Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara.
Faskare A Garin Faskari (5)
NA
ABUBAKAR HASSAN
BABI NA HUƊU
MU’AMALAR ICCE DA MAI FASKARE
4.0 Gabatarwa
Masu faskare dai, wasu rukunin al’umma ne waɗanda suka zaɓi yin wannan sana’ar ta faskare don ta kasance hanyar cin abincinsu ta yau
da kullun. Sana’ar faskare, sana’a ce wadda ake yinta da gatari, kuma matasa
masu jini a jika da dattawa waɗanda suke da sauran ƙarfi a jikinsu, su ne suka fi aiwatar da irin wannan sana’ar ta faskare. A cikin
masu wannan sana’ar, akwai waɗanda suke zuwa daji su sari icce su sayar, akwai kuma waɗanda basa zuwa daji, kawai su aikinsu shi ne idan an kawo
icce a cikin gari sai a kira su su faskara shi.
4.1 Dangantakar Masu
Faskare Da Al’ummar Faskari
Dangantakar masu Faskare da al’ummar garin Faskari, tun
farko wanann dangantaka ta samo asali ne ta fuskar sana’a. A duk lokacin da
mutanen Faskari suka buƙaci icce, to zai kasance sai sun je sun nemo mai faskare, idan suka nemo
wannan mai faskaren, to zasu tattauna da mai faskaren nan kan abinda suke buƙata, wato suna da buƙatar a yi masu faskare,
idan mai faskaren nan ya gama aikin shi daga nan sai a biya shi. To ta wannan
hanya ce alaƙa mai ƙarfi zata ƙullu tsakanin masu faskare da mutanen gari, wadda duk lokacin da mutum ya
buƙaci faskare, to waɗannan mutanen da suka yi mashi faskaren nan, to su ne zai ƙara nemowa don su ƙara yi mashi wannan
faskaren.
Bugu da ƙari, takan yiwu mutum yana buƙatar icce, to yakan nemo mai faskare
wanda yake shiga daji yana yo icce, sai ya tambaye shi ya za a yi a samo mashi
icce, walau faskare ne ko kuma gunduwa-gunduwa.
To ta irin wannan alaƙa ko dangantaka mai ƙarfi take shiga tsakanin
mutanen gari da masu sana’ar faskare.
4.2 Mu’amalar Itace Da
Mai Faskare
Mu’amalar icce da mai
faskare, mu’amala wadda ta kasance shi mai sana’ar faskare ya san itace
kala-kala. Ya san icce mai ƙarfi sosai, kuma ya san icce wanda yake da taushi. Bugu
da ƙari, mai faskare yasan icce wanda yake da ci sosai, kuma ya san iccen da ke
yin gawayi mai kyau. Mai faskare ya san irin iccen da zaran ya saro sai ya kowa
cikin gari to za a yi saurin sayewa, kuma za a siya da daraja sosai, mai
faskare ya san iccen da idan ya saro shi ya kawo shi cikin gari to ba zai sha
wahala wajen neman masu saye ba. To saboda wannan mu’amalar da take tsakanin
mai faskare da icce ce ta sanya mai faskare ya san nau’o’in icce daban-daban,
kuma ya iya sarrafa su ta yanda yake so, kamar yanda Hausawa kan ce “A san mutum a san cikinsa, in ya bari
a san ya daina”.
Daɗin daɗawa, saboda yawan mu’amala da icce
ne mai sana’ar faskare ya san duk wani abu game da icce, kuma mai faskare ya
san icce mai kyau, ya san icce marar kyau.
Haka kuma, mu’amalar icce da mai faskare ta danganci
yanda mai faskare ke sarrafa icce ta kowane irin yanayi wanda ya haɗa da:
Safara
Saukewa
Tantancewa
Ƙwari
Duk waɗannan abubuwa, mu’amala ce ta yau da kullun wadda mai faskare ke yi da icce, sanadiyar wannan mu’amala ce
ta sanya mai faskare ya san abubuwa da dama dangane da icce.
