Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazari Kan
Jawabin Kama Aiki Na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019
(1)
NA
NASIRU HASSAN
SADAUKARWA
Wannan bincike an sadaukar da shi ga iyaye maza da mata, waɗanda suke abin alfahari bisa ga irin gudummuwar da suka bayar wajen tarbiyya da ilmantarwa da duk abin da uba da uwa kan yi zuwa ga ‘ya’yansu. Allah ya jiƙansu, ya kuma saka masu da mafificin alkhairinsa amin. Bayan haka, ba za a manta da Malamai ba waɗanda suka yi tsaye wajen inganta tarbiya tare da cusa ilimi a zukatanmu, wanda da himmarsu ne tare da taimakonsu wannan aiki ya kammala. Allah ya saka masu da alkhairinsa amin.
GODIYA
Dukkan yabo
da godiya sun tabbata ga Allah mai girma da ɗaukaka. Tsira
da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da
sahabbansa da waɗanda suka bi
su da gaskiya har zuwa ranar sakamako.
Ina ƙara
miƙa godiya ga iyayena bisa ga tarbiyar da suka
bani tun daga ƙuruciya har zuwa yau. Allah ya saka masu da
mafificin alhairi. Godiya ta musamman ga Madugu uban tafiya wato Malam Musa
Abdullahi wanda ya kula da duba wannan aiki tare da ba da shawarwari da
gyare-gyare don tabbatar wannan kundin bincike ta yadda zai zama mai amfani ga
jama’a. Duk da ɗimbin aikin
da ke gabansa bai yi ƙasa a guiwa ba wajen
ba da lokacinsa ganin samun nasarar wannan bincike. Allah ya saka masa da
alhairi ya cika masa burinsa amin.
Haka ma ina ƙara
miƙa godiya ga Malamanmu na wannan sashe bisa
koyarwa da shawarwarinsu. Musamman Malam Aliyu Rabi’u Ɗangulbi mai
kula da sashen jarabawa (Eɗam officer) da Malam Isah S/Fada da kuma uwa
uba shugaban sashe wato Farfesa Aliyu Muhammad Bunza.
Haka ba zan
manta da waɗanda suka
taimaka man wajen wannan bincike ba, irin su Alh. Adamu Sani Katuru (Zamfara
Radio), Abdullahi Musa (FM Radio) Sani Adamu Gusau (Friend) da Ahmad Muhammad
Kabir (Friend) da kuma ma’aikatun gwamnati kamar Ma’aikatar Yaɗa labaru ta
jiha da Ɗakin aje bayanai na jiha (State Library) da
kuma gidan tarihi na jiha (History Bereau), Allah ya saka masu da alkhairi
amin.
TSAKURE
Wannan
bincike mai taken “Nazari kan Jawabin Kama aiki na Zaɓaɓɓun Gwamnonin
Jihar Zamfara daga shekara ta 2007 zuwa 2019” An gudanar da shi domin ganin
kalaman da zaɓaɓɓun gwamnoni
ke yi don amfani da su a matsayin hanyar jawo ra’ayin jama’a domin natsuwa da
abin da suka faɗa zuwa ga
al’ummarsu na abin da ya shafi tattalin arziki da walwala da sauransu. Wannan
binciken zai mai da hankali ne wajen nazarin jawaban tare da fito da abin da
jawaban suka ƙunsa ta fuskar manufa, salo da kuma sarrafa
harshe.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.