Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazarin Kalmomin
Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (3)
BABI NA UKU
TARIHIN KABIRU KILASIK
3.0 GABATARWA
A wannan babi za a yi
cikakken bayani a kan rayuwar Alh Kabiru Yahaya Kilasik. Da dalilin fara waƙarsa da jigon waƙoƙinsa da ire-iren waƙoƙinsa. Haka kuma za a
duba yadda yake tsara waƙarsa da kuma salon waƙoƙinsa, da irin
matsayinsa a yau.Da yadda yake amfani da hikimarsa wajen haɓaka adabin Hausa.
3.1 Tarihin Rayuwar Kabiru kilasik
An haifi Alh Kabiru
Yahaya kilasik a shiyar Ɗangawo cikin garin Talatar Mafara, a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba’in
da takwas (1978). Sunan mahaifinsa Malam Yahaya. Sunan kakansa na wajen uba
Malam Ibrahim Sunan mahaifiyarsa Safiya,
sunan kakansa na wajen uwa Mahammadu Macciɗo.Ya yi karatun allo a makarantar Malam Bawa
a garin Sabon Birnin Gobir da ke jihar Sakkwato. Haka kuma ya shiga makarantar
Boko a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da huɗu(1984) a garin Talatar Mafara, a
makarantar Abubukar Tunau Model Primary School wacce ya kammala a alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in
(1990). Kuma ya samu nasarar zarcewa zuwa makarantar Shiekh Abubakar Gummi
Memorial College Sakkwato a wannan shekara. Haka zalika, ya samu nasarar
kammala wannan makaranta a alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in da shida (1996). Daga nan
ya wuce makarantar fasaha da ƙere-ƙere ta Abdu Gusau
Polytechnic Talatar Mafara a shekarar dubu biyu inda ya yi”certificate” a
wannan shekarar..Kamar yadda mawaƙin ya nuna a cikin waƙarsa mai taken “Anpp Bani da Kowa” asalinsu
fulani ne.Kuma ba nan kaɗai ya tsaya ba domin a waƙarsa ta Gwamnanin
Arewa cewa ya yi,
Jagora: Kabiru ne tsatson ƙayatawa al’adarmu cin
furen daji,
Gwamnonin
arewa dan Allah yazan kuna kwatanta adalci,
In
kune yau Kabiru Kilasik gobe takan yu ba yazan ku ba.”
Ashe kenen idan aka
yi la’akari da waɗannan ɗiyan waƙoƙin asalinsa
Bafualatanin Maradun ne, makaƙera yadda ya bayyana da kansa.A yanzu Kilasik
yana da mata uku, ga sunayensu kamar haka:-
Matarsa ta farko
sunanta Hajiya Lubabatu.
Matarsa ta biyu
sunanta Shafa’atu.
Matarsa ta uku
sunanta Hauwa’u.
Yana da ‘ya’ya tara
ga sunayensu kamar haka:
Na farko shi ne mai
sunan mahaifinsa Yahaya,
Ta biyu Khadija,
Na uku Ibrahim,
Ta huɗu Zainab,
Na biyar Muhammadu,
Ta shida Fatima,
Ta bakwai Hauwa’u,
Na takwas Ahmad,
Ta tara Safiya.
Waɗannan su ne iyalan
Alhaji Kabiru Yahaya Kilasik,kamar yadda muka gani yana da mata uku da ‘ya’ya
tara a halin yanzu.
3.2 Fara waƙarsa
Babu wani abu da za a
gudanar face akwai dalili ko mafarin yinsa ba. Wato,dukkkan lamari da ake yi
akwai manufa ko maƙasudin aiwatar da shi. Gaskiyar masu hikima da ke cewa,”Ða walaki goro a cikin miya” wato komi ka ga an yi akwai dalili.Don
haka Kilasik ya fara waƙa ne tun shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in da shida, (1996), a loƙacin da yana ɗalibi, a wata dirama
da suka shirya a lokacin da suka ƙare makaranta.Ya fara
da waƙa mai taken “Wargaji uban noma ba ka yin tsiyar gero”
wato, waƙar noma inda yake cewa,
Jagora: Wargaji Uban
Noma,
Ba Ka
Yin Tsiyar Gero
Wargaji
Ka Yin Dawa,
Shi
Ka Yin Buhun Maiwa.
