Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Adashen Mata
A Garin Gusau (1)
NA
AMINA
ABUBAKAR
SADAUKARWA
Na sadaukar
da wannan aiki ga iyayena, Allah ya gafarta masu, Allah ya sa su aljannah da
rahama. Allah ya saka masu da alhairi, amin.
GODIYA
Da Sunan
Allah mai rahama mai jinƙai. Dukkan
yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya sanar da Ɗan’adam abin
da bai sani ba. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi
Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da waɗanda suka bi
tafarkinsa da kyautatawa.
Haƙiƙa
wannan aiki ya samu gudummuwa da shawarwari daga mutane da dama wanda ya zama
dole in miƙa cikakkiyar godiyata gare su. Godiya ta
musamman tare da cikakkiyar girmamawa ga malam Isah S/Fada wanda shi ne ya ɗauki ɗawainiyar
duba wannan aiki tun daga farko har ƙarshe. Allah
ya ba da lada.
Bayan nan
kuma ina miƙa cikakkiyar godiyata da fatar alheri ga
Shehin malami, Prof. Aliyu M Bunza, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙaro
cigaba a rayuwa.
Haka kuma ina
sake miƙa godiya da fatar alheri ga babana Aliyu
Rabi’u Ɗangulbi, tare da malam Abdullahi Musa, Allah
ya saka masu da alkhairi, Allah ya ƙaro ci gaba a
rayuwarsu.
Haka kuma ina
ƙara miƙa cikakkiyar
godiya tare da girmamawa ga malaman Jami’ar Bayero Kano, na Sashen Koyar da
Harsunan Najeriya, Allah ya saka da alkairi, Allah ya taimake su a rayuwa,
Allah ya sa su gama da duniya lafiya.
Haka kuma ina
miƙa godiyata da fatar alkhairi ga malam Haruna
Maikwari, malami a Kwalejin Ilimi da Ƙere-ƙere
ta Tarayya da ke Gusau. Haka zalika ina miƙa godiyata ta
musamman ga iyayena, marigayi Alh. Abubakar Moriki, da Fatima Muhammad Moriki
Allah ya gafarta masu, ina miƙa godiyata ga
yayyena irin su; Hajiya Hauwa’u Abu Moriki, Hajiya A’isha Abu Moriki, Jamilu
Abu Moriki, Surajo Abu Moriki, Auwal Abu Moriki, Mustapha Abu Moriki, Bashar
Abu Moriki, Aminu Abu Moriki, da Sanusi Abu Moriki.
Bayan nan ina
miƙa cikakkiyar godiyata ga ƙannena
irin su Murtala Abu Moriki, Mujtafa Abu Moriki, Muntaƙa Abu Moriki,
da kuma yar uwa Zinnira Bello Maru da A’isha Ibrahim Muhammad.
Har ila yau
ina miƙa cikakkiyar godiya da girmamawa tare da
jinjinar ban girma ga mijina Muhammad Jamil. Allah ya saka mashi da Alheri,
Allah ya sa ka gama da duniya lafiya, Allah ya sanya wa rayuwarka albarka,
Allah ya kare ka ga dukkan sharrin dake cikin rayuwa.
Ina miƙa
godiyata ga ‘ya’yana Sadiƙ da A’isha
Allah ya albarkaci rayuwarku, Allah ya baku ilimi mai albarka.
Sai godiya ga
abokan karatuna, irin su: Dayyaba M. Ibrahim, Abubakar Hassan Faskari, Mustapha
Sa’idu Faskari, Abdulrashid S. Fawa, Abdulrahman Bala, Nasiru Hassan Kabara,
Ahmad M. Kabir, Bashar Isyaku, Sani Adamu, Aliyu S. Ibrahim, Hizbullahi Ɗan
Lami, Nura Kwatarkwashi, da Hassan Galadima, Allah ya saka muku da alheri.
A ƙarshen
wannan bincike ina miƙa godiyata ga dukkan
wanda bai ji sunansa ba, da sauran al’ummar musulmi baki ɗaya.
TSAKURE
Wannan
bincike, zai yi bayani a kan adashe wato yanda ake gudanar da adashe a garin
Gusau, da kuma muhimamncin adashe da matsalolin dake tattare a cikin adashe.
Bugu da ƙari, binciken zai yi bayanin ire-iren adashe
da ake da su da kuma yadda ake gudanar da su. Bugu da ƙari, za a yi
bayani a kan taƙaitaccen tarihin garin Gusau. Daɗin daɗawa, bincike
zai yi tsokaci a kan ire-iren sana’a da muhimmancin sana’a a ga al’umma. Daga ƙarshe
kuma za a kammala bincike tare da shawarwarin da aka samu a wajen malamai da
sauran ɗaiɗaikun mutane.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.