Ticker

Nazarin Kalmomin Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (4)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Nazarin Kalmomin Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (4)

wakoki

BABI NA HUƊU

AMFANI DA KALMOMIN ZAMFARCI A WAƘOƘIN  KABIRU KILASIK

4.0 GABATARWA

            Wannan babi shi ne ƙashin bayan wannan bincike.A wannan babi za a yi bayanin ma’anar kalmomin Zamfarci da Kabiru Kilasik ya yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa.Haka kuma za a yi cikkaken bayani a kan waɗannan kalmomi.Wanda a kan sa ne aka aiwatar da wannan bincike.Da ƙarshe za a rufe da kammalawa.

4.1 Ma’anar kalmmomi

Kalma dai ita ce haɗuwar baƙi da wasali su samar da magana, lafazi ko zance mai ma’ana, ta kanta, wadda za a iya fahimta ta hanyar rubutu ko ambatonta.Sai dai akwai ra’ayoyi mabambanta da masana harshe suke bayyana ma’anar kalma da yadda kowane daga cikinsu yake kallon ta.

Crystal (2008:521-523)  ya  ce, “kalma ginshiƙi ne na bayani a cikin harshe da ake sadarwa ta hanyar furtawa ko rubutawa”. Ya ƙara da cewa curin zance ne wanda take zuwa a cikin daidaitaccen tsari.

            Jinju (1981-42-44), cewa ya yi, “kalma ƙwayar sauti ce, ko haɗuwar saututtuka waɗanda ake amfani da su ta hanyar sadarwa”,

            Kalmomi lafuzza ne masu ma’ana guda-guda.Kuma su ne zango na farko a cikin tubalai ko kayan ginin jimla.

Bisa la’akari da ra’ayoyin masana dangane da ma’anar kalmomi, za mu iya cewa, kalmomi jam’i ne na kalma, wanda ake samu ta hanyar haɗuwar baƙi da wasali su samar da kalma, idan aka haɗa kalma da kalma sai a samar da kalmomi masu ma;ana takansu.

Ga tsarin kalmomin daidaitacciyar Hausa nan tare da takwarorinsu a cikin karin harsdhen Zamfarci kamar haka.

 

Daidaitacciyar Hausa                     Zamfarci

Bacci                                                   Kwana

Kookoo                                              Kunu

Kwarkwata                                        Ƙyaayaa

Kyanwa                                             Mussa

Tsumma                                            Ragga

Kalanzir                                             Barahuni

Gyaɗa                                     Gujjiya

Sunkuyawa                                       Durƙusawa/ gurfanawa

Fartanya                                             Kwasa/ kwasahe

Awara                                                Gala

Ƙofa                                                    Gambu/ƙyaure

Ashar                                                  Ɓaci

Bazawara                                           Zaura

Ɓeera                                                  Kusu

Faɗi                                                     Gayi

Farce                                                   Akaifa

Fusata                                    Hushi

Gafiya                                    Burgu

Hanta                                                 Anta

Jure                                                     Daure

Jeji                                                       Daji

Kaciya                                                Kuidu

Kuɓewa                                             Yauɗi

Magana                                              Batu

Mahauci                                             Barunje

Minshari                                            Hansari

Musaya                                              Canza

Rahusa                                               Ragoowa

Waina                                     Masa

Yashi                                                  Rairai

Alfarma                                              Lmuni

4.2. Ma’anar Kalma

            Abdulhamid (2001) ya bayyana ginin kalma da cewa, “Ginin kalma ya shafi tsira, ƙirƙira da kuma kumburar kalma. Ya ce, ginin kalma ya rabu biyu: na ɗaya ya ƙunshi ƙirƙira tsirar  kalma daga aikatau  zuwa suna ko akasin haka. Na biyu ya shafi harɗantarwa (compouding). Wato haɗa wata kalma da wata”

            Mamman (2006) ya dubi ginin kalma in da yake cewa, “Nazari ne wanda ya shafi ginuwa ta kalma wato yadda kalma ke “kumbura” ta ba da ma’ana wato ta kumbura daga tilo zuwa jam’i ko kuma ta kumbura daga na jinsin Namiji zuwa mace. Haka kuma nazarin gini kalma nazari ne wanda ya shafi ‘tsira’  wato yadda kalma ke tsira daga Aikatau zuwa suna ko daga suna zuwa sifa”

            Alhasan (2005) ya faɗa cewa, “Idan aka ce ginin kalma ana nufin gini ne na kalmomi, saboda ana rusa  kalmomi domin a ƙwanƙwance da kuma daidaice su”.

            Idan muka yi la’akari da bayanai da suka gabata, za mu iya cewa, kalama na nufin haɗuwar baƙi da wasali su samar da ma’ana.Kuma ana fahimtar kalma ta hanyar barin fili tsakaninta da wata.

 

4.3 Ma’anar  Kalmomin zamfarci

Kalmomi                   Ma’ana          

Shingii                        Kalmar shingi na nufin darni da ake ɗan killace wani abin amfani.

Zawara                       Kalmar zawara tana nufin matar da ta taɓa aure amma sun rabu da mijinta, kuma ba tayi wani aure ba.Wato Bazawara.

Wari/ɗoi                   Kalmar wari a Zamfarci tana nufin ɗoyi, wato abin da bai da daɗin shaƙa a hanci ko mai warin da ke cutarwa.

Gaya/hwaɗi              Wannan kalma gaya/ hwaɗi a karin harshen Zamfarci kalma ce da ke nufin faɗi, wato isar da wani saƙo ga wani mutun ko wasu mutane.

Yatsa              Kalmar Yatsa a Zamfarci tana daukar ma’anar farce, wato tilon farce guda ɗaya, a cikin farutta biryar da mutun yake das u a kowane hannu ko ƙafa.

Hauya            Kalmar hauya a karin harshen Zamfarci tana nufin fartanya, wata aba da ake noma da ita, wadda ta keda ruwan fartanya na ƙarfe da kuma ɓota ta itace.

Dawo              Dawa a karin harshen Zamfarce yana nufin fura wadda ba a dama ba.

Burgu             Burgu wannan kalma suna ne na dabba, wato Kalmar tana nufin gafiya, wata dabba ce mai kama da mage kuma mai yawan barna ko satar abinci ko kayan abincin.Ana samun ta a gari ko a jeji.

Zufa                Zufa kalam ce ta Zamfarci mai nufin gumi, wato ruwa ne da ke fitowa a jikin mutun a lokacin da ya yi wani aiki na motsa jiki ko wahala, ko sanadiyar zafin rana,

Gujjiya           Kalmar gujiya suna ne na wani nau’in abinci, wanda Hausawa ke nomawa. Ita gujjiya tana yin ɗiya ne a ƙasa, wato tana cikin “maɓanɓara ƙasa,” a daidaitacciyar Hausa ana kiran ta gyaɗa.

