Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazari Kan
Jawabin Kama Aiki Na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019
(4)
NA
NASIRU HASSAN
BABI NA UKU
4.0 GABATARWA
Taƙaitaccen
Tarihin Jihar Zamfara, Jihar Zamfara na cikin jihohin Nijeriya masu amfani da
harshen Hausa. Hausawa na cikin manya ƙabilun ƙasar
nan; ba shakka irin wannan nazari, yana da matuƙar muhimmanci
ga kowace al’umma da ke da burin inganta al’amurranta da tabbatar da kyawawan
al’adunta na gargajiya da nufin ɗora jama’arta bisa wani amintaccen
tafarki wanda zai shimfiɗu a kan wata halattaciyar aƙida.
Muhimman abubuwa dangane da bunƙasar al’umma,
sun haɗa da ilimi da
sana’a da al’ada da kuma zaman lafiya. Koda yake siyasa na cike da hanyoyi da
ce-ce-ku-ce da tarzoma, Zamfara na cikin kwanciyar hankali da lumana.
4.1 TAƘAITACCEN
TARIHIN JIHAR ZAMFARA
Jihar Zamfara
ta yi suna tun ana cewa “Bature zaki”. Ma’ana tun tana a matsayin daula. Daular
Zamfara daɗaɗɗiya ce,
tarihi ya nuna cewa daular Zamfara ta kafu ne tun a ƙarni na goma
sha uku (ƙn 13), kuma tana ɗaya daga
cikin daulolin ƙasar Hausa tsofaffi (wato waɗanda suka daɗe da kafuwa).
Haka tarihi ya nuna cewa daular Zamfara wani yanki ne daga daulolin da suka
taru suka haɗa tsohuwar
daular Usmaniya a shekarun baya. Jangebe (2015).
Tarihi bai
tsaya nan ba, sai da ya bayyana mana cewa, an sami bayani a wajen Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello da sauran Malaman tarihi a addini cewa, “Yankin ƙasar
da ake kira Zamfara tana ɗaya daga sanannun ƙasashen
Bilad al-Sudan da Musulunci ya yi ƙarfi
a ciki”.
Bilad
al-Sudan ta haɗa da ƙasar
Kano da Daura da Katsina da Zazzau da Barno da Gobir da Zamfara da Kebbi da
Yawuri da Nufe da Gulma da Bargu da ƙasar Ilori. Ko
da yake tarihi Bayajida ya sa wasu masana suna ɗaukar ƙasashen
Zamfara da Kebbi da Yawuri da Nufe da Ilori ƙasashen Banza
Bakwai, amma wannan bai hana a ce masu Hausawa ba.
Zamfarawa
kamar sauran mutanen daulolin sudan ta tsakiya sun ɗauki kansu
Hausawa ne kuma sun fito daga Gabas, suka ratso ƙasar Barno,
suka isa mazauninsu na farko a Dutse.
Nadama G.
(1977) ya ce, Zamfara haɗi ne da Katsinawa da Gobirawa. Kamar
yadda Muhammadu Bello ya ce; Gobirawa su ne uwa, Katsinawa kuwa su ne Uba. A
wata ruwaya kuma asalin Zamfarawa daga Gobir suke inda aka samu auratayya
tsakanin “Fara” ɗiyar Sarkin
Gobirawa suka shiga a Birnin Zamfara a ƙarƙashin
riƙon sarkin Babari a lokacin sarkin Zamfara
Maroƙi. Gusau (2008), Daular Zamfara ta rayu kafin
mulkin Gobirawa, tana da mazaunin mulki inda sarkin Zamfara yake zaune watau
Birnin Zamfara.
Babban Birnin
Zamfara ya rushe, saboda ɓulluwa da haɓakar Daular
Gobir a ƙarni na goma sha takwas (ƙn.
18) da kuma wargaza al’adu da jama’ar Zamfara suka yi wanda ya ƙarawa
al’amarin wahala. Kuma saboda nasarar jihadi a ƙarni na sha
tara (ƙn.19) an lalata tare da rushe manyan
Garuruwan Zamfara kamar su kiyawa da jata da Banga da wasu ƙananan
garuruwa.
