Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Sarautar Fawa
A Garin Gusau (2)
NA
ABDULRASHID S. PAWA
Phone Number: 08132326047
Email: abdulrashidspawa@gmail.com
BABI NA ƊAYA
GABATARWA
1.0 GABATARWA
Bincike na ɗaya daga
cikin muhimman abubuwa da suka shafi tafiyar da rayuwa, babu wani abu da za a
samo, ko a gano sabo ba tare da bincike ba. Bincike shi ne mataki na farko da
ake bi domin samo, ko fito da wani abu sabo wanda ba’a san shi ba, kuma ake son
a san shi a kuma samar da shi, domin a yi amfani da shi ta wasu hanyoyi
daban-daban na rayuwa.
Wannan babi
zai yi magana a kan wasu matakai daya da ce mai bincike ya bi domin gudanar da
kowane irin bincike da suka haɗa da; dalilan gudanar da bincike,
farfajiyar bincike, hanyoyin gudanar da bincike, muhimmancin bincike matsalolin
bincike da kuma tambayoyin bincike.
1.1 DALILAN
GUDANAR DA BINCIKE
Babu wani
bincike da za a yi ba tare da wani ƙwaƙƙwaran
dalili ba, domin kuwa ana yin bincike ne don a gano wani abu sabo a fito da shi
domin a amfana da shi, daga cikin dalilan da ya sa aka gudanar da wannan
bincike ya haɗa da:
-
Domin samun takardar shaidar kammala karatun
digiri na ɗaya (B.A),
domin samun damar cigaba da karatu na gaba.
-
Domin zurfafa bincike don samun bayanai a kan
sarautar Fawa, domin dalibai masu nazari a kan harshen Hausa su amfana da shi.
-
Domin bayani a kan irin gudummawar da
sarautar fawa ke bayarwa.
-
Domin fito da kyawawan al’adun da ke ƙunshe
a cikin sarautar fawa.
-
Domin bayani akan taƙaitaccen
tarihin sarautar fawa. Domin bayani a kan takaitaccen tarihin garin Gusau tare
da bayyana ire-iren sana’o’insu.
-
Domin bayani akan ire-iren sarautun gargajiya
da muke da su, domin a san da irin gudummawar da suke bayarwa.
-
Domin bincike a kan ire-iren sarautu, sana’ar
fawa, da kuma bukukuwansu.
-
Domin bincike a kan duk wani abu da ya shafi
sarautar fawa.
-
Domin bayani a kan jagoranci da sarakunan
fawa suke yi ga jama’arsu wato rundawa.
-
1.2
FARFAJIYAR BINCIKE
Wannan
bincike da za a gudanar ya taƙaita ne a
cikin garin Gusau, ma’ana duk wani bincike da za’a yi za a yi shi ne a cikin
garin Gusau, farfajiyar bincike za ta taƙaita ne a
masarautar Sarkin fawa da kuma duk wasu ɓangarori da suka
shafi sarautar fawa da suka haɗa da.
Masu riƙe
da sarautun fawa, Makaɗan Fawa, Kara da ke garin Gusau, Kwata da ke
garin Gusau, masu sana’ar fawa, tsofaffin masarautun fawa, wurarenda ake
gudanar da duk wasu harkokin fawa, gidan Sarkin Zango, gidan Wakilin Fawa,
gidan Ajiyan Fawa da duk wasu abubuwa da suka shafi sarautar fawa. Haka kuma
farfajiyar wannan bincike za ta taƙaita a cikin
Kundaye, Jaridu da kuma bugaggun littattafai da suke da alaƙa
da wannan bincike.
1.3 HANYOYIN
GUDANAR DA BINCIKE
Ko wane
bincike yana da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da shi, daga cikin hanyoyin da
aka bi sun haɗa da. Bincike
a cikin kundaye, Jaridu da kuma bugaggun littattafai da suka haɗa da.
Gusau ta
Malam Sambo, Mai Dubun Nasara, Bukukuwan Hausawa, Rayuwar Hausawa, Gusau ta
Malan Sambo Sabon Bugu, Gadon Feɗe Al’ada, Dabarun Bincike, Zaman Mutun
da Sana’arsa, Darussan Hausa 1,2,3. Haka kuma an yi bincike a cikin Kundaye da
suke haɗa da Mustapha
Sa’idu (2013) da Hassana Abubakar Tunau (2003). Ɓangaren
Jaridu kuma an duba Jaridar Leadership Hausa (2019), da kuma Jaridar Aminiya
(2019). Bayan haka wannan bincike ya bi wasu hanyoyi, domin gudanar da shi da
suka haɗa da:
Takardun
Sarkin Fawa Bawa Gusau waɗanda suke ɗauke da
bayanai a kan sarautar fawa da tattaunawa da mutane, akwai tattaunawar da aka
yi da mutane da suke da alaƙa da sarautar
fawa da suka haɗa da. Sarkin
Fawa Alhaji Shehu Malami, masu riƙe da sarautun
fawa kamar Wakilin Fawa, Ajiyan Fawa, Sarkin Zango, Makaɗan Fawa,
tsofaffin mahauta da kuma rundawa masu sana’ar fawa.