Buda               Buda  wannan Kalmar tana nufin hazau, ko yanayin hunturu wanda ke canja yanayin gari, kuma ana amfani da Kalmar a wajen sawa wanda aka Haifa a wannan lokaci suna da ita.

Jalli                 Jalli kalma ce ta Zamfarci mai nufin jari.Wato kuɗi ko wasu kaya ko wani abu da mutun ya mallaka don yin sana’a ko kasuwanci.

Daure             Daure wannan kalma tana da ma’ana biyu a Zamfaci, ta ɗaya, Kalmar na nufin aiki jure, ta biyu kuwa, Kalmar mutuwa. A da idan mutun ya mutu ana cewa ashe wane bai Daure ba. Amma tsowuwar kalma ce da ake amfani da ita.

Daji                 Daji kalamr Zamfarci ce, mai nufin jeji, wato wajen gari.

Ɗankwali       Wannan Kalmar Zamfarci ce, mai nufin kallabi.Wato wata sutura ce ta mata da suke ɗaurawa a kai domin rufe gashin kansu ko kwalliya.

Yauɗi              Wannan Kalmar suna ne,na ɗaya daga cikin ire-iren miyar Zamfarawa, wato Kalmar na nufin kubewa. Wata abu ce wadda ake miya da ita, akwai ɗanya akwai busasshiya.

Guru/kuruu/makur           u          Wannan Kalmar tana nufin ƙuli-ƙuli, wani nau’in abin +amfani ne da ya shafi dangin abinci da Zamfarwa ke amfani da shi.Ana yin shi da gyaɗa.

Mussa            Mussa wannan Kalmar tana nufin mage, kuliyanwa, wata dabbace da ake ajewa a gida, domin kiwo, kuma ba don a ci ba, ko a sayar. Yawanci mutune na kiwon ta don samun lada ko don maganin ɓeraye da ke masu ɓarna a gida.

Batu                Batu a karin harshen Zamfarci, wannan kalma tana nufi magana/, zance, ko lafazi.Wato kalma ce aikatau, wadda jam’in ta shi ne batutuwa.

Barunje          Kalmar Barunje  a karin harshen Zamfarci, kalma ce da ke nufinMahauci, wato mutun da ke harkar sai da nama ko fawa.

Hurhure ko canza    Kalma ce da ke nufin musaya. Wato mutun ya ba da wani abu a ba shi wani.

Tagguwa       Tagguwa kalama ce da ke nufin riga, wata nau\in sutura da ake amfani da ita domin rufe tsaraici.

Shigihwa        Wannan kalma tana nufin soro ko daki. Wata mafaka ko mazauna ce da Hausawa ke ginawa domin zama da iyali.

Lanƙwasa      Kalma ce, aikatau mai nufin tanƙwara.Wato tanƙwara wani abu kamar ƙarfe ko itace.

Haƙo               Haƙo kalma ce da ke nufin tarko, wato dabara ce, da ake yi domin kama wani abu ko wata dabba,Kamar gafiya ko kifi, da sauransu.

Gatana            Kalmar gatana, kalma ce da ke nufin tatsuniya.Amma a karin harshen Zamfarci ana amfani da gatana.Wadda ke nufin tsohuwar hanya ko makaranta ta farko da Bahaushe ya fara amfani da ita wajen tarbiyantar da ‘ya’yansa. Mafi akasari iyaye mata da kakanni ko tsofi su suka fi yin ta.

Masa               Wannan kalma tana nufin waina, wani nau’in abinci ne, da ake yi da ake yi da masara ko shinkafa, kuma ana soya ta a tanda.

Bindi              Kalmar Zamfarci ce, mai nufin wutsiya. Kamar wutsiyar sa, ko rago/

Marece           Kalmar Zamfarci ce, mai nufin yamma, wato lokacin yamma.

Rairai             Wannan kalma tana nufin yashi, wani nau’in ƙasa mai huroza da ake ginin zamani ko siminti das hi.

Ɗiya                Kalma ce, ta Zamfarci mai nufin ‘ya’ya.

4.4 Amfani da kalmomin Zamfarci a Wakokin Kabiru Kilasik

WAƘAR USMAN ƊANKALILI MAI  SUNA” ‘DODO MAGAJIN DODO’

 Turke:           Bakura Maradun mun aminta da Ɗankalili ya gadi dodo,

                        Shi kuma Gwamna mu zaɓi dodo, fi di fi Allah sa mu dace,

                        Mu kauda waɗanda ka yaudararmu.

Jagora:            Zamfara ga fa kabiru naku kilasik mai kwanci na sayi,

Karɓi: Ɗan App zai ji waƙar ga tamkar tutu ƙwarai da ɗoyi,

Jagora:            Zamfara yau mun ussuhe Jalla an maishe mu kamar marayu,

Karɓi: Yau daɗa ba mu da mai kataɓus abinci na son gagararmu.

A wnnan baiti Kabiru Kilasik, ya yi amfani da  kalmomin Zamfarci. Inda ya yi amfani da kalmar “tutu”  ta karin harshen Zamfarci, wadda a daidaitacciyar Hausa tana nufin Bahaya. Ya yi amfani da ita a nan a matsayin kamance, inda ya kamanta wannan waƙa  da yake da  tutu a wajen ‘yan Jamiyyar ANPP ,domin waƙar ta ɗan takarar PDP ce.Ya kuma yi amfani da Kalmar ‘ussuhe’  wadda ke nufin bane ko tashin hankali a daidaitacciyar Hausa.Ita ma ya yi amfani da ita domin kwatanci, inda yake ƙoƙarin bayyana halin da al’ummar Zamfara suke ciki. Haka kuma a ɗango na uku ya yi amfani da Kalmar ‘maishe’ Maimakon’ maida’ a daidaitaciyar Hausa.Ya yi amfani da ita domin ya nuna yadda gwamnati ta azabtar da al’ummar Zamfara.Har wa yu ya  ƙara da cewa:-

Jagora:            Mata yara suna kuka ga yinwa ga yalwar ɓarayi,

Karɓi: Zamfara mun shiga ukku Allah mutane sun koma kubeyi,

Jagora:            Dagga a soke sai a halbe, kisan kai Zamfara ba a shayi,

Karɓi: Ba mu barin ta garin iyayenmu komi za a yi mun ji ga mu.

A ɗangon wannan baiti na biyu Kilasik ya yi  da kalmar Zamfarci inda ya yi amfani  da Kalmar ‘ukku’  a matsayin bala’I, ko ƙaƙa-ni-ka-yi, ya yi amfani da wannan kalma a nan domin bayyana irin mummunan halin da al’ummar Zamfarawa suke ta ta shiga.  A ɗango na uku kuwa, ya yi amfani  da karin harshe dagga’  maimakon  ‘daga’. Mai nuna cigaba da bayani.