4.2.1 Safara
Idan mai faskare ya tafi
daji ya saro icce, to akan ɗauki icce ne a kan abubuwa dabn-daban, wato abun da zai ɗauko iccen da aka sara ko aka faskara daga daji zuwa gida
ko gari. A can zamanin da, kafin ƙarafuna su yawaita a ƙasar Hausa, idan aka sari iccen a
cikin daji, to ana ɗauko shi ne a bisa kai, wato mutum yana ɗauko icce ne da kansa, ko kuma a kan jaki, wato sai a ɗauro ma jaki icce daga daji zuwa cikin gari, waɗannan mutane waɗanda suke ɗauro ma jaki icce daga daji zuwa
garin, to su ne ake ce ma “yan jakai”.
Bugu da ƙari, ana yin safarar
icce da keke ko kuma mashin, har da motoci ma duk ana yin safarar icce, wato
idan aka sari icce daga cikin daji sai a sanya daga cikin daji zuwa cikin gari
domin a sarrafa shi a yi girki da shi.
Haka kuma akwai mutanen da ake ce ma ‘yangudubale’, su
‘yangudubale, wasu mutane ne da suke
zuwa daji su sari icce su yi mashi gunduwa-gunduwa, idan sun sari iccen nan sun
tara, to sai su kira mai mota, sai su loda ma shi wannan iccen ya kawo masu
cikin gari, to idan wannan mai motar ya
kawo masu iccen nan gari, to sai su je su nemo mai sayen iccen nan, idan sun
siyar da iccen sai su sallami mai motar da ya yi masu dakon iccen nan daga daji
zuwa cikin gari. To ta irin waɗannan hanyoyi ne ake yin safarar icce daga daji zuwa cikin gari domin a
sami abinda za a yi girki da shi. Ta irin waɗannan hanyoyi ne ake yin safarar icce daga inda aka sare
shi zuwa inda ake son kawo shi don a siyar a yi buƙatun yau da kullun.
4.2.2 Saukewa/ Saukale
Idan aka yo safarra icce
daga cikin daji zuwa cikin gari, to ana sauke shi ne wuri mai fili, wato wurin
da bai matse hanyar wucewa ba, shi dai irin wannan wurin da ake sauke icce, to
ba shida wani takamaiman sunan da ake kiran shi da shi, idan aka lodo ma jaki
icce, to waɗannan mutanen masu iccen waɗanda suka loda ma wannan jaki icce, to sune suke sauke
wannan icce da kansu, ba wai wasu zasu sanya su sauke masu wanann icce.
Haka icce, idan aka lodo ma keke ko mashin ko kuma mota
icce, to waɗannan mutanen da suka ɗauko wannan iccen, to su da kan su ne sauke wannan iccen
ba wai kuma wasu mutane ne daban za su kira su sauke ba.
Bugu da ƙari, koda kuwa mota ce aka lodo ma wannan iccen, to su waɗanda suka loda
mota wannan iccen, to dama za su hawo motar ne su biyo ta har inda za a sauke
wannan iccen, to idan an zo daidai wurin da za a sauke wannan iccen to sai waɗannan mutanen da ake kira da ‘yangudubale’ su sauko daga
bisa wannan motar su sauke iccen.
4.2.3 Tantancewa
Idan masu faskare suka sari icce, ko kuma suka faskari
icce, to suna ware su daban-daban, suna ware masu kyau da maras sa kyau, kuma
suna ware masu ƙwari da maras ƙwari, suna ware masu ci sosai da kuma waɗanda ba su ci sosai. To idan sun ware waɗannan itatuwan gefe-gefe, wato idan an gama tanatance su kenan, to sai a
fara siyar da su.
Itatuwan da suka fi ƙwari, to wajen sayarwa
sai sun fi daraja, wato sai sun fi tsada.
Itacen da suka fi ƙwari, kuma suka fi
daraja wajen siyarwa sun haɗa da:
Iccen marke
Iccen ɗorawa
Iccen faru
Iccen ɗinya
Iccen kaɗanya
Iccen gamji
Iccen kanya d.s.s
To ire-iren waɗannan itatuwa sun fi tsada wajen siyarwa, kuma masu girki
sun fi jin daɗin amfani da su, saboda sun fi ci,
kuma ba su da hayaƙi sosai.
4.2.4 Ƙwari
Masu faskare suna haɗawa da abubuwa da yawa yayin gudanar da sana’arsu ta
faskare. Masu faskare, suna cin karo da ƙwari kala-kala masu cutarwa da ma waɗanda ba su cutarwa a cikin iccen da ake faskarawa.
