Ticker

Adashen Mata A Garin Gusau (4)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Adashen Mata A Garin Gusau (4)

NA

AMINA ABUBAKAR

Kudi

BABI NA UKU

ADASHE DA RABE-RABENSA.

3.0 GABATARWA:

A wannan babi za mu yi aiki ne ka’in-da-na’in, a kan ma’anar adashe, haka kuma za a yi dubi zuwa ga tarihin samuwar adashe. Bugu da ƙari za mu ga su waye ke gudanar da adashe da kuma –ire-iren adashe, daga nanan sai kammalawa.

 

3.1 Ma’anar Adashe

A lokacin da Bahaushe ya ambaci kalmar adashe to, ya na nufin wata hanya ce ta karo-karo na kuɗi da al’umma kan yi domin taimakon juna ta yanda za su kaucewa talauci na rayuwa, don biyan buƙatun yau da kullum. Ganin cewa wannan dabara tamkar ruwan dare ne ga al’ummomi daban-daban, akwai sunaye da dama da al’ummomi ke kiran sunan adashe da shi wanda ya haɗa da:

 

Al’ummar Yarbawa na kiransa adashe da sunan “Esusu” ko “Aji”. Su kuwa al’ummar Ibo suna kiran adashe da sunan “Isusu”. Mutanen “Edo” kuwa suna cewa “Osusu”. Haka kuma al’ummar  Hausawa suna cewa “Adashe”, amma al’ummar Nupawa suna kiran adashe da sunan “Dash”.

 

Masana da dama sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar adashe, kaɗan daga cikinsu sun haɗa da:

“Adashe: Ajiyar kuɗi ta karo-karo a bisa ƙyadajjen lokaci da kowane mai yi zai ɗauka.” Bayero (2006).

 

Adashe: “Wani shiri ne na tara kuɗi wanda duk ya shiga ko kuma ya ba da kuɗinsa, za a ce ya zuba adashe. Dukkan su kuwa sai a ce sun shiga adashe, wanda kuma aka ba kuɗi da aka tara ya zama ya kwashi adashe”. Abraham (1947).

 

Adashe: “Wata ƙungiya ce, da al’umma ke haɗuwa a bisa yarjejeniya su rinƙa haɗa kuɗi ta karo-karo, ana ba mutum ɗaya daga cikinsu a bayan wani ƙayadadden lokaci da suka amince ana zagayawa har a ba kowa kwasa.” Ardoner (1964).

 

Adashe: “Wani tsari ne da abokai kan haɗu su riƙa ba da kuɗi a matsayin zubi, sai a ba wani daga cikin su a matsayin ya kwashi adashe.” Bergery (1934).

 

Adashe: “Wani nau’i ne na tanadi da wasu gungun mutane suke gudanarwa a bisa wani ƙayadadden lokaci da kowa daga cikin ƙungiyar mutanen nan zai ɗauki daidai abun da ya yi tanadi a cikin ƙuniyar.” Magaji (2019).

 

Adashe: “Wata hanya ce da wasu ƙidayayyun mutane ke gudanarwa a tsakaninsu ta yin karo – karo a bisa wasu sharuɗɗa zuwa wani lokaci wanda kowa daga cikin ƙidayayyun mutanen zai ɗauki daidai da abin da ya yi karo-karo da shi a cikin tarayyar da suka yi.” Bunza (2010).

 

Saboda haka, mun fahimci cewa adashe wani abu ne da al’umma kan haɗu a ƙungiyance su riƙa bayar da kuɗaɗe duk wanda ya shiga to zai yi zubi kuma zai yi kwasa, a kan yi karo- karo domin a haɗa a ba mutum guda har a zagayo yadda kowa za a ba shi kwasa don ya biya buƙatun rayuwa.

 

3.2 TARIHIN SAMUWAR ADASHE

Hausawa mutane ne waɗanda suke da dabaru na gudanar da rayuwarsu tun kafin haɗuwa su da wasu al’ummomi. Bahaushe mutum ne wanda yake da tarihin hikimomi da fasahohi da ƙoƙarin ƙirƙirar abin da zai ingata rayuwar shi daga wahala zuwa ga jin daɗi, haka kuma, Bahaushe mutum ne mai tarin tunani mai kyau da hangen nesa, game da yadda zai gudanar da rayuwar shi.