Jagora:            Fi di fi babban gari ce, da ta yi yalwa da ɗarin iyaye,

Karɓi: Wanga ya ƙoshi da kifi wanga da nama wanga da maye-maye,

Jagora:            Sannu uwa mai ba da nono fi di fi sharan hawaye,

Kraɓi: Fi di fi ɗaki na alatu za mu shiga mu ci duniyarmu.

 

A wannan baiti mawaƙin ya yi amafni da kalmomin Zamfarci har sau uku, inda ya yi amfani da Kalmar ‘wanga’  wadda ke nufin ‘wannan’   a daidaitaccyar Hausa.Wadda ke nuni da abu ɗaya tilo, wanda ke kusa da mai magana.Amma ya yi amfani da ita domin nuna rin daɗin da al’umma ke sha a lokacin mulkin fi di fi.

 

Jagora:            Waƙar Usman ɗankalili da shauƙi Kabiru za ni yin ta,

Karɓi: Sannan in ɓarje gumina in yo wada ma su biɗa ka son ta,

Jagora:            Kilasik na iya takusheren ɗumi don waƙa zan karanta,

Karɓi: In yi kashashshaɓa in yi zari ga ƙwaro mai cin shukunanmu.

 

A wannan baiti Kilasik ya yi da kalmomin Zamfarci a wurare da dama.Aɗango na biyu ya yi amfani da Kalmar wada’  maimakon’ yadda’  a daidaitaciyar Hausa. A gaba kuma ya yi amfani da kalmar biɗa’  ta karin harshen Zamfarci a matsayin ‘nema’ a nan ya yi amfani da kalmar domin nuna yadda zai yi waƙarsa, a daidaitacciyar Hausa.Haka zalika a ɗango na uku ya yi amfani da takushere’   ya yi amfani da Kalmar domin ya ba kansa, ko kurara kansa, cewa ya iya ƙiƙirar magana ko waƙa.da kuma ‘ɗumi’  mai nufin ‘magana’ ko ‘surutu’ a daidaitacciyar Hausa.

Jagora:            Kowab bak kaza da gashi kwaɗai sai ya taɓi lahiyatai,

Karɓi: Sai ka riƙa ta mu hige Kabiru kowaƙ ƙwantan sai na ƙwantai,

Jagora:            Ku Mafara kun sare iccenku amma sai ku ka bar hawattai,

Jagora:            Ya yi tsiri ya girmu sayen da Allah yay yi da shi ya girmu.

Mawaƙin ya yi amfani da kalmomin  Zamfarci a wannan baiti, kamar inda yace, ‘kowab bak kaza’  maimakon ‘kowa ya bar kaza’  a nan ya yi amfani da waɗanna kalmomi domin yin hannuka mai sanda ga wanda yake yi wa waƙar, cewa duk wanda ya yi masa ya rama.Haka kuma, ya yi amfani da Kalmar  ya yi amfani da wannan kalma ne, domin yin zambo ga ‘yan siyasar garin  Mafara. Bugu da ƙari ya yi amfani da Kalmar Zamfarci  a ɗango na uku inda ya yi amfani da ‘lahiyata’  mai nufin  ‘lafiyarsa. Ya yi amfani da Kalmar domin ƙara tunatar da wanda yake yi wa waƙar cewa idan ya ƙyale abokin adawa to zai cutar da shi.

Jagora:            Kusu ko baƙo yag gane shi za ya kira shi ƙane ga burgu,

Karɓi: Lallai ganga ko ƙabila ya ganta tana da kamar kalangu,

Jagora:            Misallai dai na nan zuwa ‘yan’uwa ku biyo ni fa kar ku damu,

Karɓi: Da ka ga Kilasik kag ga mai Maradun ka san da akwai alamu,

A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da kalmomin Zamfarci inda ya ya  amfani da‘kusu’  a matsayin ‘ɓera’  wanda ya kawo shi ne a matsayin kamancen kasawa..Da kuma Kalmar ‘burgu’  mai ma’anar ‘gafiya’  ya yi amani da Kalmar domin nuna fifiko.Haka zalika ya yi amfani da Kalmar ‘misallai’ a matsayin ‘misalai’ a daidaitacciyar Hausa.Inda yak e lurar da mai sauraren waƙar cewa kar ya ƙagara zai zo da kyawawan misalai da za su sa ya fahimci waƙa.

 

Jagora:            Karen bana ya kashe wanga zomo, ashe bana gawa ta yi yalwa,

Karɓi: Dashen Allah, Allah ka ishe shi babu ruwan shi da mai kulawa,

Jagora:            Muna nan fi di fin amana Kilasik babu batun tsayawa,

Karɓi: Mu ƙara nitso a wajen ibada Ta’ala Jalla ka agazarmu.

 

A nan Kabiru Kilasik ya yi amfanin da  kalmomin Zamfarci, inda ya yi amfani da Kalmar ‘wanga’ mai nufin ‘wannan’ mai nuna mutun ɗaya tilo na kusa da mai magana. Kuma a nan ya yi amfani da kalmar ne domin yin zambo ga wani abokin hammaya, cewa ya sha ƙasa. Da kuma kalmar ‘ishe”  mai ma’anar ‘idar’ ko ‘ida’  wato kammala aiki, a daidaitacciyar Hausa. A nan kuma yana gugar-zana ne, ta nuna cewa wanda yake yi wa waƙa Allah ne ke tare da shi ko ba kowa idan Allah ya nufa sai ya yi.

WAƘAR  CIKI DA G ASKIYA

Turke: Anpp ba ni da kuwa, kuma kun  san ba ku da ‘niya,’

                        Kar muka kallon juna Kabiru nai maku kallon mai bisa ruwa,

A wannan baiti Kilasik ya yi amfani da  kalmomin Zamfarci, inda ya yi amfani da Kalmar ‘niya’  a matsayin ‘ni’ mai nufin mutum mai magana tilo.  Ya yi amfani da Kalmar a nan domin yin gugar-zana ga abokan adawarsa, cewa yadda bai da kowa cikin  su shi ma sun yi asarar waƙi.Da kuma kalamr ‘nai’  a maimakon ‘na yi’ a daidaitacciyar Hausa.Ya yi ta ne domin nuna yadda ya ɗauke su.

Karɓi: Mai ƙaunarka uban Faɗimatu Annabi ba shi ba gunaguni,

                        Annabi Manzo sahibul karama bayan kai ba ni da wani,

                        Ko tayi ki ƙaunarka ‘baɗininai ‘ ya zarta wa bajini,

                        Ɗaha maceci na ƙaunarka Annabi ‘niɗ ɗoka’  ina ƙawa.