A madadinsu
kuma aka sami wasu sababbin garuruwa. Daga cikin garuwan da suke ƙarƙashin
Zamfara akwai Zurmi da Mafara da Bakura da Maradun da Anka da Gummi da Zoma da
Kagara da sauransu.
Zamfara sun
daɗe suna neman
da a yi musu jiha, amma haka bata samu ba, sai a lokacin mulkin soja na janar
Sani Abacha, ɗaya ga watan
Oktoba na shekarar 1996, Zamfara ta yau, tana da ƙananan
hukumomi goma sha huɗu (14) waɗanda suka haɗa da.
·
Anka
·
Bakura
·
Bukkuyum
·
Birnin Magaji
·
Bunguɗu
·
Gusau
·
Gummi
·
Ƙaura – Namoda
·
Maru
·
Maradun
·
Shinkafi
·
Tsafe
·
Talata Mafara
·
Zurmi
A ɗaya ga watan
Oktoba ne 1996, a ka ƙirƙiro
jihar Zamfara a lokacin mulkin Janar Sani Abacha. Inda gwamnan soja na farko
shi ne “Lieutenant Kanal Jibril Bala Yakubu”. Jihar Zamfara ta samu Gwamnan
farar hula na farko a shekarar 1999. A ƙarƙashin
mulkin Ahmad Sani (Yariman Bakura). Daga nan sai mulkin siyasa ya ci gaba har
zuwa yau.
Wani muhimmin abu shi ne kasuwanci, wanda ke bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Duk da cewa kasuwanci na da faɗi, domin ana saye da sayarwa na abubuwa iri – iri. Jihar Zamfara na da matsayi da daraja wanda sana’ar noma ya samar mata. Jihar Zamfara ta shahara wajen noma kayan abinci iri – iri da suka haɗa da shinkafa, Gero, Dawa, Masara da wake da sauransu. Ana kuma noma kayan Lambu kamar Tumatir, Tattasai, Attarugu da albasa da sauransu. Wannan harka ta noma na cikin manyan abubuwa da ke haɓaka tattalin arzikin Zamfara. Jangebe (2015).
3.1.1 YAWAN
JAMA’A
Yawan Jama’a
shi ne adadin yawan jama’a ko al’ummar da ke zaune a wuri, ta haɗuwar jinsuna
daban-daban. Jihar Zamfara ƙasa ce wadda
Allah ya albarkata da yawan jama’a. Jihar Zamfara dai tana da ƙananan
hukumomi guda goma sha huɗu (14) kuma a ƙididdigar da
aka yi ta shekarar 2006, hukumar ƙidaya ta ƙasa
ta gano yawan jama’ar da ke kowace jiha.
Jihar Zamfara
tana da adadin yawan jama’a kimanin 3,278,873, inda suka ƙunshi maza da
mata. Ga jadawali yawan Jama’a a kowace ƙaramar
hukuma, inda suka ƙunshi maza da mata.
S/N |
Ƙaramar hukuma |
Maza |
Mata |
Jimla |
1. |
Anka |
72,456 |
71,181 |
143,637 |
2. |
Bakura |
92,369 |
95,772 |
187,141 |
3. |
Birnin
Magaji |
90,824 |
93,259 |
184,083 |
4. |
Bukkuyum |
108,812 |
107,536 |
258,048 |
5. |
Bunguɗu |
128,831 |
129,813 |
258,644 |
6. |
Gummi |
102,682 |
104,035 |
206,721 |
7. |
Gusau |
198,682 |
185,030 |
382,712 |
8. |
Ƙaura
Namoda |
145,548 |
139,815 |
285,363 |
9. |
Maradun |
106,403 |
101,160 |
207,563 |
10. |
Maru |
146,920 |
146,221 |
263,141 |
11. |
Shinkafi |
66,51 |
96,452 |
133,964 |
12. |
Talata
Mafara |
107,516 |
108,134 |
215,650 |
13. |
Tsafe |
129,010 |
137,919 |
266,929 |
14. |
Zurmi |
145,054 |
148,923 |
293,977 |
A jimlace idan an duba za a ga cewa jihar Zamfara
tana ɗauke da yawan
jama’a kimanin 3,278,873 a wannan ƙidaya.
