Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Ganuwar Gusau Da Kofofinta (5)
NA
UMAR YAHAYA DOGARA
BABI NA HUƊU
KOFOFIN GUSAU
4.0 Shimfiɗa
A babi daya gabata, watau babi na uku binciken
ya duba, ganuwar Gusau da tarihin ganuwar Gusau da tasirin ganuwa a gari da kuma naɗewa. Ban samu wani
kundi da ya yi bayani akan ƙofofin ko nazari game da ƙofofin
Gusau ba, wannan babi zai yi bayani a kan, ƙofofin
Gusau da sharhi ƙofofin Gusau da kuma wasu Unguwoyin Gusau, da kuma Gusau
a matsayin babban birnin jahar zamfara, da naɗewa, wannan shine makasudin wannan babi.
4.1 Ƙofofin Gusau
1. Ƙofar
kwatarkwashi
2. Ƙofar
Katsaura
3. Ƙofar
Rawayya
4. Ƙofar
Goje
5. Ƙofar
Dogo/Dokau
6. Ƙofar
Tubani
7. Ƙofar
Mani
8. Ƙofar
Jange
9.
|
Taswira mai nuna ƙofofin
birnin Gusau
Ganuwa da ƙofofin
Gusau an samar dasu a sanadiyyar yaƙe-yaƙe da hare-hare da ake
fuskanta ne wannan zamani, an gina wannan ganuwa da ƙofofi a lokacin
Sarkin Katsinan Gusau, Malam Abdulƙadir a zamin Sarkin Musulmi, Amadu dan Atiku
a shekara (1859) dukkan rubuce – rubuce da aka yi akan garin Gusau ba wani akan
ƙofofin
Gusau wannan kundin shi ne na farko da zai yi bayanin akan ƙofofin
da asalin su da kafa su, ya amfani da yin hira da mutane tsofaffin masu shekaru
kuma ‘yan
asalin wanna garin na Gusau.
4.2 Sharhin ƙofofin Gusau
Kamar yadda nayi bayani tun farko
babu wani littafi ko kundi da ya yi sharhin ƙofofin Gusau da
asalin su.
ƘOFAR KWATARKWASHI
Ƙofar kwatarkwashi na
samu bayanai daga masana guda biyu zuwa uku, sun tabbatar da samuwar wannan ƙofa
kuma sun fadi dai-dai inda ƙofar take, ƙofar tana nan wurin
MTD kusa da tankin ruwa dake sabon gari. Ita wannan ƙofa babba ce kamar
cibiya ƙofa wadda ke shigowa zuwa cikin tsakiyar garin Gusau,
(Alhaji Muhammadu Kwazo Sarkin Noma. 2018) yace “ A lokacin da aka gina ganuwar
an bude wannan ƙofar ne saboda mutanen kwatarkwashi, da ke shigowa Gusau
domin yin hulɗoɗin kasuwanci na
cinikayya da sauran mu’amaloli yau da kullum, haka shi ya sa aka saka mata
sunan ƙofar kwatarkwashi. Sannan masu tsaron wannan ƙofar
basu bari kowa ya shigo ta wannan ƙofa, sai mutanen kwatarkwashi, domin su aka
gina ma wannan ƙofar, saboda haka akwai tsari da shamakance ta babu
mutane da ke shigowa ta wannan ƙofa sai mutnane kwatarkwashi. Idan wani ya zo
wanda baya a cikin su ba za’a bar shi ya shigo ba. Haka kuma mutanen Gusau idan
zasu fita zuwa kwatarkwashi ta wannan ƙofa suke bi.
Alhaji Bello ɗan mai tuwo hirar da
nayi dashi yace “Ƙofar tana nan a wannan bangare na wurin MTD wurin tankin
ruwa”. A halin yanzu ƙofar kwatarkwashi tana cikin yankin sabon
gari.