A nan Kabiru Kilasik ya yi amfani da ginin kalmomin  Zamfarci, karma inda ya yi amfani da ‘baɗininai’  a maimakon ‘baɗininsa’  ya yi amfani da Kalmar ne domin bayyana abin da ke cikin zuciya. Da kuma ɗango na huɗu inda yayi amfani da ‘niɗ ɗoka’  mai nufin ‘na ɗauka’ a daidaitacciyar Hausa. Ya yi amfani da Kalmar domin nuna aikin da yake, wato ƙaunar Annabi(S.A.W.).

Jagora:            In ke ƙare Gusau je ki gaida Shinkahwawa kun hi kakkarai

Karɓi: Kowa ba ni da Shinkafi sai amarya matar Saminu Zulai,

Jagora:            Zan nuna maki matan ƙwarai na kirki na san su duka sarai,

Karɓi: In Allah ya kai ni Shinkafi zan zaunawa ba ni damuwa.

A ɗangon farko na wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da  kalamr Zamfarci  inda yayi amfani da ‘hi’  a maimakon ‘fi’,  ya yi amfani da ita domin nuna fifikon mutane garin Shinkafi da wasu dab a su ba. A ɗango na huɗu kuwa ya yi amfani da Kalmar ‘sarai’  ta karin harshen Zamfarci mai nufin ‘gaba ɗaya’ ko ‘duka’. Wato, amsa-kama, ya yi amfani da ita a nan a matsayin jam’i, duka ko gaba ɗaya.

Jagora:            Ga ni da sabon launi Kabiru yankan ƙauna za ni yi ciki,

Karɓi: Mai algaita shi yaɗ ɗaram ma kowa cin ribar muƙamuƙi,

Jagora:            Bayan tsoron Allah Kabiru da na daure na ci alhaki,

Karɓi: Koda ba kowa cikin garinmu ko ni ɗai sai na ci kassuwa.

Mawaƙin ya yi amfanin da kalmomin Zamafrci a wannan baiti, a ɗango na biyu ya yi  amfani da kalmomin  ‘yaɗ ɗaram ma’ a matsayin ‘ya ɗara ma’  a daidaitacciyar Hausa. Ya yi amfani da waɗannan kalmomi domin nuna fifiko ta hanyar  awo. da kuma Kalmar ‘kassuwa’  mai nufin ‘kasuwa’ a daidaitacciyar Hausa.Ya yi amfani da ita a nan domin nuna ƙarfin hali da juriya, domin ya nuna ko ba kowa a Jam’iyyarsu shi sai ya tsaya ciki.

Jagora:            Daddaɗar  magana ta mayar da zaki ɗan taure na bunsuru,

Karbi:             Ni sai na ɗinko babalange ran sallah na samu kurkunu,

Jagora:            Zamfara kun ji ina nan ashe da saurana kuma ba ni yin shiru,

Karɓi: Zamfara kowa ban daƙile ba al’umma barka da shan ruwa.

A wannan baiti a ɗango na huɗu Kabiru Kilasik ya yi amfani ginin tsarin Kalmar Zamfarci  daƙile’  mai nufin ‘bari’ ko ‘mantawa’ a daidaitacciyar Hausa.Ya yi amfani da ita a nan domin nuna cewa kowa na shi ne a Zamfara.

Jagora:            Ni mamuda Aliyu ba ni mance gwarzo na karhen hwashin tama,

Karɓi: Mai komi dozin mai gida ga Saratu taken dauri zan yi ma,

Jagora:            Don  ko yau kai ne mijin Mariya shirya zo kai shirin zama,

Karɓi: Angon Aisha mai dogaro ga Allah ka hurce  su natsuwa.

A nan ma mawaƙin ya yi  amfani da kalmomin Zamfarci inda ya yi amfani da ‘ƙarhe’ a matsayin ‘ƙarfe’, ya yi amfani da Kalmar domin yaba ko wasa ko kururuta ko  wasa mai gidansa, Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi, inda ya yi amfani da salon abuntarwa.Da kuma hwashi’  a matsayin ‘fashi’ Ya kawo Kalmar domin  nuna jarunta ko irin ƙoƙarin da maigidansa ke yi.Da kuma Kalmar ‘hurce’  mai nufin ‘zarta’ ko fi’  a daidaitacciyar Hausa.

Jagora:            Kabiru kilasik na gode Rabbana don baiwa yai mani ita,

Karɓi: In da gwamnati ke rabon fasaha da na san ba ka da ita,

Jagora:            Sai yaz zan ba magi ba ce da zinari dolin mijin wata,

Karɓi: Ai ko mina ne kag gani gidan sarki da irin shi kasuwa.

A wannan baiti a ɗango na ƙarshe mawaƙin ya yi amfani da ginin tsarin kalmomin Zamfarci, inda ya yi amfani da minane’  ‘kag gani’  Ya yi amfani da waɗannan kalmomi domin nuna cewa duk abin da ke ga wannan gwamnati to su ma suna da shi, domin sun riƙa kafin su na yanzu su zo.Kuma wannan habaici ne ya yi ga gwamnati mai ci.. Sai mawaƙin ya yi amfani da karin harshen Zamfarci.

Jagora:            Komai sai da sila kar a bar dalili tushe na kudandani,

Karɓi: Kwargon masu bara ya cike da tsaba albarkar rashin gani,

Jagora:            Mai nema ka ɗan gajeren bayani na hana kai hana wani,

Jagora:            Kowac  ce a yi hurhure na shi yar raina shi zai yi ƙwaruwa.

A wannan baitin waƙa mawaƙin ya yi amfani da fasahar saƙa kalmomin Zamfarci maimakon yayi amfani da daidaitacciyar Hausa, a ɗango na huɗu ya yi amfani da Kalmar  ‘hurhure’  mai nufin ‘musaya’  kuma ya kawo ta ne domin yin  habaici ga waɗan da suka kira shi cewa ya bisu, inda yake nuna cewa sun raina nasu mawaƙan.Da  kuma ‘kowac ce’  a maimakon ‘kowa ya ce’. Ya yi amfani da wannan kalma domin ya kammabama maganar da ya yi.

Jagora:            Alamonin tashin ƙiyama a ɗauke ilimi ba a ƙaruwa,

Karɓi: Ba neman ilimi kodayaushe jahilci ɗai za shi yaɗuwa,

Jagora:            Malamman kuma sun ka zabi duniya don ƙuna ba su damuwa,

Karɓi: Hayinka  da kuɗɗi na raina ƙasarin kalwa dan ba y a shawuwa.

A nan mawaƙin ya yi amfani da Kalmar ‘mallamai’  a maimakon ‘malamai’,  Kuma ya yi amfani da ita a nan domin nuna halin da malamai suka tsintsin kansu a cikin, na rashin bin dokokin Allah da zaɓen duniya, Da kuma kalamr  ‘hayinka’  mai nufin ‘kashedi’  Ya yi amfani da ita domin nuna yadda kuɗi ke sauya wa mutun ra’ayi ko kais hi ga halaka.Da kuma Kalmar ‘kuɗɗi’  wadda ke nufin ‘kuɗi’ a daidaitacciyar Hausa, amma sai ya saƙa ta da tsarin kalmomin  Zamfarci.

