Sani, A-U. & Abdullahi, M. (2016). Kwatanci Tsakanin Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ da Waƙar ‘Lalura’. In Yahya, A. B. Journal of Hausa Poetry Studies Vol. 1, No. 3. PP 10-22. Sakkwato, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.
Kwatanci Tsakanin Tsakanin
Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’
da ‘Waƙar Lalura’
Abu-UbaidaSANI
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau
Da
Mansur
Abdullahi
Department
of Hausa Studies
College
of Education, Ikere-Ekiti
Phone
No: 08034402746
1.0 Gabatarwa
Babban yunƙurin aikin nan shi
ne fito da bambanci da kuma kamanceceniya da ke tsakanin Waƙar Lalura da kuma
Tabban Haƙiƙan. Aikin ya kawo taƙaitaccen tarihin
marubucin waƙoƙin na asali (Shehu Usmanu Ɗanfodiyo). Baya ga
haka, aikin ya kawo taƙaitaccen tarihin Isa Ɗan Shehu da kuma
Nana Asma’u a matsayin masu hannu wajen fassara waƙoƙin daga Fillanci
zuwa Hausa, tare kuma da yi musu tahamisi. Wato Shehu Usman a matsayin wanda ya
wallafa waƙoƙin biyu, Nana Asma’u ta fassara
Tabban Haƙiƙan sannan Isan Kware ya yi mata
tahamisi. A ɗaya ɓangaren kuma, Isan
Kware ne ya fassara waƙar Lalura daga Fillanci zuwa Hausa, sannan ya yi mata
Tahamisi.[1]
Aikin ya shafi waƙa ne, sannan
rubutacciyar waƙa ba waƙar baka ba. Masana
da dama sun ba da ma’anar waƙa kamar haka:
Waƙa
wani furuci ne (lafazi ko saƙo) cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da
daidaitattun kalmomi cikin wani tsari ko ƙa’ida da kuma yin
amfani da dabaru ko salon armashi. (Ɗangambo, a cikin Habibu, 2001).
Haƙiƙa waƙoƙi suna taka
muhimmiyar rawa wurin faɗakarwa tare da
wa’azantarwa ga al’umma. Ba za a taɓa mantawa da gudummuwar rubutattun waƙoƙi ba a lokacin
jihadin jaddada addinin Musulunci ƙarƙashin jagoranci
Shehu Usmanu Ɗanfodiyo (Yahya, 1987; Zurmi, 2006).
1.2 Rubutacciyar Waƙa
Masana da dama sun kawo ma’anar
rubutacciyar waƙa. Wasu masanan a rubuce-rubucensu suna bambancewa
tsakanin waƙa, da rubutacciyar waƙa da kuma waƙar baka. Wasu kuma
suna kawo ma’anar waƙar ne kawai a dunƙule ba tare da
bambancewa ko rabewa ba.[2] Habibu,
2001 ya rawaito Yahya yana cewa:
Rubutacciyar
waƙa magana ce mai ƙunshe da saƙo a
rubuce, da ta shafi zaɓen kalmomi da tsara su cikin tsarin da ba lallai sai
sun dace da maganar yau da kullun ba. Wannan tsari yana buƙatar
karin sauti da amsa-amo. (Yahya a cikin Habibu,
2001)
1.1.1 Taƙaitaccen Tarihin
Rubutacciyar Waƙa
Masana da marubuta
da dama sun kawo tarihin samuwar rubutattun waƙoƙi a ayyukan
rubuce-rubuce daban-daban da suka yi[3]. Sai dai
wannan aikin zai kawo tarihin ne a taƙaice.