Ta ɓangaren
ziyarori sun haɗa da: Ziyara
gidan Sarkin Fawa tsoho da ziyara zuwa Kar da kwata da ZACAS da FCET da kuma
masarautar Gusau. Waɗannan sune hanyoyin da aka bi wajen gudanar
da wannan bincike.
1.4
MUHIMMANCIN BINCIKE
Ba wani abu
da za a ɗauki lokaci
ana zurfafa bincike a kanshi ya zama ba mai muhimmanci ba, domin ana bincike ga
wani abu mai muhimmanci da za a amfana da shi.
Muhimmancin
bincike a fili yake, domin duk wani abu da aka binciko sabo aka ganshi aka
sanshi aka jishi ko, kuma aka fahimce shi aka yi amfani da shi to wannan
bincike ya zama mai muhimmanci.
Muhimmancin
bincike ya zama tamkar hantsi leƙa gidan kowa
domin duk abun da ya shige ma mutum duhu daga baya ya yi bincike a kanshi ya
fahim ce shi wanda da can bai fahimce shi ba to wannan bincike ya zama mai
muhimmanci a gare shi, musamman ɗalibai masu nazari a kan fannoni na
fasaha da ilimi, da kuma nazarin harshen Hausa.
Muhimmancin bincike
shi ne bayar da wata gudummawa a fagen ilimi ta hanyar gano ko samo wani abu
sabo domin a amfana da shi.
1.5
MATSALOLIN BINCIKE
Duk wani abu
da za a yi bincike akan shi ba zai rasa wasu matsaloli da aka fuskanta ba a
lokacin da ake gudanar da shi. Matsalolin da ake fuskanta sun haɗa da. Rashin
samun wadatattun littattafai da ke da alaƙa da bincike.
Saɓa lokacin da
za a tattauna da mutane, wasu mutanen suna saɓa lokacin da
suka bayar domin tattaunawa da su.
Bincike a kan
abun da bai shafi aikin mutun ba, wani lokacin mutun kan zurfafa bincike a kan
wani abu daga baya ya fahimci baya da alaƙa da wannan
bincike. Rashin isassun kuɗi, domin cigaba da gudanar da bincike,
ita ma babbar matsala ce, domin kusan duk wani abu da za a yi sai anyi amfani
da kuɗi.
Ganawa da mai
duba bincike, rashin samun ganin wanda yake duba aikin bincike ita ma babbar
matsala ce, domin a kan ɗauki tsawon lokaci ba a kammala
bincike ba.
1.6
TAMBAYOYIN BINCIKE
Tambayoyin
bincike sun ƙunshi duk wasu abubuwa da suke da alaƙa
da bincike, tambayoyi sun haɗa da;
Taƙaitaccen
tarihin sarautar fawa da sarautunta da al’adun sarautar fawa da sauransu. Akwai
tambayoyin bincike da aka tattauna da mutane, daga cikin su akwai tambayar suna
da shekaru da sana’a da kuma mazaunin wanda aka tattauna da shi. Haka kuma
akwai wasu tambayoyin bincike da suka haɗa da.
Taƙaitaccen
tarihin sarautar fawa a garin Gusau da ma’anar sarautar fawa da sarautun da ke ƙarƙashin
sarautar fawa da masu tsarin sarautar fawa da hanyoyin da ake bi wajen zaɓen Sarkin
Fawa da masu zaɓen Sarkin
Fawa da gudummawar da sarautar fawa ke bayarwa da magungunan da sarautar fawa
ke samarwa da shugabancin Sarkin Fawa da al’adun sarautar fawa da ir-iren
al’adun sarautar fawa da Makaɗan Fawa da kuma sarakunan fawa a garin
Gusau. Waɗannan sune
tambayoyin da suka shafi wannan binciken da za a yi.
1.7 KAMMALAWA
Wannan babi
ya yi magana a kan wasu hanyoyi da ake bi domin shirya bincike sun haɗa da; dalilan
gudanar da bincike, farfajiyar bincike, hanyoyin gudanar da bincike da kuma
tambayoyi yin bincike, waɗannan su ne abubuwa masu muhimmanci
domin gudanar da kowane irin bincike.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.