Jagora:            Ɓarawo in ya gahurta za ya sata ai ba ya kashae wuta,

Karɓi: Don tsananin iko ya ma kunna Tɓ da ma ga shi ga ita,

Jagora:            Na bayar  da buhun goro dan karama na bi rabin tiyar ata,

Karɓi: Gwamma gidan kowa da dauɗa gidana in dai ga ni da ruwa.

A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da kalmomin Zamafarci, inda ya yi amfani da Kalmar ‘gahurta’   ya yi amfani da Kalmar domin nuna yadda wani ke yin sata ba  tare da jin kunyar idanun jama’a ba. Da kuma Kalmar ‘gwamma’  ƙara’ Ya yi amfani da Kalmar domin nuna son kai.

 

WAƘAR BILYA SHINKAFI

Turke: Zauna lafiya ɗan Sadauki tashi da layiya,Bilya,

                        Bilya Shiunkafi duniyar nan bata rago bace,

                        Yanzu Abuja mun yi wakili mai raba gardama Bilya.

Jagora;            Bara na gaya ma Bilya irin halayen duniya,

                        Kodan ya sani in tuna ma kunne ya jiya,

                        Ita kullun tazbaha ta nai mata kallon tsakiya.

                        Na runtse idanuna ban dubin kudun kariya.

A wannan baiti a ɗango na biyu ya yi amfani da karin harshen Zamfarci, inda ya yi amfani da ‘jiya’   mai nufi ‘ji’, ya yi amfani da Kalmar a matsayin jin magana a kunne. Wato ya tuna wa wanda yake yi wa waƙar halin duniya kodayake ya sani. Ya  kuma yi amfani da ‘nai’    ya yi amfani da ita a matsayin Kalmar ‘na yi’.wato aikin da  ke nuna aikin da ake yi.

Jagora:            Bilya Shinkafi ɗan siyasa mai raba gardama,

                        Komi girman mutum ya bi ka ya tsira da lalama,

                        Mai ƙyamar ka Bilya gidansa tuwansa ɗatun rama,

                        Mai  daraja mijin daga na dace sanin Bilya.

A wannan baiti a ɗango uku ya yi amfani da kalmar Zamfarci, ɗatu’   mai ma’anar ‘kwado’ a daidaitacciyar Hausa. Wadda ke nufin haɗa abinci iri biyu, domin a ci kamar haɗa kuli da ƙanzo ko makamantansu.Amma a nan mawaƙin ya yi amfani da ita domin gugar-zana  ga maƙiyan Bilya, inda ya nuna cewa tuwan gidansu bai wuce ɗatun rama ba.

Jagora:            Duk mai Bilya gidansa ya fi gaban ya ci karkare,

                        Ga wani ya ja da kai tuwon kwanonai ya ɓare,

                        Ya faɗa cikin shara to, daɗa bashi da ko ƙire,

                        Wagga hasara ta yi yawa daɗa baka da ko miya Bilya

A nan mawaƙin ya yi amfani da kalmomin Zamfarci inda ya yi amfani da Kalmar, ‘wagga’  a matsayin ‘wannan’  Wadda ke nuna kusancin mai magana da abu. Ya yi amfani da ita domin  bayyana irin asara da  abokin hamayyar Bilya ya yi.Da Kalmar ‘hasara’  a matsayin ‘asara’ a daidaitacciyar Hausa. Ya yiamfani da ita a nan domin nuna faɗuwa.

Jagora:            Aminu waziri membanka ya zama gulbin tsakkiya,

                        Kowa ya sha sai ya ɗiba kyauta ba biya,

                        Bilya ya kai muzakkari mai ɓad da bataliya,

                        Bilya kad da ka kasa daure na san ka iya Bilya.

A nan ma Kilasik ya yi amfanin da kalmomin Zamfarci, kamar inda ya yi amfani da kalmar ɓad’  a maimakon ‘ɓatar’  ya yi amfani da ita a wannan ɗango domin nuna jarunta ta wannan mutun. Ya  kuma yi amfani da kalmar ‘tsakkiya’  a maiamkon ‘tsakiya’ amma a nan ya yi amfani da Kalmar a matsayin mahaɗa. Har way au ya yi amfani da kalmar ‘kad’ a matsayin ‘kada’  Ya yi amfani da ita a matsayin  shawara, duk da Kalmar tana nuni da korewa ko hani. Waɗannan duk kalmomin Zamfarci ne.

Jagora:            Bilya Shinkafi martabobi Allah ya yi maka,

                        Ga adalci da taimako ga ɗinbin ɗaukaka

                        Ƙurjin zucciyar wane yau daɗa sai ya harzuƙa,

                        Na san yanda kak kwana yau haka nan kak kwan jiya.

Kilasik ya ya yi amfani da hikimar saƙa kalmomin Zamfarci a wannan baiti, kamar inda ya yi amfani da ‘zucciya’  maimakon ‘zuciya’  mai nufin wata tsoka a cikin jikin mutun. Haka zalika ya yi amfani da ‘’kak kwana’ a matsayin ‘ka kwana’ , a nan ya yi amfani da Kalmar a matsayin kalma mai nuna halin da mutun yake ciki.Duk da cewa tana nufin bacci.

Jagora:            Shinkafi Jalla kar ya haɗa ka da tuntuɓe,

                        Bilya duk inda zaka Jalla yayi maka godaɓe,

                        Mai Allah ina ruwanai da gudun wani ya laɓe,

                        Komai za a ce ma Bilya Allah ya jiya Bilya.

Mawaƙin ya yi amfani da kalmomin Zamfarci a wannan baiti, a ɗango na biyu ya yi amfani da Kalmar godabe’   mai nufin ‘titi’ ko  ‘hanyar mota’, amma a wannan baiti ya yi amfani da ita a jagora. Ya kuma yi  da  kalmar  ‘ruwanai’  a matsayin ruwansa. Ya yi amfani da ita  domin nuna rashin damuwa, ko tsoron abokin gaba.Da kuma kalmar ;jiya’  mai nufin ‘ji’  Ya kawo Kalmar domin nuna cewa Allah na tare da Bilya.

Jagora:            Ga wani ya yi biɗa ka kasai na ga shi Zariya,

                        Ya san na ga nai zai sayan kwandon kayan miya,

                        Yacce mallan ka raga man ni ne mutumin jiya,

                        Sari zan yi in nemi sisi ya san na jiya.