Masana suna ƙiyasi ne kawai na
lokacin da aka fara samar da rubutattun waƙoƙin Hausa. Babban
linzamin wannan ƙiyasi shi ne, kasancewar ba a fara samun rubutattun waƙoƙin Hausa ba sai da
Hausawa suka koyi karatu da rubutu. Wannan ya faru ne bayan sun karɓi addinin
Musulunci. Wannan ne ya sa rubutattun waƙoƙin farko suka fi
mayar da hankali kan faɗakarwar addini da
ilmantarwa da kuma wa’azantarwa, da ma sauran jigogi da suka shafi addinin
Musulunci (Habibu, 2001).
Duk da akwai masana da suke ganin
cewa addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa tun
kafin ƙarni na goma sha huɗu,[4] ba a
samu wata hujja da take nuna samuwar rubutattun waƙoƙi a wancan lokaci
ba. Hasali ma an samu ɓurɓushin rubutattun
waƙoƙin da suka fi daɗewa ne waɗanda aka yi a ƙarni na goma sha
bakwai. Waɗannan ɓurɓushin waƙoƙi da aka ƙiyasta samuwarsu
za su iya kasancewa tun a ƙarni na goma sha bakwai (17). Waƙoƙin sun haɗa da, Shi’ir Hausa da Jamuya na wani malami
mai suna Shekh Ahmad Tila. Sai dai ba a tantance ko wane ne malamin ba. Bayan
waɗannan akwai wasu
waƙoƙi na Wali Ɗan Marina da kuma
Wali Ɗan Masani, waɗanda aka tabbatar sun samu tun ƙarni na goma sha
bakwai (17) (Habibu, 2001).
Daga ƙarni na sha takwas
zuwa na sha tara kuma, (musamman lokacin jihadi), marubuta da dama sun rubuta
waƙoƙi domin faɗakarwa da kuma
kiran al’umma (Birnin-Tudu, 2002)[5].
1.2 Tarihin Mawallafan Tabban Haƙiƙan
da Waƙar Lalura
Dalilin da aka ce ‘mawallafa’ ba
‘mawallafi’ ba shi ne kasancewar sa hannun wasu daban bayan asalin marubucin waƙoƙin, ma’ana fassararta
da kuma yi mata tahamisi. Aikin zai kawo tarihinsu a taƙaice domin ya zama
tubalin ginin bayanai game da waƙoƙin biyu.
1.2.1 Shehu Usmanu Ɗanfodiyo
Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya fito
ne daga tsatson Fulani. Sun yo hijira zuwa ƙasar Hausa ne daga
Futa Toro. An haife shi a shekarar 1754 a Maratta ta ƙasar Gobir. Sai
dai ya tashi ne a Ɗegel a sakamakon hijirar da iyayensa suka yi daga
Maratta zuwa Ɗegel. Sannan a Ɗegel ne ya fara
koyarwa da kuma wa’azi, wanda hakan ne ya kai shi ga martabar da ya samu a
rayuwa (Yahya, 1987).
Shehu ya fara karatu ne a wurin
babansa. Bayan nan kuma ya yi a wurin baffansa mai suna Shekh Jibril Umar.
Bayan wani lokaci kuma sai shi da sahabbansa suka fara tafiya ƙauyukan Gobir da
Zamfara da kuma Kabi domin koyarwa da kuma kira zuwa ga Musulunci. Ya wallafa
littattafai da dama sannan ya rubuta waƙoƙi. Abubuwan da ba za
a taɓa mantawa ba game
da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, sun haɗa da ɗimbin rubuce-rubucensa da kuma
kasancewarsa jagoran jihadin ɗaukaka addinin Musulunci (Yahya, 1987; Birnin-Tudu,
2002).
Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya rasu a
shekarar 1817, lokacin yana da shekaru sittin da uku a duniya. Ya rasu ne a
Sakkwato shekaru biyu da komawrsa nan (Sakkwato) daga Sifawa (Yahya, 1987).
