Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Auren Gargajiya A
Garin Kwatarkwashi (2)
NA
NURA SANI KOTORKOSHI
BABI NA ƊAYA
1.0 GABATARWA
Wannan aiki
nawa mai taken “Auren Gargajiya a Garin Kwatarkwashi”, aiki ne da zai binciko
irin yadda al’ummar garin Kwatarkwashi ke aiwatar da aurace-auracensu; domin
samun sauƙin gudanar da wannan aiki da sauƙaƙawa
ga masu karatu a ka kasa wannan aiki a kan babi- babi har gida biyar kamar
haka.
Babi na ɗaya ya ƙunshi
gabatarwa, dalilin gudanar da bincike, manufar bincike, farfajiyar bincike,
hanyoyin gudanar da bincike da kuma muhimmancin bincike.
A babi na
biyu kuwa, binciken zai yi tsokaci a kan ayyukan da suka gabata masu alaƙa
da wannan aiki, tun daga kundayen bincike har zuwa bugaggun littattafai dai
mujallu da muƙalu.
Babi na uku
zai yi magana ne akan taƙaitaccen
tarihin masarautar kwatarkwashi da ma’anar kalmar Kwatarkwashi da kafuwar garin
Kwatarkwashi da addinin gargajiya da sana’o’i da zanen suna da kuma kaciya,
sannan sai kammalawa.
Shi kuwa babi
na huɗu zai yi
magana ne akan ma’anar aure da ire-iren aure da auren gargajiya a Kwatarkwashi
da zaman lalle da ɗaurin aure da al’adun aure kafin gudanar da
buki da al’adun aure lokaci da bayan mutuwarsa a tsakanin Kwatarkwashi. Babi na
biyar kuma na ƙarshe zai yi jawabin kammalawa da shawarwari
da manazarta.
1.1 DALILIN
GUDANAR DA BINCIKE
Idan aka ce
dalili to ana nufin asali ko mafarin duk abin da mutum ke aiwatarwa, domin kuwa
duk wani abu ko ma’amala da ba ta da dalili to bata da ma’ana ko amfani. Saboda
haka wannan bincike yana da dalilan da aka hango har aka yi sha’awar aiwatar da
shi.
Dalilan da
suka sa a gudanar da wannan bincike sun haɗa da bayyana
yadda auren gargajiya yake gudana a garin Kwatarkwashi. Wani dalili shi ne
domin a ƙara zaƙolo muhimman
bayanai da suka shafi auratayya da kuma irin kashe-kashen aure.
Wani kuma
dalilin bincike shi ne domin ya zama ci gaba a kan wasu ayyuka da suka gabaci
wannan.
Haka kuma
wannan bincike zai taimaka wajen fahimtar al’adun aure musamman a garin
Kwatarkwashi da kewaye.
Har wa yau
wannan bincike zai taimaka wa ɗalibbai da masu nazari kan wannan
fanni domin su sami abin karantawa domin cigabansu.
1.2 MANUFAR BINCIKE
Manufar
bincike shi ne ayi ƙoƙari
domin afito da abubuwan da ya sa wanda ke bincike ya nuna wa al’umma wanda ba’a
sani ba musamman yadda Kwatarkwasawa suke aiwatar da irin al’adunsu na
auratayya duk dai da cewa za’a samu kundayen da suka yi bayani a kan aure ko
wani abu da ya shafi wani bayani mai magana akan auratayya.
1.3
FARFAJIYAR BINCIKE
Wannan aiki
na gudanar da shi ne a fannin al’adun Hausawa na gargajiya, sannan kuma na keɓanceshi a kan
irin yadda Kwatarkwasawa suke aiwatar da auratayyansu a gargajiyance.
Kuma ina
fatar wannan aiki zai yi amfani ga manazarta a sashen harsunan Nijeriya musamman
masu karatun (B.A Hausa) a sashen harsuna da al’adu ga duk wanda zai yi nazari
a kan auren gargajiya. Kuma ina roƙon
Allah yasa mai amfani ne ga na bayanmu a tsakanin ƙannenmu da ɗiyanmu da ma
jikokinmu da su amfana da shi, amin.
1.4 HANYOYIN
GUDANAR DA BINCIKE
Hanyoyin
gudanar da bincike, hanyoyi ne daban-daban da manazarci ko mai aikin bincike ke
bi, wajen samun bayanai da suka dace da abin da suke nazari.
Akwai
hanyoyin samun bayanai da yawa da manazarci ke bi wajen samun bayanai. A wannan
binciken za a a hanyoyi kamar haka:
Nazartar
kundayen bincike da bugaggun littattafai da mujallu da muƙalu masu alaƙa
da abin da ake nazari akai. Domin tattaro bayanan da suka dace. Sannan kuma na
yi hira da mutanen garin Kwatarkwashi kama daga tsofaffin Malamai, maza da mata
da dai sauransu.
1.5
MUHIMMANCIN BINCIKE
Muhimmanci na
nufin amfani da abu, duk wani abu da ɗan Adam zai aiwatar a
rayuwarsa to yana da muhimmanci musamman aikin bincike.
Domin kuwa
aikin bincike aiki ne mai muhimmanci ga ɗalibai masu karatu a
makarantun gaba da sakandare.
Bincike abu
ne mai muhimmanci domin shi ke ba da dammar gano matsala da niyar samun waraka
a kan matsalar.
Wannan ya
nuna cewa bincike abu ne mai muhimmanci ga ɗalibai, domin
kuwa ya kan taimaka masu ta waɗnnan hanyoyi kamar haka:
·
Yana taimakawa ɗalibai su
samu ƙwarewa a fannin da suke nazari a kai
·
Yana taimaka masu wajen gudanar da bincike na
kansu
·
Yana baiwa ɗalibai damar
zurfafa tunani da kuma yawaitar bincike don samun haske ga abin da suke nazari
a kai
·
Yana ba ɗalibai dammar
tsayawa da kansu wajen magance matsaloli da za su iya fuskanta a nan gaba
·
Yana basu damar ƙwarewa,
musamman ta hanyar cuɗanya da mutane masu halaye da ɗabi’u
daban-daban a cikin al’umma
·
Aikin bincike na ba dalibai damar fara
tunanin wallafe-wallafen littattafai domin su bada tasu gudummuwa wajen ci
gaban ilimi ga al’umma.
Kazalika, shi
wannan aiki na bincike yana da muhimmanci ga reni domin kasancewarsa ɗaya daga
cikin sharuɗɗan dake bada
dammar samun takardar shaidar kammala digiri na farko a jami’ar tarayya
Gusau.
1.6 KAMMALAWA
An kamala
wannan Babi ne, tare da yin bayanin abubuwan da wannan babi ya ƙunsa
kamar haka; anyi tsokaci a kan gabatarwa da dalilin gudanar da bincike da kuma
manufar bincike da farfajiyar bincike da kuma hanyoyin gudanar da bincike, kai
da kuma muhimmancin bincike, duk a cikin wannan babi na ɗaya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.