Da ya yi wannan waƙa shi ne Shugaban
makarantarsu (principal) Malam Ibrahim
Liman ya nuna masa cewa yana da hazaƙa sosai, kuma ya sani
ilimi bashi zai sa mutum ya ce bai iya saran icce ba, ko turin baro.Saboda
haka ya kamata ya jaraba ya gani. Wannan
yana ɗaya daga cikin dallilin fara waƙarsa.
Haka kuma yana nuna
cewa shi bai gadi waƙa ba sha’awa ce, inda ya nuna cewa sha’awar waƙoƙin Alh Musa Ɗan Ba’u Gidan Buwai
ta ja sha’awarsa ya fara waƙa.
Daga nan bai sake waƙa ba sai da aka fara
siyasa a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in da tara (1999). A lokacin da aka koma dimukuraɗiyya inda aka nemi ya
yi wa jam’iyar NPN waƙa mai taken “Wurin
Bindiga Wane Ƙyastu” inda
yake cewa,
Jagora: Yarana
ko da bayani ciki,
Ina
waƙa
ba ku tanka ba,
Karɓii: Lallai da bayani Kabiiru,
Ka ƙi taɓo mana zancen baba.
Kilasik ya yi waƙoƙi ɗari uku da hamshin da tara (359). Ya ce a ranar sha biyu ga watan uku shekara ta dubu biyu da
goma sha takwas (12-03-2018) , zai yi waƙa ta ɗari uku da sittin
(360). Inda ya ce yana gab da aje waƙa.Daga cikin waƙoƙinsa, waƙar Walin Kurya ita ce
ta fi haskaka shi a idon jama’a. Kuma ta zama silar ɗaukakarsa a duniya. A
taƙaice
dai ita ce bakandamiyarsa. Kamar yadda ya nuna wannan waƙa abun al’ajabi
ce domin bai tsara ta ba , a wani lokaci
kawai ya ji batocin waƙar na zo masa, nan take. A cewarsa kalmomin waƙa zuwa suke yi loƙaci ɗaya da kuma sun zo
dole a rubuta su, don gudun kada su tafi domin da zarar sun tafi ba za su dawo
ba.
3.3 JIGON WAƘOƘIN KILASIK
Jigo shi ne, manufa
ko maƙasudi, ko saƙo da waƙa ke ɗauke da shi. Jigo shi
ne saƙo da mawaƙi ke son isarwa a cikin waƙrsa. Masana da dama
sun bayyana ma’anar jigo ta fuskoki daban-daban.Daga ciki akwai;
Yahaya da wasu
(1992), sun bayyana ma’anar jigo kamar haka, “jigo dai shi ne manufar waƙa wato saƙon da take ɗauke da shi a dunƙule”
Shi kuwa Gusau
(1993), cewa ya yi, “jigo shi ne abin da waƙa take magana a kansa
ya ratsa ta tun daga farkonta har ƙarshenta”
Amma Yahaya (1997) ,
ya bada ma’anar jigo da cewa,”wani muhimmin tubali ne na sharhi a kowane
hali.” Haka kuma sharhi kan jigo kan
bayyana fahimtar da manazarci ya yi wa waƙar gaba ɗaya.
Dunfawa (2008) cewa
ya yi, “A rubutattar waƙa marubuci yakan ambaci jigon waƙarsa tun a farkon waƙa ko a tsakiyar waƙa ko a ƙarshenta”
Murjanatu (2012) ,
ita ma ta yi ƙoƙarin kawo ma’anar jigo a daidai fahimtarta kamar haka:
“Idan ana maganar jigo ana magana ne a kan
a. Saƙo da ke ƙunshe cikin adabi.
b. :Manufar ƙaga ko shirya abu.
c. Abubuwan da take
karantarwa
d. Muhimmman abubuwan da
ya bada haske a kansu.
e. Jigajigan abubuwa da
aka tunkara ko aka fayyace a waƙa.
