Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazarin Kalmomin
Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (2)
BABI NA BIYU
BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
2.0 GABATARWA
Waiwaye adon
tafiya.Masu iya maagana sun ƙara da cewa ‘ tuna baya shi ne roƙo’. Wannan babi zai yi bayani a kan ayyukan da suka
gabata.Za ayi,ƙoƙarin duba ayyukkan da aka yi masu alaƙa da wannan bincike.
Domin Hausawa na cewa "idan kabi
wanda ya fi ka dole a bi ka" Dan haka wannan waiwaye zai shafi ayyuka
masu alaƙa da wannan bincike kawai,amma wannan alaƙa za ta iya zama ta
kusa ko ta nesa.Abu ne mai muhimmanci ƙwarai da gaske a duba
wasu ayyuka da suka gabata masu alaƙa ta kusa da ta
nesa.Domin masu hikma sun ce " na
gaba idon na baya " Yin hakan zai bada damar samun makamar inda kowane
aiki ya sa gaba da kuma matsayinsa a wannan fage na ilimi.
Gaskiyar masu hikima
da ke cewa ‘Abin da babba ya hango daga
zaune yaro ko ya hau sama bai hango shi’ wannan zance haka yake, duk wani
abin da mutun zai gudanar idan har yana buƙatar cin nasara,akwai
buƙatar
ya duba tafarkin da masana suka bi dangane da wannan abu. A wajen gudanar da
wannan bincike an duba ayyukkan da suka gabata waɗanda suka yi magana a kan waƙa, da kuma harshe.An
duba kundayen bincike neman digiri na daya da na neman digiri na biyu, da
mujallu da rubtattun littafai a Jami'o'i daban-daban.
2.1 Kundayen Bincike
Akwai ayyukka da dama
da aka yi masu nasaba da wannan bincike. Daga cikin wadanda suka zo hannu
akwai:
Abubakar U. da
Ibrahim S.K. (2016) A binciken su sun bayar da ma’anar waƙa da zambo da habaici
da irer-iren su, sun bayar da tarihin Kabiru kilasik. Wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da nawa
aikin, domin kuwa,duk muna magana ne a kan mawaƙi guda, kuma a kan bagere daya wato, waƙa.Sai dai banbabncin
nasu aikin da nawa shi ne sun yi nazari Zambo da Habaici, ni kuma a kan ginin
kalmomin Zamfarci a cikin waƙoƙin Kabiru kilasik.
Ɗangulbi (2003) a
cikin kundin digrinsa na biyu ya yi bayanin tarihin kafuwar siyasa a Nijeriya.
Kuma ya yi bayanin wasu jigogin waƙoƙin siyasa na
janhurira ta huɗu, kamar jigon faɗakarwa, da jigon
yabo, da jigon zambo da habaici, da sauransu. Haka kuma ya dubi waƙoƙin inda ya fito da
siffantawa, da kinaya, da alamtarwa da dabbantarwa, da abuntarwa, a cikin wasu
waƙoƙin janhuriya ta huɗu. Sannan kuma ya yi
sharhin wasu waƙoƙin ja’iyyun ANPP da PDP.Wannan aiki nasa yana da alaƙa da nawa aikin,
domin duk suna magana ne a kan rubutattun waƙoƙin siyasa na
janhuriya ta huɗu. Sai dai bambancin
aikinsa da nawa shi ne, shi ya kalli rubutattun waƙoƙin siyasa daban-daban
ya yi nazarinsu. Ni kuwa aikina ya keɓanta ne ga rubutattun waƙoƙin siyasa na Kabiru
Kilasik. Mansur.M (2017) A nasa
kundin ya kawo ma’anar waƙa da jigo da salo da tsari.Wannan aiki yana da alaƙa makusanciya da akin nawa domin yana magana ne a kan tarjamar
wasu waƙoƙin Kabiru Kilasik, kamar yadda na ke nazin wasu kalmomin
Zamfarci a cikin wasu waƙoƙin Kabiru Kilasik.Saboda haka yana da kyakkyawar alaƙa da binken da nake
gudanawa.
Abdullahi
Y.(2016),Ya kawo ma’anar waƙa. ya yi taƙaiccen bayani kan waƙoƙin siyasa.Wannan
bincike nasa yana da alaƙa da nazarin da nake gudanarwa, domin ya yi shi ne a kan
waƙa
ya kuma taɓo waƙoƙin siyasa, fannin da
nake bincike a kai.
Garba
M.M (2016), Ya bada tarihin Attahiru Jega ya kuma kawo ma‘anar waƙa da sharhin waƙar da aka yi wa Jega
ta biyu.Wannan kundi yana da alaƙa da nawa binciken.
Buhari Ɗ. (2010) Ya bada
tarihin sarki Zazzau Aminu. Ya kawo wasu daga cikin makaɗan fada irin su:
Jankiɗi da Narambaɗa da sauransu. Wannan
bincike nasa yana da rawar da yake takawa a nawa nazarin.Sai dai aikin nasa a
kan waƙoƙin baka na sarata ne, ni kuma a kan rubutattun waƙoƙin siyasa ne na
Kabiru kilasik.
Muhammad
B.B (2015), Ya bada ma’anonin waƙar baka da salon waƙar baka da kuma
tsarinta.Inda ya yi cikakken sharhi a kan jerin sarƙe a waƙoƙin baka.Babu shakka wannan kundi yana da nasaba da nawa,
duk da kasancewarsa a kan waƙokin baka aka yi shi.Ni kuma a kan rubutattun waƙoƙin siyasa.
Talatu I. (2012),a kundinta na neman digin
farko da ta gabatar a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, Ta kawo ma’anar waƙa da waƙoƙin pdp.Wannan kundi
yana da muhimmanci da kuma alaƙa ta kusa da nawa binken.
Aliyu
N. (2011),a kundinsa na neman digiri na biyu, ya kawo ma’anar waƙa da kuma waƙoƙin siyssa, da adawar
da ake nunawa a cikin waƙoƙin siyasa. Wannan bincike yana da alaƙa ta ƙut-da-ƙut da nawa aikin.
Muhammad
S.A (2012), a kundin neman digirinsa na farko a Jami’ar Ahmadu Bello Zarira,ya
bada tarihin Jankiɗi da wasu daga cikin
waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa da jigon waƙoƙinsa.Ya kuma kawo
ma’anar waƙa. Wannan kundi na da nasaba da nawa binciken.
Ibrahim
B. (2011) Ya kawo tarihin Sardauna da kuma waƙoƙin da aka rubuta a
kansa ya yi sharhin wasu daga ciki. Wannan kundi na da rawar takawa a nawa
kundin.