3.1.2
ALBARKATUN ƘASA
Allah (SWT) ya
albarkaci jihar Zamfara da wata ƙasa ta noma
da bishiyoyi ko itatuwa da ma’adinai iri-iri. Zamfara na da manyan gonaki da
fadamu da ƙoramu da ke taimakawa wajen noman rani. Ana
yin noma iri biyu a Zamfara wato noman damina da na rani.
A noman
damina aka fi noma mafi yawan abinci kamar gero, dawa, maiwa, wake, da
sauransu. A noman rani kuwa an fi noma kayan marmari. Don haka, noman da
Zamfara ke yi, ya ƙunshi na ci da na
sayarwa. Kayan marmarin sun haɗa da tumatur, tattasai, tarugu,
albasa, barkono da sauransu. Akwai irin su lansir da ayayo da karas da kabeji
da dankali da rogo da mankani (Gwaza) da sauransu. Bishiyoyi da ke jihar
Zamfara duk masu amfani ne, akwai na ci kamar tsamiya da kanya, ɗoruwa da kaɗanya da faru
da sauransu. Akwai kuma waɗanda ake amfani da su wajen yin ababen
amfani a gida da magani da sauransu.
3.1.3
SANA’O’I
Dangane da
sana’o’i ko tattalin arziki, jihar Zamfara ta faro ne daga tonon kuza ko haƙarta,
wanda idan muka duba kusan duk garuruwan da suka ci gaba da zama birane suna
zaune ne a yankin da ake haƙar tama ko
kuza. Kuma abu mafi muhimmanci a jihar Zamfara shi ne noma, saboda ta kasance
tana da rayayyar ƙasar noma. Saboda tun ƙarni na
sha-shidda (ƙn 16) an san da cewa ƙasar Zamfara ƙasa
ce ta noma, wadda kusan shi ne ya haɗa ƙasar da
sauran makwaftanta.
Jihar Zamfara
ta samu ci gaba ta hanyar kasuwancin fatu da ƙiraga da rini
da dukanci da kuma sassaƙa. Haka ma
tattalin arzikin Zamfara ya haɗa da sana’ar noma da kiwo da ƙira
da jima da saƙa da ɗinki da kaɗi da fawa da
gini da kitso da ƙwadago da koda da dillanci da dako da
sauransu. Don haka, al’ummar Zamfara kowa da sana’ar da ta jibance shi, kamar
yadda Hausawa ke cewa “Kowa da bikin da ya karɓe shi, wai
makwafcin mai akuya ya sa yi kura”. Mutanen Zamfara suna da sana’o’i daban-daban,
wannan ya zama al’ada ta mutum, wato samun abin yi don biyan buƙatar
kai. Jangebe (2015).
3.1.4
YANAYINTA
Jihar Zamfara
ƙasa ce mai ɗauke da
yanayi iri biyu, rani (dry season) da kuma damina (rainy seasons). Yanayin
jihar Zamfara yana da ɗumi ƙwarai duk
tsawon shekara in ban da watan Fabareru zuwa watan biyar da ake sanyin hunturu
(harmatan). Damina kan fara daga watan maris/Afrilu zuwa Satumba/ Oktoba har
zuwa watan ɗaya na Hausa.
Don haka ƙasa ce ta ciyawa mai itatuwa jefi-jefi masu ƙaya
da masu faɗin ganyaye
daban-daban.
A jihar
Zamfara rani na kamawa daga watan Oktoba ya ƙare watan
Mayu. Daga nan sai a samu yanayin ya rabu gida biyu wato hunturu (harmatan) da
kuma bazara (hot period).