ƘOFAR KATSAURA
Wannan ƙofa itama, akwai
ra’ayyi akanta, Alhaji Sulaiman (Makaho) mai shekara (95) ya tabbatar mana da
cewa, ƙofar tana nana unguwar toka dai-dai wurin inda ake wankin
‘yankunne kusa da ginda burodi, wurin gidan ‘yan darika a yanzu. Ya bayyana man
cewa asalin Kalmar katsaura sunan mutumen katsaura, kuma mutumin garin Nahuce
ne, a lokacin da a ka ba Malam Sambo ɗan Ashafa tuta, ya biyo ta garin Nahuce ya faɗa masa cewa an gama
yaƙi
kuma Shaihu Usman Ɗanfodiyo, ya bashi
tuta, sai Malam Sambo ɗan
Ashafa ya nemi Katsaura daya biyo shi Gusau, su zauna. Katsaura yace sai ya
nemi izinin ‘yan uwansa sai ya tambayi ‘yan uwansa kuma suka bashi dama, sai ya
biyo Malam ambo ɗan
Ashafa ya zo Gusau ya zauna (Malam Adamu Minista hirar mu 2018) yace” ƙofa
tana nana Unguwar toka wurin gidan ‘yandarki amma sai dai ya nuna cewa katsaura
saunan gari ne wanda cikin garin Bunga kusa da garin Ƙaura-Namoda.
Idan aka duba lokacin da aka yi ganuwa Sarkin Musulmi Amadu Dan Atiku (1859) ya
ummurci da mutana Ƙaura Namoda da su taimaka wurin ginin ganuwar Gusau. Zai
iya yiyuwa mutane Bunga da Katsaura sun taimaka wurin aikin kuma sun yi har aka
sakawa ɗaya
daga cikin ƙofofin sunan garin. Ala kulli halin waɗannan sune ra’ayoyin
da suka zo a game da wannan ƙofar ta katsaura, kuma kowannen su zai iya
kasancewa. Sarkin Noma Muhammadu Ƙwazo, ya tabbatar da cewa tananan Unguwar
toka. A halin yanzu ƙofar katsaura tana cikin yankin Madawaki.
ƘOFAR RAWAYYA.
Akwai ra’ayoyi
na mutane akan inda wannan ƙofa take, asalin ƙofar
Rawayya, ƙofar Rawayya an kafa tane saboda mutane garin Rawayya da
suke shigowa ta wannan ƙofa idan sun zo kasuwanci Gusau, haka mutanen
Gusau idan za su tafi Rawayya ta wannan ƙofa suka bi, Bisa
bayanin da na samu daga hirar da nayi da (Garba mai Gudu a shekarar 2018) yace
“ya nuna man cewa ƙofar tana nan a bakin tsohuwar kasuwa wurin gidan Alhaji
Goga kusa da gidan Makera, Alhaji korar hirar da nayi da shi yace” ya tabbatar
man da cewa tana nan wurin shigo wurin da ake said a magani na nasiha dake
tsohuwar kasuwa” Sarkin Noma Muhammad Kwazo yace” ya nuna cewa ƙofar
Rawayya tananan dai-dai shagon sule mamuda da ke tsohuwar kasuwa kusa da gidan ɗan Iya”. Haka kuma
bisa ga hirar da nayi da, Aliyu Rufa’I Gusau (ɗan Masanin Wonaka) mazauni ƙofar yana kusa da shagon
Sule Mamuda . sai dai mun tafi akan bayanin da muka samu daga jikan mai tsaron ƙofar
cewa muhallin ƙofar a yanzu yana dai-dai da gindan Alhaji Ammani a
tsohuwar kasuwa wurin shagon sai da magani na Bayanaka. In ji Bello Ummaru ƙofa,
hirar mu da shi ya.
Idan aka tattara
dukkan waɗannan
bayanai za’a ga cewa ƙofar Rawayya tana nan dai a wannan yanki na
tsohuwar kasuwa tsakanin shagon Sule Mamuda da Nasiha. Zai iya yiyuwa ƙofar
babba ce tana da tsayi sosai ta yadda tsawonta zai iya game dukkan wannan yanki
bayanin jikokin waɗanda
suka yi tsaron ƙofar, sunan mai tsaron ƙofar Rawayya,
Muhammadu ƙofa, manomine kuma makeri ne, zuri’ar sa har yanzu tana
wanzuwa kuma gidan sa yana na gab da gidan Alhaji Idi Mai kwai, bakin kasuwa
tsohuwa. Daga cikin jokokin sa akwai, Bello Ummar Muhammad ƙofa.
