Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazarin Kalmomin
Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (1)
BABI NA DAYA
SHIMFIƊA
1.0 GABATARWA
A
nazarin adabi da al'ada na kowace al'umma akwai muhimman abubuwa da ke bijirowa
masu buƙatar nazari na ƙwaƙƙwaf.Wannan bincike za
a gudanar da shi ne domin bayar da gudummuwa a fagen adabin Hausa musamman abin
da ya shafi waƙa.Kasancewar waƙa na ɗaya daga cikin adabin
al'ummar Hausawa,kuma muhimmiyar aba da ke da tasiri a rayuwarsu.Tasirin yasa
ake amfani da ita don faɗakarwa da nishaɗntarwa da
wa'azantarwa da kuma ilmantar da al'umar Hausawa.Bisa wannan dalili ne aka ga
ya dace a yi nazari a kan Ginin Tsarin Wasu Kalmomin Zamfarci A Wasu Waƙoƙin Kilasik.
Wannan
kundi an kasa shi zuwa babobi biyar.Bibi na daya
za a yi tsoƙaci a kan munufar bincike da dalilin bincike da hasashen
bincike da muhimmancin bincike, da dabarun bincike da farfajiyar bincike da
hujjar cigaba da kuma kammalawa.A babi na biyu za a yi waiwayen ayyukkan da
suka Gabata masu alaƙa ta kusa da ta nesa da wannan aiki.Domin masu hikima na
cewa "Na gaba idon na baya"
A babi na uku za a yi bayani game da tarihin wannan mawaƙi tun daga fara waƙarsa har zuwa
matsayinsa a yau.
A babi
na hudu za a yi tsoƙaci kan yadda mawaƙin ke amfani da
kalmomin Zamfarci a cikin jerin gwanon waƙoƙinsa.A babi na biyar
kuwa za a kammala wannan bincike, tare da kawo shawarawri da ra’ayin mai
bincike da kuma ratayen wasu waƙoƙi da aka yi amfani
das u.
1.1 MANUFAR BINCIKE
Manufata ta gudanar
da wannan bincike ita ce yin tsakure gwargwadon fahimtata a kan bayanan masana
da kuma dalibai 'yan'uwana da suka gudanar da bincike a kan adabi da al’ada da
harshe daban-daban. Za a gudanar da binciken a kan waƙoƙin Kilasik da kuma
karin harshen Zamfarci.Domin ƙara fitowa da fasaha da hikimar da
Allah ya yi wa kilasik don dalibai 'yan'uwana su san muhimmancin da karin
harshen Zamfarci yake da shi,da kuma irin gudumuwar da wannan mawaƙi ke bayarwa wajen
bunƙasa
karin harshen Zamfarci.
1.2 DALILIN BINCIKE
Kamar yadda Hausawa
ke cewa, "Ruwa ba ya tsami banza " wato,komai da ake yi akwai
dalilin yin sa,.ba haka kawai ake yin abu gaba-gaɗi ba, musamman a fagen ilimi.Wannan
bincike za a gudanar da shi ne domin zaƙulo wasu kalmomin
Zamfarci da irin tsarin da waɗannan kalmomin suke da shi a cikin waƙoƙin klasik, domin
amfanin masu bincike da 'yan'uwana musamman daliban ilimi da za su biyo baya a
wannan fanni.
1.3 HASASHEN BINCIKE
Wannan bincike za a
aiwatar da shi ta yin hasashen gano kalmomin Zamfarci a cikin wasu waƙoƙin Kabiru kilasik. Da
irin hikimomin wannan mawaƙi,da irin yadda yake amfani da azanci
yayin sassaƙa waɗannan kalmomin a cikin waƙarsa.Haka kuma,wannan
bincike zai yi tasiri wajen sanin
matsayin karin harshen Zamfarci da yadda ake amfani da shi don binciken harshen
Hausa da gudumuwar da yake ba adabi musamman a fagen rubutattun waƙoƙin siyasa.
1.4 MUHIMMANCIN BINCIKE
Ana iya cewa dukkan
wani abu da mutum zai gudanar, ko ya aiwatar da shi,to ba zai yi shi ba sai ya
tabbatar cewa yana da amfani gare shi da sauran jama'a musamman idan ya shafi
fagen ilimi.
Saboda haka, wannan
bincike yana da muhimmanci ƙwarai da gaske ba ma ga fagen ilimi,
ko ga mai nazari kawai ba, har ma ga masu sha'awar waƙoƙin siyasa. Bugu-da-ƙari, binciken zai haɓɓaka wannan fannin na
adabin Hausa ta hanyar fito da hikimomi da fasahar wannan mawaƙi, a fili domin masu
saurare da sha’awar waƙoƙinsa su amfana da abubuwan da yake faɗa cikin waƙoƙinsa.