3.2 MA’ANAR
HARSHE
Masana da
yawa sun yi bayani kan harshe da muhimmancinsa da sigoginsa da dangantakarsa ga
rayuwar al’umma. Waɗannan masana sun ƙunshi
al’ummomi iri-iri, domin wasu daga turai suke, wasu daga Amurka wasu kuma daga
Afrika.
Wannan ya
nuna cewa harshe al’amari ne na kowa (bil adama). Mutum shi ke amfani da harshe
wajen harkokinsa na yau da kullum, domin samun biyan buƙatu na
zamantakewa. Don haka, a bayyane yake cewa mutum kaɗai ke iya
sarrafa shi (harshe) ta hanyar amfani da kalmomi.
Rabi’u M.
Zarruƙ da A. Kafin Hausa da Bello Y. Alhassan
(1986). Sun ce, Harshe magana ce wadda ake ji a fahimta. Harshe shi ne abin da
ya bambanta ɗan adam da
sauran dabbobi. Harshe a wurin ɗan adam linzami ne na tunani. Sauran
dabbobi kuma sai dai su yi kuka ko gurnani ko haushi ko haniniya don su nuna
fushinsu ko murnarsu ko wuyarsu ko daɗinsu. Mutum ɗai ne ke iya
riya abu a zuciyarsa ko ya gani da idanunsa ko ya ji da kunnuwansa, sannan ya
faɗa da fatar
baki. Duk lamurran rayuwa harshe ne abin kwatantasu da adanasu a ka ko a rubuce
da kyautatasu.
Harshe baiwa
ce da ɗaukaka da
Allah ya ba ɗan’adam, da
shi mutum ke sadarwa da mu’amala. Ba a fahimtar wannan baiwar sai an dubi irin
faman da ake yi kafin a fahimci abin da bebe ko jariri ke buƙata.
Harshe shi ne
maƙunshin ilimi da tarbiyyar al’umma da
hikimominsu ilimi da tarbiyyar al’umma da hikomominsu da abubuwan sonsu da na ƙinsu,
duk da harshe ake faɗarsu da adanasu har zuwa ga na baya. Ta haka
ne al’umma ke renon ‘ya’yanta bisa kyawawan al’adunta, saboda haka, harshe ne taskar
ilimin al’umma da tarihinta.
Skinner (1977),
ya ce: Harshe shi ne magana” shi kuwa “Noam Chomsky” kamar yadda Fromkin da
Rodman (1976:1) cewa ya yi, harshe shi ne “Mutuncin ɗan’adam wanda
ya sa ya yi fice”. Haka kuma a wannan ruwaya, an fassara harhe da cewa babbar
alfarma ce ga mutum wadda ta bambanta shi da wasu halittu.
Masana da
dama sun yi bayani kan harshe irin su Dyelaran, O.O (1990:22) cewa ya yi harshe
muhimmin abu ne wajen bayyana al’adar mutane.
Bisa waɗannan bayanai
na masana da suka gabata a iya cewa harshe wata riga ce ta alfarma wadda ɗan’adam ke
sawa domin ta bambanta shi da wasu halittu.
4.3 MA’ANAR SIYASA
Masana irin
su Bargery (1984) da Yakasai (2012) da ƙamusun Hausa
(2006) da sauransu sun bayyana ma’anar siyasa kamar haka.
Bargery
(1934) cewa ya yi siyasa na nufin rangwame ko farashin kowane abu ko kuma
tausayawa a cikin al’amura. Yakasai S.A (2012) kowace rayuwa tafe take da abin
da ke yi mata jagora domin samun nasarar gudanar da al’amuranta na yau da
kullum. Wannan jagoranci shi ake kira shugabanci. Wannan shugabanci ya fara tun
daga maƙamin Sarauta ta gargajiya har zuwa
shugabancin ƙananan hukumomi da jahohi da kuma ƙasa
baki ɗaya. Ƙamusun
Hausa (2006), siyasa ita ce tafiyar da al’amuran jama’a ta hanyar neman
ra’ayinsu da shawarwarinsu.
