Nazari Kan Jawabin Kama Aiki Na Zababbun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019 (3)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Nazari Kan Jawabin Kama Aiki Na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019 (3)

NA

NASIRU HASSAN

Jawabi

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0 GABATARWA

Waiwaye adon tafiya, duk wani bincike da za a gudanar wajibi ne a duba abubuwan da suka gabata waɗanda suke da tasiri da kuma dangantaka da binciken da ake so a yi domin yin haka shi zai sa aiki ya yi inganci ƙwarai da kuma samun fahimtar inda aka dosa da kuma inda za a tsaya. Duk da cewa wannan aiki sabo ne, amma dai za a ga cewa yana da alaƙa ko ɓirɓishi da wasu ayyukan da suka gabata.

 

A ‘yan shekarun baya, an yi rubutu da ke da alaƙa da wannan bincike, kama daga bugaggun littattafai da kundayen bincike da maƙalu da jaridu da yanar gizo (Internet) kamar yadda za a gani.

 

2.1 BUGAGGUN LITTATTAFAI

Masu iya magana kan ce tuna baya shi ne roƙo, don haka, za a fara da duba ayyukan magabata da ke da dangantaka da wannan bincike da ya shafi dangantakar harshe da siyasa a matsayin tudun dafawa.

 

Sani, (2011) a littafinsa ya yi bincike kan maganganun ‘yan siyasa, don haka, wannan aikin na da dangantaka da wannan binciken da za a gudanar wanda ya shafi jawabin kama aiki na gwamnonin jihar Zamfara a keɓance. Saboda haka, wannan binciken ya mayar da hankali ne kan fahimtar siyasa, domin samun dammar yin tsokaci kan jawabin ‘yan siyasa da nufin fayyace saƙonni da ke ƙunshe a cikinsa.

 

Mafara (2010); A na shi littafin ya yi magana kan ma’anar siyasa da asalin kalmar siyasa. A cikin littafin ya kawo siyasar mulkin mulukiyya da siyasar dimokaraɗiyya.

 

Da yake ayyukan kan siyasa ne, littafin yana da dangantaka da wannan binciken da za a yi.

 

2.2 KUNDAYEN BINCIKE

Kusan za a iya cewa babu kundayen musamman a matakin dirigi na ɗaya da ya yi nazari ko bincike da ke da alaƙa ko dangantaka da wannan aiki. Sai dai an samu wani bincike a kundin digiri na biyu da yake da alaƙa da wannan aikin. Wannan ya ba da dammar yin bita domin fito da alaƙar da ke cikin aikin.

 

Jangabe (2015) A binciken da ya yi a kundin digirinsa na biyu, binciken nasa ya mayar da hankali ne kan jawaban da ‘yan siyasa a jihar Zamfara suka yi musamman a shekarar (2011). Inda ya yi nazarin jawabi goma (10) da suka shafi na maza da na mata. Wannan aiki yana da dangantaka da binciken da za a gudanar, domin ya shafi nazari kan jawabai, don haka, zai taimaka da ƙara haske wajen nazarin jawabin kama aiki na Gwamnonin Jihar Zamfara.

2.3 MAƘALU DA SAURAN TAKARDU

Ba kasafai akan samu maƙalu da aka yi nazarin jawabai kai tsaye ba, sai dai abin da ya shafi harshe da siyasa.

 

Ɗantumbishi (2010) a takardarsa ya yi sharhi kan siyasa da Hausa. Ya ce, Hausawa na da ilimi iri uku, na farko na gargajiya, na biyu na addini, na uku kuma na Turawa.

 

Saboda haka, Hausawa na da ilimin siyasa. Wannan takarda ta ƙara haske ga wannan bincike inda za a fahimci muhimmancin siyasa ga rayuwar ɗan’adam. Kuma ta yi alaƙa da binciken ta fuskar harshe da siyasa.

 

Yakasai (2013); A wata maƙalarsa, da ya gabatar, inda ya yi bayanin matsayin matani a harshen magana da kuma nazarin wasiƙar da Obasanjo ya aikewa Buhari, ya dubi wasiƙar ta fuskar manufa da tsari da kuma salo da sarrafa harshe. Wannan nazari yana da dangantaka da binciken da za a yi kan jawabin kama aiki na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara, daga shekarar 2007 zuwa 2019. Saboda haka, wannan maƙala ta haskaka matuƙa wajen fahimtar yadda za a ɗora wannan aikin.

 

Daily Trust (2019); A wannan takarda (Jarida) ta fitar da jawabai na ‘yan siyasa da shuwagabani ciki har da jawabin kama aiki na Gwamnan Jihar Zamfara wato “Alhaji Bello Muhammad (Matawallen Maradun)” wannan aiki da wannan jarida ta fitar ya taimaka matuƙa, domin a nan ne aka samu shi kansa jawabin wanda yana cikin jawabin da za a yi nazari a wannan aikin.

 

Leadership (2019); Haka ita ma wannan takardar (Jarida) ta ɗauko jawabai daban-daban ciki har da jawabin kama aiki na gwamnan Bauci inda ya yi jawabai na jan hankali da albishir zuwa ga mutanensa. Wannan aiki ya yi kama da wannan bincike kuma ya ƙara haske matuƙa.

 

2.4 YANAR GIZO (INTERNET)

Babu shakka a Yanar Gizo (internent) ma akwai jawabai da suka shafi siyasa da harshe na gida da na waje, waɗanda za su taimaka wajen tafiyar da wannan binciken.

 

Dylgjeri (2017); A wannan aikin an yi ƙoƙarin nazari ne ko sharhi kan jawaban siyasa inda aka kwatanta siyasa da harshe. An bayyana cewa ba zai yuwu a yi nazarin siyasa ba, dole sai an yi la’akari da harshe, domin a tare suke tafiya. Wannan aiki yana da dangantaka da wannan bincike da za a yi, kuma ya ƙara haske matuƙa.

 

Choi (2016); Wannan aiki ya yi nazarin masu jawabai da waɗanda ake yi wa jawaban da ma muhallin da ake gabatar da shi. Inda aka yi bayanin muhimmancin bagiren gabatar da jawaban da matsayin jawaban da saƙon jawaban kan isa zuwa ga masu sauraro da kuma irin martanin da masu sauraron jawaban kan mayar. Wannan aiki yana da alaƙa da wannan bincike da za a yi kasancewar ya shafi nazarin jawabai kuma ya ƙara haske matuƙa.

 

2.5 KAMMALAWA

A taƙaice, wannan babi na biyu, ya yi bayani ne kan bitar ayyukan da suka gabata wanda ya haɗa da gabatarwa da waiwaye kan bugaggun littafai da kundayen bincike wato kundin digiri na biyu da takardu da muƙalu da Jaridu da kuma abin da ya shafi Yanar Gizo (Internent) da suke da alaƙa da wannan binciken ko nazari da kuma kammalawa.

Post a Comment

0 Comments