 

 A nan kilasik ya yi amfani da kalmomin Zamfarci, kamr inda yace, ‘biɗa’  a matsayin ‘nema’  ya yi amfani da kalmar ne a matsayin takara a nan. Da kalmar ‘kasai’  mai nufin ‘kada shi’, ya yi amfani da ita domin nuna faɗuwa.Sai kuma kalmar ‘nai’  maimakon ‘sa’ ko mai nufin mutum na uku, wato shamagana tilo. Haka kuma ya yi amfani da kalmar ‘Yacce’  maimakon ‘yace’ da Kalmar ‘mallan’ mai nufin ‘malam’, ya yi amfani da ita a matsayin ɗan kasuwa. Haka zallika ya yi amfani da Kalmar ‘jiya; mai nufin ‘ji’ a daidaitacciyar Hausa.

 

Jagora:            Mine ne na ɓoyo saboda sana’a ce kakai

                        In ka samu riba ka sai dawo in ta yi kai,

                        Don jarinka bai sayen shinkafa ƙarya ka kai,

                        In kuma ka yi zwari ka taɓe dan shi ka iya.

A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da kalmar Zamfarci a ɗango na farko, inda ya yi amafni Kalmar, ‘kakai’ a matsayin ‘kake’ mai nufin aikin da ake cikin yi, ya yi amfani da ita a nan domin bayyana aikin da wannan mutn ke yi.A ɗango na huɗu ya yi amfani da kalmar, ‘zwari’  a maimakon ‘zari’ mai nufin wuce-gona-da-iri a daidaitacciyar Hausa. Amma a nan ya kawo ta domin tsoratarwa.

Jagora:            Ni dai in da Allahu yat tsaisan nan nit tsaya,

                        PDP nikai ko akwai wani mai man tambaya,

                        Shi gulbi komi girmanai bai kai maliya.

                        Don haka nir riƙe PDP ta don ita na iya.

 

A ɗango na farkon wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da kalmomin Zamfarci, inda ya yi amfani da ‘yat tsai san’  a maimakon ‘ya tsaida ni’,  ya yi amfani das u domin nuna ɗa’a ko biyayya.Da kuma ɗango na biyu in day a yi amfani da  ‘nikai’  a maimakon ‘nake’ ya yi amfani da kalmar domin nuna Jam’iyya da yake. Haka  kuma a ɗango  na uku ya yi amfani da ‘girmanai’ a matsayin ‘girmansa’ ya yi amfani da ita domin kwatance.

WAƘAR IBRAHIM AMMA

 

Turke: Asalamu alaikum ‘yan’uwa,

 Tanbihi ne na zo da shi na gaskiya, Allah ya gani,

PDP Ciyaman sai Nasiru Ibrahim Ammani,

Gaba dai-gaba-dai ba baya ba.

Jagota:            Kai birnin Sambo muna nan dai har yanzu damu bamu ƙaura ba,

                        Kuma PDP muka yi  har yau kuma masu biɗa baku girma ba,

                        Im ma kun girma da sauranku hansari ne ku baku ƙusa ba,

                        Da ma in Allah ya tsaya ma wani bai iya muzanta ka ba.

A nan Alhaji Kabiru ya yi amfani da karin harshen Zamafrci, indaya yi amfani da Kalmar ‘hansari’  mai nufin ‘rubabe ko hirtsi”  ya yi amfani da kalmar domin nuna ƙaranatr ko kasawar abokan adawa. Ya kuma yi amfani da kalmar ‘biɗa’ a  maimakon ‘nema’ a daidaitacciyar Hausa.Ya yi amfani da kalmar a matsayin masu neman mulki

Karɓi: Kabiru Kilasik na taso da  gudu na ci illar begara,

                        Ta kwana da yunwa na ɓoye cikin buhu ta ga tubagara,

                        Abin ya zarce tinanina bari in gwama kida kokara,

                        In dan kyilla ko shingi kyalla wallahi dai baki tsira ba.

A nan ma mawaƙin yi yi amfani da kalmar karin harshen Zamfarci inda ya yi amfani da kalamr ‘killa’ mai nufin ‘darni’ a daidaitacciyar Hausa.Ya yi amfani da ita domin nuna haɗari dake fuskantar abokan adawa.

Jagora:            Karsa yaron masu abinci an ƙware ga satar malmala,

                        Kullun fuskatai ga sanhwara ko dan ya ga tsoka santala

                        Mu yanzu mun gane ke ka shigo kaga aikin ƙwanƙwala,

                        AI dama yaron karuwwai bai damu ya koma baya ba.

A ɗango na biyu ya yi amfani da karin harshen Zamfarci inda ya yi amfani da kalmar‘sanhwara’  mai nufin ‘tale’ da kuma Kalmar  ‘karuwwai’  maimakon ‘karuwai’ da ake amfani da ita a daidaitacciyar Hausa.

Jagora:            Ni ɓarawo na ban shawa in dai ba a kamik ke shi ba,

Shi wanga ɓarawon an cinmai gudunka ƙato ba ka tsira ba,

Kuma an ka gwado shi ga NTA aka ce ba hairi ya yi ba,

Am bar wa iyali abun hwaɗi har yanzu kare bai tuba ba.

A wannan baiti Kilasik ya yi amfani da kalmomin Zamfarci, kamar kalmar, ‘shawa”  a maimakon “sha’awa” , amma a nan mawaƙin ya yi amfani da kalmar a matsayin ba’a, wato maganar da ba haka ake nufi ba.da. Kuma  “kamik ke”  a matsayin ‘kamo’ A ɗango na biyu ya yi amfani da kalmar “wanga” a maimakon ‘wannan’. Ya yi amfani da ita domin nuna kusancin shi da wannada yake yi wa zambo. Waɗanan duk kalmomi ne, da ake amfani da su a karin harshen Zamfarci.

Karɓi: Ya gadi mutunci tun farko sabba ya ɗauke ‘yan’uwa,

                        Da wane yazan Ciyaman Gusau, ai gara a yo ɓannanr ruwa,

                        Ɗandaudu kana da halin mata wani mai bakin shan romuwa,

                        Gun fasta yayi wani gadan-gadan ya aza ban ganikke shi ba.

A wannan baitin ma Kilasik ya yi amfanin da kalmomin Zamfarci, kamar kalmar ‘sabba’ mai nufin ‘bare’ wato wanda ba ɗan’uwa ba. Da kuma kalmar ‘ganikke’  maimakon ‘gano’  ya yi amfani da ita a matsayin fahimta.

WAƘAR  ABDULLAHI MUHAMMAD TALBAN  ZURMI

Turke: Mazan ƙwarai na Mamuda ban raina ma ba,

                        Talban Zurmi mijin Khadija alkairi yay yi,

                        Mijin Inno Sa’a da taf fi manyan kaya.    

 

Jagora Mazan ƙwarai suna  Zurmi masu ma alfarma,

                        Irin nau Talban Zurmin ka ji zakin fama,

                        A kyauta haza wassalamu kai ne kurma,

                        Taho maza ba ji ba gani kiɗe turɓaya.