A halin yanzu ƙofar rawayya tana cikin yankin rikon Galadima idan aka shiga
mazaunin ƙofar Rawayya; daga
gabas zata sadar da mutum zuwa
tsohuwar tasha, daga yamma zata sadar da mutum zuwa makabarta da gangaren
gulbi, kudu kanwuri da zawiyya daga arewa, asibitin Farida.
ƘOFAR GOJE
Wannan ƙofa kamar yadda
marubuta tarihi suka rubuta akwai sunan wannan ƙofa, to amma a cikin
binciken nawa, ban samu tabbacin inda wannan ƙofar take. Sannan a
cikin mutanen da na yi fira da su, suna gayaman Gusau tana da kofofi guda tara
(9) amman ba su san wannan ƙofa ba, amman duk rubuta da akayi a wannan
gari na Gusau ana sanya sunan wannan kofar ta goje, amman dukkan mutanen da na
yi fira dasu sukan gayaman cewa ba su san da wannan ƙofar ba, sai dai
sukance man abin da ake nufi da goje shi ne manomi, kila takan iya yiyuwa ƙofa
ce ta hanyar manoma wato hanya ce ƙila ta manoma.
ƘOFAR DOGO/DOKAU
Kamar yadda na samu bayanai daga ma
zauna wannan garin na Gusau, domin su bani bayani in da ƙofar
ta ke ta dogo, duk wanda naje wurinsa na tambaye shi sai dai ya yi maganar ƙofar
dokau suka sani, ba kofar dogo ba. Haka kuma dukkan wanɗanda na sami bayani
wurins su suna lissafawa da ƙofar dokau, amman basu lissafawa da ƙofar
dogo bayan haka akwai wasu mutane dake cewa akwai ƙofar dogo, idan na
tambayi ƙarin haske sai su kawo min littattfan da aka rubuta takan
iya kasancewa ƙila ƙofar dokau ce, sai suce ƙofar
dogo. Kuma babu wani littafi da ya yi bayani ko sharhin waɗannan ƙofofin
na Gusau.
Ƙofar dokau, ƙofa
ce ta mu’amala tsakani mutanen garin Gusau, da na mutanen garin dokau, mutane
Gusau sukan bi hanyar zuwa dokau, haka mutanen dakau, kamar yadda muka samu
bayani wurin sarkin noma Alh. Hassan Muh’d Ƙwazo. Ya sheda muna cewa
wannan ƙofar ta dokau na nan wurin filin gunza, wurin gidan ‘yan
goro, shi ma Malam Shehu Ladan Kurmi, ya gayaman ƙofar dokau tana nan
wurin gidn mai shanu wurin gidan ‘yan goro. Ƙofar dokau tana cikin
yankin Gundumar Mayana, a gabas za ta kai ka maƙera ta tsohuwar
silima, kudu za ta kai ka kwanar birnin ruwa, yamma za ta kai ka gidan sarkin
kudu.
ƘOFAR TUBANI
Ƙofar tubani ɗaya ce daga cikin ƙofofin
Gusau. Mazaunin wanna ƙofar tana nan wurin bayan maƙera
ta gidan Isah Mayana, yanzu haka, (Hirarmu da Malam Sani Madugu da Sani Ɗan
Kwamma da Sarkin Noma Muhammadu Ƙwazo kamar yadda na samu bayanin, shi tubani
manomi ne, kuma shine ya yi tsaron kofar, babu wanda ya sami asalin sa kamar
yadda mazuana wurin suka fada. ƙofar na nan kusa da ginda Muhammadu Noma,
kusa da inji nin nika, kamin zawuyya da gabas tana fita da mutum ƙofar
mani daga kudu, yamma kuma gan garen na damau zuwa kauyoka, ƙofar
na cikn rikon Mayana.
