Ganuwar Gusau Da Kofofinta (6)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Ganuwar Gusau Da Kofofinta (6)

NA

UMAR YAHAYA DOGARA

Ganuwa

BABI NA BIYAR

KAMMALAWA

5.0              SHIMFIDA

Masu iya magana kance “komi yayi farko zai yi karshe, amman ban da ikon Allah” Wato duk abin da aka sa masa rana, komi    daren dadewa sai ya zo. A wannan babi ne binciken ya kammalu, kuma ya tuke, domin a cikin wannan babi ne ake nade aikin gaba dayansa, ta yadda aka bayyan shi a dunkule. Haka zalika, a cikinsa ne aka kamala aikin, ta hanyar bayyana dukkan abin da binciken ya hango, ko ya gano game da “ganuwar Gusau da kofofin” wato an tattauna ssakamakon da nazari ya gano dangane da aikin da ake yi a kan Ganuwar Gusau da kofofin ta.

5.1 Nadewa

Wannan binciken mai suna “Ganuwar Gusau da kofofinta” nazari ne dake kunshe a cikin babi. A babi na farko wanda shi ne, shinfidar wannan bincike yana dauke da gabatarwa, wato yadda nazarin ya kasance, ta hanyar bayyana dalilin bincike da manufar ɓbincike da muhimmancin bincike da farfajiyar bincicke da has ashen bincike da hanyoyin gudanar da bicike, daga karshe sia aka  nade babi. Babi na biyu kum, babi ne  wanda ya yi waiwayen ayyukan magabata wadanda suke da alaka ta kusa ko ta nesa da wannan bincike, wato ayyukan da ake gudanar a game da Ganuwar Gusau da kofofinta.

Hari ila yau, babi na uku na wannan nazari, babi ne da ke dauke da Ganuwar Gusau da tarihin garin Gusau da tarihin Ganuwar Gusau da tasirin Ganuwar Gusau da nadewa, a babi na hude yayi bayani game da Kofofin Gusau, da kuma sharhin kofofin Gusau, ta hanyar anfani da hira da mutane, kuma aka yi bayani wasu unguwoyin garin Gusau da kuma gusau a matsayin babban birnin jahar zamfara, sai a nade  babin.

A babi na karshe, na wannan binciken kuwa, shi ne babi dad a ya kunshe abubuwa a takaice ne na wannan bincike ta hanyar takaita abubuwan day a gano ta hanyar takaita su a babi.

5.2 Shawarwari

            Yana da kyau manazarta su zage wajen gano al’amura daban – daban da adabic Hausa ya kunsa yadda wannan rundi ya tarke, Ganuwar Gusau da Kofofinta. Abu ne mai wahala kuma mai sauki da burgewa, idan manazarta suka kawo wa fagen falsafa dauki, domin babu wani da zai yi una wannan aiki sai mu.

            Shawarwari ta gaba it ace, manazarta da masu sha’awar Hausa su sa himmar gano yadda al’umura suke zuwa yau, domin haka zai sa bahaushe ya dade sanin kansa, kuma ya gane inda ya kai bugu, da kari, idan mahukunta na kananan hukumomi da jahohi da kuma gwamnatai tarayya suka tallafa wa bincike irin wannan, lallai na gaba kadan za a kara fuskantar alkiblar da t ace, kuma al’amura za su kara iyan ta a kasa  saboda ana nazartae ala’adu adabin kasa.

            Wannan bincike yana dauke da muhimman shawarwari da za su taimaka wa manazarta a fage na ilimi da suaran al’umma baki daya. Shawara ta farko, shawara ce ga manazarta harshe da fagen ilimi daban – daban, das u kasance masu hakuri da ladabi da biyyay ga malammansu da abokin karatunsa, domin samun alabarkar ilimi da tarbiyya, domin ilimi, da duk ya samu ba tarbiyya, bay a albarka, ya domin ilimi da dan ba’ura, haka kuma, su kasance a koyaushe cikin bincike da waiwayar ayyukan magabata, ba domin su samu maki ba kawai domin su ciyar da ilmi gaba.

Manazarata

Tuntuɓi Amsoshi

Post a Comment

0 Comments