Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Sarautar Fawa
A Garin Gusau (3)
NA
ABDULRASHID S. PAWA
Phone Number: 08132326047
Email: abdulrashidspawa@gmail.com
BABI NA BIYU
WAIWAYE A KAN
AYYUKAN DA SUKA GABATA
”RUWA NA ƘASA
SAI GA WANDA BAI TONA BA
2.0 GABATARWA
Wannan babi
zai yi magana ne akan wasu ayyukan da suka gabata, domin an ce waiwaye adon
tafiya, kuma lafiya da waiwaye na maganin mantuwa. Daga cikin ayyukan da wannan
babi zai yi magana akansu, sun hada da. Kundayen bincike, Jaridu da kuma
bugaggun littafai.
2.1 WAIWAYE
AKAN AYYUKAN DA SUKA GABATA
Babu shakka
wajibi ne ga duk wani mai bincike tilas ne ya waiwaya baya, domin, duba wasu
ayyukan da suka gabata domin yasan inda aka kwana ko aka tsaya.
Ta hanyar
duba ayyukan da suka gabata ne mai gudanar da bincike yake samun kwarin guiwa,
wajen gudanar da bincikenshi ta hakan ne zai ɗauki wasu
ayyukan ko kuma ya gina wasu da ba su ba.
2.1.1
KUNDAYEN BINCIKE
A cikin
ayyukan da a ka duba akwai:
Tunau H.A
(2003). A cikin kundin ta kawo ma’anar fawa da asalin sana’ar fawa da yadda ake
gudanar da sana’ar fawa da kayayyakin aikin sana’ar fawa da masu yin sana’ar
fawa da muhimmancin sana’ar fawa da rashin muhimmancin sana’ar fawa, da kuma
al’adun sana’ar fawa.
Wannan aikin
nata yana da matuƙar alaƙa da binciken
da za a yi, domin tayi bayani a kan sarautar fawa da kuma wasu sarautun sana’ar
fawa, amma bata zurfafa bincike a kan sarautar fawa ba
Haka kuma an
duba kundin; Shamsu, Z. da Wasu (1988). A cikin wannan kundi an kawo ma’anar
fawa, da al’adunta na da da na yanzu. An ƙarfafa bayani
a kan kayan da ake amfani da su a cikin mahauta, ko wajen sana’ar fawa da
wuraren da ake gudanar da ita.
Wannan aiki
yana da alaƙa da binciken da za a yi, domin sana’ar fawa
ita ta samar da sarautar Fawa, sai dai mai wannan kundin bai yi magana akan
sarautar fawa ba, a nan ne binciken da za a yi suka bambanta.
Sai wani
kundi da aka duba na; Wada, A. (2003). A cikin wannan kundi an bayyana irin
sauye-sauyen da sana’ar fawa ta samu, da kuma tasirin zamananci a cikin sana’ar
fawa.
Shi wannan
aiki yana da alaƙa da binciken da za a gudanar, amma sun
bambanta, domin shi mai wannan kundi ya yi bincikensa ne a kan sana’ar fawa, a
wannan binciken za a duba sarautar fawa, alaƙar su ita ce
dukkansu suna magana ne a kan harkar fawa.
Daga nan kuma
an duba kundi; Bala, M.Z da wasu (1997). A wannan kundi an bayyana ire-iren sana’o’in
Hausawa kamar Noma, Saƙa, ƙira,
Fawa, da kuma jima da sauransu. Sannan kuma an yi magana akan sana’ar fawa,
amma bayyi bayani a kan sarautar fawa ba, alaƙar wannan
aiki da binciken da za a gudanar ita ce fawa, amma sun bamban, domin mai wannan
kundin bayyi cikakken bayani a kan sana’ar fawa da kuma sarautar fawa ba.
2.1.2 JARIDU
A ɓangaren
jaridu da suka yi magana a kan sana’ar fawa, da kuma sarautar fawa daga cikin
su akwai.
Rabi’u, N
(2019) ya ce “Sana’ar fawa na da matuƙar muhimamnci
ga rayuwar kowa ce al’umma, haka kuma ya ce ita sana’ar fawa sana’a ce ta
dogaro da kai wadda take da darajja.