Aishatu
(2012) ta yi bayanin a kan rubutattun waƙoƙin siyasa, da ma’anar
salo da ier-irensa da kuma ma’anar sarrafa harshe. Kuma ta yi bayanin salo da
dabarun jawo hankali da kuma sarrafa harshe a wasu waƙoƙin jam’iyyun PDP da
ANPP a jihohin Kano da Jigawa.Haka kuma ta kwatanta wasu waƙoƙin jam’iyyun ANPP da
PDP tare da kawo kamanci da bambancin salon waƙoƙin.
Binciken Aishatu da nawa suna da alaƙa, domin domin duk an
yi bincike ne a kan rubutattun waƙoƙin siyasa na Hausa.
Sai dai ita ta kalli salon sarrafa harshe a cikin wasu waƙoƙin na jam’iyyun PDP
da ANPP a jihohin Kano da Jigawa, ni kuma kuwa a aikina nazrin ginin kalmomin
Zamfarci a cikin wasu waƙoƙin Kabiru Kilasik.
Mashi
(1986) a kudin digirinsa na biyu, ya yi bayanin ma’anar waƙa da tarhinta da
rabe-rabenta, haka kuma ya kawo ma’anar siyasa da manufofinta, da kuma tarihin
kafuwar siyasa a ƙasar Hausa.Har wa yau kuma a cikin kundin bincike ya yi
bayani sigogi da rabe-raben waƙoƙin siyasa da kuma
matsayin makaɗan baka a cikin
siyasar jam’iyya.Sannnan kuma ya yi sharhin wasu waƙoƙin jam’iyyun NPC da
NEPU da kuma PRP.
Wannan bincike da nawa suna da alaƙa domin duk suna
magana ne a kan waƙoƙin siyasa na Hausa. Bambancinsu shi ne, nasa aikin
bincike ne a kan waƙoƙin baka na siyasa na janhuriya ta ɗaya da ta biyu. Nawa
aikin kuwa nazarin ginin kalmomin Zamfarci a cikin wasu waƙoƙin siyasa na Kabiru
Kilasik.
Abazarri
(2008), A nasa kundin binciken neman digiri na ɗaya. Ya bayyana tarihin rayuwar Aminu
ala da waƙoƙinsa da yadda yake tsara waƙoƙinsa da ire-iren waƙoƙinsa da yanayin waƙoƙinsa.Bayan nan kuma
ya kwantanta waƙoƙin ala da na mandiri, har ila yau ya kwatanta waƙoƙinsa da na fim, ya
kuma nuna yadda za a nazarci waƙoƙin.Wannan bincike
yana da alaka da nawa binciken.
Hamza
R.A (1998) Ya kawo ma’anar waƙa da kuma rubutattun waƙoƙin siysa da aka yi a
wannan lokaci.Wannan bincike yana da nasaba da nawa.
Adamu
(2002) Ya kawo tsokaci da masana suka yi kan ma’anar jigo da jigon so da jgon
bege da jigon faɗakarwa da jigon
siffantawa ya yi bayani ɗaya bayan ɗaya a kansu.
Har ila yau ya kawo
mawaƙan da suka yi waƙar da waƙoƙinsu da jigoginsu da
salon sarraf harshe da warwarar jigo da tsarin waƙar.Wannan kundi na da
alaƙa
da nawa bincike.
Abdullahi
(2001) Manazarcin ya yi ƙoƙarin kawo ma’anar waƙar baka, da waƙoƙin mata musamman na
daka da reno da daɓe. Wannan bincike
yana da alaƙa da nawa.Sai dais hi a kan waƙoƙin baka ya yi nasa
binciken, ni kuma a kan waƙoƙin siyasa na Kabiru
kilasik.
Ibrahim
(2008), ya bayyana cewa akwai hanyoyi uku da
masana suka bayyan wajen nazarin waƙa, hanyoyin su ne:
- Jigo
- Zubi
da tsari
- Salon
sarrafa harshe
Wannan bincike yana
da alaƙa da nawa,domin yana magana ne a kan hanyoyin nazarin waƙa
Salamatu (2006) ta
bada ma’anar waƙa ta kawo waƙoƙin siyasa..Wanda
wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin, kancewar nazarina a kan waƙoƙin Kabiru kilasik ne
shi kuma mawaƙin siyasa ne.
Husaini
(2007) Ya bada ma’anar waƙaya karkasa waƙoƙi kan jigo wato,jigon
gargaɗi da faɗakarwa da yabo.Wannan
bincike yana da dangantaka da nazarin da nake.
Isma'il
(1985),Ya fara ne da ma'anar fada makaɗan fada da kuma abin da waƙarsu ta ƙunsa .Makaɗan sun hada: Buda Ɗantanoma da kuma
Ibrahim Narambaɗa,rayuwarsu da
ayyukkasu.Da kuma zababbun makaɗan Fada na zamani waɗanda suka hada Musa Ɗankwairo da Sa'idu
faru.Wannan bincike yana da alaƙa da nawa,domin yana magana ne akan waƙa, kamar yadda nake
nazari akan waƙa.Sai dai nasa aikin a kan waƙar baka da mawaƙn fada ne,nawa kuma a
kan rubutattun waƙoƙin siyasa na Kabiru kilasik.
Umar (2002) A nasa
binciken na neman digiri na ɗaya da ya gabatar a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria,Manazarcin
ya bayyana ma’anar bara da kuma matsayin bara a cikin al’ummar Hausa da kuma
nau’in waƙoƙin bara da ire-iren bara da kuma lokutan da ake yin
wannan bara.Wannan kundi yana da dangantaka da nawa domin a kan waƙa ne kuma ya kawo
ma’anar waƙa a ciki.
Wakalla
(2008),ya yi tsokaci ne a kan tarihin Haruna Uji, ƙurciyarsa da yadda ya
fara waƙarsa tare da kawo bakandamiyar waƙarsa.
Bayan nan ya kawo
ma’anar jigo inda ya ce “jigo wani saƙo ne ko wani abu ne
da waƙa ta ƙunsa,Wannan bincike yana da alaƙa da nawa domin ya
bada ma’anar waƙa da jigo da tarihin mawaƙin da salon waƙarsa.Waanan bincike
yana fa alaƙa da nawa, duk das hi a kan waƙoƙin baka ne, ni kuma
rubutattun waƙoƙin siyasa na Kabiru kilasik
Sa'adatu
(1995),ta yi cikakken sharhi akan wasu waƙoƙi kamar Tabarƙoƙo da Hawainiya da
Sabuwar Nijeriya da kuma Lebura, a cikin waƙoƙin fasahar Aliyu na Aƙilu Aliyu.
A takaice wannan
bincike na da alaƙa da nawa,saboda. ta yi nazari ne a kan Zambo da Habaici
a rubutattun waƙoƙi,kamar yadda nake gudanar da nawa bincikn a kan
rubutattun waƙoƙi. Saboda haka akwai alaƙa a tsakanin
bincikenmu.