ƘOFAR MANI
Ƙofar
Mani na daya daga cikin ƙofofin Gusau, ta amu sunan ta ne daga wani
mutum manomi mai suna Mani. Ma zaunin ta a yau unguwar kofar mani (an sakawa
unguwar sun ƙofar Mani) ƙofar na nan inda wata ‘yar kasuwa take, kuma
gidan shi mani yana nan gefe ana satar da hatsi a wurin. A dukkan binciken da
na yi ban samu wani birbishin zuri’ar Mani ba, haka na iya nuna cewa bai taba
haihuwa a rayuwarsa ba. (Hirar da nayi da Malam Audu Mai wanki 2018) mazauni unguwar ƙofar mani mai shekara
(80) a duniya, haka kuma akwai Malam Yahaya wanda yake makwabcin gidan Mani. A
halin yanzu kofar Mani tana cikin yankin Mayana, idan aka shigo ta mazaunin ƙofar
Mani daga gabas zata iya kai mutum makarantar boko ta “kanwuri” zuwa gidan
sarki, da kuma unguwar zawuyya, da tullukawa har zuwa gulbi.
ƘOFAR JANGE
Ƙofar Jange asalin
muhallin da, ƙofar mashaya ce; wuri ne da yake magudanar ruwa mutane na
dibar ruwa a wurin kuma suna shayar da dabbobin su, Jange sunan wani mutum ne
Mayaƙi, Jarumi, Maharbi, da ke zaune a wurin yana farautar
namun daji lokacin da aka gina ganuwa sai aka sakawa ƙofar
da ke wurin sunansa. ƙofar ta na nan kusa da gidansa gaba kadan da
gidan Alhaji Namadi Bola. Gidansa har yanzu yana na kuma na samu shiga gidan
har muka yi fira da wata mace mai suna Indo mai shekera (80) daga cikin
zuri’arsa, kuma na samu wasu kayan tarihi das hi Jange ya bari. Ba’a shigowa
Gusau ta wannan ƙofar. Asalin jange badakkare ne ya fito daga garin Zuru,
babban sadauki ne wanda an nuna cewa ba’a taba cinsa yaƙi
ba. Jikan yarsa Indo ta sheda man cewa har yanzu duk Jarumnta wadda suka yi
gado daga kakan su. ƙofar Jange tana daga cikin ƙofofin
Gusau da suka samu shahara da daukaka har yanzu sunan yana wanzuwa ko karamin,
yaro aka tambaya za’a ga cewa ya san wannan ƙofa dalilin da haka
har aka sakawa Unguwar dake kusa da wurin sunan ƙofar Jange. A halin
yanzu ƙofar Jange tana cikin yankin Galadima.
KOFAR MATSATTSA
Ƙofar matsattsa a yau
mazauni ta yana nan a marnar talilkkai gab da makaranta Allo ta Malam Sanda
Asalin wannan ƙofa sanadiyyar wani da ake kira “kako” kakansu (Senator
Hassan Nasiha da Muhammadu Bawai) wanda mutumin Katsina ne ya fito daga ‘yan
Tumaki. Lokacin da ya zo Gusau, sai ya tafi bayan gari ya zauna, saboda
sansanin ne na mayaƙa, nan suke bi. Ammamn shi kuma kako ya nuna dai nan yake
so a bashi, karshe dai ya bashi mazauni a bayan gari ya zauna, wannan a
sandiyyar sa ne aka gina wannnan ƙofa. Idan mayaƙa sun shigo sai masu
tsaron ƙofar su bede masa ya shigo cikin gari, sannan a rufe,
idan sun wuce ya dawo wurin sa. (Hirar da nayi da Muhammadu na Kumgu mai
shekara 103) yana zaune a marnanr talikkai, Malam Muhammadu ya bani labarin
cewa kakansa ya yi tsaron wannan ƙofar ta matsattsa. Sunan kakan na sa
Muhammadu ɗan
Mairi, it ace ƙofa ta ƙarshe
cikin ƙofofin Gusau. A yau ƙofar matsatstsa tana
cikin yankin Galadima, daga gabas zata sadar da mutum, rijiyr sarki da ƙofar
Rawayya da kasuwa, yamma makabarta kudu ƙofar Jange, Arewa
danfili da Sabon fegi.