1.2.2 Nana Asma’u
Nana Asma’u ita ce
ɗiyar da ta fi
sanuwa a cikin ‘ya’yan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. An haife
ta a shekarar 1792 a Ɗegel, wato bayan dawowar Shehu daga Zamfara inda ya yi
wa’azin tsawon shekaru biyar. Ta auri Usman Giɗaɗo wanda aka fi sani da Waziri Giɗaɗo. Nana Asma’u ta
rubuta waƙoƙi da dama, sannan ta fassara wasu
zuwa harshen Hausa, waɗanda Shehu Ɗanfodiyo ya
rubuta. Ɗaya daga cikin waƙoƙin da ta fassara
ita ce Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ ta Shehu
Usmanu Ɗanfodiyo. Daga cikin waƙoƙin da ta rubuta
akwai Kiran Amada da Gwadaben Gaskiya da waɗansu daban-daban
da ta rubuta cikin harshen Hausa da Fillanci (Yahya, 1987).
Bayan rubutun waƙoƙinta, ɗaya daga cikin
abubuwan da za a tuna Nana Asma’u da shi, shi ne kasancewarta jagorar ‘Yan Taru. Wato ƙungiyar fafutukar
ilimantar da mata. wadda ta yi ƙoƙarin haɗa kan mata tare da
ilmantar da su. Nana Asma’u ta rasu a shekarar 1817 (Yahya, 1987).
1.2.3 Isa Ɗan Shehu
An haifi Isa Ɗan Shehu a
shekarar 1870, wato watanni kaɗan bayan rasuwar mahaifinsa (Shehu Usmanu Ɗanfodiyo). Yarsa
(Nana Asma’u) ita ce ta riƙe shi har zuwa girmansa. Wasu
masana suna ganin cewa, wannan ne ya sanya masa sha’awar rubuta waƙa, saboda Nana
Asma’u marubuciyar waƙa ce (Muhammad, 1986; Yahya, 1987).
Isan Kware shi ne ɗan auta a wurin
Shehu. Ana masa laƙabi da Isan Kware ne saboda naɗa shi da aka yi Sarkin
Yamman Kware. Wanda ya naɗa shi, shi ne
Sultan na wancan lokaci, wato Muhammadu Bello. Isah ya fassara waƙoƙin Shehu da ma na
Nana Asma’u da dama zuwa Hausa. Baya ga haka, ya yi tahamisin waƙoƙi da dama, ɗaya daga ciki ita
ce ‘Tabban Haƙiƙan’ ta Shehu Ɗanfodiyo (Yahya,
1987).
Yahya (1987) ya ce, akwai kokonto
game da taƙamaimai ranar rasuwarsa. Sai dai ya ce, Ɗangambo ya rawaito
Junaidu yana cewa, Isan Kware ya rasu ne a shekarar zuwa 1970. Sai dai wasu
masana sunan ganin bai kai wannan lokaci ba.
1.3 Tsokaci Kan Tabban Haƙiƙan
da Waƙar Lalura
Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ ce ta fara
samuwa kafin ‘Waƙar Lalura’. Ɗanfodiyo ya rubuta
waƙar
ne da Fillanci. Bayan wani lokaci sai Nana Asma’u ta fassara ta zuwa harshen
Hausa. Daga ƙarshe kuma Isan Kware ya yi mata tahamisi. Waƙar ta kasance mai
tsauri sosai, kusan babu sassauci a cikinta ko kaɗan. Za a iya lura da hakan yayin da
aka dubi baitocin waƙar, wato yadda suke tabbatar da shiga wuta ga masu
aikata wasu zunubai (waɗanda aka zayyano a
cikin waƙar) ba tare da kawo uzuri ba (Birniwa, 2016). Ga
misalin ɗaya daga cikin
irin waɗanan baitoci:
Masu
cin kura kasuwa duk akwai su,
Wansu
keri su kai su samo bukinsu,
Wansu
na nan ina faɗa ma kamassu,
Masu
cin dukiya ta baital wasunsu,
Su wuta kan ci gobe tabban haƙiƙan.