Ibrahim
A. (2000) Ya bada tarihin Zamfara ya kawo Zamfarci da bambancin Zamfarci da
daidaitacciyar Hausa. Babu shakka, wannan aiki yana da nasaba da nawa, kuma ya
taimaka wajen ɗora ni a kan hanya,
kancewar aikina ya shafi karin harshen Zamfarci. Kenan wannan nazari na da alaƙa ta kusa da nazarin
da nake gudanawa.
Maharazu
B.A da wasu(2008)A kundinsu na neman digiri na farko a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. A
ciki sun yi bayanin Zamfarci da rabe-raben Zamfarci da gidan Zamfarci, da
sauransu. Wannan aiki yana da alaƙa da nazarin da nake
a kai. Saboda bincikena ya kunshi karin harshen Zamfarci, a cikin waƙoƙin Kabiru kilasik..
Sule
(2011) , ya yi bayani a kan Ɗankwairo da ire-iren waƙoƙinsa, waƙoƙin fada waƙoƙin noma da na jama'a
da waƙoƙin ta'aziya da waƙoƙin siyasa.
Bisa la'akari da cewa
wannan bincike ya ginu ne a kan waƙa, kuma, an taɓo waƙoƙin siyasa inda Kabiru
kilasik ya ƙware.Ya nuna cewa wannan nazari na da alaƙa da nawa, ta fuskoki
da dama.
Muhammad
Y.T (2003)A ƙudinsa na neman digiri na farko, a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Ya bayar da tarihIn Dankurma Gombe da kuma jigogin waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa, Wannan bincike
yana da tasiri da kuma alaƙa da nawa bincike, domin kuwa, a kan
waƙa
aka gudanar da shi.
Sayinna
A.(2003),Ya ba da abubuwan da ake yabon mutum da su, da matsayin yabo a adabin
Hausa da dangantakar yabo da kirari. Kuma ya bada ma'anar Zambo da Habaici da
dalilin da ke sa a yi su. Saboda haka, wannan bincike yana da alaƙa da nawa binciken
saboda a kan waƙa ne aka gudanar da shi.
Saminu
(2006), Ya ba da tarihin waƙoƙin siyasa a ƙasar Hausa, sannan ya
kawo tarihim sani Shu'aibu (Sani Dangiwa), da Haruna Aliyu Ningi (K.K), da Aminu Ibrahim Ɗandago.Ya kawo waƙar "Adon Gaskiya
Baya Ɓata" da Waƙar Tsohon Gwamnan
jihar Zamfara Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi.
Wannan bincike yana
da nasaba da nazarin da nake gudanarwa domin akan waƙa ya yi shi.Kuma ya
taɓo waƙoƙin siyasa,, in da nan
ne nawa binciken ya fi mai da hankali musaman waƙoƙin siyasa na Kabiru
kilasik.
2.2 Bugaggun Littafai
Masana da dama sun
wallafa littafai masu alaƙa da wannan nazari. Daga cikin littafan da suka zo hannu
akwai:
Bunza A.M
(2017), ya yi bayani cikakke wanda zai iya zama jagora ga duk wani mai
gudanar da bincike na neman digin farko da na biyu da mai Phd, kai da ma duk
wani mai gudanar da bincke a fagen ilimi. Ya yi bayani a kan ma’anar bincike da
dabarun bincike da mahimmancin bincike da matsalolin bincike da bitar ayyukan
da suka gabata da sauran fannonin da suka shafi bincike ta fuskar adabi da
al’ada da harshe. Wannan littafi ya zama turba ko in ce ya share man fagen
binkena tare da zama jigo ko fitila mai haska man hanyar gudanar da wannan
nazari. Haƙiƙa Hausawa sun yi gaskiya da suka ce "Tafiya da babba daɗin yaro" wannan littafi ya ba ni gudummuwa sosai wajen
gudanar da wannan aiki.
Bunza A.M (2013), Ya kawo cikakken tarihin
Narambaɗa da iyalansa da
abokansa da Waƙoƙin sa, da iren-iren waƙarsa da sauran
abubuwan da suka shafi rayuwarsa na yau da kullum.Wannan gagarumin littafi ya
haɗa abubuwa da dama
masu muhimmancin gaske ga wannan nazari nawa. Gaskiyar masu iya karin magana da
ke cewa, "Ruwa na ƙasa sai
ga wanda bai tona ba" Haƙaƙi wannan gagarabadon
littafi ya zame mani jagora ga wannan bincike.
Ibrahim Y.Y (1988),
ya yi bayani a kan ɓangarori da dama, a
ciki har da tarihin samuwar rubutattun waƙoƙi.wanda ya taimaka a
wajen gudanar da wannan bincike.
Ɗangambo A. (2007) ,ya
yi cikakken bayani a kan waƙa, ya ba da ma'anar waƙa da hanyoyin nazarin
waƙa
da sauransu.Kuma wannan littafi yana da matuƙar muhimmancin a
wannan bincike.
Sani M.A.Z (1999),ya yi bayanin ilimin furuci da lokutan
Hausa in da ya taɓo ginin jimala, wanda
ginin jimla ya shafi bincikena domin haka wannan littafi yana da alaƙa ta kusa da wannan
nazari. Kuma ya taimaka ƙwarai da gaske.
Gusau
S.M (1996), ya yi rubuta dangane da
tarihin rayuwar makaɗa da mawaƙa guda talatin da uku
(33), haihuwarsu da nasabarsu da asalinsu da ƙurciyarsu da
sana'o'insu da yadda suke tsara waƙoƙisu da falsafarsu da
sauran ayyukkan da suke yi a rayuwarsu ta yau da kullun.Wannan aiki yana ba da
haske dangane da makaɗa, don haka a iya
samun saurin fahimtar darussan da suke kunshe cikin waƙoƙinsu,wanda zai zama
haske a wannan nazari.
Ibrahim
(1983), ya yi bayani a kan makaɗan sarauta da jigoginsu da kuma salon sarrafa harshe.Kuma
ya yi bayani kan makaɗan jama'a a waƙoƙin kasuwanci. Ya yi
bayani a kan Sana'a da makaɗan Maza da sauransu.Saboda haka wannan litafi yana da alaƙa da bincikena.
Dunfawa
(2003),Ya bayar da ma'anar aruli da ƙafiya, kari wato da
Balaraben kari da Bahaushen kari,.Haka kuma ya kawo sauti (zahafi) da gwauron
sauti da tagwan sauti da sakiyar illa da sakiya mai ragi da kuma sautin rabawa.
Sannan ya kawo amsa-amo da amsa-amon gaɓar sauti da babban amsa-amo da karamin
amsa-amo da amsa-amon farawa da amsa-amo mai zaman kansa da kuma amsa-amon
sauti.