Sanin kuwa ne cewa,
duk abin da aka tsara to da manufarsa, don haka jigon waƙoƙin Kilasik shi
ne siyasa.A wata tattaunawa da aka yi da
mawaƙin a gidan Talbijin na
RTƁ, dake cikin garin Sakkwato a shirin su na ‘Daga Bakin
Mai Ita” Mawaƙin ya bayyana cewa
‘yan siyasa yake yiwa waƙa, kuma su ne abokan hulɗarsa. Wannan zance haka yake domin
kashi casa’in cikin ɗari na waƙoƙinsa duk na siyasa
ne. Duk da a kan ɗan sami wasu da ba na
siyasa ba. Kamar na Sarauta irn waƙar Sarkin Musulmi da
ta Sarkin Gusau, da Sarkin Jabo da sauransu.
Haka kuma ya yi wata
waƙa
wadda ta sauya mashi salon shi na zama maƙikin siyasa ya dawo
wani, domin yara ne ya yi wa waƙar ‘ya’yan masoyinsa Barade. Ya
bayyana cewa a halin yanzu babu wata waƙa da yake so a cikin
waƙoƙinsa kamar wannan waƙar. Kuma waƙar ta samu karɓuwa. Waƙar ita ce,
Jagora : A watse kashi a sake rabo,
Fahad da Abubakar ku sani,
Duk Sakkwato wa ya kai ku
uba,
Ɗiyan Ahmed Barade
ubammu,
Ƙane ga Alu na har
abada.
Wannan waƙa Kilasik yana son ta
sosai.Kamar yadda bayani ya gabata kilasik mawaƙin siyasa ne,Kuma
mafi akasari ‘yan siyasa yake yi wa waƙa.
Amma duk da haka a
‘yan siyasar ba kowa yake yi wa waƙa ba sai wanda ya
yarda da halinsa da mutuncinsa. Kuma, ko a wacce jam’iya yake ba sai a jam’iyar pdp yake ba.
Akwai jigogi da dama
da waƙoƙin Kilasik suka ƙunsa, musamman yabo
da zambo da habaici da gugar-zana da arashi da makamantansu. Ga misalan wasu
daga cikin jigogin waƙoƙinsa:
-Gaskiya Mugunyar
magana
-Rumfar kara da ɗoriyar garwashi
-In an ba albasa ruwa
mugunyar
--Jijjihin bubbukuwa
-Iya ruwa fidda kai
-Ruwa kar da bakin ƙwarya
-Angulu da kan zabo
-Ciki da gaskiya
-Ramau ta fi farau
zafi
Wato mafi akasarin waƙoƙinsa tun a sunayensu
yake buɗewa da zambo ko yabo
ko habaici ko gugar zana domin isar da manufarsa ga al’umm
3.4 Yadda Kabiru Kilasik Ke Tsara Waƙoƙinsa
A nan za a duba yadda
wannan mawaƙi ya ke tsara waƙoƙinsa, A haƙiƙanin gaskiya komi
yana buƙatar tsari domin idan ba a tsara yadda za’a gudanar da
shi ba dole ne za a cikaro da matsaloli.Tsari ya zama wajibi musamman ma a waƙa domin kowane mawaƙi yana da yadda yake
tsara waƙarsa ko kiɗansa. Idan muka duba ƙarfin tunanin wannan
mawaƙi, za mu ga cewa mawaƙin yana tsara waƙoƙinsa ta hanyar sigogi
daban-daban.
A wasu waƙoƙin yakan fara gabatar
da lambar wayarsa sannan kiɗa ya biyo baya. Amma a wasu waƙoƙin sukan fara da kiɗa ne. Wasu kuma a
gabatar da sunan waƙar ko takenta, sannan kiɗa ya biyo baya. Kuma yana sadaukar da
waƙoƙin ne ga wasu mutane.
Haka kuma wani lokaci
sai ya gabatar da jigon sannan ‘yan amshi su ci gaba. A ya yin da ƙalilan daga ciki ‘yan
amshi ke farawa. Haka kuma mawaƙin kan yi amfani da salon buɗe waƙarsa da addu’a bayan
ya gabatar da jigon duk da kasancewar ba ya amfani da addu’ar wajen rufewa sai
dai ya rufe da kiɗa.