Tarihin samuwar adashe, abu ne wanda ba za a iya ƙayyade takamaimen lokacin da aka same shi ba, abu ne wanda masana suke ganin cewa sai dai a yi waiwaye ga al’adar Bahaushe domin duba wasu abubuwa da suke gudanarwa, waɗanda za mu iya kiran su da abubuwa ma su kama da mu kira su da cewa su ne tushen adashe, abubuwan sune kamar haka:

·         Biki

·         Ziyara

·         Zamantakewa tsakanin al’umma

Biki: Al’adar Bahaushe ce wadda yake gudanar da ita a tsarin rayuwar shi, kamar bikin aure, bikin haihuwa, bikin baiko da sauran su. Bahaushe idan ya tashi gudanar da bikin haihuwa ko wani biki, idan za a je wurin bikin za a riƙa wani abu a tafi da shi domin a ba wa mai biki gudummuwa, wannan wata babbar al’ada ce da Bahaushe yak e amfani da ita wajen gudanar da rayuwar shi, haka kuma, shi wanda aka baiwa, ya san cewa zai maida, ko dai ya maida dai-dai abun da aka ba shi, ko kuma ya ƙara a kan abin da aka ba shi.

 

Ziyara: Bahaushe mutum ne mai son sada zumunci a tsakanin ‘yan‘uwan shi, yakan tashi daga garin da yake zaune ya je wani gari daban domin yin ziyara ga ‘yan’uwan shi, kuma wannan ziyara idan ya tashi yin ta, za ya nemi wasu abubuwa domin ya yi tsaraba wa iyalin gidan da za ya je. Idan ya tashi dawowa, shi ma za a bashi wata tsaraba wadda za ya dawo da ita, ko daidai da abin da ya kai ko kuma fiye da abin da ya kai. Idan muka lura, za mu ga cewa wannan ma wani nau’i ne na adashe da aka daɗe ana gudanarwa a tsakanin al’ummar Hausawa.

 

Zamantakewar Al’ummar wuri ɗaya: Shi ma wani abu ne wanda za mu iya cewa ya taka rawar gani wajen haifar da adashe. Misali fira da wata tsohuwa wacce take ganin bayan biki da ziyarar sada zumunci, zamantakewar mutane wuri ɗaya shi ma yana ɗaya daga cikin abin da ya haifar da adashe. Dalilinta kuwa shi ne ta ce “A gidanta da ta yi aure suna zaune a wani ƙauye da ke cikin jihar Sakkwato ta ce “sun kai su wajen goma sha biyar (15), tana zaune da uwar miji (suruka), da matan ƙannen mijinta,” ta ce “kowa yana gudanar da wata ‘yar sana’a ta hannu, amma ba wanda yake sayen wani abu da kuɗi mai muhimamnci, sai dai ci banza ci wofi,” ta ce “daga baya surukar su ta ba su shawara a kan su haɗu su riƙa haɗa wani ɗan abu duk sati ana ba wa mutum guda, sai su dinga sayen wani abu mai muhimmanci na kiyo ko siyan kayan sana’a,” ta ce “sun haɗu, kuma sun yi aiki da shawarar da surukarsu ta ba su.” 

 

To a nan zamu iya cewa tarihin samuwar adashe ya samu ne daga waɗannan abubuwa guda uku, wato biki, ziyara da kuma zamantakewar al’umma wuri ɗaya, da cewa yana daga cikin abin da ya kawo ko ya samar da adashe a tsakanin al’umma.

 

Bahaushe dai mutum, ne da yake da dabarar samar da wurin tanadin kuɗin shi, ko ajiya tun kafin zuwan Turawa, domin mata na ajiyar kuɗin su ne ta hanyar buɗe kwallayen jeren su, su yi ajiya a cikin ko su yi ɗan gini su saka tukunya cikin ƙasa su yi ajiya domin yin tanadii don su biya buƙatunsu.

 

3.3 SU WA KE GUDANAR DA ADASHE

Adashe dai wani abu ne da mutane kan haɗu su shirya tsakaninsu, don ra’ayin kansu ba tare da tilastawa kowa ba, bisa ra’ayin cewa kowa zai riƙa ba da kuɗin da aka aminta da a bayarwa a matsayin zubin adashe, da nufin a riƙa zagayawa ana ba kowa kuɗin da aka tara a lokaci guda. Idan mutum yana da ra’ayin shiga adashe, a kowane lokaci zai iya shiga,  idan sauran mutanen da ke yin adashen sun amince da shigar sa, shi kuma ya amince da tsarin su na zubi da kwasa. Haka kuma duk wanda ya shiga adashe to ana tunanin yana da wata buƙata ta musamman da yake son biya.