Wannan littafi yana
da muhimmanci domin yana nuna mizanin waƙa da masana suka
rubuta masu alaƙa da wannan bincike.Wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da nawa,
domin ya yi cikakken bayani akan amsa-amon ciki da amsa-amon waje, wato babban
amsa-amo da ƙaramin amsa-amo.Wanda duk mai nazarin rubutattun waƙoƙi dole ne ya san su
ya kuma fahimce su, domin yana ɗaya daga cikin abinda ya bambanta rubutattun waƙoƙi da na baka.Bugu da ƙari ya kawo ma’anar
waƙa.
Gusau
S.M (2008),Ya bayyana tarihin Salihu Jankiɗi Sarkin Taushi da waƙoƙinsa. Wannan littafi
yana da muhimmanci ga wannan bincike.Domin ya bayar da ma’anar waƙa da kuma yadda ake
yin nazarin waƙa, duk cewa shi a kan mawaƙin baka ya gudanar da
wannan aiki ni kuma nawa a kan waƙoƙin siyssa na Kabiru
kilasik.
Gusau
S.M (2008) ya bayar da tarhin waƙoƙin baka a ƙasar Hausa yanayinsu
da sigoginsu da suka haɗa da kiɗa na Hausa da kayan
yinsa. Kuma ya binciki makaɗan baka na Hausa da halayyarsu da nau’o'in waƙoƙin baka na Hausa da
kuma turke da ire-irensa a wƙoƙin baka na Hausa.
Wadannan littafai
suna da muhimmanci domin sun tabo wakokin siyasa, muhimmin fagen da nake
gudanar da bincike a kan shi.
Maƙaloli
A ɓangaren Maƙaloli masana da dama
sun yi rubuce-rubuce a kan batutuwa masu alaƙa da wannan nazari.
Don haka za a iya cewa sun bayar da gudummuwa wajen gudanar da wannan bincike.
Dumfawa
da Yahaya (2010), Sun bayyana irin
bijirewa da yaudarar da 'yan siyasa ke wa talakawa.Wannan maƙala a kan 'yan siyasa
aka yi ta,kuma tana da alaƙa da wannan bincike,kasancewar waƙoƙin da nake bincike na
siyasa ne,kuma mawaƙin mafi akasarin waƙoƙinsa duk na siyasa
ne. Kuma 'yan siyasa su ne abokan mu'amalarasa.
Usman
(2011). ya gabatar da wasu turakun waƙoƙin baka na Hausa.
Kamar ilimantarwa da faɗakarwa da wayar da
kai da wa'azantarwa da yabo.Wannan maƙala ta na da nasaba
da wannan bincike domin a waƙoƙin da nake nazari duk
akwai kwatankwacin waɗannan ababe.
Funtua
(2011), ya gabatar da tarihin rayuwar shata da waƙoƙinsa a fagen rayuwar
al’umar Hausawa kamar: kirari da zambo da raya sana’a.Wannan maƙala tana da alaƙa da nawa nazarai
domin a kan waƙa ya gudanar da ita.
Bello
(1976) ,Marubucin ya bayyana cewa kiɗa ya zama jinin ɗan Adam. Bayan haka
ya rarraba kiɗan maza da kiɗan sana’a. Wannan maƙala tana da laƙa da bincikena.Domin
a kan waƙoƙi aka gabatar da ita, kuma ni ma nazari na a kan waƙoƙi ne.
2.2 TARIHIN ZAMFARA A TAƘAICE
Ƙasar Zamfara ta kafu
tun a ƙarni na sha biyar (15 century). Ta kasance a bangaren
Arewancin Nijeriya, A lardin Sakkwato inda
daga baya ta kasance a matsayin jiha. Ta ƙunshi ƙananan hukumomi guda
goma sha huɗu,tare da
hidikwatarta da ke garin Gusau.Ta yi iyaka da Jihar Sakkwato a arewa.A jihar
Katsina kuwa,ta yi iyaka ne ta gabas.Sannan ta yi iyaka da jihar Kaduna a ɓangaren kudu.Daga ƙarshe,ta yi iyaka da
jihar Neja da jihar Kabi ta ɓangaren kudu maso yamma.
A ɓangaren faɗin kasa kuwa, jihar
Zamfara tana da kimanin murabba'in kilomita dubu talatin da takwas da ɗari huɗu da arba'in da
takwas (38,448). Kamar yadda sauran jihohin arewacin Nijeriya suke, ita ma
jihar Zamfara tana da yanayi huɗu a shekara.Akwai yanayin "rani" dana
"hunturu" wanda ke farawa a watan Nuwamba zuwa watan Mayu.Sai kuma
yanayin "kaka" dana "damana" da kan fara daga watan Yuli
zuwa watan Oktoba (wannan bayani, an samo shi daga littafi mai suna (Zamfara As
It Is).
Jihar Zamfara tana da
manyan gulabe guda huɗu, Gulaben su ne:
Gulbin Bunsuru da gulbin ka,da gulbin Zamfara da gulbin Gagare.Haka kuma akwai
manyan tafkuna guda biyu.
Tafkunan su ne;
tafkin gulbin kakale da tafkin Bakura. Baya ga waɗannan manyan tafkuna, akwai kananan
tafkuna irin su tafkin saru,a cikin ƙaramar hukumar
Gummi,da tafkin Jena a ƙaramar hukumar Zurmi.A ƙaramar hukumar mulki
ta Maradun akwai babban dam wanda ake kira dam ɗin Bakalori.
Ana hasashen cewa
jihar Zamfara tana da yawan mutane kusan miliyon biyu da dubu ɗari biyu ta talatin
da ɗaya da ɗari huɗu da biyu
(2.231,402).Amma a ƙididdigar da aka sake yi a shekarar alif dubu biyu da
shida (2006 21-03) lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Obasanjo. Sakamakon ƙididdigar ya nuna
cewa jihar Zamfara na da kimanin mutane million uku da dubu ɗari biyu da hamsin da
tara da ɗari takwas da arba’in
das hid, (3,259,846).
2.3 ZAMFARCI
Kafin a cigaba da
bayani game da Zamfarci, yana da kyau in ƙaci a kan harshe, da
karin harshe. Domin Zamfarci karin harshe ne a cikin kare-karen harsunan ƙasar Hausa.
Harshe wata tsoka ce
da ke cikin bakunanmu wadda muke magana, muke cin abinci, muke shan ruwa kuma
muke haɗiyar yawu da shi.
Masu yin nazarin
harshe sun yi ƙoƙarin ba da ma’anarsa a ilmance sun bi hanyoyi daban-daban
domin su fahimtar da dalibansu wannan ma’anar amma ga baki ɗayansu sun yi ittifaƙi a kan wasu abubuwa
kamar haka: - Harshe suna ne gama-gari mai nufin hanyar sadarwa ɗaya cikin hanyoyi uku
na sadarwa. Biyun su ne: Rubutu da Ishara. ( Yakubu S.Z. 2014-P 115).