Alhaji Kabiru Kilasik
na amfani da ƙafiya a dukkan waƙoƙinsa. Akwai amsa-amon
ciki da na waje,wato babban amsa-amo da ƙarami a waƙarsa.
Gaskiyar masu iya
magana da suka ce, “yabon gwani ya zama
dole” Kilasik na amfani da wani irin tsari na musamman mai burgewa da ƙayatarwa da kuma ban
sha’awa da ba kowane mawaƙi ke amfani da shi ba a mawaƙan zamani. Ba a yi
laifi ba idan aka ce karɓeɓeniya ita ce ƙashin bayan waƙoƙinsa.Mafi akasarin waƙoƙinsa duk suna da karɓeɓeniya, ƙalilan ne babu ta a
ciki.Duk da cewa magabata da suka yi aiki a kan wannan mawaƙi sun nuna cewa yana
amfani da karɓeɓeniya iri biyu, wato, karɓeɓeniyar baiti sukutum da kuma karɓeɓeniyar cikin baiti ɗaya. Haƙiƙa sun yi ƙoƙari. Amma hausawa na
cewa “Abin da wayo ya ɓoye hankli ke gano
shi” wato a duk lokacin da mutum ya duƙufa a kan binciken
wani abu ta hanyar bin diddiƙinsa tare da tonon silili da nazarin ƙwaƙƙwaf a kan wanan abin
zai gano duk wani sirri da ke cikinsa.Ta haka ne na fahimci cewa Kilasik na
amfani da karɓeɓeniya iri uku ne ba
biyu ba, kamar yadda waɗanda suka gabace ni
suka fahimta. Tsarin kaɓeɓeniyar shi ne, karɓeɓeniyar baiti sukutum,
da karɓeɓeniyar cikin baiti ɗaya da kuma karɓeɓeniyar ɗango ko layi ɗaya. Saboda haka
wannan tsari ne da ba kowane mawaƙi ke amfani da shi
ba.Misali a waƙarsa “In an ba
albasa ruwa”
Jagora: Rabbi Allah sarki ka maida
jam’inmu guda,
Har
haɗa kawunan musulmi mu
zamo har abada,
Tunda
kai ke baiwa ka fid da mu gun maraɗa,
Dukka
musulmi na duniya mu kauce tarkon sababi.”
Amshi: Musɗafa manzona Annabi
madalla da kai,
Ni
a ƙyaleni
a bar ni ka isan in yi da kai,
Karramammen
bawa na matsu in sadu da kai,
Mai
kamala Ahmadu Annabi tushen ladabi.”
Idan aka lura a waɗannan baituttuka za a
ga baiti sukutum take karɓewa.Haka kuma akwai
karɓeɓeniyar cikin baiti in
da zai faɗi layi ɗaya ta faɗi ɗaya. Ga ƙarin misali:a waƙarsa mai taken”Baba dawo baba dawo”
Jagora: “Kusu ya tsare turbar kyanwa ya ce, “shege
ka bi wajenga,
Karɓii: Ashe kare ya yi mai katanga da shi da
kusu sun ka yi jinga,
Jagora: In ban cin faɗa da mai rabo ya ya
turu za ya ja da ganga,
Karɓii: Kowa dai ya tsaya matsiyi nai in ba
neman yawan faɗa ba”
A nan Kilasik ya yi
amfani da tsarin karɓeɓeniyar cikin baiti,
bayan ya faɗi na ɗaya sai ta faɗi na biyu.Akwai kuma
karɓeɓeniyar layi ɗaya. Ga misali a wata
waƙarsa
da ya yi wa Hajiya Sarutun Mamuda fes ledi.
Jagora: “ Ya Allahu gagara misali,
Mai Nijeriya mai Itali,
Waƙoƙi ala kulli hali,
Jagoara: Zan yo wa ga matar ubana ka sa
idonta ba su kau ga ran ba,
Karɓi: Zan yo wa ga matar ubana ka sa
idonta ba su kau ga ran ba.”
A nan Kilasik yana
amfni da karɓeɓeniya ta cikin layi
ko ɗango guda.