A wannan baiti a ɗango na biyu Kilasik ya yi amfani da karin harshen Zamafrci inda ya yi amfani da kalmar ‘nau’ maimakon ‘nawa’ ya yi amfani da ita domin nuna dangantaka ko mallaka. Da kuma kalmar ‘kiɗe’  mai nufin ‘ture’ a daidaitacciyar Hausa, amma shi ya yi amfani da ita a matsayin zuga.Haka zalika ya yi amfani da kalmar ‘taho’  mai nufin ‘zo’ amma sai ya yi namfani da Kalmar ta amfani da karin harshe.

Jagora:            Ashe gadagi ya zame hasarar gero,

                        Mawaƙan dauri suna faɗi musamman Ƙwairo,

                        A bar ni da damma na a jakkuna in ɗauro,

                        Idan na gaji kahin zurmi na huta kurya.

A nan ma mawaƙin ya yi amfani da kalmomin Zamafrci, inda yace, ‘jakkuna’ maimakon ‘jakuna’ mai nufin jam’i na jakai.kuma ya yi amfani da kalmar ‘kahin’ maimakon ‘kafin’  wanda karin harshen shi ne na Zamfarci.

Karɓi: Kabiru kilasik bana ina da sha’war noma,

                        Awo dai ya dame ni ga iyali su ma,

                        Da gona  ta kuyya bakwai na dama ni ma,

                        Cikin wari na kar a barni nine baya.

A wannan baiti a ɗango na karshe Kilasik ya yi amfani da Kalmar ‘wari’ mai nufin ‘tsara a daidaitacciyar Hausa. Kuma ya yi amfani da ita ne a matsayin kamancen daidaito.A karin harshen Zamfarci ana amfani da kalmar ‘wari’ domin a bayyana mutane masu shekaru ɗaya ko tsarar juna.

 

WAƘAR  CIGARIN  ƘAURA  “RAMAU TA FI  FARAU ZAFITA”

Turke: Baba dawo baba dawo,

Cigari I.O maza da mata,

Yara da manya suna jiranka,

Kacancanta da mulki Ƙaura,

Dan ba ka saba da yaudara ba.

JJagora:           Kusu ya tare turbar kyanwa ya ce shege ka bi wuringa,

Karɓi: Ashe kare ya yi mai Katanga da shi da kusu sun ka yi jinga,

Jagora:            In ban cin hwaɗa da mai rabo ya ya turu za ya ja da ganga,

Karɓi: Kowa dai ya tsaya matsayi nai  in ba neman yawan hwaɗa ba.

Kabiru Kilasik ya yi amfani da kalmomin Zamfarci a cikin wannan baiti. Ya yi amfani da Kalmar ‘kusu’   amma a nan kalmar bay a yi amfani da ita bane domin nuna ɓarna ko sata, ya yi  amfani da kalmar domin nuna abin da bay a yiwowa ne.  Amma a sanadin wani dalili sai ya kasance ya yiwo. Da kuma Kalmar ‘wuringa’ a matsayin ‘wajennan’  ya yi amfani da ita a nan domin nuna bagire.da kuma kalmar ‘hwaɗa’ mai nufin ‘faɗa’ a daidaitacciyar Hausa.

Jagora:            Mai riga da maho an taɓe girtsatstse bai ƙi cin tayi ba,

Karɓi: Wane siyasa riƙe ta wasa ba gaba ko yawan hwaɗa ba,

Jagora:            Ai in bai yi hwaɗa ba gaba ɗai ya gwaji bai gadi kangara ba,

Karɓi: Mai neman kuka tun farko ba zai rena ma tunkuɗa ba.

,Anan mawaƙin ya yi amfani da Kalmar ‘girtsattse’  domin nuna fanɗara ta wannan mutun da rashin nutsuwa. Da kalmar ‘hwaɗa’  maimakon ‘faɗa’ da kalmar ‘tunkuɗa’  mai nufin  ‘turi ko mangaza’,  ya yi amfani da ita a nan a matsayin dalili.

Jagora:            Halshe ya ji gamin garwashi rannan ko ƙala bai hwaɗi ba.

Karɓi: Ashe  wurin wargi aka wargi mu ba mu saba da gallaza ba,

Jagora:            Zamfara kun ga irin ta ashe MAS ba mai watse jahar ku ne ba,

Karɓi: Yau bakin magana ya ƙare su wane zaben ku bai yi kyau ba.

A wannan baiti a ɗango na farko ya yi amfani kalmar ‘halshe’  maimakon ‘harshe’  ya yi kawo kalmar ne domin nuna raki ko rashin juriya. Da kuma kalmar ‘wargi’  a matsayin ‘wasa’, amma a nan yana nuna bambanci ne. Haka kuma, ya yi amfani da kalmar ‘watse’  mai nufin ‘watse’, amma a nan ya kawo ta ne a domin kariya ga wanda yake yabo. Da kuma kalamr ‘gumi’ mai nufin ‘zafi’ ko ‘kaifi’ misali, kamar mutum yace, yajin nan ya cika gumi.

Jagora:            Mallamai ko dai ku bi Allah kad da ku manta da Annabinku,

Karɓi: Dan Allah ku ji tsoron Allah kun san kabri yana jiran ku,

Jagora:            Bayan wannan cikin  kushewa mala’iku za su tambayar ku,

Karɓi: Akwai azaba wurin mutum in dai bai amsa ma  tambaya ba.

A nan Kilasik ya yi amfani da karin Harshin Zamfarci, kamar ‘mallamai’  a matsayin ‘malamai’  kalmar suna ne, amma a nan jam’in sunanan ne.Ya yi amafani da ita domin  jawo hankali da bada shawara.da kuma ‘wurin’ a matsayin ‘wajen’ amma a nan ya yi amfani da ita ne, a matsayin kalma mai nuna dangataka.Wanɗannanhduk kalmomin karin Harshen Zamfarci ne.

 

Jagora:            In su ɗai suke babu bagarde kare da kura ba su ƙawance,

Karɓi: Wagga siyasa ni na gane cikin biyat ukku yaudara ce,

Jagora:            In bayan gyaran addini yanzu siyasa abun gudu ce,

Karɓi: Guda-gudatta baƙar manufa ce ba wai duk zani ambata ba.

A wannan baiti Kilasik ya yi amfani da ginin kalmoni Zamfarci, karma inda yace, ‘wagga’ maimakon ‘wannan’ da kuma Kalmar ‘abun’  maimakon ‘abin’ sai kumaa Kalmar’ukku’ mai nufin ‘uku’ da Kalmar ‘biyat’  maimakon ‘biyar’ . Haka kuma inda yace, ‘guda-gudatta’   maimakon ‘guda-gudarta’  ya yi amfani da kalmomin domin nuna adadi.