Kamar yadda na faɗa a cikin bayanai a
baya ana radawa kofa suna sanadiyar wata salsala ko kuma nasaba kofa dai tana
samun asalin suna sanadiyar wata nasaba, idan muka duba tsofoffin garuruwa waɗanda suke da ƙofofi,
duk suna da wata nasaba daya da aka rada masu suna. A nan
garin Gusau ƙofofin namu sun, samu
suna ne sanadiar wasu nasabobi: Misali: kamar ƙofar rawayya da ƙofar kwatarkwashi da
kuma ƙofar Mani, da Jange,
wadannan ƙofofin akwai dalilin raɗa masu waɗannan sunaye. Jange mutun ne kuma shi ke tsaron ƙofar, haka ƙofar Mani mutun ne zarumi kuma manomi, sannan ƙofar kwatarkwashi an rada mata suna ne saboda mu’amala
dake tsakenin Gusau da Kwatarkwashi ita ma ƙofar Rawayya mu’amala dake akwai tsakanin mutanen Gusau da na Rawayya, haka
kuma ita ma ƙofar dogo/dokau.
4.3 WASU UNGUWOYIN GUSAU
Garin Gusau ya samu cigaba da habaka
da bunkasa da kere-keren ganuwa, saboda wasu mutane baki, a bisa ga wannan
karuwa Gusau ta Samu wasu shiyoyi da kuma Unguwoyi da yawa, a cikin littafin
(Gusau ta Malam Sambo 2012) an yi bayanin Unguwoyin Gusau.
SABON FEGI. A zamanin Sarkin Katsina Gusau Muhammadu
Bello mai a kwai (1929-1943) aka yayyanka gonaki aka ba mutnae fegi fegi son su
samu wurin zama kamarsu , Hassan Maigwada, Basakwacce da Mamman Audu Bazzazagi
mai dinkin Tela, Sune suka fara zama wurin da kuma, Halilu Emos Bakatsine da
sauran su. Ana kiran Unguwar da wannan suna saboda fegogi ne sababbi aka
rarraba wa ja’ama, wannan unguwa yanzu ta samu bunkasa da haЪaka da yalwa ta ƙara samun yawan
mutane saЪanin wancan lokacin
kamar Alhaji Ɗan Manga, Alhaji Umar Tanko, da Alhaji Aliyu Haido duk
suna cikin wannan yanki na sabon fegi ayanzu, Tana karkashin ri kon Galadima.
SHIYYAR TUDUN WADA
Lokacin
da aka yi ƙarin kasuwa da asibiti aka tayar da mutane da ke wurin
wato unguwar ka-fama-ni aka mayar da Tudun Wada a 1958. Da mutane suka koma
wurin sai suka yalwata, suka wadata, sai suka rika kiran sa da sunan tudun
wada, wurin da mima wato tudun wada mai wada ta (Hirarmu da kungiya mutane
1978). Unguwar tudun wada ta kafu ne a zamanin Sarkin Kudun Gusau (1948).
Yanzun shiyar tasamu bunƙasa da ha Ъaka
da yalwa da yawan mutane, Kamar Alhaji Shehu Idirs Zuru, Alhaji Ibrahim Ruwan
Dorawa, Alhaji Aminun Makaranta, Alhaji Abdullahi Zabarma, da Farfesa Bawa
Hassan, tana cikin yankin Gundumar Tudun Wada.
