Ticker

Karin Harshen Zamfarci (Musamman A Garin Gusau) (6)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Karin Harshen Zamfarci (Musamman A Garin Gusau) (6)

NA

BASHIRU HARUNA

Walwalar Harshe

BABI NA BIYAR

KAMMALAWA

5.0 SHIMFIƊA

A babin da ya gabata an yi magana ne akan karin harshen garin Gusau da Daidaitacciyar Hausa da tsarin sauti da ƙirar kalma da ma’anar akalmomi da gignin jumla. A wannan babi zai yi magana a kan taƙaitawa, hasashe da kammalawa da ratazye sannan kuma da manazarta.

5.1 TAƘAITAWA

A taƙaice wannan aikin mai taken Karin harshen Zamfarci musamman a garin Gusau, ya kasu babuka guda biyar. A babi na ɗaya: Gabatarwa ne, wanda ya ƙunshi bitar ayyukan da suka gabata da gudunmuwar aikin ga ilimi da dalilin yin bincike da tsarin gabatar da aiki. Babi na biyu ƙasar Hausa: Babin ya ƙunshi taƙaitaccen tarihin ƙasar Hausa da taƙaitaccen tarihin Zamfara da taƙaitaccen tarihin garin Gusau. Babi na uku mai suna: Kare-karen Harsuna, an yi bayanin ma’anar harshe da ma’anar karin harshe da dalilin samuwar karin harshe da rabe-raben karin harshe. Daga ƙarshe karin harshen gabas da karin harshen yamma. Babi na huɗu: Karin harshen garin Gusau da Daiadaitacciyar Hausa An yi bayanin karin harshen garin Gusau da ma’anar Daidaitacciyar Hausa da tsarin sauti da ƙirar kalma da ma’anar kalmomi da ginin jumla. Babi na biyar: Taƙaitawa da kammalawa da Rataye da kuma manazarta.

Harshen Zamfarci (Musamman a garin Gusau) domin cika ƙudiri na kammala wannan kundin digiri, domin samun digiri B. A (Hausa) a ƙarƙashin sashen jkoyar da harsuna da al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

5.2 HASASHEN BINCIKE

Kamar yadda ya riga ya gabata, wannan bincike ya yi nazari ne kan “Karin Harshen Zamfarci musamman a garin Gusua’, wanda nazari ne kan karin harshen ƙasar Hausa. Haka kuma sanin ce wane harshen Hausa ya yi ambaliya zuwa ƙasashen kusa da na nesa wanda haka ya ƙara wa harshen bunƙasa musamman a tsakanin al’ummomi masu asali (wato harshe da al’adu) daban da na ƙasashen Hausa. A yau harshen ya zamanto ba wai harshe hulɗa ba ne kawai, harshe ne da ya mamaye ƙabilu da dama a harkokinsu na yau da kullum ta yadda har ma da waɗansu da ba ‘yan asalin harshen ba, harshen ya sanya masu riga suka zama Hausawan ƙarfi da yaji.

Bugu da ƙari tasirin kasuwanci da siyasa da addini da ilimi da nishaɗi da ma matsayin harshe wajen watsa labarai a gidajen talabijin da na rediyo da jaridu da littatafan ilimin zamani musamman Adabi, da matsayin harshen wajen kafafen watsa labarai musamman a jihohi da ƙasashen da ba ma na Hausawa ba sun taimaka wa harshen matuƙa wajen haifar da tasiri a rayuwar al’umma da dama. Haka kan haifar da wani salon magana da daban kuma mai sauƙi. Lura da wannan dalilai ne wannan bincike zai nazarci waɗannan, kamar haka:

1.      Waɗanne al’ummomi ne ake samu a garin Gusau, kuma wane harshe/harsuna suke amfani da su, sannan wacce irin dangantaka ce tsakaninsu da harshen Hausa?

2.      Harsunan da ake samu a garin Gusau sun yi tasiri a kan juna kuma wane harshe ne ya fi tasiri kan sauran harsunan?

3.      Harsunan al’umma na wane ake samu a garin Gusau kuma a waɗannan muhalli aka fi yawaita amfani da harshe/harsuna.

5.3 NAƊEWA

Wanna babi shi ne babi na ƙarshe dangane da nazari da kuma binciken da aka gabatar a kan karin harshen Zamfarci (musamman garin Gusau) domin kammala wannan kundin digiri, don samun digiri B.A (Hausa) a ƙarƙashin sashen koyar da harsuna da al’adu na Jami’ar Tarayya da ke Gusua.

MANAZARTA

Tuntuɓi Amsoshi.

Post a Comment

0 Comments