Waɗannan ƙananan halittu da suke rayuwa a cikin icce, waɗanda ababuwan cutarwa ne, waɗansu kuma ba masu cutarwa ba ne. To idan ya kasance masu
faskare sun fara saran iccen da waɗannan ƙwari suke, idan waɗannan ƙwari mugaye ne to suna iya kawo ma mai faskaren nan hari su cutar da shi. Idan kuma waɗannan ƙwari ba manya ba ne, to ba bu ruwansu da wannan mai faskaren, sai dai su kama wani wuri su
canza muhalli na daban.
Ire-iren Ƙwarin da masu faskare ke
cin karo da su yayin gudanar da aikinsu sun haɗa da:
Kiyashi
Tsutsa
Muzanya
Maciji
Kunama
Ɓera
Gafiya
Cinnaka
Tarmani.
To waɗannan su na ɗaya daga cikin ire-iren ƙwari da masu sana’ar
faskare ke cin karo da su yayin gudanar da aikinsu na saran icce. A cikin waɗannan ƙwarin, akwai waɗanda suke masu cutarwa, akwai kuma waɗanda basu cutarwa.
Ƙwari masu cutarwa sun haɗa da:
Maciji
Kunama
Cinnaka
Tarmani.
Ƙwari waɗanda basu cutarwa sun haɗa da:
Kiyashi
Ɓera
Gafiya
Muzanya.
To waɗannan sune ire-iren ƙwarin da ake iya samu a cikin icce.
4.3 Nau’o’in Masu
Faskare
Kowace irin sana’a ta duniya,
tana da rukuni-rukunin al’ummar da ke aiwatar da ita. To haka shi ma faskare,
kamar kowace irin sana’a yake, yana da nau’o’in mutanen da ke aiwatar da shi,
daga cikin su akwai:
-
‘yan jakai
-
‘yan ina-da-faskare
-
‘yan gudubale
-
Masu yo icce da mashin/
keke
-
Masu yo icce da baro
-
Masu zama waje ɗaya sai an kira su.
(i)
‘Yan jakai: - ‘Yan jakai
su ne masu zuwa yo icce daji da jaki ko jakai, idan sun saro iccen nan sai su
zo gari su siyar. Daga cikin su akwai ma su zuwa da jaki ɗaya, wasu kuma fiye da ɗaya.
(ii)
‘Yan –ina-da-faskare: -
su ne waɗanda ke yawo layi-layi,
kwararo-kwararo, suna yawo da gatarin su rataye a kafaɗa suna neman inda za su yi faskare, ko kuma wanda zai
kira su su yi ma shi faskare.
(iii)
‘Yan gudubale: - Su ne
waɗanda su ke zuwa daji su sari icce
mai yawa, idan sun sari wannan iccen,
sai su kira wani mai mota ya yi masu
lodin wannan iccen sai ya kai masu cikin gari a siyar, idan an saida sai su
biya mai motar dakon da ya yi masu.
(iv)
Masu yo icce da mashin
ko keke: - Su ne waɗanda su ke zuwa daji da mashin ko keke ko baro sai su sari icce sai su yo
lodin shi sai su kawo shi cikin gari su siyar, don su rufa ma kan su asiri.
(v)
Masu zama waje ɗaya sai an kira su: Suma waɗannan gungun masu faskare ne, waɗanda ba yawo suke yi ba, kuma ba su zuwa daji don yo
icce, su suna zaune a gida ne, idan mutum yana da buƙatar
a yi mashi faskare, to sai dai ya je ya kira su.
4.4
Muhallin da ake Faskare
A lokacin da ake gudanar da faskare, ana buɗatar a sami fili mai faɗi, wanda zai isa a ajiye itatuwa komi yawansu, to idan
aka sami irin wannan filin ana iya yin faskare a cikin shi, a ƙofar gida ko kuma a cikin gida. Ba’a ware wani fili na
musamman ba wanda ake yin faskare a cikin shi ba.
Bugu da ƙari, duk filin da aka samu, za a iya yin faskare a cikin shi, walau a cikin
gida yake, ko kuma a waje.
4.5
Kammalawa
To kamar dai yanda muka gani
a bayanin da ya gabata, faskare dai kamar kowace irin sana’a yake mai cin
gashin kanta, yana da irin nashi hanyoyi ko tsare-tsaren da ake bi domin
gudanar da shi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.