SABON GARI
Wannan
unguwa wani mutumin siraliyo ne Wanda ake cewa Morgan ya fara zama a cikin,
kuma ya riki mai unguwarta, kafin ta sami hakimi, a lokacin Sarkin Katsinan
Gusau Muhammadu Mai’akwai (1929) Morgan shi ne ya fara karЪar haraji a wurin, daga baya, ta sami magaji
Muhamamdu Taula wanda aka ɗauka
daga mada ya zama hakiminta na tan a farko. Da tafiya ta mika aka sami kabilu
daban-daban suka zauna a wannan unguwa ta sabon gari, daga cikin akwai Igbo da Yarbawa
da wasu Hausawa, yanzun wannan unguwa ta samu bunƙasa da ƙaruwar
jama’a, kamar su Alhaji Ladan Mada, Alhaji Adamu Samanja, tana cikin gundumar
sabon gari.
BIRNIN RUWA
Ana
kiran wannan wuri da suna Birnin Ruwa, saboda wuri ne mai dausayi da ni’imar
sanyi, wuri ne har ko da yaushe baya rabo da ruwa a lokacin damina, a zamanin
Sarkin Gusau Muhammadu TuЪuri (1976) a nan ne
kuma aka yi wa mutane da ake turawa Jos zuwa aikin masauki kuma ake fara aikin
B.C.G.A har wayau, nan leburorin zinare suka yi wa kan su dakunan bacci. Daga
nan, unguwar ta bunkasa har a zamanin Sarkin Katsina Gusau Muhamamdu Giɗe ya haɗa tada birnin haza
Matsayin hakimi ɗaya
ubandawaki Buharin Haza, wannan unguwa yanzu ta kara samu habaka da bunkasar mutane, tana
cikin gundumar Mayana.
‘YARLOKO
Wannan unguwa ta
tsiru azamnin Sarkin Katsinan Gusau ummaru Malam (1917-1929) mutane sun fara zama a wurin a
shekara 1929, lokacin da masu aikin tashar jirgin kasa suka kafa dakunan baccin
su a wurin. Daga cikin ma’aikatan jirgin kasan akwai kabilar Fulani da suaran
wasu mutane (Hirarmu da M.M.W.N Gusau 1978).
4. 4 GUSAU A MASTAYIN BABBAN BIRNIN JAHAR ZAMFARA
an kirkiro Jihar Zamfara daga
tsohuwar jihar sakkwato ta wancan lokaci, jihar tayi iyaka da jihar sakkwato
daga arewa, jihar katsina daga gabas, Jihar niger daga yamma, da kuma jiihar
Kaduna daga kudu, kanana hukumomin zamfara bayan Gusau, sun kunshi:- Gummi,
Kaura-Namoda, Shinkafi, Birnin Magaji, Tsafe, Bakura da Zurmi, an nada kanar
Jibril Bala Yakubu, FSS, Mss, Pcs Matsayin gwannan farko na jihar zamfara.
Gwagwarmaya day akin neman jihar
zamfara abu ne mai tarihi a kasar
zamfara ta kasance daula ce mai cin gashin kanta tun a da c an kamar yadda
masana tarihi suka rubuta. Kasa ce mai tsarin muliki da tarihin sarauta da tayi
gwagwarmaya da yake-yake da gobirawa da kabawa da katsinawa. Bayan zuwan
turawan mulkin mallaka sai daulolin Hausa suka fadi kuma tsarin mulkin
gargajiya da iyakokin kasa ya samu sauye-sauye masu yawa. Turawa a farko sun
raba yankin arewa zuwa larduna sannan daga baya sai suka kirkiro jihohi, bayan
samu ‘yanci kai a shekarar 1960 sai kasar zamfara ta zamanto karkashin rikon
tsohuwar jihar sakkwato. Kasancewar zamfara kasa ce mai yalwar mutane, karfin
nomad a kiwo ingantaccen tattalin arziki, da tarihin albarkatun kasa ne ya kara
kaimi ga ‘yan jihar wurin dagewa da kokarin akan fara yakin neman kafuwar jihar
zamfara mai zaman kanta.
Duk wasu alkalumma da sharudda da
ake bukatar cikawa domin jiha ta samu ikon zama da kafa funwanta kasar zamfara
ta cika su. Hakan ya nuna cewa kasar zamfara za ta iya rike kanta a matsayin
jiha mai cin gashin kanta. Wannan hakikancewa shi ne mafarin guguwar yakin
neman jihar zamfara inda wasu zakarkaru, jajirtattu, hazikan ‘ya’yan jihar suka
zage damtse, wurin fafutuka, rook, lallashi, kai kawo, da yekuwar ganin cewa
wannan mafarki na su ya zama gaskiya.