A ɗaya ɓangaren kuma, Ɗanfodiyo ya rubuta
‘Waƙar
Lalura’ ne sakamakon koke da sahabbansa suka yi game da tsauri na waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’. Saboda haka
ne Ɗanfodiyo
ya yi takwararta (Waƙar Lalura). A ciki ya nuna cewa, akwai lalura game da
duka hukuncin da ya shafi kowane laifi. Misali, a baitin sama da aka kawo, an yi
nunin hukuncin wuta ga masu cin dukiyar da ba ta halarta ba gare su, kai tsaye
ba tare da sassauci ba. Akwai takwaran wannan baiti a ‘Waƙar lalura inda aka
nuna akwai sassaucin hukunci idan dai akwai lalura. Ga misali daga cikin waƙar:
Ka
jiya min abinga dut na faɗa ma,
Kada
ka bar ko guda karanta ka kama,
Shaihu
yac ce riƙe batun mai karama,
Dukiyaj
jangali da gado ku koma,
Har ta yaƙi wuta halam shi
larura.
1.4 Kamanceceniya Tsakanin ‘Tabban Haƙiƙan’
da ‘Waƙar Lalura’
Akwai
kamanceceniya tsakanin ‘Tabban Haƙiƙan’ da kuma ‘Waƙar Lalura’. Wannan
kamanceceniya ta shafi sigogin waƙoƙin biyu, da zubi
da tsarinsu da ma tarihin rubuta su. Saboda haka, za a iya raba waɗannan kamaceceniya ta fuskoki kamar
haka:
1.4.1 Tarihin Rubutun Waƙoƙin
Haƙiƙa idan aka bi
tarihin waƙoƙin biyu za a tarar cewa suna da
tushe ɗaya. Dalili kuwa
shi ne, dukkaninsu biyu, marubucinsu shi ne Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. An
bayyana hakan a cikin baitocin waƙoƙin biyu na
kammalawa. Ga yanda abin yake:
A waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ an ce:
Shehu na yaf fa waƙi waƙa ta asali,
Nana
Hausance taf fa maishe ta badali,
Isa
tahmisi yay yi kau ya halili,
Ya
yi Hausance kun ji shi ko dalili,
Wa’azu na don ku ji shi tabban haƙiƙan.
A takwararta ma an
tabbatar da Shehu ne ya rubuta ta, misali:
Shehu asalinta Isa na bi ma baya,
Don
fa lada ta samu har dud da shirya,
Niy
yi Hausance don darajjassu manya,
Nan
da can in gane shi in samu tariya,
Don darajassu sun bi sunna larura.
1.4.1.1 Fassara
Fassarar da aka yi
wa duka waƙoƙin biyu shi ma yana mazaunin wata
kamanceceniya a tsakaninsu. Dukkannin waƙoƙin biyu, Shehu ya rubuta
su ne da Fillanci, sai daga baya aka fassara su zuwa Hausa. A cikin waƙoƙin akwai baitoci
da ke tabbatar da fassara waƙoƙin aka yi. Idan
aka duba misalin da aka bayar a sama na ‘Tabban Haƙiƙan’, za a ga inda
aka kawo cewa Nana Asma’u ce ta fassara waƙar. Misali:
“Nana Hausance taf fa maishe ta badali,”
A ɗaya ɓangaren ma, Waƙar Larura an
rubuta ta ne da Fillanci, sai daga baya ne aka fassara ta zuwa Hausa. Misali:
Na
gama kuma zaton da niy yo na khairu,
Shaihu Fillance yay yi to ka ji
Baharu,
Taulafina
garai iyaka na daharu,
Sheɗara lajju shekaran
nan ta Huru,
Cana Aljanna yo ƙida don larura.
1.4.1.2 Tahamisi
‘Waƙar Larura’ da ‘Tabban
Haƙiƙan’ duka an yi
musu tahamisi. Kasancewar tahamisin da aka yi wa waƙoƙin biyu na zaman
wata kamanceceniya tsakanin waƙoƙin biyu (Birniwa,
2016).