 

Samun nasarar yin wannan adashen yana sa a kawar da talauci a kuma samu hanyar biyan buƙatun rayuwa. Akwai rukunnai daban-daban na mutane masu aiwatar da wannan al’adar adashe a garin Gusau.

 

Mutane masu sana’o’i suna shirya adashe a tsakaninsu. Kamar adashe na ƙungiyar masu gyaren mota da babura da na ƙungiyar kafintoci, da na ƙungiyar manoma da ‘yan kasuwa da na direbobin mota da ƙungiyar telolin keke da masu sana’ar sai da goro da dai sauran su.

 

A irin wannan adashe a kan sami ƙungiyar mata na cikin unguwanni masu gudanar da sana’o’i daban-daban, kamar masu sana’ar kunu, masu sana’ar tuyar waina (masa) da masu sana’ar ƙuli-ƙuli, sana’ar ƙosai, sana’ar tuwo-tuwo da sana’ar fura-fura, bugu da ƙari da masu sana’ar da daddawa da kayan miya da masu kitso, nakiya, alkaki da dai sauran sana’o’in mata waɗanda sukan gudanar domin samun ɗan abun biyan buƙatu. Bugu da ƙari, daga cikin kuɗin da suke samu ne sukan cire ɗan wani abu su bada ajiya wajen uwar adashe a matsayin zubin adashe. Ta haka ne suke tara wasu kuɗaɗe masu yawa don cimma wata manufa ta biyan buƙatar rayuwa.

 

Adadin masu yin irin wannan adashe da mata ke gudanarwa ya danganta ne da yawan matan da aka samu, wannan ya ƙunshi matan aure da kuma ‘yan mata da maza, adadin yana kamawa daga biyu zuwa adadin da aka samu.

 

Haka kuma, ko da an fara ƙofa a buɗe take ga wadda take da ra’ayin shiga matuƙar masu yi sun aminta da halinta na nuna gaskiya da riƙon amana.  Masu aikin Gwamnati, su ma suna irin wannan sana’a ta gudanar da adashe. Sana’ar adashe ta samu ne sanadiyar haɗuwar al’ummar Hausawa da baƙin al’ummu, wannan ya kawo masu wata sabuwar hanyar rayuwa, ta samun abun biyan buƙata.

 

Bincike ya nuna mata, su ne al’ummar Hausawa na farko waɗanda suka fara gudanar da adashe a tsakaninsu, wanda ya shafi hulɗa da kuɗi a gargajiyance domin kaucewa talauci ta hanyar tanadi da tsimin ɗan kuɗin da ke a hannunsu, don biyan buƙatunsu na rayuwar yau da kullum. Wannan hanya ta neman tanadin ɗan abin da aka samu bayan an gudanar da wata sana’a ita ce, hanyar wadda iyaye da kakanni mata suka daɗe suna gudanarwa a tsakanin su, domin kyautata zamantakewarsu da ƙarin danƙon zumunci a tsakanin al’ummar Hausawa da kuma inganta rayuwa.

Baya ga mata harwa yau a wannan rukuni ana samun maza musamman magidanta masu gudanar da sana’o’in hannu na gargajiya. Waɗannan sun haɗa da ƙungiyar manoma, da ƙungiyar mahauta da majema da marina da maƙera da dai sauransu.

 

Haka kuma, ana samun masu sana’ar fatauci domin Gusau wuri ne na zangon fatake masu zuwa daga wasu garuruwa da kuma wasu ƙasashe don gudanar da harkokin saye da sayarwa. Ƙungiyar ‘yan kasuwa manya da ƙanana, suma ba a bar su a baya ba. Duk suna gudanar da adashe don su inganta raywarsu.

 

3.4 RABE-RABEN ADASHE

Nazarin kwakkwafi na adashen Hausawa shi ya ba da haske ga nau’oin adashe daban-daban, saboda haka, tun da mun ga masu aiwatar da adashe,  yanzu za mu yi tsokaci ga rabe-rabensa.