Masana da dama sun
bada ma'anar harahe. Daga cikinsu akwai:
Fagge
(2001), ya ce, "Harshe wata hanyar sadarwa ce da ɗan Adam yake amfani
da shi mai ma’ana wanda kuma yake haka ne a kowacce al’umma da ke zaune a doron
ƙasa
take fahimtar abubuwan da ke ƙunshe a zukatan Jama’a kamar tunani,
ra’ayi, hikima, sha’awa da sauransu”.
Ladan
(1996), ya ce: "Harshe abu ne da ya ƙunshi alamomi da ɗan Adam yake amfani
da su wajen bayyana tunaninsa, ya cigaba da cewa alamomin harshe sun ƙunshi sautukan da ake
furtawa a jajjere, kuma ake amfani da su cikin tsari"
Azare
(2011), ya ce:” Harshe tsararriyar hanya ce da mutane ke amfani da ita wajen
isar da saƙon da yake zukatansu ko tunaninsu, watau mai kyau ko
maras kyau, na farin ciki, ko na nuna damuwa ta hanyar furuci. Allah (SWT) ya
halicci ɗan adam tare da
harshe ya halicce shi, tun lokacin Annabi Adam(AS) tare da Hauwa’u, Allah (SWT)
ya sanar da Annabi Adam (AS) dukkan komai-da–komai harma da harasa da za’ayi
magana da su.( Ƙur’ani Sura Baƙara,Aya Ta 31)
A taƙaice za mu iya kiran
harshe da furuci, ko sadarwa, ko kuma, hanyar sadarwa a tsaƙanin al'umma.
Shi kuwa, karin
harshe yana nufin bambance-bambancen da ake samu tsakanin masu magana da harshe.Ta
sanadiyar bambancin wuraren zama, ko nisantar juna.Ga abin da masana suka ce
game da karin harshe.
Amfani
(1993), cewa ya yi, "Karin harshe bambanci ne da ake samu ta fuskar
kalmomi da furuci da kuma sadarwa.Karin harshe yakan faru saboda dalilai:
Saboda yankuna da ake samu tsaƙanin al'umma masu amfani da harshe
guda, kuma domin bambancim muhalli ga mutanen da ke amfani da harshe
guda".
Yakasai
(1998), ya bayyana cewa, " Karin harshe na nufin yadda wani gungun al'umma
ke maganaa cikin harshe guda wanda ke da alaƙa da tarihin al'umma da ke magana da shi".
Trudgil
(1974-17), ya ce " Karin harshe na nufin bambancin da ake samu a cikin
harshe tsakanin kalmomi nahawu da kuma furuci".
Neil
Skinner (1977:8) ya nuna cewa, "Karin harshe wani bambanci ne da ake samu
a cikin harshe, sai dai baya nuna cewa wani harshe ne na daban".
Shi
kuma Kamus na Encyclopedia (uolume 4.16 Edition), ga abin da ya ce, "Karin
harshe wani bambanci ne da ake samu a cikin harshe,Wanda wani bangare na mutane
da suke amfani da shi, bambancin ya shafi kalmomi da nahawu da kuma furuci
wanda hakan ya bambanta shi da wani karin harshe na wannan harshe".
karin harshe shi ne
ya bambanta sauran harsuna wajen tsarin sauti, da fadar kalmomi da kuma kirar jimla. Wato irin waɗannan bambance-bambancen
suna da nasaba ne dangane da irin yanayin wurin zama da zamantakewa da kuma
abubuwa da suka shafi rayuwa.
Zamfarci yana daya
daga cikin karin harsunan da ake magana
da su a ƙasar Hausa. Sama da mutum miliyon biyu ne ke amfani da
harshen Zamfarci.Kamar sauran kare-karen harshen Hausa, Zamfarci ya banbanta ta
hanyar sigogi da suka shafi ginin jimla
da gundarin sauti da ginin kalma da ma'ana.
Ta hanyar waɗannan ne za mu iya
fahimtar Zamfarci, a kan sauye-sauyen da ake samu tsaƙanin baƙi da baƙi ko wasali da wasali
daga daidaitacciyar Hausa zuwa Zamfarci. Saboda haka yana da kyau mu san cewa
Zamfarci yana ɗaya daga cikin
kare-karen harshen Hausar yamma,yayin da sauran kare-karen suka haɗa da kabanci da
Gobiranci da Sakkwatanci da kurfayanci da Arewanci.
Dukkaninsu karin harsuna ne masu zaman kansu,kuma suna
da alaƙa da juna ta hanyar furuci.
Kasancewar ƙasar Zamfara ta yi
iyaka da wasu jihohin arewacin Nijeriya,ya haddasa samuwar rabe-raben Zamfarci.
Daga wani yanki na wata ƙaramar Hukuma zuwa wata.Saboda haka za a duba wasu daga
waɗannan ƙananan hukumomi.
Daidaitacciyar
Hausa K/ ANKA
Baci Kwana
Gyaɗa Gujjiya
Aure Amre
Kananzir. Barahuni
Kookoo. Kunuu
ƙyaure. Gambu
Tsumma. Ragga
Daidaitaciiyar
Hausa K/ BAKURA
Zogala ‘Yam
Makka
Rantsattse
Rantcattce
Ritsimi Rintcimi
Tseeree Tceeree
Tsimi Tcimi
Waatse Waatce
Daidaitacciyar Hausa
K/ BUKKUYUM
Feɗe Heɗe
Feƙe Heƙe
Feesa Heesa
Leefe Lehe
Refe Rehe
Shafew Shahe
Daidaitacciyar Hausa K/BUNGUƊU
Saɓa Swaɓa
Safa Swahwa
Fanti Hwaranti
Mtsi Matci
Tsiri Tciri
Kintsi Kintci
Daidaitacciyar Hausa K/KAURA
Kuli Bakuru
Riɗi Kantu
Awara Shala
Ganwo Tarɗi
Bayi Yauce
Zogala ‘Yam
makka
Daidaitacciyar Hausa K/ MARU
Ƙuli Guru
ko ƙuli-ƙuli
Awara Ƙwai da ƙwai ko awara
Bayi Makewayi
Kananzir Barahuni
Cingam Bazuka
Daidaitacciyar Hausa K/ MAFARA
Zauna Zamna
Tauna Tamna
Shuka Shubka
Sauna Samna
Fiɗa Hiɗa
Fari Hwara
Daidaitacciyar
Hausa K/ SHINKAFI
Taushi
Tabshi
Shuka Shikka
Farce Hwarce
Faci Hwaci
Faɗa Hwaɗa
Faɗuwa Hwaɗuwa
Faifai Hwaihwai
Fansa Hwansa
Daidaitacciyar
Hausa K/ ZURMI
Lafiya Lhiya
Auki Abki
Saurayi Samrayi
Tunki Tumkiya
Farce Hwarce
Fari Hwari
Farmaki Hwarmaki
Daidaitacciyar Hausa K/B.MAGAJI
Fashi Hwashi
Hantsi Hantci
Kafaɗa Kahwaɗa
Fira Hira
Fifiko Hihiko
Littafi Littahi
Safiya sahiya
Rufe Ruhe
Kwatsewa. Kwatcewa.