1.4.2 Jigo
Waƙoƙin guda biyu sun
kasance suna da jigon wa’azi. Akwai baitoci da dama da suke nuni da hakan a
cikin waƙoƙin guda biyu. Wasu daga cikin hani
da aka kawo koyarwa ne daga Alƙur’ani mai tsarki, wasu kuma daga
cikin hadisan Manzon Allah (S.A.W.). A cikin waƙar Tabban Haƙiƙan an faɗa ƙarara cewa:
Kun
jiya wa’azu na daɗa ‘yan uwana,
An
fa tasshe ku duk zumai dag ga kwana,
Don
ku kau tuba kun jiya muminina,
Duk
faɗin nan da anka yo
gaskiya na,
Sai fa rahama da ceto tabban haƙiƙan.
A ɗaya ɓangaren ma, ‘Waƙar Lalura’ tana da
jigon wa’azi ne. baitocin waƙar da dama suna nuni da hakan.
Misali:
Ka
jiya min abinga dut na faɗa ma,
Kada
ka bar ko guda karanta ka kama,
Shaihu
yac ce riƙe batun mai karama,
Dukiya
jangali da gado ku koma,
Har ta yaƙi wuta halam shi
larura.
1.4.3 Zubi da Tsari
Zubi da tsarin waƙoƙin biyu ma na nuni
da kamanceceniyar da ke tsakanin waƙoƙin biyu. Sun yi
kamance da juna a fuskar amsa amo babba da ƙarami. Kowa ce waƙa tana da uwar
goyon amsa amo wato kalma ɗaya ce sukutum kowa ne baiti yake ƙarewa da shi a
matsayin amsa-amo, wato tabban haiƙan da lalura. Kuma kowaccensu tana da ƙaramin amsa-amo a
kowane baiti. Wato kowane baiti yana da irin tasa gaɓar da yake ƙarewa da ita. Baya
ga wannan, ga bisa dukkan alamu kowacensu tana hawa karin Aruli na waƙoƙin Larabci. Sannan
kowace na da mabuɗi da marufi da ƙirgen lokacin
wallafa na Ramzi da ambaton sunan mawallafi mai fassara da mai tahamisi. Sannan
a karon farko suna da zubin tagwai. Bayan wani lokaci ne kuma aka yi musu
tahamisi. Kenan a nan sun yi kamance ta ɓangaren zubi da tsarinsu.
1.4.2 Salo
Salon waƙoƙin biyu yana ƙara danƙon kamanceceniya
da ke tsakaninsu. Hasali ma dai, zamani da yanayi da ma sauran abubuwan da suka
shafi rayuwar marubuci na yin tasiri a cikin waƙarsa[6]
(Muhammad, 1986). Wannan ya sa dole a samu kamanceceniya ta ɓangaren salon waƙoƙin biyu, domin
kuwa duka mutum ɗaya ne ya rubuta
su.
1.4.2.1 Salon Wasa da Kalma
A duka waƙoƙin guda biyu an yi
wasa da kalma. Misali a waƙar Tabban Haƙiƙan ana cewa:
Masu
iko su mai da himma su kyauta,
Kun
jiya masu ji daɗa kada ku ɓata,
Ba ɗa tsangini garin
biɗowab buƙata,
Masu
matsuwat talakka ko don sarauta,
Su ka matsuwa ga gobe tabban haƙiƙan.
A shaɗara ta biyu an
kawo jiya, sannan aka ce masu ji. Wannan wasa da kalma ne kamar
yadda aka jero cikin ɗango ɗaya. Sannan a ɗango na huɗu aka ce: “Masu matsuwat
talakka ko don sarauta.” A nan matsuwa na nufin takurawa ko musgunawa. A ɗangon ƙarshe na baitin
kuma sai aka ce: “Su ka matsuwa ga gobe tabban haƙiƙan.´A nan kuma
kalmar matsuwa tana nufin uƙuba ta ranar gobe kiyama.
