Ticker

Faskare A Garin Faskari (6)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara.

Faskare A Garin Faskari (6)

NA

ABUBAKAR HASSAN

faskare 

BABI NA BIYAR

KAMMALAWA

5.0 Gabatarwa

A wannan babi za a kammala dukkan abubuwan da ake binciko a kan wannan aiki tare da yin nazarin kowane babi ɗaya bayan ɗaya a taƙaice. Haka zalika, a nan ne za a kammala wannan aiki.

            Bugu da ƙari, cikin wannan babi ne za a ga shawarwari da aka yi wajen aiwatar da wannan bincike. A ƙarshe ne ake sa ran yin bayani na kammalawa tare da manazarta.

5.1 Taƙaitawa

            A babi na ɗaya an yi bayani ne game da manufar bincike da dalilin bincike da muhallin bincike da matsalolin bincike da kuma farfajiyar bincike,  sai kuma a ƙarshen babin aka yi kammalawa.

            Babi na biyu, ya yi bayani ne a kan bitar ayyukan da suka gabata da kuma ma’anar sana’a da tarihin garin Faskari da kuma ma’anar faskare.

            Sai kuma a babi na uku, an yi bayani a kan asalin sunan faskare, sana’ar faskare a garin faskari, da kuma muhimmancin faskare a garin Faskari da kuma ire-iren itatuwa da kuma ƙalubalen da masu faskare ke fuskanta a garin Faskari da kuma hanyoyin  da za a bi a shawo kan matsalar faskare a garin Faskari, sai kuma daga ƙarshe aka yi kammalawa.

            A babi na huɗu, an tattauna muhimman abubuwa kamar haka:

Dangantakar masu faskare da al’ummar Faskari, da mu’amalar itace da mai faskare da kuma nau’o’in masu faskare da kuma muhallin da ake faskare daga ƙarshe kuma aka kammala babin.

            A babi na biyar ne aka kammala wannan binciken, wannan babi an yi tsokaci a kan abubuwa kamar taƙaitawa da kuma kammalawa, sai kuma shawarwari tare da kuma manazarta.

5.2 Kammalawa

Kamar yadda mai bincike ya yi bincike a kan rubuta wannan kundin neman digiri na farko kan abin da ya shafi “Faskare a garin Faskari”, wato yanda shi kan shi faskaren yake da kuma yanda ake gudanr da shi. Haka kuma, mai bincike ya raba aikin sa zuwa babi-babi, tun daga babi na ɗaya har zuwa na biyar.

            A babi na ɗaya, mai bincike ya yi bayani a kan manufar bincike da kuma dalilin bincike da matsalolin bincike da kuma farfajiyar bincike daga  ƙarshe kuma aka kammala.

            A babi na biyu kuma mai bincike ya yi bitar ayukan da suka gabata.

A babi na uku kuma an yi yalwataccen bayani a kan/ game da yanda ake aiwatar da sana’ar faskare.

            A babi na huɗu,  shima  bayani ne da mai bincike ya yi a kan yanda ake aiwatar da sana’ar faskare da kuma nau’o’in masu faskare daga ƙarshe kuma aka kammala.

            Sai kuma a babi na biyar, mai bincije ya yi bayani a taƙaice game da yanda aka gudanar da wannan aiki, sai shawarwari da kuma kammalawa sai kuma manazarta.

5.3 Sakamakon Bincike

·         A sakamakon wannan bincike an gano itatuwan da ba a faskara su, sai dai a ɗebi wani sashe daga jikin su.

·         Haka kuma, an gano itatuwan da ba a girki da su.

·         A sakamakon wannan bincike, an gano matasa masu jini a jika sun fi yin wannan sana’ar ta faskare.

·         Bugu da ƙari, a sakamakon wannan bincike, an gano sana’ar faskare ta fi cin kasuwarta a can lokacin baya, saboda yanzu sana’ar tana ja da baya saboda tasirin zamananci.

·         A sakamakon wannan bincike, an gano itatuwa masu sauƙin faskare da masu wahalar faskare.

·         Haka kuma, a wannan  binciken an gano cewa a lokacin da mai sana’ar faskare ya tsufa, wato ya manyanta kenan to jikin shi yana yi ma shi ciwo sosai.

5.4  Shwarwari

To, a nan shwarwari da za a yi basu wuce  na malami da ɗalibai masu nazarin al’ada ba. Shawarata a nan ita ce, aci gaba da nazarin al’ada da kuma sana’o’in Hausawa na gargajiya, saboda muhimmancinsu.

            Haka kuma, yana da kyau hukumar makaranta ta sanya wannan bincike a cikin tsarin bincike da ake rubuta maƙala a kan sa, idan muka yi la’akari da muhimmancinsa, domin ya taɓo ɓangarori da yawa na yanda ake gudanar da faskare da ma sauran sana’o’i daban-daban.

            Bayan haka kuma, gwamnati ita ma ya kamata ta inganta wannan sana’ar ta faskare yanda za ta dace dai-dai da zamani, saboda faskare yana da matuƙar muhimmanci  ga rayuwar al’umma.

            Daga ƙarshe kuma ya zama dole ɗalibai masu nazarin harshen Hausa a makarantu daban-daban, kama  daga takardar Diploma, NCE da digiri na ɗaya da na biyu da na uku, da su tsunduma a kan sha’anin bincike akan faskare, ta hanyar rubuta kundayensu na kammala karatu a kan Hausa. Ba ɗalibai kawai ba, har da malamai masu koyar da harshen Hausa a makarantu, tun daga firamare har zuwa jami’a, ya kamata su zurfafa bincikensu wajen gano abubuwan da suka danganci faskare. To wannan hanyar kaɗaice za a kauda ƙishin ruwan da ke damun mutane na rashin wani abun dubawa wanda ya yi magan a kan faskare.

            Haka kuma, ina ƙara ba ɗaliban neman ilimi ‘yan uwana shawara da su ƙara zurfafa bincike a kan wannan  fanni na faskare domin a sami abin dubawa, kuma domin a ƙara faɗaɗa wannan fannin ya bunƙasa.


 

MANAZARTA

Tuntuɓi Amsoshi.

Post a Comment

0 Comments