Wannan shi ne
takaitaccen bayanin Zamfarci da misalan Zamfarci kamar yadda aka gani.
2.4 MA’ANAR WAƘA
Idan ka hadu da mutum
a kasuwa ko a bakin titi ko a wani wuri na gargajiya,ka tambaye shi abin da ake
nufi da waka da Hausa, abin da zai iya fada maka shi ne,jan magana ko nanata
zance kan wani abu da ake son yi.Shi ya sa za ka ji mutum yana cewa kullun ina
wakar zan zo mu gaisa amma abun ya faskara.Kenan wakar abu na nufin ka yi ta
kururuta batu ko jan batu a zuci na tsawon lokaci amma ba aikatawa
Waka wani azanci ne
da ake ta hanyar zaben kalmomi wadanda ke kunshe da hikimomi da ake rubutawa ko
a rera da fatar baki cikin sautin murya na musamman.
Masana da dama sun
bayar da ma'anar waƙa.Kmar haka:
Yahaya (1985)
ya ce, “ waƙa ta ƙunsh ƙololuwar hikima da
tunani ɗan Adam ta yin amfani
da ƙwayoyin
muryoyi aunannu cikin kalmomi zaɓaɓɓu wanda ake jeran ta su cikin tsari fitacce,ƙayyadadde,rababbe ta
yadda za su fa’idantar, wanda ake rerawa a kan Karin murya ƙayyadadde kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na
musamman.
Yahaya
(1997), cewa ya yi "waka tsararriyar maganar hikima ce da ta kunshi sako
cikin zababbun kalmomi da aka auna domin maganar ta reru,ba furtawa kurum
ba".
Dangambo
(1982) ya bayyana cewa " waka wani sako ne da aka gina kan tsararriyar
ka'ida ta baiti ko dango da ake rerawa kan kari ko amsa-amo; da sauran da
sauran ka'idoji da suka shafi daidaita kalmomin"
Muhammad
(1980), cewa ya yi "waka tana zuwa ne ta sigar gunduwoyin zantuka wadanda
ake kira diyoyi kuma ake rerawa da wani irn sautin murya na musamman".
Gusau
S.M (1993),cewa ya yi " waka magana ce ta fasaha a cure a wuri daya a
cikin tsari na musamman"
Zaruk
da wasu (2010), sun ce: “Waƙa magana ce cikin sarrafaffiyar murya
wadda ake rangwanɗawa bisa wani tsari”
Tsoho
(1983), ya ce “Waƙa ba tare da banbanta rubutatta ko ta baka ba,salo ne na
tsara kalmomi yadda za su ba da sauti mai rauji ko daɗi da kuma ma’ana
yadda za ta gamsar da yawancin masu saurarenta”
Hadiza
(2007), a nata nazarin ta yi ƙoƙarin ba da ma’anar waƙa da cewa”Waƙa zance ne
sarrafaffe,ayyananne wanda da shi ake bin hawa da saukar murya,mai zuwa
gunduwoyi layuka da ake rerawa bisa wani daidaitaccen tsari,wani lokaci tare da
kiɗa.
Saboda
haka,za mu iya cewa waƙa wani azanci ne da ake shiryawa ta hanyar zaben kalmomi
waɗanda ke ƙunshe da hikimomi da
ake rerawa da fatar baki ko a rubuta a cikin sautin murya na musamman, a kuma
rerata a rubuce.
2.5 WAƘAR BAKA
Waƙar baka abu ce mai daɗaɗɗen tarihi a rayuwar
al’umma, domin idan aka yi la’akari dangane da nazarce-nazarce da malamai, da
manazarta da dama suka yi,za a tarar da mabanbabntan ra’ayoyi a kan asalin ita
kanta wakar.Haƙiƙi waƙoƙin baka suna da asali
kuma sun sami karɓuwa a zukatan
al’ummar da ake amfani da harshensu wajen a gudanar da ita,kasancewar suna da
muhimmanci wajen gudanar da ita,kasancewar tana da muhmmanci a wajen bayyana
halin
rayuwar al’ummar da
kumabayyana hikimominsu.Waƙoƙin baka suna da
tasiri a cikin zukatan al’umma ga mai ilimi ko maras ilimi.Wani lokaci har ma
wanda baya jin harshen da ake amfani da shi,yakan yi sha’awar muryar waƙoƙin.
Masana da dama sun yi
tsokaci wajen ba da ma’anar waƙar baka dangane da fahimtarsu.Waɗannan masana da
manazarta waƙoƙi sun haɗa da:
Gusau
(2003), da (2014), Umar (1987), da Yahaya (1981), da Ɗangambo (1982), da
Malumfashi (2011), da sauransu.
Ɗagambo (1982), ya
bayyan waƙar baka da cewa,”Wani furuci ne a cikin azanci da ake
aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi a cikin wani tsari ko ƙa’ida,da kuma yin
amfani da dabara ko salon armashi”.
Umar
(1987), ya ce,” Wakar baka ko waƙa, ita ce nau’in
gunduwoyin zance da ake kira ƙayyadajje,kuma ake rerawa da wani irin
sautukan murya na musamman”.
Tanko (2010), ya
bayyana cewa, “Waƙar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci,da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da
daidaitawa a rera cikin sautin murya,da amsa-amo, kari da kiɗa da kuma amshi”
Sa’id
(1981), ya faɗi cewa, “Waƙar baka ita ce wadda
ake rerawa dan jin daɗi a ajiye ta aka a
kuma yaɗa ta a baka”
Yahaya
(1979),cewa ya yi,”waƙar baka tta ƙunshi wasu abubuwa
muhimmai kamar zaɓen kalmomi da kuma
sarrafa su cikin hawa da saukar murya tare da hikima,”
Yahaya
(1997), ya bayyan ceawa,”Wakar baka wata tsararriyar maganar hikima ce wadda
aka tsara da wasu zaɓaɓɓun kalmomi masu
ma’ana kuma aka rera ba faɗa kurum ba, wadda ake iya
amfani da kiɗa da nufin isar da
wani saƙo”.
Yakawada (1ss983), ya
ce “Waƙa ba tare da banbanta rubutatta ko tabaka ba,salo ne na
tsara kalmomi yadda za su ba da sauti mai rauji ko daɗi “.