A ‘Waƙar Lalura’ ma
akwai wurin da aka yi wasa da kalma. Misali:
Dubi
aikinka aikata yo ma Allah,
Kowane
kaj jiya da aikin jahala,
An
faɗi ka jiya bi addin
ka lela.
Maslaha
an aje guda kankamala,
Dai
buƙata
guda tana kan larura.
A ɗangon farko an yi
amfani da kalmar aiki sau biyu, inda aka ce; “Dubi aikinka aikata
yo ma Allah.” A ɗango na uku ma an
maimaita kalmar: “Kowane kaj jiya da aikin jahala. A waɗannan ɗangogi aiki na nufin
bautar Ubangiji Maɗaukaki.
1.4.2.2 Salon Aron Kalma
Akwai wuraren da aka yi aron kalma a
cikin duka waƙoƙin biyu. Misali a Tabban Haƙiƙan ana cewa:
Wanda
duk ya zamo yana shina son salama
Nan
da can gobe sai shi bar yin zalama,
Kwaƙ ƙi foron ga dut
shina yin nadama,
Wanda
yaz zam fa hakimi yay yi rahama,
Shi ka tsira ga gobe tabban haƙiƙan.
Kalmar salama wadda ta fito a ɗangon farko kalamr Larabci ce. Asalinta a
Larabci shi ne salamatun, wanda ke
nufin aminci ko tsira. Kalmar zalama kuwa
asalinta a Larabci shi ne az-zulmu,
wanda ke nufin zalunci. Asalin kalmar nadama
kuwa a Larabci shi ne an-nadamu,
wana ke nufin da-na-sani. Sannan kalmar rahama,
asalinta a Larabci shi ne ar-rahma.
A cikin ‘Waƙar Lalura’ ma
akwai baitoci da suke ɗauke da aron kalmomi.
Misali:
Bari
ƙasak
kufru kar ka zamna yi ƙaura,
Wanda
bai tashi duk shina cim ma sharra,
Don
zaman nan cikinsa shi ag garura,
Ba halat na ba fun musulmi shi barra,
Sai zama dole na shikai kan larura.
A nan, kalmar kufru ta samo asali ne daga Larabci wato al-kufrun. Kalmar na nufin duk wani wanda bai karɓi addinin
Musulunci ba. kalamr sharra kamar
yadda ta zo a ɗango na biyu ta
samo asali ne daga kalmar Larabci ta sharrun.
Kalmar tana nufin abin ƙi ko a she sharri/sheri. Kalmar halat ma daga Larabci aka aro ta. Asalin
kalmar ita ce al-halal, wanda ke
nufin abin da aka amincewa. Kalamar musulmi
ma an aro ta ne daga Larabci. Asalinta shi ne al-muslim, wanda ke nufin duk wani mabiyin addinin musulunci.
Waɗannan misalai da ma wasu da dama da
za a samu a cikin baitocin waƙoƙin suna nuni ne
zuwa ga dangantaka ko kamanceceniya da ke tsakanin waƙoƙin guda biyu.
1.5 Bambance-bambance Tsakanin ‘Tabban Haƙiƙan’
da ‘Waƙar Lalura’
Haƙiƙa duk da cewa
akwai alaƙa ko kamanceceniya tsakanin ‘Waƙar Lalura’ da ‘Tabban
Haƙiƙan’, akwai kuma
wurare da suka bambanta da juna. Waɗannan bambance-bambance za a iya karkasa
su kamar haka:
1.5.1 Tarihi
Tarihin rubuta waƙoƙin ya samar da
kamanceceniya tsakaninsu ta wasu ɓangarori. A ɓangare guda kuma, tarihin ya samar
da bambanci a tsakaninsu. Kamar yadda aka faɗa a sama, duka waƙoƙin an fassara su
ne daga harshen Fillanci. Bambancin a nan shi ne na waɗanda suka yi
fassarar. Nana Asma’u ce ta fassara ‘Tabban Haƙiƙan’, yayin da Isan
Kware kuma ya fassara ‘Waƙar lalura’. Akwai baitocin waƙar da suke
tabbatar da hakan. Ga nan abin da aka faɗa a ‘Tabban Haƙiƙan’:
Shehu
na yaf fa waƙi waƙa ta asali,
Nana Hausance taf fa maishe ta badali,
Isa
tahmisi yay yi kau ya halili,
Ya
yi Hausance kun ji shi ko dalili,
Wa’azu na don ku ji shi tabban haƙiƙan.