Tsarin da Kilasik ke
amfni da shi a cikin jerin gwanon waƙoƙinsa ya sha banban da
na sauran mawaƙan siyasa na zamani.Ba don kar na cika baki ba da na ce a
duk mawaƙan siyasa na wannan
ƙarni
da muke da su a yau, a kasar Hausa,babu mawaƙi mai azanci da
hikima da tsari da jera tinani a waƙa da ya taka sawun
Kabiru kilasik.
3.5 IRE-IREN WAƘOƘIN KILASIK
Duk da wasu na ganin
cewa ba jinsi da kilasik yake yi wa waƙa in ban da ‘yan
siyasa, amma akwai iren-iren waƙoƙinsa da ba na sisaya
ba. Kamar yadda muka gani cewa ya fara da waƙar noma ne ta dirama
da suka yi a lokacin ƙare makarantarsu. Daga baya ya koma waƙoƙin siyasa, haka kuma
Kilasik yakan yi waƙoƙin sarauta da na aure, amma ya nuna baya waƙar aure sai in an
matsa mashi, amma ya nuna bai iya waƙar aure ba. Yana waƙoƙin faɗakarwa kamar waƙar “Gwamnonin Arewa”
inda yake cewa
Jagora: Kabiru ne tsatson ƙayatawa al’adarmu cin
huren daji,
Gwanonin Arewa dan Aallah ya
zan kuna kwatanta adalci,
In ku ne yau Kabiru Kilasik
gobe takan yu ba ya zan ku ba.
Yanzu haka ya yi waƙoƙin bege na yabon
Annabi Muhammad( SAW)..Daga cikin waƙoƙin begen day a yi
akwai wannan:-
Jagora: Ga alƙawalin da niɗ dauka,
Yau za ni cika shi ba
shakka,
Na yi alwashi na
baitukka,
Na begen daha mai
makka,
Buwayi tsalkake ruhina
sa in yi shi domin Allah
Jigo: ( Fiyayye Annabin rahama na Kadijatu
Manzon Allah)
Duk da kasancewar kilasik mawaƙin siyasa wani loƙaci yakan yi waƙar aure. Daga cikin
waƙoƙi da ya yi na aure
akwai waƙar, Ibrahim IB da Habiba.Inda yake cewa:
Jagora Manzona sunnarka na yi,
Na bi umarnin yadda ka yi,
Sa mu gidan rahama Nabiyi,
Ya baban ma’asumiyarmu
Fatima-Zara dab a ta ƙarya.
Akwai
wata waƙar auren Sabo Anka da Amaryasa Samira. Yana cewa:
Jagora: Ya Allah mamallakina mai ikon dare da
rana,
Ka ba ni daman a raya sunnah
aure ne a zuciyana,
Wannan sunnah ta Manzo ce bani
bari a bar ni baya.
Haka kuma wajen waƙoƙin siyasa ya fi yi wa
‘yan fi di fi waƙa, domin shi ɗan jam’iyar fi di fi ne kamar yadda yake faɗa a waƙoƙinsa da dama. Misali
a waƙar I.O. Cigarin Ƙaura yana cewa:
Jagora: Fi di fi Kilasik yake yi kuma ita nir riƙe ko yaushe,
Amshi: Ko a mafalki nic ci tuwan masara sai na
matsa na maishe”
Ga abin da yake faɗa a wata waƙa da ya yi wa A.A.
Yari..
Jagora: Wasu da sun ga na yi ma Shehi waƙa za su ga fi di fi
nika yi,
Karɓi: Bara na ƙara faɗawa mutane Kabiru fi
di fi yaka yi”
Haka ma bayan gama zaɓen shekara ta dubu
biyu da goma sha ɗaya, bayan jam;iyar
ANPP ta yi nasarar lashe zaɓe an ta raɗe raɗIn Kilasik ya koma ANPP, don haka ya yi wata
waƙa
dan tabbatarwa al’umma cewa yana nan a pdp, in da yake cewa:
Jagora:ANPP ba ni da
kuwa,
Kuma
kun san ba ku da niya,
`Kar
muka kallon juna,
Kabiru
nai maku kallon mai bisa ruwa”
Ba a nan Kilasik ya
tsaya ba, akwai wata waƙa da ya yi wa Mamuda mai taken “Baba dawo baba dawo” yana
cewa:
Jagora: Fi di fi Kilasik yake yi an ja an ja na ƙi barin ta,
Karɓii: Jam’iyata ta yi mini komi kowace waƙa ina yaba ta.”