Bisa la’akari da maganganum magabata. Za mu
iya cewa,.waƙar baka wata aba ce da ake shiryawa da ka a adana a ka a
kuma rera da fatar baki,a cikin wani irin sauyin murya na musamman. Ana ganin
cewa mata su suka fara waƙar baka.Irin waƙoƙin reno,waƙoƙin daɓe,waƙoƙin biki.da sauransau.
2.6 SAMUWAR RUBUTACCIYAR WAƘA
Yanayin samuwar
rubutattun waƙoƙi a ƙasar Hausa,za mu iya raba su zuwa loƙuta kamar aji huɗu,na farko kafin
zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa, na biyu tun daga zuwan
addinin musulunci ƙasar Hausa har ya zuwa ƙarni na goma sha
shida zuwa ƙarni na sha takwas (16-18),na uku ƙarni na sha tara da ƙarni na asShirin.
Abin da masana suka
fi raja'a a kai shi be kafin zuwan addinin musulunci ƙasar Hausa, Hausawa
ba su da ilimin Larabci,saboda haka ba su iya rubutu ko karatu ba.Wannan shi ya
sa ake ganin a wancan lokaci ba su da wata rubutacciyar waƙa.Waƙar da aka tabbatar
akwai ta ita ce waƙar baka ta farko ta farauta.Sannan ta ibadar gargajiya
kamar ta kiraye-kirayen bori da sauransu.
Duk da haka wasu
masana sun bayyana cewa wata ƙila lokaci mai tsawo da ya wuce
hausawa sun taɓa cin karo da rubutu.
Suka kuma bayyana cewa akwai tarihin wata rijiya a kano mai suna
"Akwa" wadda ake ganin cewa ita wannan kalmar ta "Akwa" na
nufin ruwa kuma an bayyana cewa lokacin da daular waɗannan mutanen da haɓaka sun shigo ƙasar Hausa.Haka ma an
ce a wajen ajiye kayan tarihi na London akwai wani dutse da aka yi ajamin Hausa
a kansa da harshen Yunananci, wannan rubutun ma dai ya daɗe sosai.
Haka kuma akwai waɗansu zane-zane da aka
samu a kan wasu duwatsu a Birnin Kudu an ce su ma daɗaɗɗu ne ƙwarai.Wannnan ya nuna
muna cewa ana kyautata zaton cewa Hausawa sun taɓa cin karo da 'yan rubuce-rubucen da
ba su taka kara suka karya ba,abin da ke nuni da cewa ga dukkan alamu ba a taɓa samun wata
tsararriyar rubutacciyar waƙa ba.
A cikin ƙarni na goma sha
bakwai zuwa na sha takwas (17-18),an samu ci gaba da yaɗuwar addinin
musulunci da samuwar malamai waɗanda suka yi suna da daukaka a tannin addinin musulunci.
A wannan ƙarni na goma sha bakwai aka samu wali Ɗanmarina da wali Ɗanmasani. Waɗannan malamai
dukkansu sun yi rubuce-rubuce da damar gaske.Misali, wali Ɗanmarina ya rubuta waƙoƙi da dama waɗanda suka haɗa da: Daliyya da
Nuniya da waƙar Sharun Tana da sauransu.
Wali Ɗanmasani ya rubuta waƙoƙi irin su sharhen
Ishimawi da Ishiriniya da Alfazazi da sauransu.
Haka kuma akwai malam
Muhammad na Birnin Gwari da ya rubuta waƙoƙi kamar haka:
Ma'akuba da Gwahiratu da Bilahirarmu da sauransu. Sai kuma malam Shitu dan Abdurra'uf
Wanda ya rubuta waƙoƙi kamar haka: Fassarar Arshada da waƙar Wawiya da jirmiya
(waƙar
tuba) da sauransu.
Duk waƙoƙin da suka yi suna
magana ce a kan madahu, da gargaɗi,da wa'azi da koyar da shika-shikan addini.
A ƙarni na goma sha tara
kuwa,Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da almajiransa da yaransa sun rubuta waƙoƙi da dama a cikin
harshen Larabci da Fillanci da Hausa da nufin yin kira ga jama'arsu da
shuwagabanni da su kula da harkokin addini su kuma gyara halayyarsu ta fuskar
ma'amala da jama'a.
A ƙarin na goma sha tara
lokacin da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da almajiransa suka rayu,lokaci ne da mutane
suka tashi tsaye wajen neman ilimin addinin musulunci. Saboda tsayuwarsu ne ga
neman ilimin addini aka samu jihadin daukaka addinin musulunci da yaɗa shi a ƙasar Hausa. Musulunci
a wannan lokaci ya yi ƙarfi don haka duk waƙoƙin da aka rubuta a
zamanin suna Magana ne a kan addinin musulunci tsantsa.Kuma duk wata waƙa da ba ta addinin
musulunci ba ce ana daukar ta a matsayin "Hululu".Waƙoƙin da aka rubuta a ƙarni na goma sha tara
sun shafi wa'azi da gargaɗi da furu'a da
tauhidi da sauransu.
Rubutattun waƙoƙin Hausa sun bunƙasa sosai a ƙarin na sha tara,kuma
da yake manufar rubuce-rubucen ita ce ,su yi wa'azi da yabon Ubangiji da begen
Annabi (s a w) da tauhidi da fikihu,babau mamaki idan marubutan sun yi amfani
da dukkan abubuwan da suka shafi addini a cikin rubuce-rubucensu.
2.7 WAƘOƘIN SIYASA
A ma'anar kalmar
Siyasa ta kurkusa tana nufin hanya ko dabara da ake amfani da ita don a cimma
wani mataki na shugabancin al'uma.
A tsarin siyasa akwai
siyasar addini da siyasar kishin kai da siyasar kishin ƙasa da siyasar
jam'iyya. (M.Garba Gusau IJMB Note).
A ƙarƙashin siyasar
jam'iyya za a sami shuwagabannin jam'iyya da 'yan takara,akwai muƙamai da gurabu na
mulkin jama'a daban-daban. Sannan za a yi zaɓe a rantsar da waɗanda suka sami nasara
su cigaba da gudanar da mulki.
Makadan Hausa sukan
shirya waƙoƙi a kan ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa da aka bayyana a baya da suka
shafi al'amuran siyasa. Irin waɗannan waƙoƙin suna ƙarƙashin jigon siyasa
ne.Waƙoƙi ne da ake yin su da nufin bayyana manyan saƙoni na siyasa. Kamar;
bayyana manufofin jam'iyya ko yi wa jam'iyya kamfen ko wayar da kai kan zaɓe ko yabon 'yan
siyasa da sauransu.