A ‘Waƙar Lalura’ kuma
cewa aka yi:
Shehu
asalinta Isa na bi ma baya,
Don
fa lada ta samu har dud da shirya,
Niy
yi Hausance don darajjassu manya,
Nan
da can in gane shi in samu tariya,
Don darajassu sun bi sunna larura.
1.5.2 Salo
Duk da cewa waƙoƙin guda biyu suna
da jigo guda, akwai bambanci tsakanin yadda aka isar da saƙonnin da ke cikin
waƙoƙin. ‘Tabban Haƙiƙan’ dai ta kasance
mai tsauri sosai. An lissafo laifuka sannan aka tabbatar da cewa mai irin waɗannan ayyuka wuta
zai shiga. A ɗaya ɓangaren kuma, ‘Waƙar Lalura’ tana da
rangwame. Laifuka da dama da aka yi maganarsu, tare da nuna hukuncinsu a
matsayin wuta, an nuna a cikin ‘Waƙar Lalura’ cewa,
wani dalili zai iya kawo rangwame a hukunci. Misali a ‘Tabban Haƙiƙan’ ana cewa:
Wansu
ko sun bi sun tsaya inda haddi,
Wadda
Allahu yay yi sun yo jahadi,
Wansu
ba su bi su sun ƙiya sun bi liddi,
Masu
yawon gari suna yin fasadi,
Su ka yawon wuta fa tabban haƙiƙan.
A cikin ‘Waƙar Lalura’ akwai
takwaran wannan baiti. Sannan ya zo ne da nuni da cewa, akwai rangwame saboda
lalura. Ga nan yadda baitin yake:
Anniya
kan ta nan akan aikatawa,
Kowane
za ka yi ka bar daƙilewa,
Bari
fululu da munkari jimre kewa,
Maslaha
aikata ƙi banna da kowa,
Tsari ibada ka san ta shi al larura.
A wani baitin kuma
na daban a cikin ‘Tabban Haƙiƙan’, an tabbatar
da wuta ga mai mulki ko babba da yake danne na ƙasa da shi:
In
daɗa ka zamo imamun
mutane,
To
tsare alhakinsu balle ubanne,
Ka
ji kyauta daɗa fa don kar ka ƙone,
Wanda
yaz zam imamu don cin mutane,
Shi wuta kan ci gobe tabban haƙiƙan.
A ‘Waƙar Lalura’ akwai
takwaran wannan baiti. A ciki ya zo da sassaucin zance. Ga baitin kamar haka:
Wanda
yab bi ka duk bar sa shi kuka,
Masu
iko kuna jiyawa ku falka,
Kun
ji Allah abin da yac ce ku ɗauka,
Bari walakanta wajibi kway yi suka,
Ha
wuta Walla ha wuta sai larura.
Haƙiƙa a waɗannan misalai da
ma wasu da dama da za a gani a cikin waƙoƙin, ‘Waƙar Lalura’ tana da
sassaucin hukunci.