Kenan waɗannan dalilai sun isa
su gamsar da mu cewa Kilasik ɗan jam’iyar pdp ne, kuma ita ce ya fi yi wa waƙa.Har ma yakan kirata
jam’iyarsa kamar yadda muka gani. Kuma jam’iyar ta tsayar da shi a matsayin ɗantakarar majalisa a
(2015). Yanzu haka an ba Alh kabiru Yahaya kilasik SA a ƙaƙrƙashin tutar Apc wanda
ya ba shi shi ne mai gidansa Alh Mamuda Aliyu Shinkafi.
3.6 SALON WAƘOƘIN
KILASIK
Salo na ɗaya daga cikin ginshiƙan gina waƙa domin duk waƙar da ba ta da salo
ba za ta samu karɓuwa ba a wajen
jama’a. Kasancewar Kabiru Kilasik mawaƙin siyasa yana da
salailai da yake amfani da su don waƙoƙinsa su samu karɓuwa ga jama’a kuma su
yi armashi/Yana amfani da salo daban-daban domin jaddada manufarsa, musamman
abin da ya shafi adon harshe da gwanintar harshe,da kuma salon sarrafa harshe.
Ɗangambo.A (2006) Ya
bayyana cewa: “Salo wani yanayi ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko
furuci.Wannan yana nufin yin amfani da wata kalma .lafazi, yanayi, hanya ko
tunanin a maimakon wani”
Bunza A.M (2013) Ya
ce salo shi ne “Dabara da fasaha da wayon tafiyar da wani abu cikin basira da
natsuwa domin a kai ga wata manufa ta musamman.Matakan da za a bi wajen sarrafa
hikimomin baka ko rubuce ko a aikace ya kasance mai jan hankali ne da burgewa
ga mai sauraro ko karatu ko kallon aikin”.
Ɗangulbi (1996) ya ce;
“Sslo na nufin duk wata hanya da mawaƙi ke bi domin isar da saƙo a cikin waƙarssa.
Kamusun Hausa na
CNHN, cewa suka yi: “Yayi ko sauyi ko launi ko fice”
Nulic (1971) Ya ce;
‘salo hanya ce da ake bi wajen isar da
saƙo
ko manufa”
Leech (1981), Ya
bayyana cewa: “Salo shi ne kwalliyar tunani wajen isae da saƙo”
Zaɓin da duk mutum ya yi wajen isar da saƙon da yake so ya isar
zai yi tasiri ga wanda ake isar da saƙon gare shi.Salo
dabara ce da mawaƙi kan yi amfani da ita domin jawo hankalin mai sauraran
waƙa,
ya fahimci saƙon da ake so ya isa gare shi..
Kuma yana amfani da
salon aron kalmomi, daga wasu harsuna, musamman
a harshen Larabci da
Ingilishi.
Haka kuma yana amfani
da karin harshen Sakkwatanci da Zamfarci domin shi Bazamfare ne.Wannan ma shi
ya haifar da Nazarin Ginin Kalmomin Zamfarci A Wasu Waƙoƙin Kilasik.
3.7 Kammalawa
Alhaji Kabiru Yahaya
kilasik, ya fara waƙa tun tsawon shekara ashirin da biyu (22), da suka shuɗe. Ya fara ne da waƙar was an kwaikwayo.
Kamar yadda bayyani ya gabata. Mun ga tarihinsa da ire-iren waƙaoƙinsa da kuma salonsa
da yadda yake jera tunanesa a cikin waƙoƙinsa. Mun ga irin
matsayinsa da ɗaukakar da Allah ya
yi masa a fanninsa na waƙa. Kuma waƙa ita ce babbar
sana’arsa, ya kuma samu ɗaukaka a cikin harkar
waƙa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.