Idan aka ce
siyasa to akwai ɓukatar a san
mene ne siyasa? Wannan kalma ce ta Larabci wace a halin yanzu an mayar da ita
Hausa. Wadda kuma ke nufin sauƙi ko rangwame
ko jinƙai. A da can, idan aka cewa mutum ɗan siyasa to
ana nufin mutum mai jinƙai, mai rangwame, mai
nasiha, watau mutum mai kyautata wa al’umma. A Hausance siyasa tana nufin wani
tsari na jawo ra’ayin mutane da su haɗa ƙarfi
wuri ɗaya su zaɓi wasu ko
wani mutum don ya shugabancesu bisa ga tsarin dokokin ƙasa. Siyasa
wata dabara ce ta neman mutane su zama masu ra’ayi ɗaya domin su
zaɓi wakilinsu
ga shugabancin ƙasa ko jiha ko ƙaramar
hukuma.
4.4 YAƊA
LABARUM SIYASA
Dangane da yaɗa labarai, a
jihar Zamfara, an fi tallata duk siyasar da ke kan karagar mulki, wato ta
gwamnati domin a daɗaɗawa Gwamna. Dalili shi ne, ma’aikatan
gidan redoiyo da Talabijin da Jarida, suna ganin kamar wannan gwamnati suke yi
wa aiki ba jama’a ba, ganin cewa gwamna ke naɗa shugabannin
waɗannan kafafe.
Wannan ne ya sa sai abin da gwamnati ke ra’ayi suke yaɗawa, musamman
a nan jihar Zamfara.
Alal misali
gidan rediyon Zamfara wanda ake faman tallata Gwamna da manufofinsa da waƙoƙinsa
tare da barin na ‘yan adawa. Haka abin yake a gidan Jaridar “The Legacy”
(Legacy, 2011).
Wannan jarida
mallakar jihar Zamfara ce, wanda duk abin da ke faruwa a Zamfara “radiyo” na
siyasa, irin sa ne ke faruwa a gidan jaridar “The Legacy”.
4.5 KAFUWAR
JAM’IYUN SIYASA
Siyasa a
Nijeriya ta kafu ne bisa hanyoyi guda uku (i) Siyasar gargajiya ta (ii) Siyasar
Musulunci ta (iii) Siyasar dimukraɗiyya. Siyasar gargajiya ita ce, ta
sarauta, watau ta gado, wadda yan gidan sarauta ne kawai ke da damar neman muƙami.
Siyasar musulunci kuwa na aiki da Al’ƙur’ani mai
girma da Hadisai na Manzon Tsira Muhammad (SAW).
Rukuni na uku
shi ne siyasar dimokuraɗiyya, wannan ita ce siyasar zamani, wannan
siyasa ta ra’ayi ko ta zamani ta kasu kashi da dama kamar haka; (Jangebe:
2015).
Akan yi ta
don kishin al’umma ko kishin jam’iyyu ko aƙida ko
siyasar ƙasa ko ta ƙabila.
Siyasar dimokuraɗiyya ce ta fi
fice a yau, kuma tana amfani da jam’iyyu. Irin wannan siyasa ta fara kankama a
Nijeriya tun lokacin da ‘yan kishin ƙasa suka
farga da irin zalunci da danniya da Turawa ke gudanarwa a ƙasarsu.
Wannan shi ya fara kawo siyasar gwagwarmayar neman ‘yanci. Mashi (1986) ya ce;
a shekarar (1920) aka kafa kungiyar ƙasashen Afrika
renon Ingila (National Congress of British West Africa (NCBWA).