Kammalawa
Aikin ya kawo
ma’anar waƙa da ma’anar rubutacciyar waƙa, sannan taƙaitaccen tarihin
samuwar rubutacciyar waƙa. Baya ga haka aikin ya kawo tarihin mutane uku – a
taƙaice
– da ke da hannu cikin rubutun waƙoƙin biyu. Daga nan
sai aikin ya yi taƙaitaccen tsokaci kan waƙoƙin guda biyu. Haƙiƙa ‘Tabban Haƙiƙan’ da ‘Waƙar Lalura’ tamkar
tagwaye suke. Baituka da dama daga cikin Tabban Haƙiƙan na da takwara a
cikin Waƙar Lalura. Baya ga haka, jigon waƙoƙin wa’azantarwa
ne. A ɗaya ɓangaren kuma,
akwai bambanci a tsakanin waƙoƙin kamar ta wurin
sassaucin da ke cikin ‘Waƙar Lalura’ koma bayan ‘Tabban Haƙiƙan’ da ke da
tsauri sosai.
Shawarwari
1.
Ya
kamata ɗalibai da sauran
al’umma su tuna cewa, rubutattun waƙoƙi suna ɗauke da ɗimbin darrussa, ba
nishaɗi kawai ba. A riƙa nazartar waƙoƙi tare da gane saƙonnin cikinsu.
2.
Malaman
waƙa
su ƙara
ƙaimi
wajen fayyace falsafar da ke cikin waƙa ga ɗalibai tare da
danganta saƙonnin waƙar da rayuwar
yau-da-kullum.
3.
Masana
waƙa
su ƙara
ƙaimi
wajen nuna wa marubuta waƙa irin tasirin da waƙoƙi suke da shi a
cikin zukatan al’umma. Marubutan su riƙa karkata jigogin
waƙoƙinsu zuwa ga
abubuwan da za su kawo cigaban al’umma ba koma-baya ba.
Manazarta
Tuntuɓi masu takarda.
[1]
Sai dai akwai waɗanda suke kallon cewa,
Abdullahi Mai Boɗinga shi ne ya yi wa Waƙar Lalura tahamisi, ba Isan Kware ba
(Birniwa, 2016). Sai dai ko ma yaya abin yake, ya tabbata cewa an fassara waƙar ne daga Fillanci zuwa Hausa sannan
daga baya aka mata tahamisi.
[2]
Masana da marubuta waɗanda suka yi tsokaci kan
ma’anar waƙa sun haɗa
da: Gusau, 1993; Ƙaura,
1994; Yahya, 1996; Bunza, 1988; Habibu, 2001; Zurmi, 2006.
[3]Daga
cikinsu waɗanda suka kawo tarihin samuwar
rubutacciyar waƙa
akwai Habibu, 2001, da kuma musamman Birnin-Tudu, 2002 inda ya yi ƙoƙarin
tattaro bayanai sosai game da tarihin samuwa da bunƙasar rubutacciyar waƙa.
[4]
Wasu na ganin cewa addinin Musulunci ya shigo ƙasar
Hausa tun ƙarni na goma sha
biyu. Wasu ma sun ce tun ƙarni
na bakwai (Habibu, 2001). Amma akwai tabbacin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa tun zamanin sarkin Kano
Ali Yaji. Wato shekarar 1349 zuwa 1385 (Birnin-Tudu, 2002).
[5]
Bayan an yi nasarar jihadi, Musulunci ya yi ƙarfi,
rubutattun waƙoƙi sun ci gaba da bunƙasa har aka shiga ƙarni na ashirin. Bayan nan ne kuma
jigogin waƙoƙin suka bunƙasa, suka wuce iya na addini kawai,
suka shafi na duniyaci (Birnin-Tudu, 2002).
[6] Saboda
haka ne ma ake iya hasashen yanayin mawaƙi
da yadda rayuwarsa take ta hanyar nazartar waƙoƙinsa kawai. Sannan wannan na ɗaya
daga cikin abubuwan da suka bambanta waƙoƙi daga ƙarni
zuwa ƙarni. Dalili kuwa shi ne, kowane ƙarni na zuwa da abin da ke jan
hankalin marubuta waƙoƙin, sannan yana tasiri kan tunaninsu.
1 Comments
Ku rubuta tsokacinku a ƙasa.
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.