1.      Adashen Kwasa

2.      Adashen Gata

3.      Adashen Tallafi

4.      Adashen Kati

 

 

 

3.4.1 ADASHEN KWASA:

Adashen kwasa, shi ne ainihin adashe da aka sani tun asali wanda mata da yara ke gudanarwa a tsakaninsu. Wannan nau’i na adashe ya samu sunansa ne daga irin kwasan zubin da ake yi. Mata sukan tanadi ɗan kuɗin da suka samu bayan sun aiwatar da wasu sana’o’i ko wasu aikace-aikace, ko ta hanyar kyauta. Mata dai na yi wa irin wannan adashe laƙabi da “adashen kuɗin cefane”. Suna gudanar da irin wannan adashe ta hanyar amincewa da juna da kuma nuna riƙon gaskiya da amana. Kafin a fara shi, uwar adashe ce kan ba da sanarwa ga ‘yan uwanta mata da abokan arziki, da ma yara waɗanda ake tare da su, cewa tana son ta fara adashe. Bayan ta samu masu yi to, sai maganar ƙayyade kuɗin zubi da za a yi kafin a yi kwasa. Idan sun amince da yawan kuɗin zubin da aka cimma yarjejeniya da kuma tsawon lokacin da za a yi kwasa, to sai a ci gaba da kawo zubi, uwar adashe na tarawa. Idan lokacin kwasa ya yi to, sai a ba mai kwasa.

 

Wasu ƙungiyoyin mata, sukan yi zubi sau ɗaya a sati, wasu kuwa ƙasa ko fiye da haka. Bayan an haɗa uwar adashe za ta ba mai kwasa kuɗin da aka tara. Zubi na iya kasancewa sau biyu a sati, wasu kuma a ƙarshen sati, wasu bayan kwana goma, wasu kuma za a yi ta zubi kullum sai bayan sati biyu ko a ƙarshen wata a yi kwasa. Haka kuma sukan tsara ainihin yadda za a riƙa yin kwasar adashe, watau tun daga na farko har zuwa ga na ƙarshe, ya danganta da yawan su.

 

Haka kuma uwar adashe, da sauran masu yin adashe kan yi la’akari da wadda take da wata buƙata ta musamman a cikin su domin a taimaka mata a ba ta kwasa, wannan zai ba ta dammar warware matsalolinta, kamar biki ko suna da sauransu. Kuma wadda ta yi ƙarshe to ita za a bawa kwasar farko. Wadda kuma ta fara zubi, ta kasa ci gaba da zubi, to uwar adashe ita ce ke da alhakin hukunta ta, sai a jinkirta ba ta kuɗin da ta zuba, sai kowace mata ta yi kwasa, sa’annan waɗanda ta yi wa zubi, su mayar mata da abin da ta zuba masu.

 

3.4.2 ADASHEN GATA

Adashen gata shi ne a dashen da ake ba uwar adashe kuɗin zubi, ana sakawa a asusu har zuwa wani lokaci kuma a buɗe rana ɗaya, abawa kowa kwasa. Kamar yadda na yi fira da Hajiya Ade mai adashe a garin Gusau, ta shaida mani cewa “Irin wannan adashe ya samu ne ga al’ummar Gusau, bayan wani lokaci mai tsawo ana gudanar da adashen kwasa na ƙungiya. Hanyoyin samun kuɗi sun fara yawaita arziki ya ƙaru sai uwayen adashe suka fara gudanar da irin wannan dubarar ta kawar da talauci dan biyan buƙatunsu na yau da kullum. Mafi yawa dai mawadata ne ke yin irin wannan adashe, daga baya masu ƙaramin ƙarfi suka fara gudanar da shi dan tanadin ɗan abin da ke hannunsu.”

Ta shaida mani cewa “Masu yin irin wannan adashe, sun ƙunshi mutane daga biyu zuwa adadin da ya samu, kuma a ƙungiyance ake gudanar da shi kamar adashen kwasa, kuma ana yin sa ne a ka, ba tare da an rubuta ba. Sai dai wasu na tafiyar da shi a rubuce, dan gane wanda ya yi zubi da wanda bai yi ba.

 

Lokacin zubi ya danganta ne ga yadda uwar adashe da masu zubi suka ƙayyade. Yana iya kasancewa kullum a yi zubi, ko duk bayan sati ɗaya, ko sati biyu, ko bayan wata ɗaya. Duk lokacin da aka ba da kuɗin zubi, ana ba uwar adashe ne ta saka a asusu har zuwa lokacin da aka ƙayyade za a buɗe asusun.

 

Lokacin kwasa, wannan ya danganta ne da yawa ko ƙarancin abin da suke sakawa a asusu, saboda haka, yana iya ɗaukar tsawon watanni shidda ko shekara ko kuma ƙasa da haka. Kuma a lokacin da za a fasa asusu takan fasa ne a gaban masu ba da zubi dan alissafa kuɗin da aka tara, a raba daidai a ba kowa kwasarsa.

