allah ya saka mata da mafificin alkhairi, Allah ya saka mata da gidan aljanna, kuma Allah ya albarkaci zuri’arta amin.

            Bayan haka, ina farin cikin miƙa godiyata ga malamaina na sashenmu da irin gudunmawar da suka bani da kuma shawarwari.

            Ina miƙa godiyata ta musamman ga malamai na kamar haka: Prof. Aliyu M. Bunza, da Dr. Tahir, da malam Rabi’u Aliyu Ɗangulbi, da Malam Musa Abdullahi da Prof. Magaji Tsoho Yakawada da Prof. Ahmad Halliru Amfani da Dr. Nazir Abbas da Prof. Balarabe da Dr. Fadama da malam Isah S. Fada  da dai suaransu. Allah ya saka masu da mafificin alkhairi amin.

            Bayan haka, ina miƙa godiya da jinjina ga malamina, kuma mai duba wannan aiki nawa Dr. Tahir, bisa jajircewa da ya yi da kuma shawarwarin da ya bani na ganin cewa wannan aiki ya kammala, Allah ya saka masa da mafificin alkhairi amin.

            Ina miƙa godiyata  zuwa ga abokaina kamar: Yahaya Umar Barau, Musa Magaji, Abubakar Abdulrahman (Attah), Kabir Tajudddeen, Abubakar Muhammad (Dodo),. Ibrahim Nasir (Ibson) da sauransu. Nagode sosai Allah ya saka da mafificin alkhairi.

            Bayan haka ina miƙa godiyata zuwa ga aboka nan karatu na kamar Mustapha Sa’idu Faskari,  da Abdulrahman Bala da Abdulrashid Sifawa da Ɗayyaba Mustapha Ibrahim da Amina Abubakar da  Nasiru Hassan da Ahmad Muhammad Kabir da Sani Adamu da Bashir Isiyaku da Hizbullahi Ɗanlami da Nura Sani Kwatarkwahi da Aliyu S Ibrahim da Hassan Galadima, da dai sauransu. Allah ya saka da alkhairi amin.

Post a Comment

0 Comments