 

WAƘAR BACIRI SARKIN FULANI

Turke:             PDP zan yabawa, Fati mai karramawa,

                        Baciri sarkin Fulani, Maru Bunguɗu shi za mu zaɓa.

Jagora:            Wanga in lokacin kamfen ya zo ban san me za yace ba!

Shi da maigidanai wani ƙauyen in sun tafi ba zasu sha ba,

Maigidan burgu shi kuma kusu, Allah waddan ku ban ruhe ba,

Ita ijjiya in in tana ruwa kwali tuzali in ayo ba za ya yi ba.

A nan ma Kabiru Kliasik ya yi amfani da kalmomin Zamfarci, ya yi amfani da Kalmar ‘matanai’  maimakon ‘matansa’  ya yi amfani da ita domin nuna alaƙa.Da kuma  “gidanai”   a maimakon  ‘danginai’ , ya kawo kalmar domin nuna mallaka.Har way au ya yi amfani da kalmar ‘wanga’  mai nufin ‘wannan’. Da kalmar “burgu”   amma a nan yana nufin babban ɓarawo. kalmar “kusu”  kuwa, yana nufin ɓarawo ƙarami, Idan muka lura za mu ga cewa kusan duk da kalmomin karin Harshen Zamfarci mawaƙin ya gina wannan baiti.

Jagora:            Zomon bana kad da ka hau turba don na ga kare na jiran ka,

Baƙin maƙwabci mai cin gona duk ya ɗebe min iyaka,

Wanga cin iyaka ya yi yawa ranar tsayuwa kaico kanka!

Da dai ka mayar tun a duniya ba yahe ma zani yi ba.

Mawƙin ya yi amfani da kalmomin Zamfarci a cikin wannan baiti, ya yi amfani da ’kad da’  maimkaon ‘ka da’  ya yi amfani da kalmar  domin yin kashedi, ko hani.Da kuma ɗebe’  mai nufin ‘cire’   ya yi amfani da kalmar ne, domin nuna irin zaluncin da aka yi masa. Haka kuma, ya yi amfani da ‘yahe’  a matsayin ‘yafe’ da kuma ‘wanga’  a maimakon ‘wannan’. Idan muka lura mawaƙin ya yi aiki da karin harshen shi na Zamfarci.Inda ya yi amfani da Kalmar ‘hanƙuri’ maimakon ‘haƙuri’ da kuma ‘hannunai’ maimakon ‘hannunsa’  haka kuma ya yi amfani da ‘kaɗa’ a matsayin ‘auduga’  a daidaitacciyar Hausa.

Jagora:            Burgu tafi da gidan ka yakai, akwatin sawa a ce kumatu,

Shi nan yaka ɓoye gujjiyatai domin ta biya mai buƙatu,

Mai gyaɗa cikin baki jama’a ya zaya fahimatr karatu?

Idan mallami ya ce ya faɗi da alama ba zai faɗi ba.

A nan ma Kilasik ya shigar da wasu kalmomi na karin Harshen Zamfarci, kamar Kalmar ‘burgu’ mai nufin ‘gafiya’ da ma kalmar ‘gujjiya’ mai nufin ‘giɗa’  a ɗango na huɗu ya yi amfani da kalmar  ‘mallami’  maimakon ‘malami. Da muke da shi a daidaitacciyar Hausa.

 

Jagora:            Kowane tsuntsu ya dai riƙe kukan gidansu,

Komai lalacewar mussa ku san cewa ta hi kusu,

Waɗansu maza sun mace, Allah Ka jiƙan su,

Sun shiga ramin da ba matsera ba hitowa ba.

A wannan bati Kilasik ya yi amfani da ginin kalmomin Zamfarci  inda ya yi amfani da kalmar ‘kusu’ wadda ke nufin ‘ɓera’ da kuma kalmar ‘mace’ wadda ke nufin ‘mutu’ a daidaitacciyar Hausa. Haka kuma ya yi amfani da kalmar ‘mussa’ mai nufin  ‘mage ko kyanwa. Sai kuma kalmar ‘hitowa’ maimakon ‘fitowa’  da kuma ‘hi’ maimakon ‘fi’, Waɗannan duk kalmomin Zamfarci ne.

Turke: Mu Shinkafi mun gode Allah bai bar mu ƙarshe ba,

                        Koguna za ya sake maimaici Allah ya riga ya yi,

                        Ya Allah mun yi godiya jama’a bas u ba mu baya ba.

Jagora:            ‘Yan Shinkafi salamu alaikum na zo nuna tau baiwa,

Yaro har da manya da tsawhi i ba na tsambarin kowa,

Mata har da ku a waƙata ba na sanya gaugawa,

Tun da fashin baƙi ya tashi taɓarya ba zata ƙahwa ba.

A nan mawaƙin ya yi amfani da kalmomin Zamfarci karma kalmar ‘tsawhi’ mai nufin ‘tsofaffi’ da kalmar ‘gaugawa’  maimakon ‘gaggawa’, ya yi amfani da kalmar domin nuna nutsuwa. Haka zalika ya yi amfani da kalmar ƙanhwa’ a matsayin ‘ƙanfa’.  Ya yi amfani da ita domin nuna gushewar abu y azan babu shi.Idan muka lura a nan mawaƙin ya yi amfani ne, da tsarin kalmomin karin Harshen shi na Zamfarci kansancewar shi Bazamfare.

Jagora:            Mai alka ga kumci ta goge biɗi wanzami ya tusa maka,

Karɓi: Ko ka taɓa jin ban kaunarka yau na shirya na faɗa maka,

Jagora:            Cire takalmiki ƙawar waƙa na yarda da ke ki wuce ɗaka,

Karɓi: Omo shi ne babban gaccin dauɗar  matar ɗan garuwa ba..

A wannan baiti a ɗango farko Kilasik ya yi amfani da Kalmar “alka” mzi nufin ‘tsaga’  ya yi amfani da ita a nan domin yin zambo. Da kuma Kalmar “biɗa” mai nufin ‘nema’. Haka kuma, ya yi amfani da Kalmar ɗaka”  mai nufin ‘cikin ɗaki’ Wadannan duk kalmomin karin harshen Zamfarci ne.

4.5 Kammalawa

            Kamar yadda bayani ya gabata, wannan babi shi ne ƙashin bayan wannan aiki. Kuma a cikin shi ne aka yi cikkaken bayanin  wurare da baituttukan na waƙoƙi da Kilasik ya yi amfani da karin harshen Zamfaci na waƙoƙinsa da aka nazarta. Haka zalika, an yi bayanin ma’anr kalmomi, da tsarin kalmomin Zamfarci, kamaryadda Kabiru Kilasik ya yiamfani da su a cikin waƙoƙinsa.

Post a Comment

0 Comments