Ita wannan
tattaunawa da jaridar leadership Hausa ra’ayi da Malam Rabi’u Nasiru tana da alaƙa
da binciken da za a yi, domin ita sana’ar fawa ita ce ƙashin bayan
sarautar fawa.
Usman (2019)
ya ce “Sarautar Fawa amana ce a masarautar katsina” ita shugabanci ce da ake
bayarwa domin samun cigaban sana’ar fawa. Daga nan da a cikin bayaninshi da ya
bayyanawa ɗan jaridar
wasu muhimman abubuwa dangane da sarautar fawa, daga cikin su akwai; Asalin
sarautar fawa da muhimmancinta da kuma nasabarta da masarautar Katsina, amma
bai zurfafa bayani ba a kan sarautar fawa.
Ita wannan
tattaunawar tasu tana da alaƙa da binciken
da za a yi sai dai sun bambanta domin tana magana a kan sarautar fawa a garin
Katsina, wannan kuwa ya taƙaita a kan
sarautar fawa a garin Gusau ne. Alaƙar su ita ce
duk suna magana ne akan sarautar fawa.
2.1.3
BUGAGGUN LITTATTAFAI
Alhassan H.
da Wasu (1982). A cikin wannan littafi a shafi na (51) an bayyana ma’anar
sana’ar fawa da muhimmancin sana’ar fawa da ire-iren kayan aikin sana’ar fawa
da kuma nau’o’in mahauta manya da ƙanana.
Wannan
littafi yana da alaƙa da binciken da za a
yi, amma sun bambanta, domin shi binciken da za a yi yana magana ne a kan
sarautar fawa, alaƙarsu ita ce duk suna
magana ne akan harkar fawa ne.
Haka kuma an
dubi wani littafi na Yahaya I.Y da Wasu (2007). A cikin wanan littafi a
darasina bakwai shafi na (48-60), an kawo ma’anar sana’a da ire-iren sana’o’in
gargajiya da masu sana’ar da kuma yadda suke gudanar da ita. Haka kuma an kawo
ire-iren sarautun da ake samu a cikin kowace irin sana’a ta gargajiya.
Wannan
littafi yana da alaƙa da binciken da za a
yi, amma sun banbanta, domin shi littafin yana magana ne a kan sana’o’in
gargajiya, amma alaƙarsu ita ce ya yi
magana a kan sana’ar Fawa da sarautarta, amma bai zurfafa bayani ba a kan
sarautar fawa ba.
Littafi na
gaba da a ka duba shi ne; Ingawa, A da wasu (1948). A cikin wannan littafi an
yi bayani a kan sana’o’in gargajiya, haka kuma an bayyana cewa dukkan sana’o’in
sun samo asali ne daga sana’ar Noma.
Wannan
littafi yana da alaƙa da binciken da za a
yi, amma sun sha bamban, domin shi yana magana ne a kan sana’o’in gargajiya ne,
shi kuma binciken da za a yi taƙaita ne a kan
sarautar fawa, alaƙarsu ita ce sana’ar
gargajiya ita ta samar da duk wasu sarautun gargajiya da muke da su na
shugabanci a kan sana’ar.
Littafi na ƙarshe
da aka duba, shi ne; Yahaya, I. Y. da Wasu (1992). A cikin wannan littafi a
darasi na tara shafi na (73-75) an yi magana a kan ma’anar sarauta da asalin
sarauta da tsarin sarauta da gudanar da masarauta da duk wasu abubuwa da suka
shafi sarautar gargajiya.
Wannan
littafi yana da alaƙ da binciken da za a
yi, domin ya yi magana akan wasu sarautun gargajiya da kuma ma’anarta sarautar
da tsarinta, amma wannan littafi ya bambanta da binciken da za a yi domin shi
ya yi magana a kan sarautar gargajiya, shi kuma binciken da za a yi yana magana
ne a kan sarautar fawa. Alaƙarsu duk suna
magana ne a kan sarautar gargajiya.
2.3 KAMMALAWA
Wannan babi
ya yi magana akan wasu muhimman ayyukan da suka gabata. Wannan babi ya yi
waiwaye adon tafiya, domin tafiya da waiwaye na maganin mantuwa, domin sanin
ina aka kwana ina kuma za a tashi. Daga cikin ayyukan da aka duba sun haɗa da:
Kundaye, Jaridu, da kuma bugaggun Littafai.
1 Comments
hdld
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.