Alhaji Aminu Ibrahim ɗan Dago ya yi wa
Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko waƙa a shekara ta dubu
biyu da bakwai (2007), wanda wannan waƙa ita ce ta tallata
Aliyu har Allah ya kai shi ga cin nasara.Waƙar ita ce:
" Sakkwatawa
suna bayanka
Sarkin yamma Alla saka
ma"
( Dan dago waƙa magatakarda)
Bayan waɗannan akwai, Dauda
Adamu Kahutu rarara, wanda shi ma mawaƙin siyasa ne ya yi waƙoƙi da dama.daga cikin
wakonsa akwai:
"Zuwan
mai malfa kano"
"Mai
malfa ya karaya,
Yace
maganar zaɓe a ɗaga,
A ɗaga ko kar a ɗaga,
P.D.P
sai mun kai ta ƙasa"
ƊRarara
wakar mai malfaƙ
"Masu
gudu su gudu,
Bana
dai janaral shi ne a sama,
Mun
hallaka P.D.P,
Bana
A.P.C ita ce da ƙasa,
Mai
malfa fara shiri,
Bana za
ka fice Bila,
Da
gudun gaggawa".
Rarara
(Waƙar
murnar cin zaɓen Buhari)
"
Ga Buhari ya dawo"
"Cuta
ba mutuwa ba
(Waƙoƙin Dauda rarara)
Haka shi ma Alhaji
Kabiru Yahaya Kilasik a matsayinsa na mawaƙin siyasa, ya yi waƙoƙi masu ɗimbin yawa na
siyasa.Daga cikin waƙoƙinsa akwai:
"Walin
Kurya na Gwabna samunka da moriya,
Mamuda
mijin Saratu ma nai maka godiya,
Angon
Mariya da Aisha barka da ɗawainiya"
(Kabiru
Kilasik waƙar Walin Kurya)
"Baba
dawo baba dawo.
Dallatu
ɗan Aliyu kazo,
Mamuda
ka dawo muna jiran ka,
Ka
cincinta da mulki Zamfara,
Dan ba
ka saba da yaudara ba."
(
Kabiru Kilasik wakar MAS)
"
Ubangiji shi yay yi Nijeriya,
Yay yi
Zamfara tare da mu,
Ubanginmu
ka yarda da mu,
Da
Shehinmu Gwabna tare da mu,
Jarma
Uranti yake maka murna,
Shatima
kayi mulikinka da lafiya."
(Kabiru
Kilasik wakar Shehi A.A.Yari)
"Sakkwato
masha Allahu,
Kilasik
barakallahu,
Albishirin
da najji,
Shi zanI Sanar wa da masu kaunarmu,
Sarikin
yamma zai koma,
Da
yarda Ubangiji Allah."
(Kabiru
Kilasik waƙar sarkin yamma)
"A.N.P.P
ba ni da kuwa,
Kuma
kun sa ba ku da niya,
Kar muka
kallon juna,
Kabiru
nai maku kallon mai bisa ruwa"
(
Kabiru Kilasik waƙar Ciki da gaskiya)
"Nijeriya
ku yi mani murna,
Dan
gaba ta samu garan,
Nijeriya
muna da rabo,
Kuma
Nijar mun samu rabo,
Shugaban
ƙasa
gare muna Nijar,
S.S.G
yah haɗa mu da shi,
Mahammadu
Yusuf madoga,
Na
Aliyu magatakarda uba."
( Kabiru Kilasik
wakar Shugaban Kasar Nijar Muhammadu Yusuf)
"Zamfara mun
yarda da Tantabara uwar alkawari,
Saratu fes ledi
innar-wuro madalla da ke,
Kin wuce matan
Gwabnonin Arewa,
Ko sun ƙi su bi"
(Kilasik wakar
uwar-gidan mamuda Saratu)
Waɗannan waƙoƙi da aka kawo a
matsayin misalai, duk waƙoƙi ne na siyasa. Kuma ana yin su ne domin yabon 'yan
takara da masoya da kuma yin zambo da habaici da gugar-zana ga abokan adawa.
2.8 MAWAƘAN HAUSA
A ZAMFARA
A duk faɗin ƙasar Hausa, babu wani
yanki da Allah ya albarkata da haziƙan makaɗa kuma da
shahararrun, mawaƙa waɗanda suka bunƙasa adabin Hausa a
duniya kamar yankin Zamfara.
Maƙadan su ne:
Alhaji
Kabiru Yahaya Kilasik
- Ɗan Ƙwairo
- Salihu
jan Kiɗi
- Inka
Bakura
- Sani
Sabulu
- Gurso
- Musa
Ɗanbiri Bakura
- Makaɗa Dungum Bakura
- Abdun
Rini
- Amadu
Mailauni Bakura
- Amadu
Mainakada Bakura
- Siddi
Bakura
- Yahaya
Sahunu
- Ɗandodo Alu
- Sa'idu
Faru
- Malamin
Waƙa
- Bawa
Gabci
- Daɗi Dolen Moriki
- Hassan
Wayam
- Muhammad
Sarkin Taushin Katsina
- Ɗangiwa Zuru
- Ɗanzaki Maradun
- Ɗanbawa kaura
- Ɗankurma Maru
- Salihu
Jankiɗi Rawayya
- Mani
mai kiɗa
- Amali
sububu
- Kassu
Zurmi
- Mamman
Nata ukka
- Sagalo
mawaɗin kokuwa
- Sani
Kaka Dawa
- Ɗankurji
- Ɗanwasa Gummi
- Yahuza
Ɗangiwa
- Kabiru
Birni Magaji
- Sani
Maikuntugi na Gusau
Wanda an yi amanna
cewa marigayi Mamman Shata yakan sa a zo masa da shi su yi fira domin ya samu
kalmomin da zai yi amfani da su a tasa waƙar.
Wasu daga cikin wamaƙan Zamfara
kenan.Akwai wasu makaɗan da dama wadanda ba
a ambaci sunayensu ba.
2.9 KAMMALAWA
Dangane da bita ko
waiwaye a kan ayyukan da suka gabata, wannan waiye ya zama shi ne tubalin ginin
wannan aiki nawa, domin ya yi mani ƙarin haske wajen
fahimtar yadda wannan aiki nawa zai kasance. Wannan ne ma ya sa na dawo cikin
hayyacina tare da fahimtar inda wannan bincike ya sanya gaba,duk da dai cewa
wasu manazartan sun gudanar da nasu binciken ne a kan tasirin waƙoƙin baka na Hausa wasu
kuma sun kalli salon sarrafa harshe ya yin da wasu suka yi tsokaci kan jigon
wasu waƙoƙi, wanda hakan ya nuna cewa duk suna da alaƙa da nawa aikin.
Haka kuma wasu sun yi
nazari ne kan rubutattun waƙoƙin wasu mawaƙa.
Bugu da ƙari,wannan aiki zai
gudana ne a kan nazarin wasu kalmomin Zamfarci a cikin wasu waƙoƙin Kabiru Yahaya
Kilasik.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.