A
shekarar 1962 ne mutane zamfara suka fara yunkurin neman tabbatuwar jihar
zamfar mai zaman kanta, amma sai aka binne yunkurin har tsawon shekara ashirin
(1962-1982). A zamanin mulkin shehu shagari sai yunkurin ya dawo inda mutanen
zamfara suka gabatar da kudurin neman kafa jihar zamfara daga jihar sakkwato a
gaban majalisar dokokin ta kasa. Daga
acikin kudorora sittin da biyar (65) da aka gabatar a Majalisa, kudurin kafa
jihar zamfara shi ne a sama, gwannatin fara hula ta Sheh Shagari ta hango da
cewa da cancantar kafa jihar zamfara kuma tayi a zamar aiwatar da haka amma sai
akahambara da ita a juyin mulki shekara 1983 (Zamfara state hand book, 1997:4).
Haka aka yi a shekara 1991,
zamanin mulkin Gen. Ibrahim Badamasi Babangida lokacin da aka kirkiro jijohi
tara (9) jihar zamfara tana daya daga cikin jerin sunayen jihohin da za’a bayar
amman daga karshe sai aka canza aka baiwa jihar Kebbi wadda a lokacin bat a ma
nemi samun jahaba (Alapiki, 2005;60). Daga haka ne za’a gane cewa mutann zamfara
sun yi gagarumar hubbasa wurin neman ‘yanci ba tare da gajiya wa ko kasawa ba.
Daga cikin mutane da suka bada jijinsu da karfin su ga wannan tafiya akwai
Injiniya Abdu Gusau (Garkuwan Sakkwato). Alh. Ummaru (Dan galadima Birnin
Magaji). Malam Yahaya Gusau, da Dr. Garba Nadama da Alhaji Muhammad Lawal
Mande, Sarkin Fawa Malami, Alhaji Abubakar Tinau, Alhaji Sa’idu Muhammad
Dansadau, Alhaji Aliyu Abara Gummi, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, Injiniya
Dama Abdullahi Gusau da sauran su (Zamfara State hand Book, 1997;5)
Juriya jajircewa da addu’oin mutanen
zamfara sun kai ga gaci inda a ranar daya ga watan oktoba 1996, shugaban mulkin
soja na wancan lokacin Janar Sani Abacha ya bayyan tabbatuwar Jihar Zamfara
tare da ayyana garin Gusau a matsayin cibiya kuma babban birnin jiha. Wannan
Muhimmiyar nasara ta zama mabudi ga samun gagurumin cigaba a bangarorin ilimi
da bunkasar tattalin arziki da kuma ababen mure rayuwa da hada-hadar mutane
inda garin ya zamo babar cibiyar gudanar da mulki da huldodin kasuwanci a jihar
zamfara.
4.5 NAƊEWA
Wannann babi wato
babi na hudu, babi ne day a ƙumshi shimfida da kofofin Gusau. In da aka yi
muhimman abubuwa wadan da suka hada, da gabatarwa, kofofin Gusau, da sharhin
kofofin Gusau, da kuma wasu unguwoyin garin Gusau da nadewa, manufar wannan
binciken it ace bayyan kofofin Gusau.
Kamr yadda masu
Magana kace “Komi yayi farko yana da karshe” domin haka wannan babi na hudu ya
kawo karshe, don an yi bayanin cewa babu wani littafi ko kundi da ya yi sharhi
koffofin Gudau, kuma a cikin babi na yi sharhin kofofin da in da suke, ta yin
mafanin da hira da mutane tsofaffi ‘yan asalin garin Gusau. A cikin babi anyi maganar wasu shiyoyin na garin Gusau,
wanna babi na hudu ya yi bincike kofofin Gusau da sharhin su da unguwoyin na garin
Gusau, shi ne makasaduin wannan babi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.