Haka kuma,wannan
bincike zai tattara waɗannan kalmomi ta
yadda masu nazari za su sami ɗan abin dubawa a wannan bagire.
1.5 DABARUN BINCIKE
Na yi ƙoƙarin amfani da
mahimman dabaru ko hanyoyi na musamman,
wajen gudanar da wannan bincike. Waɗannan hanyoyi sun haɗa da binciken
littafai da kundayen neman digiri
daban-daban da aka wallafa a wannan
fanni. Da kuma duba mujallu da takardun ƙarawa juna sani da
aka gabatar a makarantu da jami'o'i daban-daban da masana suka yi a wannan
fanni. Na yi amfani da Mp3 na waƙoƙin Kabiru kilasik.
Haka kuma, na ba
tattaunawa da masana daban-daban da masu ruwa da tsaki a wannan fage na ilimi
muhimmanci ƙwarai domin samun ƙarin haske ta yadda
wannan aikin zai samu nasarar kammalawa. Domin masu hikima sun ce “Ruwa na ƙasa sai ga wanda bai
tona ba" .Na
kuma yi ƙoƙari na ganin cewa na gana da wannan mawaƙi don samun cikakken
sahihin ko ingantaccen bayani mai cike da ƙamshin gasikya daga
gare shi.Domin Hausawa na cewa "Waƙa a
bakin mai ita
ta fi daɗi" . Bugu-da-ƙari, na ziyarci ɗakunan karatu na
Jami’o’i domin samun wasu bayanai masu alaƙa da wannan aiki
nawa.Waɗannan su ne hanyoyi
ko dabarun da na bi don gudanar da wannan bincike.
1.6 MATSALOLIN BINCIKE
Gaskiyar Hausawa da
ke cewa, “kowa ya ci zomo ya ci gudu,” `tabas
haka ne,domin kuwa na cikaro da matsaloli da dama a wajen gudanar da wannan
bincike. Wanda suka shafi ƙarancin kayan aiki isassu, kasancewar
ban samu wani magabaci da ya keɓanci wannan bagire na Nazarin kalmomin Zamfarci A Wasu Wakokin Kabiru
Kilasik ba. Amma bayan faɗi-tashin da na yi ta
yi na ziyartar ɗakunan adana littafai
da kundayen digiri na cikin makarantu da dama, da hirar da na yi da Mawaƙin da wasu mutane
daban-daban ya taimaka sosai wajen warware waɗannan matsaloli.
1.7 HUJJAR CIGABA DA BINCIKE
Hujja, ko dalilin da
ya bani damar cigaba da wannan bincike nawa shi ne, dukkan ayyukkan da suka zo
hannuna ban ci karo da aiki ɗaya ba irin nawa.Duk da cewa masana da dama da kuma
daliban ilimi sun yi aikace-aikace masu ɗimbin yawa dangane da wannan mawaƙi,amma babu guda ɗaya tilo mai taken
aikina. Sai dai kama,masu hikima sun ce,"Kama da wane ba ta wane " Wannan dalili shi ya bani sha'awa da
ƙarfin
guiwar cigaba da wannan bincike.
1.8 FARFAJIYAR BINCIKE.
Wannan bincike zai taƙai ta ne kacokan kan
waƙoƙin Kabiru Kilasik.
Binciken zai ta’allaƙa ne a kan Nazarin kalmomin Zamfarci da suka ta'allaƙa a waɗannan wakoki kamar ha
Waƙar Saratun Mamuda mai
taken "In An Ba Albasa Ruwa Karo Na Biyu" (2011)
Waƙar Bilya Shinkafi mai
taken "Taka Lafiya Ɗan Sadauki"
Waƙar Usman Ɗankalili mai taken
"Dodo Magajin Dodo" (2015)
Waƙar A.N.P.P Baku Da
Niya mai taken "Ciki Da Gaskiya Wuƙa Bata Huda Shi
(2016)
Babu shakka wannan
bincike an keɓance shi ne a kan Tsarin Ginin kalmomin Zamfarci A Wasu
Wakokin Kilasik.
1.9 KAMMALAWA
Sanin Muhimmancin
bincike da dabarun bincike da kuma,Hujjar cigaba da bincike tare da fahimtar
dalili da hasashen wannan bincike, abu ne mai matuƙar muhimmancin
gaske.Da wannan farfajiyar bincike na naɗe wannan babi,da kuma Kammalawa r kanta.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.