Daga wannan
lokaci ne al’amurran siyasa suka fara kankama har zuwa lokacin da aka ba da
mulkin kai da zaɓaɓɓun wakilai
bisa jam’iyyu a 1960). Haka aka ta yin gwagwarmayar kafa jam’iyyu da siyasa har
zuwa lokacin Janar Sani Abacha da ya yi yunƙurin mayar da
ƙasar nan kan turbar siyasa, inda ya nemi ‘yan
siyasa da su kafa jam’iyyun siyasa inda gwamnati ta yi wa jam’iyyu guda biyar
rigsta a watan Satumba 1996. Daga cikinsu akwai NCPN da UNCP da DPN da GDM da
kuma NCNC, sai dai kafin a gudanar da zaɓe Allah ya yi wa
Janar Sani Abacha rasuwa 8, ga Yuni, 1998. Wannan ya kawo rushewar jam’iyyun da
shirin mai da mulki hannun farar hula. Bayan wannan janar Abdussalami shi ne ya
gadi Abacha inda shi ma ya yi alƙawarin miƙa
wa farar hula mulki. Abdussalami ya buƙaci a sake
gabatar da kundin tsarin mulki na ƙasa da zai
halattar da miƙa wa farar hula mulki cikin nasara. Kundin
tsarin mulkin na 1998, wanda ya fara aiki a 1999 ya samu karɓuwa a ƙasar
nan. Dagan an aka buƙaci ‘yan Nijeriya da
su ƙirƙiro jam’iyyun
siyasa da suke so. An ƙirƙiro
jam’iyyu da dama waɗanda suka haɗa da
jam’iyyar AD, da APP da PDP inda hukumar zaɓe ta sanar da
yi wa waɗannan
jam’iyyu uku rigista. Inda Jam’iyyar PDP ta kafa Gwamnati a matakin ƙasa
wato “Chief Olesugun Obasanjo” ya lashe zaɓe. A Jihar
Zamfara kuma Jam’iyyar APP ce ta kafa Gwamnati inda Alhaji Ahmad Sani (Yariman
Bakura ya lashe zaɓe. An rantsar da sabuwar Gwamnati a ƙasa
da Jihar Zafmara ranar 29, ga Mayu, 1999.
4.6 LAFAZIN
SIYASA DA MANUFARTA A SIYASANCE
Lafazi ko
magana shi ne wani furuci da ɗan’adam zai furta da bakinsa a bisa
wata manufa. Wanda idan maganar ta fito shi ke nan ba ta komawa, Waɗannan
maganganu manufarsu daban ne a siyasance. Wasu na ɗaukar
maganganun siyasa a matsayin ƙarya ko
yaudara. Saƙonnin siyasa a magance ko a rubuce na ɗaukar
hankalin jama’a, domin siyasa ke tafi da ƙasa. ‘Yan
siyasa suna maganganu a wajen yaƙin neman zaɓe suna kuma
rubutawa a fastoci da laƙawa kan
allunan kamfen. Amma abin dake rubuce ba shi ne ke jagorantar abin ba a siyasa
wani abin ya zama aiki ba cikawa. Kamata ya yi a ce manufasto na siyasa shi ne
ke jagorantar ‘yan siyasa sai za a yi zaɓe sannan ake faɗin za’a yi
ayyuka kaza, amma da zarar an gama zaɓe shi ke nan kaji shiru
kamar an shuka dusa. Irin waɗannan lafuzza ne za a ji ‘yan siyasa
suna faɗa, (Jangebe,
2015).
Maganganu
suna fitowa, uwayenmu da babanninmu, za mu baku takin zamani, mu samar maku da
ruwan sha, da hanyoyi, da ɗakunan shan magani. Idan kuka zaɓe mu za mu
gina maku asibitoci masu gadaje hamsin hamsin. Ina manoma za mu samar maku da
bashin shanun noma, da iraruwan shuka da galmunan shanu da takin zamani, domin
inganta noma a wannan yanki da kuma jiha baki ɗaya.
Waɗannan kaɗan ne daga
cikin lafuzza ko maganganun da ake yi a siyasance, domin samun nasarar jawo
hankalin masu zaɓe da su
jefawa ɗan takara ƙuri’a
domin ya ci zaɓe saboda
gudanar da mulkinsa na dimokuraɗiyya. Daga cikin waɗannan
lafuzzan suna cika wasu, wasu kuma yaudara ce.
4.7 KAMMALAWA
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.