 

Kuɗin gurbi ana ba uwar adashe a ranar da aka fasa asusu a ka bawa kowa kwasarsa sai ya ba da abin da ya sawaƙa. Amma daga baya sai wasu iyayen adashe suka fara nuna cewa, zubin farko da kowa ya ba da to shi ne ladar tari, don haka ranar fasa asusu ba a ba da wasu kuɗi na gurbi. Wannan shi ake kira da adashen gata kamar yadda mu ka yi bayani.  

3.4.3 ADASHEN TALLAFI

Adashen tallafi, wani irin adashe ne wanda mutum zai zuba abin da ya ga dama, kuma a lokacin da ya so, babu wanda zai tilasta maka da kayi zubi. Duk lokacin da mutum ya ga dama zai iya yin zubinsa, bayan kwana ɗaya ko bayan kwana biyu ko kuma bayan sati ko bayan wata ɗaya. Kuma mutum zai iya zuba duk abin da Allah ya hore masa. Bugu da ƙari, duk lokacin da mutum ya ce yana buƙatar kuɗinsa, wato abin da ya zuba, to uwar adashe za ta ɗauko masa kuɗin shi duka ta bashi. Sai dai za a cire kuɗin da mutum ya fara zubawa, wato zubi na farko kenan, a matsayin ladan tari, ko kuma kuɗin gurbi na adashe. Misali; Idan mutum ya zuba dubu goma (N10,000.00) a kowace rana har tsawan wata ɗaya, to ya tara/ zuba dubu ɗari uku kenan N300,000.00. To idan za a bashi kwasa, za a bashi dubu ɗar biyu da tis’in N290,000.00 an cire dubu goma kenan matsayin na uwar adashe, wato kuɗin gurbi kenan. Wannan ya sa ake kiran irin wannan adashe da adashen tallafi.

 

Daɗin daɗewa, idan mutum ya nemi a bashi kwasa tun kafin ya fara zubi, uwar adashe tana iya bashi, sannan ya ci gaba da zubin abin da ya ji zai iya zubawa har tsawon lokacin da ya biya abin da uwar adashe ta ranta masa, kuma zai biya ne daidai abin da aka ara masa ba tare da ya yi ƙari ko ragi ba. Wannan dalilin ne ya sa ake kiran irin wannan adashe da adashen tallafi.

Amma mafi yawancin ‘yan kasuwa da ke shiga irin wannan adashen tallafi suna yin shi ne tsawon wata ɗaya ne, idan wata ya ƙare, sai kuma su fara sabo.

 

3.4.4 ADASHEN KATI

Adashen kati, nau’in adashe ne da ya yi daidai da maganar da Hausawa ke cewa “kai ke kiɗan ka, kai ke rawarka”. Domin mutum shi zai ƙayyade ma kansa adadin kuɗin zubi da kuma lokacin da zai yi zubin, da kuma lokacin kwasa ba tare da wani ya tilasta masa ba. Abin da mutum ya zuba shi zai kwasa, a lokacin da ya buƙata. A irin wannan adashe, ba a haɗa zubin wani da na wani a ba wani.

 

Fasalin gudanar da irin wannan adashe ya tanadi bayar da kati ga duk mai yin zubi, wanda ke ɗauke da wata, da rana har zuwa ƙarshe. A duk ranar da aka bada zubi, zai sa hannu a kan katin, kuma ya sa hannuu a kan layin sunan wanda ya bada zubi a cikin rijistar don nuna cewa, ya karɓa. Idan ma kwasa aka yi, haka zai yi har a ƙare.

 

Haka kuma, kowa na zuba adadin kuɗin da ya ga yana da halin zubawa. Kuma ya yi kwasa a lokacin da yake so, don biyan buƙatun rayuwa.

 

Lokacin zubi irin wannan adashe na kati can asali a Gusau, masu yi na bada kuɗin zubi ne a kullum, har zuwa adadin da ake son a kwasa, wani lokaci kuma idan mai zubi ya buƙaci rance daga abin da ya zuba, to ana iya basa.

 

3.5 KAMMALAWA

A wannan babi na uku, na yi bayani ne a kan waɗansu muhimman ababe da suka shafi adashe kamar haka; Ma’anar adashe, wanda muka duba ra’ayoyin masana. Haka kuma mun yi bayani a kan tarihin samuwar adashe ta hanyar fira da masana alada. Bugu da ƙari, mun yi duba ga su wa ke gudanar da adashe, tare da yin bayani dalla-dalla a kan rabe-rabensa. Daga ƙarshe aka rufe babin da kammalawa.

Post a Comment

0 Comments